Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 27791 words

Chapter 3 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi

Ads the beginning of article before Image

01 Jun 2024

389

Ads at the middle of Article

da suka bari dare ya tsala sannan suka durfafi hanyar da zata kai su zuwa birnin Zainul-Ansar.
Tafiyar rabin sa'a kacal suka yi suka iso domin haka sai suka yiwa birnin ƙawanya,
Waziri Yazid ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku dakarun haɗin gwiwa ku yi sani cewa yaƙin ku da dakarune kawai ba jama'ar gari ba da kuma duk wanda ya yi yunkurin kawo maku tazgaro domin ku isa zuwa turakar sarki Nu'umanu,
Yana zuwa nan a zancen shi sai ya umarci masu kibbau suka ɗana bakansu sannan suka harba shi izuwa dakarun dake tsaron ƙofa,
Sannan suka afkawa birnin suka hau dakaru da sara da suka, ihun Mazaje da kururuwar su shi ne abin da ya fara sauka akan kunnuwan jama'ar birnin.
Nan fa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
Ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA masu juriya a filin fama,
A wannan lokaci babu abin da kunne ke ji face ihun mazaje da ƙarar karafniyar ƙarafa gami da haniniyar dawakai, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya aka fara yiwa ƙasa ado da jini, sassan jikkunan bil'adama suka fara shawagi a sararin samaniya suka zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman,
Nan fa gari ya hautsi ne sakamakon guje-gujen al'umma gami da ifice-ificen su.
Bayan waziri Yazid ya yi umarni an afkawa birnin Zainul-Ansar da yaƙi sai kawai ya tuntse Idanuwanshi ya karanta ɗalasiman tsafi, Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce "Tabbas "Makashin ka yana tare da kai" kuma tabbas ba a gane mutum a fuska, Inda a ce mutum yana tsaye a lokacin da waziri Yazid ke karanta ɗalasiman tsafin sai ya rantse ya ce bai Kasance musulmi ba,
Ko da gama rufe bakinshi sai ya shafi wani guru a damtsen shi na hagu na ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da su waziri Yazid da sarki Rakibu bayan sun kammala tara rundunar MAYAƘA domin kai farmakin Bazato birnin Zainul-Ansar domin hamɓarar da sarki Nu'umanu daga kan karagar mulki.
Al'amarin shugaban dakarun sarki Lamsarul-Azlam kuwa wato Sadauki Hukaiza tun sa'adda aka fyaɗa shi da ƙasa sakamakon yunƙurin da ya yi na gudanar da bincike game da yaro Usaiba mai hatimin takobin Saiful-zayyad da jaruma Rusayyat ta ceci rayuwar shi sai ya yi yunƙurin miƙe wa tsaye amma sai ya ji ya kasa,
Ko da sauran dakarun suka fahimci cewa ya kasa miƙewa tsaye sai suka zaburi dawakansu suka yunƙura izuwa inda ya ke,
Ko da ukaiza ya fahimci aniyar su sai kawai ya dube su ya daka masu tsawa cikin matuƙar fushi ya ce da su "Ya ku waɗannan dakaru ku yi sani cewa a halin yanzu ba zai yiwu a ina tashi tsaye akwai buƙatar na ɗauki tsawon lokaci a wannan waje kafin jikina ya samu lafiya,
Abin da na ke so ku yi kawai shi ne ku koma izuwa ga mai girma Lamsarul-Azlam ku labarta masa abin da ya wakana gare mu, domin ko da ba ku koma gare shi yana ba za ku iya tsere mashi ba".
Ko da jin wannan batu daga bakin Ukaiza sai hankulan dakarun ya yi mummunan tashi
Suka ce a cikin zukatansu tabbas a halin yanzu muna cikin tsaka mai wuya kuma gaban mu tsini ne baya siyaki.
Wani garjejen ƙato daga cikin mayakan ya buɗi baki cikin ƙarfin hali ya ce "Ya shugabana sanin kanka ne cewa matsawar mu ka je da wannan mummunan labari ga mai girma Lamsarul-Azlam to hukuncin kisa ya tabbata a gare mu",
Ukaiza ya ce "Ai ko da baku koma zuwa gare shi sanin kanku ne cewa zai iya tura wata Annobar da zata hallaka ku ku yi mutuwar wulakanci,
Saboda haka yanzu shawara dai ta rage ga mai shiga rijiya".
Sa'adda Ukaiza ya zo nan azancen shi sai jikin dakarun ya yi sanyi kawai sai suka sakarwa dawakansu linzami suka durfafi wani ɓangare a dajin suna masu tsala gudu zukatansu cike da matuƙar tsoro.


***
'yar gajeriyar tafiya Rusayyat ta yi a cikin gidan sarautar ta iso wata ƙasaitacciyar turaka da aka cika ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, kai tsaye ta kunna kai izuwa ciki,
Zaune ta same shi ya tafka wani uban tagumi ta isa gare shi ta zauna daf da shi ta sanya hannayenta biyu ta dafa kafaɗunshi, Haka ne ya sanya ya dawo daga duniyar tunanin da ya yi fana'i a ciki,
Sannan ta dube shi fuskarta cike da annuri ta ce "Ya uban 'ya'yana shin ina dalilin wannan tagumi na ka ?.
Ko da jin wannan batu sai Fitinatul-Amir ya mayar mata da martanin murmushin da ƙara wa fuskar shi kwarjini ya yi gyaran murya ya ce "Ya abar bege na dare da rana ki yi sani cewa bakomai ne ya sanya ni a cikin wannan hali sai bisa rashin samun Magaji,
Babban abin da ke dugunzuma hankalina shi ne yadda har yau na gaza gano inda yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad yake wanda shi kaɗai ne ya matsala wajen burina namu.
Ko da jin wannan batu sai Rusayyat ta yi murmushi a karo na biyu har kyawawan haƙoranta suka bayyana farare ƙal!, Cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa ta ce " Ya muradin raina ka kwantar da hankalinka tamkar tsimma a randa ka yi sani cewa a yau na samo wata gagarumar tsintuwa da zata maye gurbin rashin magaji a gare mu.
Cike da alama matuƙar mamaki Fitinatul-Amir ya dube ta ya ce " Ya farin cikin rayuwata shin wace irin tsintuwa ce kika yi da zata maye mana gurbin magaji?
Da jin wannan tambaya sai Rusayyat ta miƙe tsaye tsam! daga kan kujerar ta durfafi ƙofar fita daga turakar tana mai yafito Fitinatul-Amir da hannu tana nuna cewa ya biyo bayanta,
Ba tare da bata gardama ba ya miƙe tsaye ya yi ko yi da ita,
Lokacin da suka fice daga turakar sai suka wanzu suna tsara saƙo da lungu a gidan sarautar, duk inda suka gifta sai ka ga dakaru, barori, dakaru haɗe da bayi na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Jaruma Rusayyat da mai gidanta Sadauki Fitinatul-Amir.

***
Dukkan abin da ya wakana tsakanin Jaruma da Rusayyat da shugaban dakaru sadauki Hukaiza,
Sarki Lamsarul-Azlam ya gani a cikin madubin tsafin shi a lokacin da yake zaune a cikin ƙasaitacciyar turakar shi ta shaƙatawa,
Ko da ganin wannan al'amari sai ya cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa ya buɗi baki cikin kakkausar murya yana mai cewa "Haƙiƙa jaruma Rusayyat ta aikata laifi mafi muni a gare ni da ba zan taɓa yafe mata ba face ta miƙo mani yaro mai hatimin takobi,
Ko da yazo nan azancen shi sai ya sake baje alƙalumman sihirin ya sake nutsawa cikin halarar tsafin domin ya ga irin wainar da duniya ke toyawa,
Abin da ya gani abinciken shi ne ba shi da wani aiki da ya huce ya ga ya gano sabuwar hanyar mallakar yaro mai hatimin takobi.


***
Lokacin da aljani Lattul-kifas ya tsala da matsanancin gudu a sararin samaniya sai ya wanzu yana ratsa giza-gizai,
Tafiyar daƙiƙa hamsin kacal ya yi ya iso wani ƙasaitaccen gida mai girma da tsawo tamkar gari guda,
Ko da ya yi arba da gidan sai kawai ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuh! ya sauka a turba nesa ƙaɗan da inda gidan ya ke, Nan take ya kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni,
Wani abu da ya ba shi mamaki game da gidan shi ne yadda aka yi ginin shi da zallar waɗansu irin duwatsu masu ƙyalli tamkar gilashi, an yiwa dukkan katangun gidan ado da wani irin hatimin sarauta gami da turanni mabanbantan launuka masu kyawun gani da ƙamshi,
Duk inda mutum zai taka a harabar gidan an yi daɓe da koren yaƙutu,
Wohoho! haƙiƙa babu wani attajiri ko BASARAKE da zai yi arba da wannan gida face ya tabbatar wa da kanshi cewa GABA DA GABANTA, kuma sawun Giwa ya take na raƙumi,
Iya tsawon rayuwar aljani Lattul-kifas bai taɓa gani ko jin labarin gida mai ƙawatuwa tamkar shi ba,
Na rantse da gemun kakana boka Zamzarul-Dayyan ko wane ne mai mallakin wannan gida yakasance mutum mai girman matsayi a tsakanin duniyar mutane da aljanu domin wannan gida na shi a iya kiran shi da suna aljannar duniya",
Lattul-kifas ne ya yi wannan furuci a cikin ran shi ba tare da ya bayyana ba.
Ko da kammala furuci sai ya yunƙura ya durfafi gidan domin ya ganewa kwarkwatar idanunshi, domin masu iya magana na cewa gani ya kori ji, Ai kuwa sai ya hango waɗansu irin gabza-gabzan dakaru na jinsin MUTUM DA ALJAN ɗauke da miyagun makamai bila-adadin masu matuƙar barazana ga duk wata halitta mai numfashi,
Sa'adda ya yi arba da su sai firgita ainun tsoro ya kama shi duk da kasancewar gwarzon mayaƙi mai dakakkiyar zuciya,
Amma abin da ya ba shi mamaki shi ne dakarun ko ɗaga kai ba su yi ballantana su yi yunƙurin afka mashi,
Shin ko dakarun ba sa iya gani na ne ?,
Amsar tambayar da ya kasa bawa kanshi kenan kawai sai ya takaici Idanuwansu ya falfala da gudu domin ya shiga zuwa gidan batare da sun gan shi ba.
Kaico! haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce "kifi na ganin ka mai jar koma" ya yin da ya rage saura taku uku ya ketare katangar gidan sai dakarun suka yi ɗauki kan shi suka yi masa ƙawanya saboda girman dakarun da yawan su sai aljani Lattul-kifas ya zamo tamkar an ajiye kwanya guda ɗaya a gaban dubban karnuka,
Tamkar haɗin baki a lokaci guda dakarun suka afka masa da dukkan ƙarfin su suna ihu da kururuwa mai firgita ZARATAN JARUMAI komai matuƙar yawan su,
Kaico! haƙiƙa komai dakewar zuciyar jarumi da rashin tsoron shi idan ya ga yadda dakarun ke kururuwar suna ɗaga makamansu izuwa sama dole ne ya ɗimauce,
Ko da ganin hakan sai Lattul-kifas ya yi wuf! ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen shi ya tare su aka kacame da masifaffan artabu mai matuƙar muni daban tsoro, ƙarar karafniyar ƙarafa gami ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne.
Wannan shi ne abin da ya faru da aljani Lattul-kifas da boka kaddad ya tura domin ya ɗauko mashi yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad.


***
Al'amarin waziri Yazid kuwa tun sa'adda ya ɓace cikin alƙalumman sihiri bayan ya yi umarni an farmaki birnin Zainul-Ansar da yaƙi bai bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar gidan sarauta,
Ko da bayyanar shi sai ya zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayanshi ya afkawa dakarun gidan da sara da suka yana kutsawa cikin gidan sarautar.
Sa'adda Sarki Nu'umanu ya ji gidan sarautar ya kaure da guje-guje gami ifice-ificen jama'a sai kawai ya ruga zuwa turakarshi, jim kaɗan sai ga shi ya fito shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, fararen sulken ya saka haɗe da koren rawani, ya rataya waɗansu zaratan takubba biyu a gadon bayanshi,
Kawai sai ya durfafi turakar uwar gidan shi lawisat, Ya na isa dakarun suka wangame kofa ya kunna kai ciki,
Sa'adda lawisat ta yi arba da maigidan ta a cikin wannan hali sai kawai ta faɗa kan ƙirjin shi ta rungume shi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,
Da ga can sai sarki ya janye jikinshi daga na ta suka fuskanci juna,
"Shin ina dalilin wannan hawaye na ki ya Sarauniyar zuciyata?,
Ko da jin wannan tambaya sai lawisat ta buɗi baki cikin alamun damuwa ta ce "Ya uban 'ya'yana ka yi sani cewa na ji a jikina cewa wannan yaƙi da zaka fita ba alkairi ba ne, ma'ana shi ne zai zamo ajalinka.
Ko da jin wannan batu sai sarki Nu'umanu ya sanya hannayenshi ya share mata hawayen dake kan fuskarta ya dube ta cikin alamun tsantsar tsantsar so da ƙauna ya ce "Ya Annurin kalbina ki yi sani cewa RAYUWA DA HALAKA duk a hannun Allah (SWT) suke komai zai kasance wajibi ne a gare ni na fita na kare rayukan al'ummata,
Kada ki manta cewa muna kan bisa TAFARKIN TSIRA abokan gabar mu kuwa suna bisa TURBAR AJALI, Domin haka da yardar Ubangijin halitta za mu samu nasara a wannan yaƙi kuma na dawo gare ki cikin ƙoshin lafiya,
Fatana shi ne ki Kasance mai yi mani fatan alheri da nasara, idan kuma ta Allah ta kasance ki roƙa mani gafara a wajen Ubangiji".
Lokacin da Sarki yazo nan azancen shi sai lawisat ta sake fashewa da kuka a karo na biyu, Dakyar da siɗin goshi ya samu ya lallashe ta ya fice turakar suna masu zubar da hawayen rabuwa da juna.
Yana fitowa ya falfala da azababban gudu zuwa cikin gidan sarautar ba tare da ya haye bisa doki ba.
Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Zainul-Ansar bayan waziri Yazid ya kai farmakin Bazato zuwa birnin.

***
A can ƙasar Darul-Ashmar kuwa sarki Lamsarul-Azlam ya shafe tsawon kwanaki biyu yana gudanar da bincike domin ya gano hanyar da zai hallaka yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad,
Abin da ya gano shi ne ɗin shi ne ba zai iya hallaka yaro mai hatimin ba face a ranar da sadauki Fitinatul-Amir ya gano cewa yaro Usaiba shi ne wanda yake farauta tsawon shekaru,
Sa'adda ya ga wannan al'amari sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa,
Shin mene ne dalilin da ya sanya sarki Lamsarul-Azlam ke farautar yaro usaiba mai hatimin takobi dalilin hakan kuwa shi ne.
Sarki Lamsarul-Azlam ibn Rauzil ya kasance GWARZON BASARAKE kuma gawutaccen mayaƙi da ya yi shura a ilimin tsafi, daɗin daɗawa kuma ya kasance azzalumi na gaban kwatance,
Gaba ɗaya jama'ar birnin Darul-Ashmar babu wnada yake jin daɗin mulkin shi face fadawa shi kaɗai,
Saboda matuƙar zaluncin shi ne ya sanya ya mamaye birane da ƙasashen da ke makwabtaka da shi sun yi MUBAYA'A a gare shi ta ƙarfin tsiya, Bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamo babu mashahurin sarki tamkar shi a kaf nahiyar.
Wata rana da sulu-sainin dare sarki Lamsarul-Azlam na zaune a cikin turakarshi ya baje alƙalumman sihirin yana gudanar da bincike domin ganin halin da duniya ke ciki,
Yana cikin wannan hali ne sai kawai ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da ya mamaye gidan sarautar ya amsa kuwwa izuwa ko ina, Al'amarin da ya yi matuƙar janyo hankalin dakarun gidan kenan suka zare makaman su suka rugo izuwa turakar,
Ba wani abu ne ya sanya shi wannan ihu ba face wani al'amari da ya gani a madubin tsafin shi,
Abin da ya gani ɗin shi ne wani yaro mai shekaru tara dake ɗauke da zanen hatimin takobin Saiful-zayyad a gadon bayanshi da zai zamowa sarakunan duniya ƙadangaren bakin tulu kuma ciwon idanu, zai kawo ƙarshen mulkin duk wani azzalumi a doron ƙasa kuma zai samu ɗaukaka fiye da kowa ne sarki a duniya,
Yaron yakasance ɗa ne ga wani wani sarki da ake kira da suna Hidyal na birnin Baitul-Hazwar dake yamma maso gabashin duniya a gaban tekun baharul-sawara,




BABI NA TAKWAS


Lokacin da dakarun suka iso turakar sai suka yi turus! ba wani abu suka gani ba face dakarun dake gudanar da tsaro alamun dake bayyana cewa babu wani al'amari da ya gudana mara kyawu,
A lokaci guda sarki Lamsarul-Azlam ya tsuke bakinshi daga sannan ya ƙwalla wani hadimin shi kira mai suna Hukaiza ya bayyana a gare shi, sarki ya dube shi ya ce "Ya kai Hukaiza ina so ka jagoranci MAYAƘA izuwa birnin Baitul-Hazwar dake iyaka da gabar tekun baharul-sawara ku hallaka duk wata halitta dake ciki koda kiyashi kada ku bari a raye,
Cikin matuƙar ladabi Hukaiza ya miƙe ya fice daga turakar ba tare ya ce uffan ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya sarki Lamsarul-Azlam ke farautar yaro usaiba mai hatimin takobin Saiful-zayyad.
Sarki Lamsarul-Azlam na zaune a bisa KARAGAR MULKI cikin suturu na alfarma irin na hamshaƙan sarakai yana sanye da kambun Sarauta a kanshi a hannunshi yana riƙe da kwagiri na sarauta,
Lamsarul-Azlam yakasance dattijo mai kamanin shekaru hamsin, fatar jikinshi wankan tarwaɗa ce, yana da ƙasumba da gemu mai tsawon kamu biyu baƙaƙe siɗik da suka ƙara bayyana kyawun fuskarshi, Yana da rubɗeɗen ciki tamkar an kifa kwarya, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya cika GWARZON BASARAKE mai tarwatsa mazaje a filin fama.
A gefen hannun shi na dama kuwa 'yar shi gimbiya Sharilat zaune bisa kujera ta alfarma sanye cikin ƙayatattun tufafi na alfarma da suka bayyana tsantsar kyawun surar ta,
Gimbiya sharizat ta kasance mai matsakaicin kaurin jiki, idanuwanta dara-dara ne farare ƙal! masu tamkar tacecciyar madarar shanu, hancinta dogo mai lankwasa, a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓan shi suka jajur, wuyanta mai kyawu ne tamkar na barewa, kirjinta a cike yake yaƙe kuma a tsaye kyam bai rankwafa ba, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake daga baya kuma ya yi tudu tamkar a ɗora tuffa ta zauna a kai, tana da zara-zaran gaɓoɓi da fatar su ta kasance mai sheƙi, gashin kanta baki siɗik mai ƙyalli tamkar gilashi ya zuba akan gadon bayanta,
Wohoho haƙiƙa duk inda kyawu yake gimbiya Sharizat ya cika, babu wani ɗa namiji da zai yi arba da ita face ya kamu da matuƙar soyayyar ta,
A rayuwar Sharizat bata da wani buri da huce taga yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad domin ya tseratar da shi daga sharrin mahaifinta sarki Lamsarul-Azlam, domin ta ga ta kawo ƘARSHEN ZALUNCI da yake yiwa al'umma,
Bisa wannan dalili ne ya sanya duk sa'adda sarki zai gudanar da bincike game da yaro mai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads