Showing 12001 words to 15000 words out of 27791 words
Chapter 5 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi
dakarun suke ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga wani Sadaukai daga cikin dakarun wanda da alama shi ne shugaban su,
Cikin matuƙar fushi shugaban dakarun ya saka mashi tsawa da ta sanya hantar cikin shi ta kaɗa ya dube shi ya ce "Ya kai Isham shin ina harajin mai girma Lamsarul-Azlam da ka saba bayarwa?,
Cikin dattijon na tsuma ya ajiye jakar dinaren da ke hannun shi muryar shi na sarƙewa ya ce "Ka.. ga..far ce ni ya shuga.. bana bisa jinkirin fi..to..wa na tare ku har ku..ka iso nan".
Shugaban dakarun mai suna Shahral ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ya murtuke fuska cikin kakkausar murya ya dubi wani Barde dake tsaye a hannun shi na dama ya ce "Ya kai Ruhaizu yi hanzari ka lissafa mani dinaren da ke cikin wannan jaka.
Kafin shugaba Shahral ya gama rufe bakin shi Barde Ruhaizu ya tsugunna ƙasa ya shiga lissafa dinaren, jim kaɗan ya dubi shugaba Shahral cikin ladabi ya ce "Dinaren ya cika yadda ake bukata ya shugabana".
Ko da jin wannan batu sai Shahral ya gyaɗa kai alamar gamsuwa sannan ya dubi dattijon ya ce "Sai ka kasance cikin shiri domin a koda yaushe zamu iya dawo wa domin sake ƙarbar wannan haraji.
Yana gama ya juya ya shige gaba sauran dakarun suka mara ma shi baya suka sake nausa wa cikin kasuwar suna tafiya cikin hanzari,
Suna cikin wannan tafiya ne kwatsam! bazato babu tsammani sai suka hango wata tsaleliyar kyakkyawar Budurwa tana sanye cikin fararen tufafi masu yalwa a gadon bayanta ta na rataye da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta, ta tunkaro inda dakarun suke babu alamun tsoro a tare da ita,
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa dakarun mamaki kenan kuma ya ɗaure masu kai, domin tun da suke fitowa wannan ran-gadi hakan bai taɓa faruwa ba, da alamu wannan budurwa baƙuwa ce, amma koma dai baƙuwa ce ai ya kamata ace kwarjinin su ya firgita ta ?,
Amsar tambayar da dakarun suka kasa bawa kan su kenan,
Sa'adda da ya zama tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma sai dakarun suka ja suka tsaya aka fara kallon-kallo tsakanin su da budurwar.
Daga can sai budurwar ta taka da ƙafafuwanta ta durfafi inda dakarun ke tsaye batare da fargabar komai ba, kafin dakarun su farga ta shammace su ta daga wawan tsalle ta dira a daf da wani badakare ta warce jakar dinaren dake hannunshi ta rataya a gadon bayanta, sannan ya dunƙule hannayenta biyu ta gabza mashi wawan naushi a wuya, nan take wuyan na shi ya ƙarye ya yi ƙara ruƙus! Ƙas, take ya faɗi ƙasa ko shurawa bai yi ba,
Ko da dakarun suka yi arba da abin da ya faru da Barde Ruhaizu sai suka firgita ainun, zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su ƙone.
Abin da ya firgita su ɗin shi ne shin ya aka yi budurwar ta samu irin gagarumin ƙarfi da ta kashe ɗaya daga cikin su bayan cewa tun da suke fitowa wannan ran-gadi hakan bai taɓa faruwa ba,
Abin da ya fusata su ɗin shi ne ta ya ya za a mace guda ɗaya jal! ta bayyana a gare su kuma har ta yi GABA DA GABA da su,
Lokacin da dakarun suka zo nan a tunanin su sai sai shugaba Shahral ya buɗe su ya dakama su tsawa dake nuna basu umarni su afkawa budurwar,
Cikin matuƙar fushi dakarun suka yi ɗauki izuwa gare ta suna ihu da kururuwa mai firgitarwa,
Ko da ganin hakan sai budurwar ta dunƙule hannayenta biyu ta gwara tsayuwa domin fafatawa,
Al'amarin da ya sanya shugaba Shahral ya bushe da dariyar mugunta kenan bisa ganin cewa budurwar ta yi wauta da ta kusanci mayakan ba tare da ta riƙe wani makami ba.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, Ban tsoro gami da tashin hankali,
Dakarun suka wanzu suna kai Budurwar sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta,
Ita kuwa ta wanzu ta na zillewa hare-haren su cikin zafin nama gami da mayar da martani ta hanyar zabgawa dakarun naushi a sassan jikkunan su,
Duk inda ta nausa ɗin sai ka ga jini ya taru idan a baki ko hanci ne sai kaga yana yoyon jini, Nan fa dakarun suka suka dinga zubewa ƙasa magashiyan.
Wohoho! Haƙiƙa duk wanda Allah ya ba shi jarumtaka ya more, kuma gaskiyar masu iya magana da suka ce "Duk wanda ya isa ya huta" inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da budurwar ke ragargazar dakarun tamkar tana sassabe a gonar audiga dole ne ya jinjina mata ya tabbatar da cewa ta cika JARUMAR ASALI.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa hamsin dakarun Shahral suka hargitsa kasuwar, domin duk sa'adda suka kaiwa budurwar hari da takubban su idan ta zillewa harin duk abin da takubban su suka sauka a kai sai ka ga ya yi bindiga ya tarwatse,
Rumfunan kasuwa kuwa a dinga rushe su ana bazar da su a ƙasa,
Nan fa jama'a suka shiga yin guje-guje gami da ifice-ifice domin TSIRA DA RAYUKAn si,
Lokacin da ya zamana an shafe tsawon rabin sa'a ana wannan ɗauki ba daɗi sai ya zamana budurwar ta samu nasarar hallaka fiye kaso ɗaya bisa biyu na dakarun.
Sa'adda sadauki Shahral ya ga irin gagarumar ɓarnar da budurwar ke yi mashi sai ya fusata ainun ya dakawa sauran dakarun suka ja da baya, kawai sai ya dako wawan tsalle sama tamkar an harbo shi daga cikin baka yana saman ya zare waɗansu waɗansu zaratan takubba a gadon bayan shi ya kaiwa budurwar wawan hari da nufin tsinke mata wuya,
Cikin baƙin zafin nama zare takobinta ta kare harin,
Sannan suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, firgici da tashin hankali, Ana cikin wannan fafatawa ne sauran dakarun suka saci jiki suka fice daga kasuwar a bisa dawakansu suka kunna kai cikin gari tafiyar daƙiƙa hamsin kacal suka yi suka iso fadar birnin.
Fadar ta kasance ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan more rayuwa, Gaba ɗaya ginin fadar an yi shi ne da waɗansu irin duwatsu masu ƙyalli tamkar gilashi, A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a 'yan majalisa na zaune bisa ƙayatattun shimfiɗu na alfarma, kuyangi, Hadimai, Barori haɗe da dakaru na kai komo suna hidima.
Zaune bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki sarki Lamsarul-Azlam ne ya hakimce sanye ya ke cikin ƙayatattun tufafi na alfarma ya ɗora ƙafa ɗaya-kan-ɗaya ana gudanar da sha'anin mulki cikin annashiwa,
Sannu a hankali dakarun Sadauki Shahral suka shigo fadar lokacin da ya zamo tazarar dake tsakanin su da karagar mulki bai huce taku goma ba sai suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa wani cikin su ya buɗi baki cikin ladabi kanshi a sunukye ya yi gyaran murya ya ce " Ya shugabana bayan mun samu nasarar ƙarɓo jakar dinare daga hannun Sarkin kasuwa Isham kamar yadda muka saba sai mu ka yi gamo da wata hatsabibiyar jaruma har ta samu nasarar kwace jakar daga gare mu,
Kafin badakare ya gama rufe bakin shi Sarki Lamsarul-Azlam ya nuna badakaren da yatsan shi na hagu nan take wata irin gagarumar wuta ta kama ci a jikin shi nan badakaren ya shiga ihu da kururuwa, kafin cikar daƙiƙa ashirin ya ƙone ƙurmus,
Lamsarul-Azlam ya taƙarƙare ya kwarara ihu, daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da Wasikar Mutuwa,
Sannan ya buɗe bakinshi ya shiga karanta waɗansu dalasiman tsafi, Ya na gama furta dalasiman sai ga wani shirgegen muridi ya bayyana a fadar,
Shi dai muridin yakasance mai matuƙar tsawo, kauri da kauri, yana da rafkeken kai mai ɗauke da manyan idanu jajaye tamkar garwashi, ƙofofin hancin shi manya ne tamkar mazirarin iska, Gaba ɗaya jikinshi cike yake da gashi buzu-buzu tamkar wani tsohon mahaukaci,
Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan ya yi arba da muridin dole ya ɗimauce,
Sa'adda jama'a suka yi arba da muridin sai suka firgita ainun, amma saboda matuƙar tsoron sarki Lamsarul-Azlam sai kowanne ya zauna a wajen zaman shi cikin tashin hankali, Su kansu dakarun fadar a matuƙar razane suke,
Maridin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa, Sarki Lamsarul-Azlam ya dube shi ya ce "Ya kai Zabratul-ukub ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa kasuwar dake cikin birni na inda dakaruna ke fafata yaƙi da wata jaruma ka dauko mani jarumar ina so ka kawo mani ita cikin ƙoshin lafiya".
Ko da jin wannan umarni daga bakin Lamsarul-Azlam sai maridi Zabratul-ukub ya ɓarke da wata irin mahaukaciyar dariya wacce ta bayyana wargatsattsun haƙoran shi marasa kyawun gani har wani irin taririn baƙin hayaƙi na fita daga cikin su,
A lokaci guda ya turɓune fuska cikin wata irin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya ce "Ya shugabana ai wannan aiki tamkar shaƙar numfashi ne a waje na na rantse da girman halarar tsafin ka zan kawo maka jarumar cikin ƙoshin lafiya,
Ko da gama faɗin hakan sai ya ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Sarki Lamsarul-Azlam sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba.
Lokacin maridi Zabratul-ukub ya ɓace daga fadar sarki Lamsarul-Azlam bai bayyana a ko ina sai a wajen da shugaba Shahral ke fafatawa da kyakkyawar Budurwar nan,
A wannan lokaci budurwar ta samu nasarar hallaka haɗawa shugaba Shahral jini da majina sai layi ya ke yi jiri na ɗibar shi tamkar wanda ya sha barasa,
Sa'adda jama'a suka yi arba da maridi Zabratul-ukub sai suka fara cika wandon su da iska suna zurawa da gudun tsiya wasu har da sakin fitsari a wando saboda matuƙar tsoro, Kai hatta dakarun dake wajen ba a bar su a ba ya su ma dafe ƙeya suka yi suka sura da gudu domin a zaton su sarki Lamsarul-Azlam ya aiko da wata musiba domin ta hallaka kowa,
Kafin ƙiftawar ido babu kowa a filin kasuwar sai wannan kyakkyawar Budurwa,
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin ta da Zabratul-ukub,
A iya tsawon rayuwar Budurwar bata taɓa ganin halitta mai muni da kwarjini tamkar wannan maridi ba, kawai dai ƙarfin hali ne irin na JARUMAR ASALI.
Sai da daƙiƙa talatin ta shuɗe ana wannan kallon-kallo tsakanin su tamkar ba za su afkawa juna ba,
Kawai sai Zabratul-ukub ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da ya firgita duk wata halitta dake birnin gidaje suka dinga rushe suna faɗawa kan al'umma suna hallaka, ba shiri kyakkyawar Budurwar ta sanya hannayenta ta tsohe kunnuwanta, tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne Zabratul-ukub ya tsuke bakinshi sannan komai ya samu dai-dai ta,
Kawai sai ya kaiwa budurwar cafka da hannunshi, cikin wani irin baƙin zafin nama budurwar ta daka tsalle gefe guda ta zillewa harin, abu kamar wasa sai ga shi budurwar ta tsallake harin shi fiye da goma,
Al'amarin da ya fusata shi kenan ya ce a cikin ran shi yanzu ace GWARZON ƘARNI tamka ta halitta guda ɗaya ta gagare ni tabbas wannan abun kunya ne,
Ko da ya zo nan a tunanin shi sai ya kawai ya shammaci budurwar ya ƙirɓa mata wani wawan naushi a fuska, saboda ƙarfin naushin sai da ta yi sama tamkar an janye ta da ƙungiya sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim! a matuƙar galabaice hancinta da bakinta na yoyon jini, har a wannan lokaci jakar dinaren da ta ƙarɓa daga hannun dakarun tana goye a gadon bayanta.
Ko da samun wannan gagarumar nasara sai maridi Zabratul-ukub ya bushe da dariyar farin ciki ya sanya hannunshi ɗaya ya ɗauki budurwar tamkar bil'adama ya ɗauki tuffa a tafin hannunshi, sannan ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Abin tambaya a nan shi ne daga ina wannan budurwa ta fito kuma mene ne dalilin da ya sanya ta kwace jakar dinaren dake hannun dakarun sarki Lamsarul-Azlam suka karɓo a wajen dattijo Isham,
Dalilin hakan kuwa shi ne Kamar haka:-
Mu haɗu a littafi na 6 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga Mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubuta Littattafan yaƙi
08137237071
TAFARKIN TSIRA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
08137237071
BABI NA SHA ƊAYA
MADINATUL-AFNAN
Ƙasaitaccen birnin ya bunƙasa ainun a ƙarfin tattalin arziki, yawan al'umma gami da zaratan mayaƙa masu juriya a filin fama,
Gaba ɗaya jama'ar birnin suna da kyawawan halaye da mu'amala mai nagarta, hakan ya samo asali ne saboda kasancewar su ma'abota addinin musulunci,
Wannan al'amari ya janyo hankalin fatake daga sassan nahiyoyin duniya zuwa birin domin yin hulɗar siye da siyarwa, domin haka sai ya zamo tattalin arzikin birnin yana bunƙasa cikin ƙanƙanin lokaci kuma birnin ya zamo zarra a nahiyar,
Al'amarin da ya sanya biranen dake nahiyar suka kwallafa ran su akan ginin bayan birnin daga doron ƙasa amma Ubangiji baya ba su nasara.
Sarkin dake mulkin birnin yakasance dattijo ma'abocin kamala da sadaukantaka mutum ne mai son cigaban al'ummar shi ana kiran shi da suna RAYYAN IBN HUSSAIN Yana da matar aure guda ɗaya wacce ta haifa ma shi wata kyakkyawar 'ya da ake yiwa laƙabi da NUWAIRAT,
Tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce barewa ba za ta yi gudu ba ɗanta ya yi rarrafe,
Kamar yadda Sarki Rayyan yakasance GWARZON ƘARNI haka 'yarshi gimbiya NUWAIRAT ta kasance, domin a gaba daya birnin MADINATUL-AFNAN bayan sarki Rayyan babu jaruma tamkar ta, hatta kyawun halaye da tausayin al'umma Nuwairat ta gaji mahaifinta.
Tsakanin Sarki Rayyan da Sarki Lamsarul-Azlam ba a ga maciji ga juna, Lamsarul-Azlam ya zo ya kaiwa Rayyan harin bazato fiye da arba'in domin ya ga ya tunɓuke shi daga kan karagar mulki ya mallaki tarin arzikin dake birnin MADINATUL-AFNAN,
Wata rana sarki Rayyan na kwance a bisa gadon sarauta sai ya yi mugun mafarki daya sanya ya kasa rintsawa abin da ya gani a mafarkin shi ne sarki Lamsarul-Azlam ya na haɗa wani sinadarin tsafi wanda da zarar ya kammala zai samu nasara akan shi, sinadarin zai yi amfani da dukiyar da sarki Rayyan ke amfani da ita,
Bisa wannan dalili ya sanya sarki Rayyan ya umarci gimbiya NUWAIRAT ta tafi zuwa kasar Darul-Ashmar domin ta hana dakaru karɓar dinaren dake hannun sarkin kasuwa Isham,
Kuma a halin yanzu dinaren da gimbiya Nuwairat ta kwace daga hannun dakarun sune kaɗai suka rage wa sarki Lamsarul-Azlam ya mallaka domin kammala sinadarin tsafin.
***
Sa'adda Rusayyat uwar gidan shugaban 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir ta zurfafa izuwa kogin tunani domin samun mafita akan hanyar da zata shiga turakar mai gidanta ta ɗauko garin magani na sihiri, Domin ta tseratar da rayuwar Usaiba mai hatimin takobi, Sai ta shafe tsawon daƙiƙa talatin a cikin wannan hali ba tare da ta samu mafita ba,
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan ta shiga damuwa ainun, Haka dai ta cigaba da nazarin daga bisani ne ta samu mafitar, ko da samun mafitar sai kawai ta miƙe tsaye zumbur daga kan kujerar da take zaune ta fita daga turakar ta nufi turakar mai gidanta,
Da yake a wannan lokaci safiya ce ko wane waje a gidan sarautar ya cika maƙil da barori, Hadimai da bayi, Duk inda Rusayyat ta gifta sai ka ga bayi da barori na zubewa ƙasa suna kwasar gai wawa cikin girmamawa, kai tsaye ɓangaren da ake dafa abinci ta kunna kai, sa'adda da kuyangi dake hidima a wajen suka yi arba da ita sai suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa, wata dattijuwa daga cikin kuyangin da ake kira da suna Ashrila ita ce ta yi gyaran murya ta ɗago da kanta cikin ladabi ta ce "Ya shugabata lafiya mu ka gan ki a wannan lokaci da ba ki saba zuwa ba ?
Ko da jin wannan batu daga bakin kuyanga Ashrila sai Rusayyat ta daka mata tsawa ta dube ta ta ce "Ya ke Ashrila shin wane irin rashin hankali ne ya sanya ba a kai wa mai martaba uwan wanka kewaye ba, kuma an shirya abin kalaci har hasken rana ya bayyana haka?
Sa'adda Ashrila ta ji wannan tambaya sai jkinta ya kama tsuma yana ƙyarma saboda matuƙar tsoro bakinta na karkarwa ta ce " Ayi ma-ni afu-wa ya shu-gaba-ta"
"Ina so a kammala komai cikin daƙiƙa ashirin kacal!" Rusayyat ta faɗa sannan ta juya ta fice daga madafar ta nufi wata ƙofa ta musamman domin ta isa turakar mai martaba.
Lokacin da ta iso sai dakarun dake tsaron ƙafa suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa sannan suka wangame ƙofar ta kunna kai izuwa ciki, da shigarta ta tarar mai gidannata yana kwance bisa gadon sarauta yana sharar barci har da minshari,
Sai kawai ta matsa izuwa gareshi ta zauna a gefen gadon ta sanya hannayenta biyu ta shafi fuskar mai gidanta nan take ya farka ta hanyar buɗe idanuwanshi gami da yin miƙa ya zuba fararen idanuwanshi masu haske gami da kwarjini akan uwar gidant asa.
Cikin wani tattausan murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji mai hankali cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarƙewa ta ce "Barka da safiya SARKIN SADAUKAI ma'abocin kyawun sura da annuri, lafiya yau barcinka ya yi nauyi haka ?
Ko da jin wannan batu sai fitinatul-Amir ya yi murmushi mai kama da yaƙe ya ce "Tabbas kam yau na makara ya abar kaunata dare da rana kuma na yi mamakin hakan"
Rusayyat ta yi murmushi a karo na biyu sannan ta ce "Ya annurin rayuwata ai sai ka tashi ka shiga izuwa kewaye domin tuni kuyangi sun tanadi ruwan wanka"
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye tsam ta kama hannun mai gidanta ta tashe shi tsaye ta ja shi har izuwa inda kewayen ya ke sai da shigar da shi har ciki ta janyo Ƙofar ta rufe sannan ta dawo izuwa turakar ta shiga gudanar da bincike domin ta gano inda garin maganin shirin