Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 27791 words

Chapter 7 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi

Ads the beginning of article before Image

01 Jun 2024

391

Ads at the middle of Article

ɗaga mashi hannu da yake yi mashi nuni ya dakata, sannan ya buɗi baki muryarshi na sarƙewa ya ce " Ya kai likita sha'aban kayi sani cewa bana buƙatar a shayar dani maganin da zai sanya ni barci domin lokacin sallah ya yi har a alfijir ya keto,
Zai fi kyau a ƙyale shi sai na yi sallah sai na sha,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki sai likita sha'aban ya gyaɗa kai yana jin ƙaunar sarki a zuciyarshi domin kuwa ya tabbata cewa shi shugaba ne abin koyi,
Batare da wani ɓata lokaci ba sarki ya yi kabbara ya tayar da sallah yana da kwance, yana mai rufe idanuwanshi gami da ɓudewa kuma bakinshi yana motsi alamun cewa ya fara gabatar da sallar, jin kaɗan ya ya sallama, sannan likita sha'aban ya ba shi ruwan maganin a baki ya kurɓe,
Har wani daga cikin likitocin wani kyakkyawan saurayi ya buɗi baki cikin matuƙar mamaki domin ya ce wani abu amma sai sha'aban ya tari numfashi shi ya dube shi fuskarshi cike da annuri ya ce " Yakai Sultan ka yi sani cewa na san ba wata tambaya kake da bukatar kayi mani ba face yadda sarki ya gudanar da inadarshi,
To ina so ka yi sani cewa addini ya sanya sallah ta zamo wajibi ga dukkan Musulmi matsawar hankalinshi bai gushe ba, a kowa ne irin yanayi mutum zai iya yin Sallah, saboda muhimmancin sallah Annabi SAW da Sahabbanshi a yaƙi suka yi sallah, ka ga kenan da Allah zai ɗaukewa wani da ya ɗaukewa Annabin shi SAW da Sahabbanshi",
Koda jin wannan bayani daga bakin likita sha'aban sai Sultan ya jinjina kai alamar gamsuwa,
Ana cikin wannan hali ne aka jiyo motsi na kusanto turakar cikin hanzari kowa ya waiga domin aga ko wane ne, kawai sai aka yi arba da gimbiya lawisat,
Domin sai likita sha'aban da muƙarrabanshi suka juya suka fice daga turakar cikin hanzari,
A dai-dai lokacin lawisat ta iso daf da gadon da sarki ke kwance fuskarta cike da alamun matuƙar damuwa.
Wannan shi ne abin da ya wakana a cikin gidan sarautar birnin Zainul-Ansar.


BABI NA SHA HUƊU


Al'amarin waziri Yazid kuwa tun sa'adda ya ɓace ɓat! Bayan ya kammala fafata BAƘIN ARTABU da sarki Nu'umanu, bai bayyana a ko ina ba sai a cikin gidan sarautar a cikin wata ƙasaitacciyar turaka sarki Rakibu, cikin hanzari likitoci suka taru a kan shi domin ba shi taimakon gaggawa, cikin abin da bai gaza daƙiƙa talatin ba likitocin suka kammala aikin su, jim! Kaɗan da ficewar likitocin sai sarki Rakibu da sarkin yaƙi suka shigo turakar suka samu kujeru suka zauna dake fuskantar waziri Yazid fuskokinsu cike da matuƙar damuwa tsawon daƙiƙa goma babu wanda yace ƙala a cikin su,
Sai daga can sarki Rakibu ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗe baki ya ce " Ya waziri shin mene ne mafita ? Ga shi yanzu haƙan mu bai cimma ruwa ba duk shirin da mu ka yi akan sarki Nu'umanu da jama'ar ya tashi a banza",
Koda jin wannan batu daga bakin Rakibu sai waziri cikin sarƙewar murya ya ce " Ya ku manyan abokai na ku yi sani cewa ba a san MAZAN JIYA da tsoro ba, rashin nasara akan abu shi ne ke nuna alamun nasarar, domin rashin nasara shi ne zai sanya ka gyara kusakuren da ka aikata, ku yi sani cewa matuƙa kuka bi waɗansu sharuɗɗa da zan gindaya tabbas nasara ta same mu.
Da farko dai wajibi ne mu nemo ZARATAN JARUMAI da suka ƙware ainun a leƙen asiri da za su dinga kawo mana rahoton shirin abokan gabarmu,
Sannan zan sihirce wani hadimana domin ya kasance mai sura irin tawa zai tafi zuwa ga sarki Nu'umanu a matsayin cewa ni ne, wannan wata hanya ce da zata ɗauke hankalin sarki Nu'umanu da sauran al'ummarsa akan gano cewa da ni za a ci amanar su,
Sannan zamu nemi taimakon waɗansu daga cikin GWARAZAN JARUMAI na jin MUTUM DA ALJAN,
Sa'adda sarki Rakibu da sarkin yaƙi suka ji wannan dogon jawabi daga bakin waziri sai suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa,
Amma Rakibu ya buɗi baki ya dubi waziri ya ce "To amma ba ka tunanin cewa idan aka samu gawarwakin dakarunmu za a gano cewa mu ne muka kai MAMAYAR BAZATO ?,
Da jin wannan batu sai dariya ta suɓucewa waziri ya dube shi ya ce " Ya kai Rakibu ban da abin ka ai lokacin da muka ɓace daga birnin Zainul-Ansar bayan ARTABU ai tare da gawarwakin dakarunmu muka tawo,
Lokacin da yazo nan a zancen shi sai mayar da duban shi ga sarkin yaƙi sannan ya ɗora da cewa,
Kai kuma sarkin yaƙi za ka koma birnin Zainul-Ansar ka zauna tare da sarki Nu'umanu a zahiri za ka nuna kana tare da shi amma a baɗini ba haka ba ne za ka dinga bawa 'yan leƙen asirinmu bayanai ne kawai,
Da jin wannan ƙarin bayani sai dariyar farin ciki ta suɓucewa sarki Rakibu,
Ba tare da ɓata lokaci ba waziri ya ƙwallawa hadimin sa kira, jim kaɗan! Ya bayyana gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa,
Kawai sai waziri ya nuna shi a ɗan yatsanshi na hagu tare da karanta waɗansu dalasiman tsafi yana gama rufe bakinshi nan take siffar hadimin ta koma san! Ta waziri Yazid tamkar an tsaga kara, su kansu su sarki Rakibu sai da tunanin su ya dagule suka kasa tantance waziri na gaskiya da na bogi,
Faruwar hakan ke da wuya sai waziri ya sake nuna hadimin da yatsanshi na hagu a karo na biyu take ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Sannan ya yi nuni izuwa ga bangon turakar sai ga taswirar turakar sarki Nu'umanu ta bayyana yana kwance bisa gadon sarauta uwar gidansa Lawisat na zaune a gefen shi cikin alamun matuƙar damuwa, suna cikin wannan hali ne wannan hadimi mai ɗauke da siffa irin ta waziri ya shigo turakar hankalin shi ya yi matuƙar DUGUNZUMA,
Koda ganin wannan taswira sai sarki Rakibu, Sarkin yaƙi da waziri Yazid suka bushe da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa.




Al'amarin gimbiya Nuwairat kuwa tun sa'adda ta suɓuce daga hannun muridi Zabratul-ukub cikin halin suma, wannan hadimin aljani ma'abocin kyawun sura ya ɗauke ta bai tsaya ko ina sai birnin MADINATUL-AFNAN,
Lokacin da sarki Rayyan ya ga halin da gimbiya ta ke ciki sai hankalinshi ya DUGUNZUMA ainun ya tura wata kuyanga ta kirawo mashi liktar masarautar mai suna karima,
Karimat ta bayyana a gare shi tare da mataimakanta suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa cikin girmamawa,
Cikin hanzari karima da sauran likitocin suka nufi gadon da aka kwantar da gimbiya suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwarta, koda ganin hakan sai sarki Rayyan ya ɗauke jakar dinaren dake ajiye ajiye a gefen Nuwairat ya juya ya fice daga turakar cikin alamun matuƙar damuwa,
Kai tsaye harabar turakarshi ya nufa ya dinga kai-komo ya kasa zaune,
Yana cikin wannan hali ne sarkin yaƙi Zubairu ibn Saiful-Zaman ya bayyana a gare shi,
Sarkin yaƙi yakasance GWARZON ƘARNI mai tarwatsa DANDAZON MAYAƘA a FILIN FAMA, kyakkyawa ne na gaban kwatance wanda ganin farko zai ɗimauta zuciyar duk wata 'ya mace mai hankali, ya gaji sarautar sarkin yaƙi ne a wajen mahaifinshi Barde Huburul-zaman,
Ya jagoranci yaƙoƙi guda ashirin da uku kuma duk ya samu nasara,
Bisa wannan dalili yasanya sarki Rayyan ya ja shi a jikinshi duk wani abu nashi ya ke sanya shi a ciki,
Tsakanin sarkin yaƙi da gimbiya Nuwairat akwai soyayya mai ƙarfi sai dai sun gaza bayyanawa,
Sarkin yaƙi ya yi sallama irin ta ma'abota addinin Musulunci gami da risinawa ƙasa ya kwashi gaisuwa,
Sarki Rayyan ya amshi gaisuwar tare da miƙa mashi hannu suka yi musabaha, kuma ya ja hannunshi har izuwa bisa kan wata ƙasaitacciyar kujera suka zauna tare sannan ya dube shi cikin nutsuwa ya ce " Ya kai dirkar birnin MADINATUL-AFNAN kayi sani cewa bakomai ya sanya na kirawo ka nan ba sai domin na bayyana maka cewa gimbiya Nuwairat ta samu nasarar ɗauko jakar dinaren dake hannun abokin gabarmu sarki Lamsarul-Azlam gani tare da shi ya kare batun yana miƙa mashi jakar ya ƙarba sannan ya ɗora da cewa " Wannan nasara da muka samu ba za ta saka mu saki jiki ba, domin a kowa ne lokaci abokan gaba za su iya kawo mana MAMAYAR BAZATO, domin haka wajibi mu tanadi dakarun kar-ta-kwana",
Koda jin wannan jawabi daga bakin sarki Rayyan sai sarkin yaƙi ya buɗe baki cikin ladabi ya yi gyaran murya ya ce " Ya shugabana na ji dukkan bayanin ka kuma da yardar Allah SWT za a aiwatar da komai yadda ka buƙata, sai dai ranka ta daɗe shin ko a wane hali gimbiya take ciki? Ya ƙare batun cikin alamun damuwa,
Sarki Rayyan ya yi murmushi mai taushi a gare shi ya dafa ƙafadunshi da hannayenshi biyu ya ce " Kar ka damu ta ɗan samu buguwa ne a kan ta likitoci suna can suna bata kulawa zata samu lafiya",
Da jin amsar wannan tambaya sai Zuhairu ya risina ga sarki ya miƙe tsaye ya fice daga harabar hannunshi ɗauke da wannan jakar dinaren.
Wannan shi ne abin da ya faru a can birnin MADINATUL-AFNAN bayan farin hadimin aljani ya samu nasarar ceto gimbiya Nuwairat daga hannun muridi Zabratul-ukub.


TAFARKIN TSIRA 8
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071










ELEGANT ONLINE WRITER'S






Littafan Marubucin


Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi








BABI NA SHA BIYAR






A can gidan sarautar shugan 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir kuwa, lokacin da yaro Usaiba mai hatimin takobi da 'yar uwarshi Hairat suka farka daga barci sai kuyangi suka shiga da su kewaye suka yi masu wanka suka sanya masu tufafi masu tsadar gaske, bayan an shirya masu abin kalaci sun kimtsa cikinsu sai Rusayyat ta ɗauke su a bisa wani ƙayataccen keken doki ta shiga da su izuwa lambun shaƙatawa ta zaunar da su ƙarƙashin wata itaciya mai manyan rassa,
Lambun ya ƙawatu da nau'ikan shuke-shuken furanni masu kyawun launi da ƙamshi, ƙoramu na gudana da ruwa garai-garai, waɗansu irin tsuntsaye masu kyawun launi da kuka mai daɗin saurare ya shawagi a rassan bishiyu,
Wohoho! Haƙiƙa wannan lambu ya cika aljannar duniya, domin babu wata halitta a doron ƙasa MUTUM DA ALJAN da za su tsinci kansu a wannan waje face sun ƙwadaitu da su kasance a lambun har ƙarshen rayuwar su.
Shiru ne ya wanzu a tsakanin su na ɗan lokaci daga bisani Yaro Usaiba ya katse shirun da wanzu ta hanyar ɓudar baki ya yi gyaran murya ta ce " Ya ummun mu kin yi mana alkawari cewa za ki bamu labarin rayuwarki?.
Koda jin wannan tambaya sai ƙwalla ta zubo daga idanun Rusayyat,
Al'amarin da ya yi matuƙar DUGUNZUMA hankalin Usaiba da 'yar uwarshi kenan ya dube ta cikin alamun matuƙar damuwa ya ce " Ya ummina ki yi mini afuwa idan tambayar da nayi miki ta ɓata maki rai",
Rusayyat ta yi guntun murmushi a gare shi ta buɗi baki a karo na farko ta ce " Ko kaɗan tambayar ka bata ɓata mini rai ba, kawai dai ta tuna mini da labarin uƙubar da na sha a rayuwata,
Yanzu sai ku gyara zama domin ku ji yadda labarin nawa ya kasance.
Rusayyat ta fara labarin kamar haka:-

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe a yankin ƙasashen Larabawa an yi wani ƙasaitacciyar birni da ake yiwa laƙabi da Hairul-Mazwar,
Birnin Hairul-Mazwar ya bunƙasa ya bunƙasa a arziƙin noma da kiyo, suna da ZARATAN JARUMAI masu juriya a FILIN DAGA, har su fatake ke kiran sunan da suna BIRNIN SADAUKAI,
Sarkin dake mulkin birnin ana yi mashi laƙabi da Hubru ibn Kamsil,
Sarki Hubru yakasance dattijon mutum mai tausayi da jin ƙari, GWARZON MAYAKI ne mai tarwatsa DANDAZON JARUMAI a filin fama,
Bisa wannan dalili yasanya sarakunan dake maƙwabtaka da shi suke matuƙar shayin shi, Ni da mahaifana muna zaune ne a ƙauyen da ke wannan birni, kasancewar mu talakawa hakan yasanya bana samun wani jin daɗin rayuwa sosai,
Mahaifina yakasance makaho, mahaifiyata kuwa gurguwa ce bata da ƙafafu, a kowa ce hudowar rana ni da mahaifana sai mun shiga izuwa cikin birni mun yi bara, abin da muka samu da shi za mu yi kalaci, duk ranar da ba mu samu ba kuwa sai dai mu kwana da yunwa.
Wata rana ni da mahaifana muna bara a cikin kasuwa ina riƙe da sandarshi, sai mu ka zo hucewa ta rumfar wani attajiri,
Attajirin yakasance garjejen ƙato, fuskarshi mai matuƙar gwarjini ce yana da idanuwa jajur! Tamkar garwashi ya tara ƙasumba da gemu mai tsawo da ya shimfiɗo har bisa ƙirjinshi, kanshi a salsale yake babu ɗigon gashi ko ɗaya sai ƙyalli yake yi tamkar sabuwa tasa,
Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yana da ƙarfi na Allah ya isa, kuma ya tara dukiya mai tarin yawa saboda surutan dake sanye a jikinshi irin na hamshaƙan sarakai ne, kai ! Ko takalmi da kwamitin dake hannunshi abin kallo ne,
Har mun huce ta gaban attajirin sai ya kirani na zo na ƙarɓi sadaka, cikin matuƙar farin ciki ya ja sandar mahaifana da nufin na koma da baya domin tun da muka baro gida babu wanda ya bamu koda dinare guda amma bisa mamaki sai na ji mahaifana ya tsaya can! Ba tare da motsa daga inda yake ba, a tunani na ko bai fahimci abin da nake nufi ba ne sai kawai na ƙyale shi anan tsaye na nufi inda wannan attajiri ke hakimce a cikin rumfarshi,
Tun kafin na iso gare shi ya ƙura mini idanu ko ƙiftawa ba ya yi, kuma fuskarshi cike da annuri tamkar wanda aka bawa SARAUTAR DUNIYA,
Lokacin da na isa gare shi sai ɗebo dinare mai tarin yawa a cikin wata jakar fata ya miƙa mini cikin ladabi hannayena na kyarma saboda mamakin yawan dinaren wanda sai mu shekars muna bukatunmu da shi na durƙusa na ƙarɓa, sannan ya koma izuwa inda a bana ke tsaye na riƙe sandar jagora mu ka cigaba da tafiya,
Muna cikin wannan tafiya ne na waiga izuwa inda wannan attajiri yake aikuwa sai na ga har yanzu bai ɗauke idanuwanshi daga kaina ba,
Nan take n tambayi kaina a cikin raina na ce shin wannan attajiri tsananin tausayin da yake yi mana ne yansa shi wannan murmushi ko kuwa? Kuma na lura da yadda fuskar abbana ta canza a cikin ƙanƙanin lokaci,
Amsar tambayar da ba kasa bawa kaina kenan,
Kawai na dubi mahaifina cikin alamun matuƙar damuwa na ce " Ya abbana shin ina dalilin wannan fushi na ka? Shin baka farin ciki bisa wannan sadaka da muka samu da za ta iya magance mana dukkan matsalolinmu na rayuwa ?
Koda jin wannan tambaya sai abbana ya sake murtuke fuska al'amarin da ya sanya na sha jinin jikina keman,
Daga bisani ya yi ajiyar zuciya ya dube ni ya ce " Ya cikar muradin rayuwa ta kiyi sani cewa da ace kin san abin da na sani da ba kiyi gangancin ƙarbar sadakar wannan attajiri ba, domin babu wani alkairi a tare da shi,
Ina mai baƙin cikin sanar da ke cewa a halin yanzu rayuwarmu na cikin halin TSAKA MAI WUYA wajibi ne a gare mu mu yi hijira daga su tafi izuwa wata nahiyar domin shirya wa kan mu sabuwar rayuwa",
Koda jin wannan batu sai hankalina ya DUGUNZUMA ainun na dubi mahaifana cike da matuƙar mamaki na ce " Ya abbana shin mene ne sharrin da ka sani a tare da wannan attajiri da har zai sanya mu yi hijira ?,
Mahaifina ya gyaɗa kai cikin takaici ya ce " Ya 'yata ki yi sani cewa a halin yanzu babu lokacin da zan iya bayyana miki ko wane ne attajiri Kulbus, sai dai na yi miki alkawari bayan mun samu matsugunni a can wata nahiyar daban zan bayyana miki wane Kulbus, ya cikar farin ciki na ki yi sani cewa sirrin da muka daɗe ni da mahaifiyarki muna ɓoye miki duka ya tattara ne akan attajiri Kulbus, ba domin ƙaddara ta sake haɗa mu da shi ba ko da sunan shi bana so kunnuwana su sake saurare har ajali ya riske ni",
Koda jin wannan batu daga bakin mahaifana sai ƙwalla ta zubo daga idanuna kuma na fahimci cewa haƙiƙa na aikata babban kuskure ga mahaifana na karɓar sadakar attajiri Kulbus,
Mahaifina ya sake duba na a karo na biyu ya ce "Sai ki yi hanzari mu isa izuwa gida kar duhun dare ya riske mu a hanya"
Koda jin hakan sai na riƙe sandar mahaifana muka cigaba da tafiya cikin hanzari suka fice daga kasuwar har muka nausa izuwa cikin daji,
Muna cikin tafiyar ne a cikin daji wanda mun saba huce ta cikin shi ba tare da wata fargaba ba,
Kaico! Haƙiƙa rashin sani ya fi dare duhu, kuma tabbas tashin hankali ba a sa masa rana,
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ji an ɓarke da wata irin mahaukaciyar dariya mai kama da haniniyar doki, jim! Kaɗan sai ga waɗansu zunzurutun samudawan dakaru na ratsowa daga cikin duhuwar bishiyun dajin,
Dakarun suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, suna ɗauke da miyagun makamai masu barazana ga rayuwar MUTUM DA ALJAN,
Komai dakewar zuciyar jarumi da rashin tsoron shi idan ya yi arba da Waɗannan dole ne ya ɗimauce,
Kafin mu yi wani yunƙuri dakarun sun yi mana ƙawanya suna muzurai tamkar za su ci babu, koda ganin hakan ban san lokacin da hawaye suka kwaranyo daga idanuna ba na riƙe hannun mahaifina.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ji an bushe da wata mahaukaciyar dariya mai matuƙar ban tsoro, daga can sai sautin dariyar ya ɗauke, kawai sai dakarun dake ɓangaren yamma suka dare suka samar da wata 'yar siririyar hanya da mutum biyu za su iya jeruwa, kwatsam! Sai ga attajiri Kulbus ya ratso ta hanyar ya durfafo inda muke tsaye yana mai taka ƙafafuwanshi cikin ƙasaita fuskarshi a murtuke babu annuri, kuma a wannan lokaci yana shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, tun

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads