Showing 24001 words to 27000 words out of 27791 words
Chapter 9 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi
har na kai tsawon kwanaki uku ban fito fada ba?,
Haibatu ya ce "Kwarai kuwa ya shugabana"
Shin yanzu wane ne ya raina mini hankali uwar gidana, kuyanga Mushlaira ko kuwa Haibatu?,
Amsar tambayar da Fitinatul-Amir ya kasa bawa kanshi kenan, sannan ya sake bude baki a a karo na biyu yana duban Haibatu ya ce " Ka sanar da sarakunan cewa ba zan samu damar ganawa da su a yau ba dai zuwa gobe",
Daga wannan batu ne ya yi shiru aka cigaba da gudanar da sha'anin mulki kamar yadda aka saba.
Mu haɗu a littafi na 10 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
08137237071
TAFARKIN TSIRA 3
Littafin Yaki
Rubuta Labari
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
Turbar Ajali
Farautar Mazaje
Littafin kudi ne ₦300
Za'a biya kudin ta wannan account
0084279025
Usman Umar Mansur
Accces bank
Sai a tura shaidar biya ta wannan Number
08137237071
BABI NA SHA TARA
A can birnin Zainul-Ansar kuwa sai da aka shafe tsawon kwanaki uku ana bawa sarki Nu'umanu kulawa sosai ya warke sumul. A iya tsawon waɗannan kwanaki wannan hadimi mai ɗauke da siffa irin ta waziri Yazid shi ne ke lura da dukkanin wani sha'ani na masarauta, kuma duk bayan wani lokaci sai ya ziyarci turakar sarki ya ga a wane hali yake ciki a sirrance batare da wani ya gane shi ba.
A ɓangaren sarkin yaƙi lauzar kuwa shi ma ya gudanar da aiyukan da waziri ya umarce shi batare da wata matsala ba.
A safiyar wata rana ne sarki Nu'umanu ya aike wa da dukkan 'yan majalisar shi da saƙon zaman majalisar zartarwa,
Sa'adda sarki ya ga cewa kowa ya hallara a fadar kuwa an yi shiru sai ya yayi gyaran murya ya ce "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki bisa iko da ya bamu na halartar wannan taro mai albarka, tsira da amincin shi su ƙara tabbata ga Manzon tsira, bayan haka ya ku dattawam wannan masarauta tamu mai albarka bakomai ne ya sanya na tara ku a anan ba sai domin tattaunawa akan abin da ya faru a wannan birni namu na harin bazato daga maƙiya, shin yanzu wa ake tunanin ya kawo mana farmakin, sannan wane mataki ya dace mu ɗauka domin kare afuwar hakan?
Sa'adda sarki ya zo dai-dai nan a jawabin shi sai fadar ta yi tsit babu wanda yace ƙala tsawon daƙiƙa talatin sai daga bisani ne wani kyakkyawan saurayi ma'abocin kwariji wanda shi ne magatakarda ya yi gyaran murya ya ce "Ya 'yan uwana dattawam wannan masarauta mai albarka ku yi sani cewa abin da bincike ya tabbatar mini a harin bazato da aka kawo mana tabbas anyi amfani da shiri,
Hujja ta farko shi ne masu ba su ƙyale wata alama da zamu iya bincike akai ba tun daga gawarwakin dakarunsu, takobi ko tufafi,
Hujja ta biyu lokacin da na hallaka wani ɗan MAMAYAR BAZATO naga hatimin wata masarauta a jikin sulkenshi sai dai ban tsaya na lura da na wace masarauta ba ne,
Waɗannan hujjoji da na zayyana za su tabbatar mana da cewa waɗanda suka kawo farmakin sun kasance ma'abota bautar wanin Allah,
Ta wata fuskar zan iya cewa da alamu akwai wani munafuki a cikinmu da labartawa sarki Rakibu tattaunawar zaman da mu kayi a makon da ya gabata".
Lokacin da magatakarda ya zo dai-dai nan a zancen shi sai kowa ya sha jinin jikinshi kuma ya zurfafa izuwa kogin tunani, wannan hadimi mai ɗauke da siffa irin ta waziri da sarkin yaƙi Lauzar kuwa sai suka ji hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi suka dinga yiwa junansu inkiya ta wutsiyar idanu batare da wani ya lura da su ba.
Shugaban Baitul-Mali yayi gyaran murya sannan ya ce "Hakiƙa abin da magatakarda ya faɗi zai iya zamowa gaskiya, domin kuwa idan bamu manta ba Ubangiji ya faɗa a cikin littafinshi mai tsarki cewa kar mu riƙe kafirai a matsayin masu jiɓintar lamuran mu, domin su na yin umarni ne da hanyar shaiɗan...
Kafin ya gama rufe bakinshi magatakarda ya tari numfashi yana mai cewa "Ban katse ka ba ta kai ma'aji amma kafi kowa sanin cewa ba ma da wata hujja da za mu iya tuhumar sarki Rakibu bisa zargin da muke yi mishi, sannan kar ka manta cewa shi ne sarki da yafi kowa kyautata zumunta da zaman lafiya tsakanin mu da shi a kaf masarautun dake wannan nahiya tamu. Shawarar da zan bamu anan ita ce tsaurara matakan tsaro domin a fahimta ta sakacin dakaru masu tsaron ƙofa shi ne ya haifar da MAMAYAR BAZATO, wannan ita ce shawarata Allah ya taimake ka".
Lokacin da waziri Yazid yazo nan a zancen shi sai zauren majalissar ya sake yin shiru a karo na uku tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali babu wanda ya ce uffan, koda ganin hakan sai sarki Nu'umanu ya miƙe daga kan karagarshi yayi gyaran murya a karo na biyu sannan ya buɗi baki ya ce "Ya ku 'yan majalissata ku yi sani cewa tun da bamu tsayar da magana ɗaya ba, ya zama wajibi mu sake dogon nazari domin nemo bakin zaren, amma kafin wannan lokaci ba shiru za mu yi ba dole ne mu ƙara ƙarfin mayaƙanmu dodon tsaurara matakan tsaro, sannan akwai buƙatar mu yawaita idanuwansu a cikin al'umma domin samun bayanan sirri, da wannan batu nake yi maku fatan alheri sai Ubangiji maɗaukakin SARKI ya sake haɗa fusakun mu".
Koda gama faɗin hakan sai ya sauko ƙasa yana takawa da ƙafafuwanshi ya durfafi wata ƙofa ta musamman dakaru ma'abota fararen tufafi suka mara mishi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin ƙofar, sannan taron ya watse kowa ya kama gabanshi.
Wannan shi ne abin da ya wakana a can birnin Zainul-Ansar bayan harin sumane daga dakarun haɗin gwiwa.
Dukkan abin da ya wakana a wannan tattaunawa da sarki Nu'umanu ya yi da 'yan majalisar shi, sarki Rakibu da waziri Yazid sun gani a cikin madubin tsafin waziri a lokacin da suke zaune a wani lambun shaƙatawa, koda ganin wannan al'amari sai hankalin sarki Rakibu ya DUGUNZUMA ainun ya dubi waziri cikin matuƙar damuwa ya ce "Ya abokina tabbas a yanzu muna halin TSAKA MAI WUYA idan har sarki Nu'umanu ya gano cewa mu ne muka kai mishi MAMAYAR BAZATO".
Koda jin wannan batu sai waziri ya yi shiru yana mai juya al'amarin a cikin ranshi, daga bisani ya tattare hankalin shi waje guda ya dubi Rakibu ya ce "Ya kai babban aminina Kabul sani cewa koda ace sarki Nu'umanu ya gano shirin mu wannan ba zai sanya mu janye aniyar mu ta kawar da shi daga doran ƙasa ba, babban abin da nake ganin zai iya haifar mana da matsala shi ne ma'aji Kulairu,
Na fi kowa sanin wane shi domin mutum mai naci da juriya akan dukkan abin da ya sanya a gaba sai ya cimma nasara, ya zama wajibi a gare mu mu gana da shi a wannan dare, sannan za mu nufi birnin Zainul-Ansar ta dakarun yaƙin mu amma ba zamu kai farmaki ba sai lokacin da alfijir ya keto za a gudanar da sallar asuba, ina mai tabbatar maka da cewa zamu samu gagarumar nasara a wannan karon".
Lokacin da waziri ya zo dai-dai nan a zancen shi sai sarki Rakibu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin waziri Yazid na gaskiya da sarki Rakibu bayan sun ga dukkan tattaunawar sarki Nu'umanu da 'yan majalisar shi.
Mu haɗu a Littafin TAFARKIN TSIRA 11 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
TAFARKIN TSIRA 11
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Rayyan sai jama'a suka samu ƙarfin gwiwa dukkan fargaba,
Lokacin da yazamana tarar da ke tsakanin rundunonin biyu bai huce taku talatin ba sai kowanne ya ja ya tsaya aka yi kallon-kallo na tsawon daƙiƙa hamsin daga bisani sai sarki Lamsarul-Azlam ya ƙatse shirun da wanzu ta hanyar bushewa da dariyar mugunta sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da SAƙON MUTUWA ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "Ya kai tsohon abokin gaba kuma sarki mai taurin kai wajen biyayya a gare mu ka yi sani cewa yau ita ce rana ta ƙarshe da zan shafe tarihin ka daga doron ƙasa, domin kai ganau ne ba jiyau ba kuma ko ba a gwada ba linzami ya fi ƙarfin bakin kaza, kuma wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ba za ka iya ja dani domin har abada ruwa ba sa'an kwando ba ne..."
Kafin ya gama rufe bakinshi sarki Rayyan ya tari numfashin shi yana mai daka mashi tsawa ya dube shi ya ce "Karya kake ya tsahon mafi amana ka yi sani cewa komai matuƙar yawan rundunarka bazai firgita ni ba domin Ubangiji shine mai bayar da nasara, sannan har abada ƘARYA DA GASKIYA ba sa haɗuwa waje guda guda face gaskiya ta yi RINJAYE.
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Rayyan sai Lamsarul-Azlam ya fusata ainun gashin jikin shi ya mimmiƙe kawai sai ya zare wata sharɓeɓiyar Adda mai matuƙar KAIFI DA TSINI ya sakarwa dokinshi linzami yana ihu da kururuwa mai firgitarwa ya durfafi sarki Rayyan, koda ganin hakan sai shi ma ya yi koyi da shi ta hanyar zare takobinshi ya yi ɗauki kanshi yana ƙwala kabbara, lokacin da suka zo daf da juna sai Lamsarul-Azlam ya kai mishi wawan sara a kafaɗa, cikin matuƙar zafin nama Rayyan ya sanya garkuwarshi ya kare harin sannan suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, suka yi KARON BATTA irin na GWARAZANA JIYA.
Lokacin ɓangarorin biyu suka ga cewa jagororin su sun ruguntsume da artabu sai suka ɗaga makaman su suka yi ɗauki kan juna kafurai na ihu da kururuwar banza, musulmi na kabbara lokacin da aka haɗu sai aka rincaɓe da BAƘIN ARTABU ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne.
Haƙiƙa yaƙi shine matattarar dukkan wata musiba da zata samu ɗan Adam a doron ƙasa, domin yaƙi shine ke raba uwa da ɗan ta, asarar dukiya da rayuwa ma baki ɗaya.
Kaico! Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da kofatun dawakai ke kartar ƙasa suna tayar da ƙura, Hargowar aljanu da bil'adama JINI DA KASA suka cakuɗe waje guda MUTUWAR MAZAJE ta fara gudana dole ya ɗimauce.
Wannan shi ne abin da ya faru a lokacin da sarki Lamsarul-Azlam da rundunarshi suka isa izuwa birnin MADINATUL-AFNAN.
BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA
Al'amarin shugaban'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir kuwa lokacin da ya baro fada cikin matuƙar fushi bisa ga amsar tambayar da ɗan majalisa Haibatu ya faɗa mashi akan cewa yau tsawon kwanaki uku bai fito zaman fada ba, sai ya huce kai tsaye izuwa turakar su yaro Usaiba domin ya tabbatar da zargin da zuciyarshi take yi, lokacin da ya isa masu gadi suka buɗe mashi ƙofar turakar ya kunna kai izuwa ciki sai ya tarar da suna sharar barci a bisa kan gado, domin haka sai ya isa bakin gadon cikin hanzari ya sanya hannunshi ya ɗage jigar dake jikin Usaiba ya duba gadon bayanshi, aikuwa sai ya ga wayam babu zanen hatimin takobin SAIFUL-ZAYYAD, domin haka sai ya juya ya fice daga turakar zuciyarshi cike da matuƙar mamaki ainun,
Abu na farko da ya bashi mamaki shine shin mene ne yasanya zuciyarshi take bugawa da ƙarfi a duk lokacin da ya yi arba da yaro Usaiba,
Anya kuwa uwargidanka Rusayyat ba zata ci Amanar ka ba ta tseratar da rayuwar yaron.
Wata zuciyar kuma ta ce da shi ta ya ya kake tsammanin zata ci amanar ka bayan cewa za ta fi kowa burin ace ta samu haihuwa domin samun magaji. Lokacin da yazo dai dai nan a tunanin shi sai hankalin shi ya kwanta ya ji ya gamsu cewa yaro Usaiba ba shine mai hatimin takobi ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarkin 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir.
Fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa gami da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da abin da idanu ba su taɓa gani ba, duk ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a wannan fada dole ya tabbatarwa kanshi cewa GABA DA GABANTA aljani ya taka wuta, a wannan lokaci fadar ta cika maƙil babu masaka tsinke duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke, a kowacce kusurwa a dakarun tsaro ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro suna ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro.
Bisa wani zagayayyen tudu mai matattakala bakwai a ƙasan shi anan aka ajiye wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta da ƙarfen zubar daju aka yi mata feshi da koren lu'ulu'u, wani shirgegen mutum ne tamkar giwa, ƙasumba da sajen shi baƙaƙe siɗik! Sune suka tona asirin kyawun surarshi, kuma suturun dake jikinshi suka dace da shi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya cika GWARZON MAYAƘI mai ƙarfi na Allah ya isa, a wannan lokaci fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara, kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wani mutum ya bayyana tsulum! A tsakiyar fadar tamkar an aiko shi daga sama, mutumin yakasance gajere baki wuluk! Fuskarshi mummuna ce tamkar bai taɓa dariya ba, jikinshi cike yake da gashi buzu-buzu da layi, da guraye na sihiri babu kyawun gani tamkar wani tsohon mahaukaci, babu wani tufafi a jikinshi face bante na fatar damisa da ya suturce al'amuran shi, a hannunshi na hagu yana dogare da wata SANDAR TSAFI, kaico! Haƙiƙa babu wani mahaluki a doron ƙasa da zai yi arba da wannan mutum ba face ya firgice, ba wani ba ne face boka kaddad.
Sannu a hankali kaddad ya yi tattaki da ƙafafuwanshi yana mai dogara sandarshi ya durfafi inda karagar mulki take, lokacin da ya rage saura kamar taku goma ya isa sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa,
Cikin annuri fuska mutum dake zaune bisa karagar ya ƙarɓi gaisuwar ta hanyar gyaɗa kai sannan ya buɗe baki cikin kakkausar murya mai kama da saukar aradu ya ce "Lale marhabun da Dodon bakoye hadari malafar duniya, lafiya na gan ka a wannan lokaci da baka saba zuwa ba ?
Koda jin wannan tambaya sai boka kaddad ya buɗe baki a karo na farko cikin murya mai kama da haushin kare ya ce "Ya shugabana ka ji sani cewa bakomai na ya kawo ni gare ka sai domin na sanar da kai wani abin farin ciki, bincike da na gudanar bisa halarar tsafi na ya bayyana mini maganin da zai warkar da gimbiya da cutar makanta da take damun ta, shi ne wani ALLON TSAFI, dake ajiye a ƙarƙashin tekun Baharul-Saljir a cikin wani masifaffen kada,
Ya kai Hulaifu ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya babu wata dabba dake rayuwa a cikin teku da ta kai kadan ƙarfin damtse da na sihiri,
Za a warkar da gimbiya ne idan aka karanta ɗalasiman tsafin dake jikin Allon sannan a shafa mata a fuska take idanuwanta za su buɗe garau!"
Koda jin wannan jawabi daga bakin boka kaddad sai sarki Hulaifu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa fuskarshi ta faɗa da murmushi ya dube shi ya ce "Ya masanin ilimin tsafi tsawon lokaci za mu ɗauka kafin tafiya nemo wannan ALLON TSAFI?
Boka kaddad ya bushe da dariyar mugunta sannan ya ce "Ai a gobe za mu yi wannan tafiya domin masu iya magana na cewa da zafi-zafi akan daki ƙarfe, kuma a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, sai dai dole ne tafiyar sai an tafi da gimbiya domin kuwa Allon yana da wani sharaɗi idan har aka fito da shi daga gadan idan har ya huce tsawon sa'a ɗaya ba ayi amfani da shi ba zai lalace kaga kenan an sha wahalar banza".
Koda jin wannan batu daga bakin boka kaddad sai sarki Hulaifu ya cika da matuƙar farin maral-musaltuwa, take kaddad ya sake ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba, sarki ya tashi daga faɗa ya shiga izuwa cikin gidan sarauta, kowa ya watse ya kama gaban shi.
Mu haɗu a TAFARKIN TSIRA 12 Domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
TAFARKIN TSIRA 12
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Ƙarya Da Gaskiya
Gasar Sarauta
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan shugaban 'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir ya yi kalaci ya caɓa ado sai nufi fada domin ganawa da sarakunan da zasu gabatar da haraji. Bayan kowa ya hallara sarki ya hakimce bisa karaga 'yan majalisa sun kammala mika gaisuwa,
Lokacin da sarakuna birane ashirin da uku suka gurfana a gaban sadauki Fitinatul-Amir sai sarki na farko da ake kira da suna Madsur ibn Zauhil ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya buɗi baki cikin ladabi kanshi a sunkuiye ya ce "Ya sarkin sarakuna, GOBARAR DAJI mai share abokan gaba, KAIFIN TAKOBI mai raba tsakanin masoya, kai ne SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA dake saukar da ANNOBA ƊARI, gani tafe da ɗan abin da bai taka kara ya karya ba ina roƙon a ƙarba domin na kai ba".
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Madsur sai Fitinatul-Amir ya bushe da dariyar farin ciki maral-musaltuwa bisa kirarin da ya yi mashi, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da SAƙON MUTUWA ya dube shi cikin taƙama da BAƘAR IZZA ya ce "Yakai Madsur haƙiƙa dukkan abin da ka faɗa gaskiya ne saboda haka dukkan abin da ka kawo an karɓa tafi abin ka".
Cikin matuƙar