Showing 21001 words to 24000 words out of 27791 words
Chapter 8 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi
da nake a rayuwata ban taɓa ganin sadauki mai kwarjini tamkar attajiri Kulbus ba,
Ya yin da yazamana cewa tazarar dake tsakanin mu da shi ba ta huce taku goma ba sai kawai ya ja ta tsaya cak! Yana mai ƙura mana idanu ko ƙitawa ba ya yi,
Al'amarin da sanya tsoro ya sake kama ni ainun kenan jikina ya kama ƙyarma!,
Tsawon daƙiƙa talatin muna cikin wannan hali sai daga bisani ne attajiri Kulbus ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya dubi abbana ya ce " Ya kai makaho Zafiyar ka yi sani cewa tsawon lokaci ina farautar ka a cikin wannan birni amma ban samu nasara ba sai a yau, ko ka manta cewa na faɗa maka indai kere na yawo zabo na yawo wata rana sai sun gamu",
Koda jin wannan batu daga bakin Kulbus sai mahaifana ya fusata ainun ya daka mashi tsawa ya ce " Ya kai babban maci amana kuma mayaudari ka yi sani cewa har abada ƙarshen maci amana mutuwar wulakanci, ina yi maka albishir da cewa yau zan hallaka ka".
Ko da jin wannan batu daga bakin abbana sai Kulbus ya bushe da dariya ya ce " Ya kai Zariyar ka fi kowa sanin cewa ko ba a gwada ba linzami ya fi ƙarfin bakin kaza, kar ka manta cewa a halin yanzu kai makaho ne idanuwanka ba sa gani, kuma tsufa ya fara kama ka ba ka da jarumtakar da za ka yin KARON BATTA da ni ba, sannan wannan 'ya taka ba ta da ƙarfin da za iya kare ka daga ka ba".
Kafin Kulbus ya gama rufe bakinshi na tari numfashin shi ina mai daka ma shi
tsawa na na buɗe baki da nufin na furta wani abu amma sai mahaifana ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga mini hannu, kawai ya ɗaga sandarshi ya shammaci Kulbus ya make takobin sa ke hannunshi ya taƙarƙare ya gabza mashi wawan naushi a fuska da dukkan ƙarfin shi,
Saboda ƙarfin naushin sai da Kulbus ya yi taga-taga zai faɗi ƙasa amma sai ya turje ya shafa fuskarshi da hannunshi na hagu take ya ji jini na zuba a hancinshi,
Al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan kuma ya ɗaure mini kai, domin a iya sani na mahaifana ko da wuƙar yankan tuffa bai iya riƙewa, amma ya ya aka yi ya samu wannan gagarumin ƙarfi haka? Amsar tambayar da na kasa bawa kaina kenan,
Shi kuwa attajiri Kulbus sai ya fusata ainun ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da ya firgita duk wata halitta dake dajin, yana gama rufe bakin shi sai dakarunshi suka zare makamansu suka yi ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a FIKIN DAGA, suka ɗauki izuwa kan mahaifina,
Koda jin hakan sai mahaifana ya daka wawan tsalle tamkar an harba shi daga cikin baka ya sauka a daf da dakarun tamkar yakasance mai gani ba makaho ba, ya shammaci mutum huɗu a cikin su ya gabza masu wawan naushi a fuska a lokaci guda suka zube ƙasa magashiyan suna nishin wahala.
Lokacin da Jaruma Rusayyat ta zo dai-dai nan a labarin da take bawa su yaro Usaiba sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta, sannan cigaba da cewa
BABI NA SHA SHIDA
Sa'adda na ga an kacame da azababban yaƙi tsakanin mahaifina da dakarun sai na ruga izuwa bayan wata bishiya na rakaɓe ina leƙen abin da ke wakana zuciyata cike da matuƙar mamakin jarumtaka irin ta abbana duk da kasancewar shi makaho,
Wani ɓangaren a zuciyata kuwa cike yake da tsoro akan abin da zai iya biyo baya idan attajiri Kulbus ya samu nasara akan abbana, wani tunani da ya faɗo mini a rai ya dungunzuma hankalina shi ne mahaifyata da baro a gida shin ko a wane hali take ciki,
Sa'adda na zo nan a tunanina sai hawaye suka kwaranyo mini,
Duk inda abbana ya sanya a gaba sai dai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar ana karkaɗe busassu ganyeyya kin bishiya a lokacin hunturu, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa, jini ya dinga kwanya, tsartuwa yana malala a ƙasa,
Nan da karafniyar ƙarafa da ihun MAZAJE ta cika dodon kunne,
Wohoho! Haƙiƙa jarumtaka baiwa ce da zaɓi na Ubangiji dukiya ko mulki ba sa bayar da ita,
Komai hassadar mutum idan ya ga yadda makaho Zafiyar ke ragargazar dakarun dole ne ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya shiga MURUCIN KAN DUTSE..,
"Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan Baƙin ARTABU babu sassauci,
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI sai dakarun Kulbus suka fara galabaitar da mahaifana suka haɗa mashi jini da majina har ta kai cewa ya faɗi ƙasa magashiyan yana numfashi da ƙurar! Al'amarin da sanya ni zubar da hawayen baƙin ciki kenan,
Koda samun wannan gagarumar nasara sai attajiri Kulbus ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a damtsenshi daga cikin kubenta ya taka da ƙafafuwanshi har izuwa inda mahaifana ke kwance ya sanya KAIFIN TAKOBI ya yi wa abbana yankan rago ya yi jifa da gawarshi gefe guda".
Lokacin da Jaruma Rusayyat ta zo dai-dai nan a labarin rayuwarta sai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya hawaye suna kwaranyo daga idanuwanta, al'amarin da ya sanya yaro Usaiba da yar uwarshi Hairat su ka fara zubar da hawayen saboda matuƙar tausayin ta,
Tsawon daƙiƙa talatin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Rusayyat ta share hawayenta ta dube su a lokacin da idanuwanta suka kaɗa suka yi jajur ta ce " Ya ku 'ya'yana ku yi sani cewa wannan labari nawa da na ba ku ba a ɗauki kaso ɗaya bisa biyar ɗin shi ba, kuma wanda zan ba ku anan gaba ya fi shi ban tausayi da takaici".
Koda jin wannan batu daga bakin Rusayyat sai yaro Usaiba ya dube ta cikin alamun matuƙar damuwa ya ce " Ya ummina haƙiƙa attajiri Kulbus ya cika baƙin azzalumi marar tausayi, shin ta ya aka yi kika kuɓuta daga hannun shi sannan mene ne abin da ya faru da mahaifiyarki?, Koda jin waɗannan tambayoyi sai ƙwalla ta zubo wa Rusayyat ta dube shi ta ce " Ya ɗan abin alfahari na ka yi sani gaba ɗaya amsar tambayoyin da ka yi mini suna cikin ƙasashen labarina, yanzu za mu koma izuwa gida domin lokacin yin kalaci ya yi, zuwa gobe zan cigaba daga in da na tsaya".
Koda gama faɗin hakan sai Rusayyat ta riƙe hannayen su suka tashi tsaye ta ɗora su a bisa wannan keken doki, ta hau ta zauna ta bisa dokin keken ta sakar ma shi linzami suka fara tafiya suna durfafar hanyar da zata sadasu da harabar gidan sarauta.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin jaruma Rusayyat uwar gidan shugaban'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir tare da su yaro Usaiba mai hatimin takobi.
Mu haɗu a Littafin TAFARKIN TSIRA 9 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa lakabi da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
0813723771
TAFARKIN TSIRA 9
Littafin Yaƙi
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littafan Marubucin
Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi
BABI NA SHA BAKWAI
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin sadauki ukaiza shugaban dakarun sarki Lamsarul-Azlam da ke farautar yaro mai hatimin takobi tare da dakaru dake tsaron ƙofar birnin Baitul-Ashmar, sai yaƙin ya zamto abin tsoro gami da tashin hankali, yawan dakarun ya zamo a banza domin ukaiza ya wanzu yana aika rayukan su izuwa barzahu KAIFIN TAKOBInsa ya dinga ratsa sassan jikkunan su JINI DA ƘASA suna cakuɗuwa da juna,
Kaifin shudewar daƙiƙa hamsin ukaiza ya hallaka fiye da rabin dakarun, al'amarin da ya razana sauran kenan domin tun da suke gadin wannan ƙofa ba a samu GWARZON MAYAKI da ya samu nasara akan su na shin wane ne wannan sadauki? Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan,
Ana cikin wannan ARTABU ne wani tunani ya faɗo wa ukaiza tunanin kuwa shi ne, idan har ka bari aka ɗauki wani lokaci ba tare da ka yi nasara ba to dakarun dake cikin gari za su samu rahoton abin da ke faruwa domin haka za a tsaurara matakan tsaro,
Sa'adda Ukaiza ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya dinga amfani da hikima ya na kashe fitilun dake wajen , yayin da ya fahimci cewa wajen ya yi dubu dunɗum! Sai kawai ya shammaci dakarun ya kunna kai izuwa cikin birnin, ya bar dakarun suna ta ƙoƙarin kunna fitilun, kai tsaye gidanshi ya nuna domin ya ga wane hali iyalinshi ke ciki,
Lokacin da isa sai ya tarar ƙofar gidan a buɗe kuma ko wane waje a ciki haskake yake da fitilar ice, al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan, kuma zuciyarshi ta buga da ƙarfi, amma sai ya kunna kai izuwa ciki yana sanɗa hannunshi dafe da kuben takobinshi domin shirin kar ta kwana, ya yin da ya yi kamar taku shida a zauren gidan sai kawai ya ji an gabza ma shi wani wawan naushi a ƙeyarshi saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katan-tanwa sai uku sai ya faɗi ƙasa tim! A matuƙar galabaice yana mai kurma ihu, kafin ya yi wani yunƙuri waɗansu irin samudawan dakaru ma'abota jajayen tufafi sun ɗaure shi tamau da wata irin murtukekiyar igiya sannan ɗaya daga cikin su ya ɗauke shi ya ɗora shi a kafaɗarshi ya nufi ƙofar fita daga gidan, sauran dakarun mutum shida suka yi koyi da shi, suna fita kai tsaye suka durfafi wata hanya da zata sadasu da kurkukun birnin suna tafiya cikin hanzari.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin sadauki ukaiza da dakarun sarki Lamsarul-Azlam.
Al'amarin boka kaddad kuwa tun sa'adda ya tura aljani Lattul-kifas domin farauto mishi yaro mai hatimin takobi sai ya shafe tsawon kwanaki biyu bai ji ɗuriyar shi ba, yayin da ya fahimci cewa wankin hula zai kai shi dare sai kawai ya yanke shawarar ya gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi domin gano abin da ke wakana,
Sa'adda ya gudanar da bincike nan take ya ga dukkan abin da wakana tsakanin Lattul-kifas da dakarun dake gadin gidan sarkin 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir, koda ganin hakan sai ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, sautin ihun ya amsa kuwwa har izuwa cikin dajin ya tashi ha hankulan tsuntsaye dake kan bishiyu suka bazama wajen canja sheƙunansu,
Tsawon daƙiƙa ashirin yana cikin wannan hali sai daga bisani ne ya murtuke fuska an aiko mishi da sakon mutuwa,
Sannan ya sake baje alƙalumman sihirin shi ya cigaba da gudanar da bincike, yana cikin wannan hali ne kuma sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki,
Ba wani abu ne ya sanya shi wannan dariya ba sai domin ya gano cewa har abada ba zai taɓa cimma burin shi na shan jinin yaro mai hatimin takobi ba kuma har ya kawar da Jaruma Rusayyat da mai gidanta ba face ya mallaki wata hula da ake yiwa laƙabi da Lauhul-Sihir,
Hular Lauhul-Sihir ta kasance mallakin sarkin bokayen aljanun duniya wanda a ƘARNI UKU bayan yaƙin duniya na farko ba a samu GWARZON MAYAKI tamkar shi ba,
Binciken masana da masu hasashe ya tabbatar da cewa boka ƙaddamul-Barzahu yana iya yaƙar gari guda shi ƙadai ya cinye shi da yaƙi b zai bar koda ƙiyashin birnin a raye ba,
Kuma an ce ya shafe tsawon shekaru ɗari bakwai yana sana'anta hular Lauhul-Sihir bayan ya kammala ne ya shiga yaƙar sarakunan duniya yana mayar da su izuwa ƙarƙashin ikon shi, wata ƙasa ce ta ma'abota addinin musulunci kawai ta zamo mishi cikas wajen cimma burin shi na BAUTAR SARAKAI na duniya, bisa wannan dalili yasanya masana ke yi masa laƙabi TARKON SARAKAI,
Daga cikin amfanin da hular Lauhul-Sihir shi ne duk mahalukin da ya mallake ta zai mulki dukkan sarakunan duniya,
Tana ɗauke da sirrkan tsafi guda miliyan biyu da babu wanda zai same su face wanda ya mallaki hular,
Duk wanda ke sanye da hular zai iya shafe tsawon sa'o'i yana ARTABU ba tare da ya ci ko ya sha ba,
Babu wani makami da zai yi tasiri akan shi, duk tsawon shekarun da mutum ya shafe yana jinya inda aka sanya mishi ita nan take zai warke sumul tamkar bai taɓa jinya ba,
Sirri na ƙarshe shi ne mutum na iya sanya hular izuwa kowa ne nau'in makami kuma ya aikata zuwa inda yake so ta aiwatar da dukkan abin da ya nufa,
A halin yanzu hular Lauhul-Sihir tana ajiye a wani kogon dutse mafi haɗari a duniya, kafin mutum ya isa inda yake sai ya ƙetare waɗansu miyagun dazuka guda sha biyu,
Babu wani mahaluki da doran ƙasa da zai iya shiga kogon face ya mallaki wani ALLON SIHIRI,
Allon yana ajiye a cikin wani masifaffen kada dake zaune a ƙarƙashin tekun Baharul-Saljir, kadan ya haɗiye Allon ne a lokacin da waɗansu manyan matsafan duniya suka fafata yaƙi a saman tekun domin ɗayan su ya mallaki ALLON SIHIRIn,
Wannan shi ne abin da yasanya boka kaddad ya yi wannan dariyar farin ciki,
Tun daga wannan rana kaddad ya fara shirye-shiryen tafiya domin mallakar hular Lauhul-Sihir.
Wannan shi ne abin da faru da boka kaddad bayan ya tura hadimin aljanin shi domin farauto mishi yaro mai hatimin takobi.
BABI NA GOMA SHA TAKWAS
Al'amarin shugaban 'yan fashin duniya sadauki fitinatul-Amir kuwa, tun sa'adda uwar gidanshi Rusayyat ta shayar da shi hodar banju domin ta samu nasarar tseratar da rayuwar yaro Usaiba mai hatimin takobi. Sai ya shafe tsawon kwana ɗaya a cikin wannan hali sannan ya farka ta hanyar buɗewa idanuwanshi ya yi miƙa gami da hamma, kuma ya ji kanshi na juya mishi,
Kawai sai ya ƙwalla wa wata kuyanga kira,bayan ta bayyana gare shi ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa sai ya dube ta ya ce "Ya ke mushlaira shin har tsawon wane lokaci na ɗauka ina barci kuwa?
Koda jin wannan tambaya sai Mushlaira sai ta buɗi baki cikin ladabi ta ce "Ya shugabana ai yau tsawon kwana ɗaya kenan ka shafe kana barci"
Sa'adda fitinatul-Amir ya ji wannan batu sai ya cika da matuƙar mamaki da al'ajabi, har buɗe baki da nufin yace wani abu sai ya ji alamun ɓuɗe ƙofar turakar don haka sai mayar da duban shi izuwa ga wajen domin ya ga wane ne ke tafe.
Aikuwa sai ya yi arba da uwar gidanshi Rusayyat ta caɓa ado mai ƙayatarwa fuskarta cike da annuri,
Koda Mushlaira ta yi ga cewa gimbiya ta shigo sai ta miƙe tsaye zumbur! Ta durfafi ƙofar fita daga turakar,
Sannu a hankali Rusayyat tana takawa da ƙafafuwanta har ta iso inda mai gidanta yake ta zauna a daf da shi har suna jin numfashin juna,
Cikin tattausan murmushi mai ɗimauta zuciya Rusayyat ta ce "Barka da wannan lokaci ya JARUMIN JARUMAI farin cikin zuciyata", fitinatul-Amir ya mai da mata da martanin murmushin, wanda ya fi kama da yaƙe sannan yayi gyaran murya ya ce "Ya uwar'ya'yana wai shin tsawon wane lokaci na ɗauka ina wannan barci ne?
Da jin wannan tambaya sai Rusayyat ta ce "Ya abin ƙaunata ai baka huce tsawon sa'a ɗaya ba, ko ka manta ne cewa ɗazun nan ba jimawa muka yi kalaci yanzu kuma da farka ai lokacin fita faɗa ne",
Koda jin amsar wannan tambaya sai tunanin fitinatul-Amir ya rikice yace a cikin ranshi, shin tsakanin matata da kuyanga Mushlaira wane ne ya raina mini hankali? Tabbas duk wanda na samu da laifin hakan sai na yanke mishi hukunci mai tsanani",
Koda gama tunanin hakan sai ya miƙe tsaye ya nufi kewaye, jim! Kaɗan ya fito bayan ya tsaftace fuskarshi ya riƙe hannun Rusayyat suka durfafi ƙofar turakar, suna fita waɗansu zaratan dakaru masu jajayen sulke ɗauke da miyagun makamai suka mara masu baya,
Duk wajen da suka durfafa a cikin gidan sarautar sai ka ga dakaru, kuyangi da hadimai na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa, yayin da aka iso daf da turakar Rusayyat sai suka yi bankwana fitinatul-Amir da sauran dakarun kuma sai suka ci-gaba da tafiya,
Tafiyar daƙiƙa arba'in kacal! Suka yi aka iso fadar birnin,
Ita dai fadar ta kasance ƙasaitacciya da aka yi mata ado da nau'ikan kayan ƙawa da alatun more rayuwar duniya, gaba ganin fadar an yi shi ne da zallar jauhari da zubar-daju,
Masana da masu hasashe sun tabbatar da cewa babu wata faɗa da ta kai ta ƙawatuwa, waɗansu daga cikin masana na kiran fadar da suna ALJANNAR DUNIYA.
Kai tsaye fitinatul-Amir ya nufi inda karagar mulki take ya taka matattakalar fadar, a lokacin da gaba ɗaya jama'ar fadar suka miƙe tsaye domin girmamawa a gare shi,
Bayan Fitinatul-Amir ya hakimce bisa karagar mulki sai suka dinga tashi daga wajen zamansu suna zuwa gare shi suna kwasar gaisuwa, talakawa ne suka fara tasu gaisuwar sannan attajirai, sai 'yan majalisar sarki, su dai 'yan majalisar sun kasance GWARAZAN JARUMAI da Fitinatul-Amir ke amfani da su domin kai farmaki zuwa wata ƙasa, don FATAUCIN BAYI da ganimar dukiya, mutum shida daga cikin 'yan majalisar sun kasance GWARAZAN SARAKAI saboda matuƙar tsoron Fitinatul-Amir ya sanya suka haƙura suka bar sarautar suka koma KANGIN BAUTA a ƙarƙashin shi. Shiru ne ya wanzu a fadar na tsawon lokaci tamkar an yi ruwa an ɗauke, sai daga bisani ne wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko daga cikin 'yan majalisar ya buɗi baki cikin ladabi da ƙasƙantar da kai ya buɗi baki ya ce "Ya shugabana yau tsawon kwanaki uku kenan Ayarin sarakuna guda ashirin suna so su gana da kai domin su bayar da harajin su kamar yadda suka saba"
Koda jin wannan batu daga bakin ɗan majalissar sai Fitinatul-Amir ya sake cika da matuƙar mamaki ya dube shi ya ce "Ya kai Haibatu shin yau