Showing 9001 words to 12000 words out of 27791 words
Chapter 4 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi
hatimin takobin sai ita ma ta shiga binciken bisa halarar tsafin ta domin gano ko yaro mai hatimin ya bayyana.
A wannan lokaci duk inda mutum ya kalla a fadar babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke tamkar DANDAZON MAYAƘA,
A gefe guda kuwa 'yan majalissar sarki na zaune a bisa shimfiɗu na alfarma kawunan su a sunkuye tamkar masu neman gafara.
Ana cikin wannan hali ne sarki Lamsarul-Azlam ya lura cewa lokacin ta shi daga fada ya yi domin haka sai ya miƙe tsaye tsam! daga kan karagar shi ya yaƙi matattakalar fadar ya sauko ƙasa ya rike hannun gimbiya Sharizat suka nufi wata ƙofa ta musamman a fadar take waɗansu ZARATAN DAKARU ma'abota baƙaƙen tufafi suka mara masu baya har suka ƙule izuwa cikin ƙofar,
Nan take fadar ta watse kowa ya kama gaban shi.
***
Tafiyar daƙiƙa hamsin Rusayyat da mai gidanta Sadauki Fitinatul-Amir kacal suka yi suka iso zuwa turakar da su yaro usaiba ke ciki, cikin hanzari dakarun masu tsaro suka wangame ƙofar shiga tare da miƙa gaisuwa, kai tsaye Rusayyat ta jagoranci mai gidanta har zuwa gadon da su Usaiba ke kwance suka zauna a gefen shi,
Sa'adda Fitinatul-Amir ya yi arba da yaro Usaiba sai zuciyarshi ta buga da ƙarfi alamun tsoro ƙarara suka bayyana a fuskarshi, sannan ya mayar da duban shi ga Hairat ya ɗauki tsawon lokaci yana nazarin kyakkyawar fuskarta,
Daga bisani ya mayar da duban shi ga Rusayyat cikin tattausan murmushi da ya fi kama da yaƙe ya ce "Madalla da wannan tsuntuwa ya abar ƙaunata haƙiƙa na kasance cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, kuma naji a jikina cewa waɗannan yara za su maye mana gurbin magaji a gare mu,
Yanzu zan tafi zuwa ya sake komawa barci domin na wartsake kafin lokacin fita fada ya yi zan samu lokaci sai mu ƙara tattaunawa akan wannan al'amari".
Gama faɗin hakan ke da wuya sai ya miƙe tsaye tsam! ya taka da ƙafafuwanshi ya nufi ƙofar fita daga turakar yana mai waigen uwar gidan shi suna yiwa juna lallausan murmushi mai gusar da dukkan damuwa.
Koda ficewar shi sai Rusayyat ta faɗa izuwa kogin tunani, Abu na farko da ya faɗo mata a rai shi ne,
Anya kuwa mai gidan ki ba bincike ya tafi ya gudanar akan waɗannan yara ba ki lura da irin kallon da ya yi masu mana alamu suna nuna bai aminta da su ba,
Wani tunanin da ya faɗo mata shi ne mai zai hana ko gudanar da binciken domin ki gano gaskiya al'amari game da waɗannan yara,
Sa'adda Rusayyat tazo nan a tunanin ta sai sai baje alƙalumman sihirin ta ta shiga gudanar da binciken.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin shugaban'yan fashin duniya Sadauki Fitinatul-Amir da uwar gidan shi jaruma Rusayyat.
***
Sa'adda sarki Nu'umanu ya falfala da azababban gudu hannunshi riƙe da takobin tsirara yana mai fuskantar hanyar da zata sada shi da kofar fita daga gidan sarauta,
Yana cikin wannan hali ne ya hango wani badakare fuskarshi rufe da rawani Idanuwanshi kaɗai ake gani ya durfafo inda yake ya na hallaka dakarun dake gaban shi yana samarwa da kanshi hanya ya ƙarfin tsiya.
Sa'adda sarki Nu'umanu ya lura da irin muguwar ɓarnar da badakaren ke yi mashi sai kawai ya ƙwalla kabbara da ƙarfi ya durfafi inda yake cikin mugun tanadi.
Lokacin da ya rage bai huce taku shida a tsakanin su ba sai badakaren ya dako wawan tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka ya dira a daf da inda sarki Nu'umanu yake suka tari juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban sha'awa,
Suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, Duk sa'adda makaman yaƙin su suka haɗu da juna sai dai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tsoro ne da tashin hankali wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi, domin yaƙi shi ne ke ƙarya tattalin arziki da duk wani jin daɗin rayuwa ta ɗan adam,
Inda a ce mutum zai ha yadda ruhikan mutane ke rabuwa da gangar jikin su yara da mata na zamowa marayu dole ya zubar da hawayen baƙin ciki, Duk da kasancewar dare ya tsala amma sai garin ya zamo tamkar safiya ce saboda yadda haɗuwar makaman yaƙi ke haddasa wani haske a sararin samaniya.
Aɓangaren sarki Rakibu da sarkin yaƙi lauzar kuwa sun wanzu suna yiwa dakarun birnin Zainul-Ansar muguwar ɓarna yazamana cewa duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga,
A ɓangaren dakarun birnin Zainul-Ansar kuwa waɗansu zakwakuran MAYAƘA ne masu zafin nama gami da nacin tsiya keta faman yiwa dakarun haɗin gwiwa muguwar ɓarna ,
Nan fa jini ya dinga kwaranya tamkar na ɓalle ƙorama, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman, Hankakan mutuwa ya wanzu yana kai komo wajen ɗaukar rayuka, gidaje suka dinga kamawa da wuta suna rushewa, Musulmi na yin kabbara kafirai na ihu da kururuwar banza, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihun mazaje suka cika dodon kunne, dawakai suka dinga jefar da mahayansu suna nausawa izuwa cikin daji saboda azabar yaƙi,
Komai kallon ƙurillan mutum ba zai iya bambance ɓangaren da suke da nasara ba saboda yadda filin yaƙin ya yamutse,
Lokacin da sarki Rakibu da sarkin yaƙi lauzar suka ga irin mummunar ɓarnar da waɗannan zakwakuran MAYAƘA na dakarun Musulunci ke yi masu sai suka canza salon faɗansu,
Yazamana cewa sun ƙara zage damtse wajen ragargazar dakarun sarki Nu'umanu babu sassauci,
Ba wasu ba ne waɗannan mayaƙa da ke ɓangaren dakarun Musulunci ba face shugaban baitul-mali, galadima tare da sarkin fada uwaisu,
Koda shugaban baitul-mali ya lura da irin ɓarnar da su sarki Rakibu ke yi masu sai ya canza salon faɗan shi, Da ganin hakan sai sarkin fada da galadima suka yi koyi da shi yazamana sun zare sabbin makaman a jikin su sun ƙara afkawa abokan gaba.
A ɓangaren sarki Nu'umanu da badakare kuwa sun shafe tsawon Sa'a ɗaya suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta domin salwantar da rayukan juna amma babu alamun nasara ga kowa ne ɓangare,
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Sarki Nu'umanu kai kenan kuma ya ba shi mamaki domin tun da yake artabu da manyan jarumai hakan bai taɓa wanzuwa ba, ya yin da ya zo nan a tunanin shi sai ya cigaba da ambaton tsarkakan sunayen Allah a cikin ran shi yana neman taimakon shi,
A ɓangaren badakaren kuwa ba haka abin yake ba domin ba shi da wani buri da ya huce ya ga hallaka sarki Nu'umanu,
A cikin gidan sarauta kuwa al'amarin gimbiya lawisat uwar gidan sarki Nu'umanu kuwa duk sa'adda ta ji gidan sarautar ya kaure da guje-guje gami ifice-ificen jama'a sai hawayen su sake kwaranya daga idanuwanta tana tunanin halin da mai gidanta sarki Nu'umanu ya ke ciki,
Wannan shi ne abin da ya wakana a can birnin Zainul-Ansar.
***
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban sha'awa tsakanin aljani Lattul-kifas da waɗannan dakaru masu tsaron wannan ƙayataccen gida, Sai yaƙin ya zamo abin tsoro da fargaba yazamana cewa dakarun suna kaiwa aljani Lattul-kifas sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA suka yanyame shi tamkar yadda ƙudaje ke yanyame ƙwallon ma Gwari,
Aljani Lattul-kifas ya wanzu yana kare hare-haren dakarun cikin juriya da nacin tsiya duk sa'adda da ya kare harin mayaƙan sai kaga ya durƙushe ƙasa saboda ƙarfin saran dakarun idan kuwa shi ya kai masu hari sai dai takobin shi ta nutse a cikin ƙarƙashin ba tare da ya samu nasarar koda lakutar jikin ɗayan su ba,
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan ƙazamin artabu babu sassauci babu nasara ga kowa ne ɓangare,
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Lattul-kifas kai kenan kuma ya zurfafa zuwa ƙogin tunani,
Abu na farko da ya faɗo mashi a rai shi ne kasancewar shi GWARZON BASARAKE mai tarwatsa maza a filin fama komai matuƙar yawan abokan gaba yana iya maishe su fawa cikin 'yan daƙiƙu, amma sai gashi waɗannan dakaru sun gagare shi hallakawa,
Sannan shin Waɗannan dakaru bana sihiri na ne kuwa? Idan haka ne shin tsakanin mai mallakin wannan gida da mai gidana boka kaddad wane ne yafi wani shahara?
Wani ɓangaren a zuciyarshi na cewa da shi ai shi ilimin tsafi Kogi ne komai nutson ka ba zai yiwu ka ƙure ƙarshen shi ba.
Lokacin da aljani Lattul-kifas yazo nan a tunanin shi sai hankalin shi ya dugunzuma ainun abin da ya ɗugunzuma hankalin na shi shi ne haƙiƙa a kowa ne lokaci ƙarfin damtsen shi zai ragu ainun kuma hakan zai iya bawa dakarun nasara akan shi, domin haka sai ya fusata ainun ya sake zage zage damtse yana cigaba da kai masu hari ta ko ina tamkar wani ifritu,
Yana cikin yaƙin ne kawai sai ya yi jifa da takobinshi ya shiga yaƙar dakarun da tsagwaron ƙarfin damtsen shi.
Wohoho! haƙiƙa "idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canza" kuma masu iya magana na cewa idan kaji ana ga ƙi gudu to sa gudu ne bai zo ba" faruwar hakan ke da wuya sai aljani Lattul-kifas ya gano lagon dakarun yazamana cewa duk wanda ya gabzawa naushi a wuya sai kaga ya karye jikake ruƙus ƙas! a wasu sai dai ka ga ya kama badakare ya yagashi gida biyu yana tamola da dasu,
Nan fa sassan jikkunan dakarun suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa, jini ya dinga kwaranya tamkar an ɓalle ƙorama, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ihu da kururuwar mazaje haɗi da ƙarar karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne,
Kaico! haƙiƙa a wannan rana waɗannan dakaru suna ganin tashin hankali gami da annobar mutuwa,
Kafin shuɗewar daƙiƙa ɗari biyu Lattul-kifas ya ragargazi dakarun baki ɗaya, Babu wani a cikin su da rage a ruhi a tare da shi.
Wani abu da ya bawa Lattul-kifas mamaki kuma ya ɗaure mashi kai shi ne yadda aka yi takobinshi a ɗazu taƙi yin tasiri akan dakarun, Bayan cewa komai ya sara da takobin koda ƙarfe take ya ke narkewa, Abin da bai sani ba shi ne sihirin dake jikin takobin ta shi ce ba zai yi tasiri a jikin dakarun ba,
Koda samun wannan gagarumar nasara sai kawai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta gami da sanya hannayenshi biyu yana dukan ƙirjinshi tare da yiwa kanshi kirari yana mai cewa.
"Sai ni GOBARAR DAJI maganin ƙananan hatsabibai.
"KAIFIN TAKOBI nake mai raba tsakanin masoya.
"KOGON ANNOBA nake MUTUWAR
SADAUKAI.
"Sai ni kangarau uban gagarau mai shayar da duniya GUGUWAR HALAKA.
"Na ci dubu sai ceto karo da ni dai-dai yake da buɗe taskar ANNOBA DARI.
Haka ya wanzu yana yiwa kan shi wannan kirari, bayan ya kammala ne ya ya lura cewa duhun dare ya fara bayyana a sararin samaniya domin haka sai ya yanke shawarar ya kwana a nan da safe sai ya shiga wannan gida, ko da kammala wannan shawara sai kawai ya shimfiɗe fuka-fukanshi ya bararraje ya fara sharar barci.
Wannan shi ne abin da ya faru da Sarkin matasan aljanu na baƙaƙen fata aljani Lattul-kifas, a kan hanyar shi ta farautar yaro usaiba mai hatimin takobin Saiful-zayyad.
**
Yalwataccen daji ne mai cike da tarin ni'ima, duwatsu, ƙoramu, da tarin dogayen bishiyu, wata irin ni'imtacciyar iska mai tattare da ni'ima ya kaɗai sassan tsirrai suna rangaji, waɗansu irin kyawawan tsuntsaye na shawagi a sararin samaniya suna fitar da wani irin sautin kuka mai daɗin saurare,
Komai ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a wannan waje dole ne yakasance cikin nishaɗi da annashiwa,
Amma abin mamaki sai ga shi wata halitta ta wanzu a wannan waje amma ta kasance cikin matuƙar baƙin ciki, bakomai ne zai tabbatar maka da hakan ba sai idan kayi arba da wani mutum bisa ƙarƙashin wata itaciya ya tafka uban tagumi hawaye na zuba daga idanuwanshi, ba wani ba ne wannan Mutum ba face Sadaukai Hukaiza shugaban rundunar sarki Lamsarul-Azla,
Ba wani abu ba ne ya sanya shi zubar da hawayen ba sai bisa tunanin irin baƙin zaluncin da sarki Lamsarul-Azlam yake yiwa al'umma, ya sanya shi kashe rayukan al'umma da ba su ji ba su gani ba,
Wani tunanin da ya faɗo masa shi ne shin yaushe ne zai cire zuri'ar su daga KANGIN BAUTA waɗanda suke a matsayin bayi a masarautar shi, ya zama wajibi a gare ka da ka kwashe iyalan ka domin ku tafi can wata nahiyar daban domin yin Sabuwar rayuwa,
Wata zuciyar kuma na cewa da shi kada ka manta da wasiyyar da mahaifinka ya yi maka inda yake cewa " ya ɗana kada ka taɓa cewa zaka yi gaggawa wajen ɗaukar fansa akan sarki Lamsarul-Azlam domin kuwa gaggawa aiki ne na da nasa ni ka riƙe haƙuri haƙiƙa nasara tana tafe a gare ka da zaka cika mani burina na cire zuri'ar mu daga BAUTAR MUTUWA a ƙarƙashin ikon sarki Lamsarul-Azla.
Ya yin da Hukaiza yazo nan a tunanin shi sai hawaye suka ci gaba da kwaranya daga idanuwanshi,
Wannan shi ne abin da ya faru ga Sadauki Ukaiza shugaban dakarun sarki Lamsarul-Azlam da ya tura domin farautar yaro usaiba mai hatimin takobin Saiful-zayyad.
Mu haɗu a TAFARKIN TSIRA 5 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
08137237071
TAFARKIN TSIRA 5
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Wthapp Number
08137237071
BABI NA TARA
Kamar yadda Jaruma Rusayyat ta faɗa haka al'amarin yakasance, domin kuwa mai gidan ta Fitinatul-Amir yana shiga izuwa cikin turakarshi sai ya ɓaje dukkan alƙalumman sihirin shi ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi akan yaro usaiba sai da ya shafe tsawon sa'o'i yana gudanar da bincike batare da ya samu nasarar gano komai ba,
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin shi kenan kuma ya fusata shi ainun, Babban abin da ya fi dugunzuma hankalin shi shi ne lokacin da ya haɗa idanu da yaro Usaiba sai ya ji zuciyar shi ta buga da ƙarfi ya kasa samun nutsuwa, anya kuwa ba shi ne yaron da nake farauta ba,
Nan fa ya sake zurfafa cikin Kogin tunani domin samun mafita, Tsawon daƙiƙa goma yana wannan nazari sai daga bisani ne ya samu mafita, Mafitar kuwa ita ce kawai ya duba gadon bayan Usaiba domin ya tabbatar da zargin shi,
Ko da samun kyakkyawar mafitar sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, kawai sai ya kishingiɗa domin ya huce gajiyar da ke tare da shi.
A ɓangaren Rusayyat kuwa lokacin da ta gudanar da binciken ta bisa halarar tsafin ta nan take ta gano cewa yaro Usaiba shi ne yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad da mai gidanta Sadauki Fitinatul-Amir ya ke farauta,
Sa'adda ta ga wannan al'amari sai hankalin ta ya dugunzuma ainun, Cikin hanzari ta sanya hannayen ta ta kware rigar dake jikin Usaiba tana duba gadon bayanshi nan take ta yi arba da hatimin takobin Saiful-zayyad,
Ko da ganin hakan sai hankalin ta ya dugunzuma ainun fiye da kowa ne lokaci bakomai ne ya dugunzuma hankalin ta ba sai domin ta tabbatar da cewa matuƙar mai gidanta Fitinatul-Amir ya gano cewa yaro Usaiba shi ne yaro mai hatimin takobin Saiful-zayyad tabbas sai ya yi yunƙurin hallaka shi kuma bata da ikon hana shi,
Nan take ta shiga tunani mai zurfi domin samun mafita, Bayan shuɗewar daƙiƙa ashirin ta samu mafitar, Sai dai mafitar na da matuƙar wahalar gaske abin da za ta yi shi ne dole ta ɗauko wani garin magani dake ajiye a turakar mai gidanta,
Garin magani na farko zata yi amfani da garin maganin wajen shafawa Usaiba a gadon bayanshi domin ɓatar da zanen hatimin takobin,
Garin magani na biyu kuwa shi ne zai bayyana zanen hatimin idan aka shafa shi,
Nan fa hankalin ta ya sake ɗugunzuma ta sake zurfafa cikin Kogin tunani domin samun hanyar da zata shiga turakar mai gidannata har ta ɗauko garin maganin cikin sirri ba tare da asirin ta ya tonu ba,
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin shugaban'yan fashin duniya Sadauki Fitinatul-Amir tare da uwargidanshi jaruma Rusayyat.
BABI NA GOMA
Dakaru ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi su kimanin ɗari biyu riƙe da miyagun makamai suna tafe cikin hanzari, kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci cewa sun kasance azzalumai n gaban kwatance, Abin da zai tabbatar maka da hakan shi ne idan ka yi duba da fuskokin su sai ka yi tsakanin basu taɓa dariya ba.
Kai tsaye kasuwar birnin suka durfafa wacce ta cika maƙil da jama'a, duk inda mai kallo ya kai duban shi babu abin da zai gani face masu siye da siyarwa na yi, Duk wajen da dakarun suka durfafa a cikin kasuwar sai dai ka ga jama'a na dare suna buɗe masu hanya tare da tattare kotsan su tamkar sun hango mutuwar su,
Haka dai dakarun suka ci gaba da kutsawa saƙo da lungu na kasuwar suna muzurai tamkar za su ci babu, Sai da suka shafe tsawon daƙiƙa hamsin suna tafiyar sannan suka iso wani ƙasaitaccen gida mai girma da faɗin gaske da aka yi ginin shi da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske, Ba tare da wani jinkiri ba wani garjejen ƙato daga cikin mayaƙan ya matsa daf da ƙofar ya ƙwanƙwasa har sau uku da ƙarfi.
Jim kaɗan da faruwar hakan sai ƙofar ta buɗe kwatsam! sai ga wani dattijo ma'abocin cikar kamala ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da wata jakar fata, Sannu a hankali har iso izuwa inda