Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 41816 words

Chapter 6 - AUREN ƘIYAYYA by Nana Khadii Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

534

Ads at the middle of Article

da nunfashin mutum saka makon mugun bugawar da zuciyarta tayi ta tsorata ne shine ya haifar mata wannan abun amma bbu komai insha Allah zamuyita mata alluran bacci har tadawo hayyacinta.






Da gudu ya faɗo cikin gidan har matan dasuka zo ta'aziya sanda suka tsorata ganin yaddah yashigo a firgice,Anty Nusaiba ce tamiƙe cikin zafin rai tafara Magana "baka da hankali ne zaka shigo gida haka daga gadi lalle kasamu guri,haki yakeyi sosai ga zufa ya wanke shi kaman anjikasa da ruwa guri yane ma ya zauna yanata hakkinsa,da kyar yayi controlling kansa ya kalla Ammih yace "gawar ta tashi wlh fatalwu wa ta miƙe wlh fatal wace yau nagani da idona,cikin ɓacin rai Anty Nusaiba ta daka masa tsawa tana faɗin ashe mahaukaci ne kai bamu sani ba tashi kabar nan dan kana buƙatar addua naga mutuwar kaman tamafi taɓaka fiye da kowa,duk harga gin da take masa baiko kulata ba dan shi yasan abunda yagani, masu ta'aziya kam sai tausayin sa akayi daga gani sun shaƙu ne kowa sanda ya tausaya masa agun.






Still motan kai gawan Salkhan yashiga zuwa gida daga shi sai boxers da vest kasa shiga yayi saboda mata ne acikin gidan,da kyar ya tura ƙofa kansa a ƙasa ya kutsa zuwa Parlour inda Ammih ke zauna ya tsuguna saide yakasa cewa komai duk matan dake gun da mamaki suka zuba masa ido duk sai yaji bai sake ba,cikin ƙarfin hali yace yana son ganin Ammih da kyar ta iya miƙewa sbd yadda zuciyarta ke ciwon dan yadda Dr yabata mgani bata ma ko tuna dashi ba bare tasha, gefe suka koma sunkuyar da kansa yayi ƙasa,da kallo Ammih tabisa saide bata ce komai ba,ɗagowa yayi ya kalleta yace "Ammih Nanah fa bata rasu ba tafarka tana asibiti Dr yace dogon suma tayi,zaro ido Ammih tayi tana faɗin "ban gane ba kana nufin Nanah na bata rasu, kodai mafarki nakeyi kokuma kaima dai ka tabune, kallonta yayi yace Ammih yanzu haka daga asibiti nake muje kigani da idon ki,wani tsalle tayi ta rungume Salkhan tana faɗin "Alhamdulillah ashe Nanah na bata tafi tabarni ba muje ka kaini na ganta,kafin yayi wani mgna tuni tafita Parlour tana ihu tana faɗin "jama'a Nanah na bata rasu ba wlh tana asibiti,da ido duk suka bita nan mai gadi ya miƙe yana faɗin "kunji ko ba ƙarya nayi ba ai na faɗa muku kikace bani da hankali,kafin kace wani abu garin kano ya gauraye da lbrin gawa ta tashi haka gidan rasuwa tuni ya rikice,masu kukan farin ciki nayi masu murna nayi.






Anty Nusaiba ce ta haura sama ta ɗakko hijab da car key dinta ta sakko dama Ammih da hijab ɗinta ajikinta suka kama hanya zuwa asibiti.




Ɓangaren Nanah kam baccinta takeyi bata ma san inda takeba Ammih da Anty Nusaiba suna shiga,office din Dr suka wuce ko knocking basuyi ba suka kutsa,shima bai damuba dan yasan halin da suke ciki, agigice Ammih ta ƙarasa tana faɗin ward nawa take Dr ka faɗa mun naganta, murmushi yayi yana faɗin calm down muje na raka ki Hajiya kafin yayi shiru Ammih takai bakin ƙofa Anty Nusaiba na biye da ita.






Room 8 yakai su tana kwance da oxygen abakinta tana bacci lakadan,wani kuka Ammih ta fashe dashi da bata san na meye ba ta ƙarasa ta riƙe hannunta tana kuka mai tsuma zuciya tajima agun kafin Anty Nusaiba ta ɗagata itama tana share nata hawayen ganin yaddah Nanah takoma kaman tsinke tsabar ramar datayi ne yasa sanda cikinta ya nuna,nanfa zuciyan Ammih yakama ciwo sosai agun ta zube da gudu Anty Nusaiba tafita kiran Dr itama admitting dinta Dr yayi.






One week later,Anty Nusaiba da Salkhan suke lura da Ammih da Nanah,Ammih taji sauƙi sosai Alhamdulillah nan suka dakkufa lura da Nanah har roƙon Allah Ammih tasa akeyi mata dan Dr yace so yake tasamu like one month tana hutawa, kuma Dr yasanar ma da su Ammih cewa bbu abinda yasa mu cikin datake ɗauke dashi lfyn sa ƙlau bbu abinda ya same shi bbu wanda baiyi mmki ba,lalle bbu mai wannan iko sai Allah haƙiƙa idan kana jin wani abu sai kazata ƙaryane kuma yafarune a hakikanin gsky.......






Ɓagaren Maina kam yaci alwashi ko menene yau sai yaje ya duba Nanah siyayyah sosai yayi cikin booth ya kama hanyan asibitin,da tambaya aka raka sa har ɗakin da Nanah take Ammih na waje tana sallah Anty Nusaiba taje gida bbu kowa a ɗakin sai Nanah dake baccinta hankali kwance,sallama yayi bbu kowa ledojin hanunsa ya ƙarasa inda take hanunsa yasa ya riƙe nata yana ƙare mata kallo turo ƙofan da akayi ne nasa shi daga ido nan suka haɗa ido da Ammih da Salkhan dake biye da ita zaro ido yayi ya miƙe........








*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝




*Nanah khadii* 💅🏽🛍️






*08069224458*
[8/28, 1:12 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥








*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚


*A short story* 💋






*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️








*Marubuciyar👇🏽*






*Cousins ne*


*Aruwan sama* *kaddara tasame*


*Almajiri ko attajiri*


*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽




*Auren kiyayya*








🅿️2️⃣2️⃣🔁2️⃣3️⃣










*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lot to me* 💝💖










*Bismillahir rahmanin* *Raheem*






Baki buɗe Ammih kebin sa da kallo,cikin zafin nama Salkhan ya ƙarasa zuwa inda Maina ke tsaye,Maina duk ya razana jiran mezai faruwa kawai yakeyi.




Salkhan na ƙarasa wa gun ya kai masa mari,a tsawa ce yace "bayan ka kashe mata auren kasata cikin damuwa kuma still har kana right din daza ka shigo ka riƙe mata hannu, "oh! Sorry namanta kazo duba babyn ka ko?


Duk rashin kunyar Mainah,kasa mgna yayi kansa aƙasa,Ammih kasa fahimtar me Salkhan yake faɗa tayi,ƙara sowa tayi cikin tashin hankali tana faɗin "wai meyake faruwane? Idon Salkhan da sukayi ja kaman gaushi ya ɗago ya kalleta yana faɗin....




"Ammih wannan shine baban babyn da Nanah zata haifa, kafin yayi wani mgna Ammih ta sake salati tanafa faɗin, "Mainah ashe baka rabu da Nanah ba? "Kaga halin da ta shiga sbd kai ko kuma baka rabu da ita duk da hka kasake biyota sbd rashin mutunci harda riƙe hannunta,wannan abu dame yayi kama wuce kafita Allah ya isah tsakani na dakai ka ɓata mun rayuwar ƴa, tana kaiwa nan ta fashe da kuka mai ratsa zuciya.....




Kaman muna fiki ba tare da yace komai ba yabi ta gefen Salkhan ya fice a asibitin ransa a mugun ɓace to the extent da baisan tukun da yake ba,shi dai yabuɗe ido yagansa a asibiti ne kawai......






Ammih kuka takeyi sosai mai cin zuciya agun ta zube tana kukanta, Salkhan ganin ba iya rarrashin ta zaiyiba kawai yasa ƙafa ya fice a asibitin.......




Nanah nasamun kula sosai gun Ammih da Drs dan har roƙon Allah tasa ake tayata sosai,kuma cikin ikon Allah tana samun sauƙi sosai.






Wasa² yau kwannan Salkhan huɗu rabon sa da asibiti kuma Ammih nakiran wayan sam baya tafi a switch off yake abu duk yada mi Ammih sam bata cikin hayyacinta.








Yau watan su Ammih ɗaya a asibiti kuma yau Dr yayi sallama dan Nanah taji sauƙi garau bbu wani abu dake damunta.




Haɗa kayan su sukayi bayan Ammih ta clearing bill dinsu driver yazo zai kaisu gida har sun kama hanya, kaman daga sama Nanah taji Ammih na faɗin "gidan salkhan zaka kaimu zaro ido Nanah tayi tana faɗin "Ammih muyi me kuma? "Ubanki zamuyi acan uwar mgna da tambaya,jin haka yasa Nanah yin shiru ba tasake mgna ba har suka isa....








Saide gate din a rufe da key amma daga alama ƙofar ana shiga Ammih da kanta bbu mgna ta sauka, knocking tafarayi saide shiru kuma sake bugawa tayi still bbu mosti ganin haka tasa ta juya tafara barin gun sai kuma taji an buɗe ƙofan,juyowa tayi sukayi ido biyu da gateman din har ƙasa ya tsuguna ya gaida ta,ta ansa nan take tambayansa Salkhan,shiru yayi kaman mai nazari kafin yace, ya koma Abuja da aikin sa lst week yanzu weekend yake zuwa.






Zaro ido Ammih tayi cikin jimami da farga ba tace masa "tom idan ya dawo kace mishi dan Allah ina neman sa naci albarkacin iyayen sa yazo ingansa,tana faɗin hka ta wuce motan tana share hawaye.






Jikin ta asanyaye tashi ga motan suka kama hanya kallo ɗaya Nanah tayi mata ta juya kai zuwa window har suka isa gida bbu mai mgna a motan..








Haka rayuwa taci gaba Maina ya ɗanji sauƙi sbd yajijji ciwo sosai anata cinyan sa, Salkhan kuma ko waigo su baiyi ba tun ranar,Nanah kuma ciki sai girma yake abin du niya duk ya dameta kullun ta zauna kallon cikinta take tana hawaye tana tausa ya wa abunda zata haifa sbd ita kanta bata san cikin wa take ɗauke dashi ba yanzu, Salkhan ne ko Mainah duk ta lalace tayi wani iri sai cikin jikinta da yayi girma masha Allah kaman ma zai jata,duk faɗan da Ammih ke mata na daina kuka da tunanin nan abanza daga ta buya sai kuka.








8months later Nanah ce a labor room tanata fama dan tun dare take labor gashi yanzu kusan asuba duk ta gala baita ta fita a hayyacinta,"innalillahi wa'innah ilaihinji'un wayyo kute makeni zan mutu, "sorry dear insha Allah bazaki mutu ba Allah zai rabaku lfy,gyara ta Dr yayi ganin yanzu kam abun da gske ne wani nishi tayi tana faɗin "wayyo Allah Ammih zan mutu cikin ikon Allah kuwa saiga baby da ihu nan da nan aka shirya babyn,itama aka shirya ta duk da bata cikin hayyacinta sosai bai hanata cewa Dr she wants to see the baby ba, murmushi Dr yayi yace nurse din amiko mata babyn,nurse kam da saurin ta ta ƙarasa tana nuna mata babyn aiko jitayi zuciyarta ta wani buga ganin kaman babyn.........






Ɓangaren Ammih kam sai up and down take tana duk adduan daya zo bakinta tana faɗin Allah ya raba lfy,duk bata cikin hayyacinta damuwarta taga an fito dasu lfy........




*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝




*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️






*08069224458*
[8/28, 1:13 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥








*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚


*A short story* 💋






*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️








*Marubuciyar👇🏽*






*Cousins ne*


*Aruwan sama* *kaddara tasame*


*Almajiri ko attajiri*


*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽




*Auren kiyayya*








🅿️2️⃣4️⃣🔁2️⃣5️⃣










*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lot to me* 💝💖










*Bismillahir rahmanin* *Raheem*








*_Idan kinsan bazaki_ _mun comments ba sticker zaki turo pls ki riƙe sticker dinki_ _nagode_*🥰🥰😘














"Congratulations it's a baby girl,cewar nurse din.


Murmushi kawai tayi ayayin da wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga idonta,jikin nurse din ta ɗaura mata bayan,aiko rungumeta tayi bata san tym din da hawaye suka cigaba da zuba a idonta ba,ga wani jin son yar data keyi yana ratsa zuciyanta,kiss tamata agoshi tana faɗin,"Alhamdulillah welcome to the world swthrt,karban babyn nurse tayi aka fita dasu da sauri Ammih ta ƙaraso tana miƙa hannun ta karɓa babyn, bata san tym ɗin da idonta ya cicciko tana faɗin"Alhamdulillah Allah nagode nurse me muka Samu?? Murmushi nurse din tayi tana faɗin baby girl,"shikenan bbu wani garda ma ƴa kam ta Salkhan ce,kanta Ammih tabuɗe ko kwayar gashi bbu yanda ake haifan yaran turawa haka ƴar nan tafito,idan ba ance ba baza kace uwarta baƙa bace.




Ɗakin suka wuce Ammih na rungume da babyn suka shiga,nan suka gaggyara Nanah aka ɗaura mata drip suka fita,yayin da bacci yayi gaba da Nanah.




Ammih na riƙe da babyn ta miƙe zuwa office din Dr da sallama tashi ga yana rubutu ganin Ammih yasa shi ajiye file din da biro ya ɗago,kujera ya nuna mata ta zauna shirune ya ɗan biyo baya kafin tace "dama dan Allah huɗuba zaka temake ni kayi ma yarinyar nan,ɗagowa yayi ya kalleta baice komai ba ya miƙa hannu yakarbe ta,kallon Ammih yayi yace"da wani suna??shiru tayi kaman mai nazari kafin tace "Sofia sunan Maman baban ta knan dashi zaka matabbu ɓata lokaci yayi mata huɗu ba,Ammih ta ƙarbe ta suka koma ɗakin,Nanah kama baccin take sosai harda mun shari,haka yasa Ammih kiran ƙawarta kuma aminiyarta wato sa'ade takira akan tazo ta zauna da Nanah zata je gida ɗakko abun da suke bukata,batafi 30mins ba ko ta iso.


Daga Nanah har babyn bccin su suke tsakanin su da Allah,har Ammih taje ta dawo sai wajen magrib Ammih na sallah,babyn tafara kuka Nanah da takeji kaman a mafarki saide kukan gaba yakeyi, afirgice ta mike tana rarraba ido ƙokarin miƙewa tayi da kyar ta ƙarasa gun dan ancire mata drip din ta ciro babyn datake kuka sosai.


Rasa yazata yi da ita tayi kuma sai ta tsaya tana kallon yadda babyn ke kuka,Ammih na idar da sallah tafara mata faɗa "to kin tsaya kina kallonta baki iya rarrashi bane? Hannu tasa ta ƙarbe ta Nanah kuma takoma gadonta ta zauna dan yunwa takeji,Kaman yadda musulunci ya tanadar zam zam da dabino aka bata ta tasha ta koma bacci,nan Ammih ta kwantar da ita ta dama tea taba Nanah ko tass ta shanye ita ta koma baccin.....






Sai wajen ƙarfe 10 kukan babyn ya sake gau raye ɗakin dai² Ammih na zaune tana cin abincin da Anty Nusaiba ta kawo dan bata jima da tafiya ba,da sauri Ammih ta mike ta ɗauko ta tasata a jikinta saide kukanta take tsakani da Allah,hakan yasa Ammih tashin Nanah ta miƙa mata babyn,zaro ido waje tayi tana faɗin "Ammih mekuma zan mata? Kallonta Ammih tayi tace "mekika ga yadace ki mata koba nono zaki bata ba? Ji tayi zuciyarta ta buga ita fa tun rayuwar ta idan taga ana bada nono cewa take bazata iya ba,haka kawai ita sam shayarwa ma baya tsarin rayuwarta,ganin bata da niyan yin komai ne ga babyn sai kuka take yasa Ammih daka mata tsawa tana faɗin "wai kallonta nace kiyi ne?




"Ni Ammih da dai madara aka bata ni bada nonon nan sam wlh ban so, Ammih bata san tym ɗin data cire hannunta a abinci ba ta miƙe zuwa bakin gadon, "dan ubanki keda madarar na reneki kika girma? Bazaki bata ba amma zaki bawa wasu ƙartai daba muharra manki ba awaje suyi yadda suke so ko??


Jin mgnar Ammih yasata bata san tym ɗin da hawaye ya fara zuba a idonta ba,tuni ta ɗaga riga tama fara ɗaga rigar nan tweens dinta da suka cika suka tsattsaya suka bayyana,rasa ta inama zata sa ta tayi nan Ammih ta matso ta gyarata aiko tuni ta karɓa tafara sucking da ƙarfinta take ja Nanah har ranta takeji saide bbu yadda zatayi tunda ta fara sucking Nanah ke kuka harta gaji sa tasake tayi bacci,Ammih ta ƙarbe ta ta maidata gun baccin ta ta zubama Nanah tuwo shinkafa miyan ɗayar kubewa,da kyar Nanah ta iya cin loma uku sbd mgnar da Ammih ta faɗa mata yayi mata ciwo sosai...








Washe gari da safe aka discharging dinsu suka tafi gida,Ammih tasa aka ɗaura ruwan wanka tafara yima babyn kafin tayima Nanah da duk jikinta yake asanyaye,nan aka fara shirin suna sosai sai ana gobe suna Ammih tasanar mata sunan babyn,taji daɗi sosai nan tace ma Ammih dan Allah tana so akirata da (Noor) idan bbu damuwa "bbu komai Allah yakaimu.




Duk abun duniya ya dami Ammih duk yadda takeso tasamu taga Salkhan ko sakonta ya isar masa abu ya gagara gidan ma ya sallami mai gadin yanzu bako wani weekend ma yake zuwa ba sai ya bushi iska,haka ta hkra.




Ana gobe sunan Anty Nusaiba da yaranta suka iso gidan ranar Nanah taji daɗin ganinta sosai dan ta ɗauke mata kewa sosai,saide abu ɗaya ke damun ta tsotson Noor yayi yawa ko da tawa Anty Nusaiba complain hkri kawai ta bata tace kowani baby da yana yin cinsa.




Washe gari da asuba ka rada ma yarinya suna Sofia wace za'a dinga kira (Noor) tunda aka ce an raɗa suna babyn na hanunta tayi kyau sosai cikin set of lemon green tana bata nono kawai ta fashe da kuka,tana kallon babyn yadda take sucking hankalinta kwance idan ta tuna da abubuwan da suka faru sai tausayin babyn ya kamata,sosai take kukanta Anty Nusaiba ce tashigo tana ansa waya ganin kukan da takeyi yasata katse wayan ta ƙarasa inda take tana faɗin "subhanallahi meyafaru kuma me jego da kuka hanu tasa ta karɓa Noor dabata ƙoshi ba itama kukan tasa alamun bata ƙoshi ba,mayar da ita gun uwarta tayi tana faɗin "to acici mala'ikun tauna karɓan ta tayi saide kin mayar da ita tayi kawai ta rungumeta taciga ba da kukanta,guri Anty Nusaiba tana faɗin "Nanah Khadija me babban suna yada ɓacin rai kuma ranar farin ciki? Ɗago kanta tayi ta kalla Anty Nusaiba tace "Anty Nusaiba wlh inajin tausayin yarinyar nan inajin tausayin yadda zata taso tana kaiwa nan tafashe sosai da kuka mai ratsa zuciyan duk mai sauraro,jikin Anty Nusaiba sanyi yayi tasan akwai pains a abun saide daurewa tayi tace "mezai faruwa da ita Nanah gaki ga Ammih gamu muma insha Allah Noor bazata to zarta ba zata taso cikin gata da kulawa kaman ko wani ɗa, maganganun Anty Nusaiba sosai yasa taɗan ji sanyi tayi shiru.


Yan uwa da abokan arziƙi duk sun taru a sunan Ammih kwati biyar tayi uku na Noor biyu na Nanah kayan kam sai Masha Allah kowa na walwala banda Nanah data rasa meke damunta....




Life goes on haka rayuwa taci gaba Nanah bata ko fita kullun tana gida ko abu takeso saide Ammih da kanta tafita ko ta aika driver ya sayo mata Noor kam masha Allah tayi kiba kumatun nan na yaran turawa kaman zai zubo gashin kan sul sul yaso ma fita brown dashi ko makiyinta ya kalleta sai yasake kallonta,saide tana damun Nanah da tsotso kaman me har takai Nanah na bata rabo da abinci agefenta,dan ma tym to tym idan ba Ammih agun saita bata ruwa tayita rarrashin ta harta hkra takoma baccin......




Wasa² fa bbu ɗuriyar Salkhan bbu ɗuriyar Mainah akwana atashi yau watan Noor 8 harda yan hakorinta guda biyu tayi kyau sosai idan kashi go gidan ma kaganta zaka zaci mamanta da babanta turawa ne dan bbu wani abu data ɗakko na bakkin fata, gashinta akwance har gashi ga blue eyes datake da ga hanci yarinyar ta haɗu masha Allah abinda nima Nanahkhadii nace knan,Nanah ce zaune ta idar da sallah Noor

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads