Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 41816 words

Chapter 10 - AUREN ƘIYAYYA by Nana Khadii Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

543

Ads at the middle of Article

yasha fa a iya wayanda suka sani ma knan bare kuma munje ɗaukan fansa ya bazu a duniya ni ƴata kawai nake tausaya wa yanzu, shi kansa mgnar sosai ta taɓa zuciyar sa basar kawai yayi yana faɗin,
"Karki damu insha Allah tunda har kin gane kin tubawa Allah bazaiyi nasara akanki ba kuma zanyi tunani naga ta ina zamu ɓulowa wannan abun,and promise me bazaki faɗa ma Ammih ba kinga bata da lafiya sbd blood pressure din datake fama dashi bako mai zamuke faɗa mata ba ko? Kai kawai ta ɗaga masa yaja motan suka bar gun.


"Koda suka isa gida bai shiga da motan sa,karban Noor yayi suka shigo dai² Ammih ta fito daga kitchen tanayi ma Hajara me aikin faɗa,saide ganin face ɗin Nanah tuni yata ta ƙaraso tana faɗin "lfy meyafaru kuma? Kafin tayi mga tuni Salkhan ya karɓa da faɗin, "Ashe raguwa ce allura ne yasata kuka, murmushi Ammih tayi tana faɗin "tunda baki kukan allura sai yanzu da har haihuwa kinyi bansan shashan wlh, murmushi tayi ma Ammih tace zataje ta kwanta karɓan Noor tayi da mgnanin suka haura sama, Salkhan kuma ya wuce gun aikin sa.




"Wlh Nanah saina zama miki damuwa a rayuwarki dole ki aure ni muyi zama na Mata da miji mu zuba mugani,gida ya wuce direct ko sallama bbu yashigo,zaune take kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin damuwa duk tarame tayi wani iri, "sannu da dawo wa, "Sau nawa zance kidaina kulani shegiya mara zuciya wlh duk randa nagaji da ganinki da wannan tsinannan cikin dake jikinki saikin tafi gida,ba zumunci ba komeye zai lalace saide ya lalace mtssss!!yayi shigewar sa ɗaki agun ta zube tashiga rera kukanta kaman ranta zai fita.






Salkhan kam ko daya shiga office yakasa aikata komai sai up & down kawai yakeyi hankalin sa sam baya jikinsa.




Yau kwana uku knan dayin abunnan Nanah duk tayi wani iri Ammih duk tambayan da Ammih tayi mata sai tace mata bata jin daɗine,saide duk da hkan Ammih bata fasa yimata faɗa ba tare da nasiha wani zubin daga Ammih tagama yi mata faɗa ko nasiha sai tayi kuka iya ƙarfin ta tama Allah godiya tare da tsananin dana sanin abunda ta aikata.


Yau dai bbu laifi ta tashi a ɗan sake bbu yabo bbu fallasa dan yanzu Noor dinma ta rage rikicin sosai tafara sabawa,wayanta ne yayi ringing dake hanunta suna chatting da teemah da moon,ganin sunan Jamal yasa tafara tsilli tsilli da ido dan kwana biyu basu yi waya kuma tasan dole yau zaiyi mgnar alƙawarin su,har wayan ta tsinke bata ɗaga ba sake kira yayi yajima yana ringing kafin tayi wani nannau yan ajiyan zuciya tayi picking.


"Hlo love ykke?"wato kinji ni shirune shine ko kine meni anya kinaso na kuwa?rasa me zatace masa tayi ajiyan zuciya ta sauke tare da faɗin,
"Bani da lfy ne nima 2days but am so sorry, "what baki da lfy shine baki sanar dani ba gsky nayi fushi,kuma nadaina fushin at the same time tunda kin bada hkri, ya jikin naki kinje asibiti kona zo muje ya ƙare mgnan cikin nuna damuwa,
"Munje an bani mgni da sauƙi yanzu Alhamdulillah, "Allah yaƙara sauƙi bana gari but am on my way yanzu hka zanzo na duba ki.
"Ok thank you" shirune ya ɗan biyo baya kafin katse shirun ta hanyan faɗin, "tom karna dameki tunda baki da lfy ya alƙawarin mu kisan tym yayi har yaɗan wuce inajinki yanzu am all ears, ajiyan zuciya tayi tama rasa me zatace masa harga Allah batajin ƙin sa saide tana tsoron kar yazo yasan komai ya guje ta tana cikin tsaka mai wuya ganin bata niyan mgana ne yashi faɗi, "kona dameki ne and karki ɓoye mun idan har ranki ban miki ba karkisa ma kanki damuwa am a free man just tell me kinji ya ƙare mgnan da zolaya.


"Wani ajiyan zuciya tasake sauke wa tare da faɗin "um um um nace um eh i accept you,"Alhamdulillah Nanah am speechless kin sani farin cikin dana jima banyi irinsa ba Nanah wlh ban taɓa zaton zaki accepting dina ba,Insha Allah gobe zan shigo nagaida mmnmu idan nazo, "mamakin yadda ya gauraye da farin ciki takeyi jikinta asanyaye tace masa, "sai yazo sallama sukayi ya kashe wayansa.


Duk wayanda suke tafiya tare dashi sanda suka ga canji har hira yayi dasu mutumin da mgna idan ba wacce tazama dole ba baka isa kayi a gaban saba kallo ma kaɗai ya isheka.




Tana kashe wayan zuciyarta takasa sukuni gani take tajama kanta damuwa kodai takirasa tace masa aa ne,dan gani take daga yaji abunda yafaru zai gudu duk jikinta asanyaye ta ajiye wayan taja pillow ta kwanta,sai tunani kala² takeyi aranta,Daga ƙarshe ta mike zuwa ɗakin Ammih ta sanar mata Ammih tayi farin ciki sosai amma itama ta wani ɓan garen zuciyar tata bbu nutsuwa acikinta, "sai mu hana idon mu bacci mu kaima Allah kukan mu Allah ya wuce mana gaba, "tom Ammih"
"Ɗauki yarki kuyi gaba nima na huta tunɗa zu take kiran sunanki nayi kaman banji ba yanzu kina fita ba zama zatayi ba.


Washe gari Nanah tunda ta tashi jikin ta bbu ƙwari da kyar take komai take komai,cikin wata doguwar riga shadda milk colour ta musu anko ita da Noor yaji zubi banda na Noor dayake iya guiwa,da ƙaramin hannu sai sucks da cover shoe brown tasa mata ta kwatar da gashin kanta tayi kyau sosai,itama tayi kyau sosai koda yau har red lips tayi sosai tayi kyau hotuna tashiga watsa musu,sun yi kyau sosai wanda yafi kyau tasa a profile dinta,Kiran Jamal ne yashigo sanda tabari ya ɗanyi ringing kafin tayi picking,cikin farin ciki yake sanar mata after asr prayer zaizo insha Allah, "Allah ya kawo lfy abinda tace knan sun ɗan jima suna hira kafin sukayi sallama.


Wajen 4:30 ya iso yakirata yasa nar da ita,fitowa tayi a jiye Noor a ɗakin Ammih zata fita saide,tsala ihu Noor tayi tana kuka tana kiran sunanta har takai stairs kuma sai tsaya jin bazata iya tafiya tabarta ba yasata,koma wa ta ɗakko kota suka fito tunda ya hangu su yasake baki yana kallon su har suka isoh, murmushi ne ɗauke a face dinsa yana faɗin, "Masha Allah ashe ƴar tamu tafi Maman ta kyau gsky za'a bani kyautar ta Masha Allah balarabiya knan, murmushi Nanah tayi batare da tace komai ba hanu yamika ma Noor har Nanah zatace tana ƙiyuwa kuma sai tayi shiru,ga mmki kuwa yana miƙa mata hanu taje sama ya cillata yana faɗin i love children most especially daughters banida mace duka ukun are boys,murmushi tayi suka isa zuwa Parlour tamasa iso kiran Hajara me aiki tayi tasa ta kawo masa ruwa juice da snacks ta haura sama kiran Ammih.


Shigowan Salkhan knan ya hango motar sa ji yayi wani abu ya tsaya masa a zuciya, Parlour yanufo dan bai zaci yana Parlour ba yana shiga suka haɗa ido,wani abu ya haɗiye me ɗaci cikin ƙarfin hali ya ƙaraso suka gaisa cikin fara'a Noor ce tafara miƙa masa hanu yasa ya karɓe ta suka fice zuwa side dinsa,dai² da sakkowan Nanah tana murmushi tace masa Ammih nazuwa,kasa hkri tayi tana tambayan sa Noor kallonta yayi yace mata, "yayanki ya karɓe ta murmushi kawai tayi ta buɗe juice zuba masa ta koma gefe ta zauna.


Bbu jimawa Ammih ta sakko cikin shigarta ta manyan mata a mutunce,yana ganin Ammih ya sauka ƙasa ya zauna tana isowa yafara gaida ta Nanah kam gudu sama tayi tabarsu agun,nan yayi mata bayanin kansa family dinsu sanannu ne sbd zamanin mahaifin sa attajiri ne sosai yana da Mata biyu mahaifiyar Jamal itace amarya kuma Jamal shine danta nafari sunyi zama zaman da mahaifiyar Jamal ta wahala a hanun uwar gidanta da makirci wanda idan ba kasani ba kuma baza kace hkanba,sbd makirci irin na hajiya Rabi,sosai hajiya Dije ta wahala ahanunta.


Kuma yanemi izini kan cewa yana so yaturo mutanen sa ayi tambaya,idan ansa masa rana sbd shi ba yaudara yazo yiba tsaka ni da Allah yazo auren Nanah,sosai Ammih taji daɗi kuma tace bbu damuwa ai sanannu ne su insha Allah zaiji rana gun Nanah, 50k ya ajiye mata yafice yana fita yakira Nanah yace mata yana dayan Parlour din cikin sauri tafito karo sukayi da Salkhan da Noor a hanunsa dake wasanta,ganin Nanah kuwa yasata tafara miƙa mata hannu harta sa hanu zata ƙarbe ta amma ga mamaki saita ga Salkhan ya rungume Noor sun shige ciki ji tayi idonta sun cicciko amma saita matse ta shige.


Tana shiga tanemi guri can gefen sa ta zauna,kallonta yayi yana faɗin, "sannu sarauniyar kunya wato shine kika gudu kika barni nida mamah ko zan rama bari Allah ya kawo ranar da zan kaiki gun ummih na nima hkan zan miki, "murmushi tayi tace kaima kace naji kunya tom shikenan naji dama haka akeson mace ai.
"Dama kinada brother ne shiru tayi kafin da kyar tace, "masa aa cousin dina ne kuma shine daddyn Noor har ransa yaji kishi saide ya daure cikin tsoka na yace "ashe anan Noor tasamo kyau murmushi tayi batare da tace komai ba,hira suka ɗan taɓa kafin sukayi sallama yatafi,ta ɗan ji daɗin hira dashi sosai da fara'arta tashiga ta tarar da Ammih da Salkhan suna hira.
"Ammih ce takirata take sanar da ita yadda sukayi saide tace zata sa yayanta yayi bincike akan sa,kaman daga sama sukaji Salkhan na faɗin, "Soja ne kuma lieutenant colonel ne one star kuma one eagle shine fari gun mahaifiyarsa hajiya Dije yanada ƙanne huɗu uku maza ɗaya mace cikinsu akwai,Auwal,sadeeq,Abdul maleek da lst born dinsu Rahma kuma duk sunyi aure suna gari daban² macen kuma tana Spain da mijinta da ƴarsu ɗaya dukan su ma'aikatan government ne,ta ɗayar kishiyar kuma yaranta takwas biyar Mata uku maza matan duk suna aure ne suma gari daban² saide duk cikin Nigeria,mazan sauran suma ma'aikata government ne duk sunada Mata biyu na gari nan ɗayane yake kudu da matarsa da yaransa,iyayen su har yanzu suna gida ɗaya duk hidima tare yaran ke musu bbu banbanci barina tsaya anan na dawo kan Jamal,yana da Mata da yara uku duka maza sunan matarsa Hajiya Nabila kuma bata fiye zama a Nigeria ba shidai bayida da damuwa a iya bin cike na danayi,mutum ne shi me temakon talaka kuma bayida damuwa sam kowa faɗan kirkin sa yakeyi iya bincike na dai knan saide Ammih kisa aƙara bin cikawa zaman aure ba wasa ba,amma shikan mutum ne meyi nayi bin cike tun ranar daya fara zuwa gidannan,yana gama faɗin hka ya miƙe ya miƙama Ammih Noor yafice duk da mamaki sukabi sa da kallo.


Bbu wanda yasake mgna Nanah ta hau sama Ammih tafara kiran Brother dinta ta sanar masa da halin da ake ciki nan yasar mata da insha Allah gobe zai fara bin cike insha Allah.


3days ltr Brother din Ammih ne yazo har gida still yasake mai² ta mata cewa duk inda yayi sheda tagari ake basa,sosai Ammih taji daɗi saide basuyi saurin sanar dashi akan ya turoba sai da kusan bayan kwana 8, ranar da Nanah tasar dashi yayi murna sosai kuma yace Mata insha Allah jibi za'azo, Ammih na lura da Salkhan sosai ya rage shigowa sometimes ko Noor yake son gani zuwa yake ya ɗauke ta ba kaman da da suke hira ba duk ya canza sosai,Ammih ce takira sa tayi masa nasiha sosai tare da faɗa yaji daɗi sosai ranar har yaɗan sake.


Washe gari Jamal yakira wayan Nanah yake sanar mata cewa gobe zasu zo nan gidan su zasu ko akwai wasu dangin babanta da zasu kaiwa gaisuwar,ce masa tayi bari ta tambayi Ammih nan tasanar da Ammih tace nan zasu zo,saide ga mamakin ta yace shi gun dangin mahaifinta yakeso akai gausu wa ai mahaifin ta suna da main house,Nanah jin zancen sa sanda zuciyarta ta buga dan tasan komai dake ƙasa ce masa tayi tom bari tasa sake sanar da Ammih,jiki bbu ƙwari ta mayar ma da Ammih ita kanta ji tayi zuciyarta ta buga ta ina zata soma ita rabon ta dasu ai tamanta kuma yanzu meye abunyi daga dukan alamu wannan mutum yasan su sosai, "shikenan yau karya ta taƙare yanzu ya zanyi shiyasa akace dan gin uba sune akan gaba Ammih ranar har hawaye sanda tayi dan batasan ta ina zata fara ba lalle tana cikin wani hali.


Ranar ko abinci bata iya taci ba hankali ta da yayi dubu ya tashi wannan wani irin abune daga wannan damuwa ka koma wancan,cema Nanah tayi tace masa ya daga zuwan ya bari nanda 3days hkan ko akayi ta faɗa masa yace bbu damuwa.


Yaukam Ammih tunda ta tashi bbu sukuni hka ta shirya jiki a sanyaye tare da Nanah da Noor Salkhan ne yaja su zuwa main house,tunda ga shirgar su duk wanda sukayi karo dashi kallon tara saura quarter yake musu duk jikinsu bbu ƙwari duk wanda suka gani ahakan suke gaida shi wani ya ansa wani ya cilla musu harara ya wuce,ɗakin kakar su Nanah suka shiga,zaune take kan wata kujera Salkhan ne suna shiga yace, kaga tsohuwa mai ran ƙarfe nifa nagaji da jiran cin wainar sadaka sandar hanunta ta buga masa cikin wasa tana faɗin, "aini zan fara cin naka wato shekaran jiya kasa na ajiye maka dambu kaƙi dawowa ko?dariya yayi yace, "banaƙi dawowa bane aikine ya riƙe ni yanzu yana Ina? "Bansan shekiyan ci irin naka jiranka zaiyi bai lalace ba naba yara, "Wai ince ko sirikar tawa ka kawo mun ne?
"Aa me ran ƙarfe Nanace takwaraki fa baki ganeta ba? "Kasan sunada yawa wacce aciki cikin dariya yace, "tagun marigayi nawa jenki mana, "kaifa ka iya shekiyan ci mezai kawo wannan guna? "Wlh da gske ita da mamanta ga kishirya ki ma yana samata Noor a cinya koda ta kalla Noor saita ce masa Masha Allah ga tanan kaman su daya da mamanka,Ammih ce tafara gaida ta saide shiru bata ansa ba hka Nanah duk ƙin ansawa tayi,daga ƙarshe ma cewa tayi su tashi su fice mata a ɗaki,kuka sosai Nanah ta fashe dashi ta kama ƙafar kakarta saide jan karfat tayi ta dogara sandar ta zata miƙe, "kakah Dan Allah kiyi hkri neman yafiyarki suka zoyi, "wai guna lalle matar nan abunda tamun wata shariya sai a lahira tana kaiwa nan tafara tafiya,Ammih ce ta zube agun tafara magiya amma ko kulasu batayi ba ta wuce uwar ɗaki abunta.




*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝


*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️


*08069224458*
[9/3, 11:45 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥








*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚


*A short story* 💋






*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️








*Marubuciyar👇🏽*






*Cousins ne*


*Aruwan sama* *kaddara tasame*


*Almajiri ko attajiri*


*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽




*Auren kiyayya*








🅿️3️⃣8️⃣🔁3️⃣9️⃣


_Kuyi hkri nayi mistake mamah ashe tarasu,bagun ta sukaje ba gun kishiyarta knan zai zama hajiya surayyah wacce take kishiga ma Mamah yar uwa ga Alh Muhammad_ wato kakan su_ _Salkhan.fatan zaku fahimci mistake dina zan gyara komai_ _a page dinnan insha_ _Allah_ .😭😔










*Bismillahir rahmanin* *Raheem*






Salkhan duk sai yaji bbu daɗi ɗaki ɗaki yabi haj surayya yana faɗin hba tsohuwa mai ran ƙarfe ba'ayi hka ka kiyi hkri ki yafe masu mana,da kallo tabi shi tana faɗin, "baka san wahalar da yar uwata tasha gunta bane?mu muka san komai matar nan da bakin cikin wannan sirikata ta rasu,ko zan karɓe ta saina kira ƴaƴanta su Aisha naji ta bakin su sbd hka suje zasuji komai abakinka,da kuka ta fashe masa tana faɗin munyi zama na amana bata ɓoye mun bana ɓoye mata sbd hka saina tara yaran naji ta bakin su,bai musa mataba yoto shikenan hajiya mai ran ƙarfe jibi zanzo naji yadda kukayi ko nasan idan kikace musu dole subi abinda kika faɗa,kuma nasanki ai da halinki na kirkin nan ko kakarmu sanda ɗauka tana faɗin, "karka dameni da surutu sai kazo jibin, "to ga jikar taki baki samata albarka ba karɓan Noor tayi tasha kanta, "tace Allah ya albarkaci rayuwarki kuka take sonyi ganin hka yasa shi saurin karɓan Noor suka kama hanyan fita.


Batare da yace musu komai ba cewa kawai yayi sutafi bbu musu jikin su asan yaye suka fita tunda suka shiga motar bbu wanda ya iya mgna har suka isa sa gida.


Koda suka iso gida Salkhan masjeed ya wuce yayi sallah kafin ya shigo a Parlour ya tarar dasu duk sunyi jigum jigum,kusa da Ammih ya zauna cikin sanyin murya ya fara mgna, "Ammih nasan zakiyi mmki dakika ji ina zuwa gidanko? "Kiyi hkri karki ga ko kaman nazame kaina ne nake zuwa, "daka tar dashi Ammih tana faɗin, "ba saika yimin bayanin komai ba tunda gashi zuwan naka yamana anfani dan badan albarkacin ka ba yau bansan wani wulaƙan ci zamu fuskanta ba,banga laifin haj surayya ba komai tayi mana sbd sunyi zama na amana da kakarku kansu a haɗe yake,bbu wanda yakejin tsakanin su hkan harya sa dangin kakanku suka tsane su kuma haj surayya tasan sirrin mama Dije sosai shiyasa ma ban je gun kowace ba sai ita nasan su,Anty Fatima zasu fi jin mgnarta sosai fiye da kowa,haƙiƙa nayi baban kuskure a rayuwa ta wanda sai yanzu suke tambaya ta muna musguna wa iyayen miji,muna manta wa dasu suka haifi yaransu suka raine su mukuma sbd son zuciya muzo mura basu da ƴaƴan su haƙiƙa abun akwai ciwo,dangi miji mun maida su banza basu da mutunci a idonmu wani sa'in ma gara mana kishiya dasu wa'iyazubillah hkan baban kuskure ne, kuma sune gatan ƴaƴan mu tunda dangin uwa basuda ƙarfin aurar da ƴaƴa saide dangin uba,gsky ina kira da yan uwana mata mugyara ko anan musan dangin miji sune gatan ƴaƴan mu,dan Allah mugyara halayen mu mudinga tuna wa abinda mukayi shi za'ayi mana tana kaiwa nan ta fashe da kuka mai cin zuciya,rarrashin ta Salkhan da Nanah suka shigayi dakyar tayi shiru.


Bbu wanda yake da sukuni cikin kwana biyu nan Salkhan ne keta sintiri zuwa gidan Kakar tasu da zuwa gidan yayun baban sa saide abu acitura sam sunce sufa sun yafe su,gashi Jamal ya matsa duk hankalin su atashe yake kallo ɗaya zaka musu kasan basu cikin kwanciyar hankali,wasa² abu harya kusa sati shiru bbu wani lbri Ammih ce tace Salkhan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads