Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 41816 words

Chapter 7 - AUREN ƘIYAYYA by Nana Khadii Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

538

Ads at the middle of Article

ta rarrafo zuwa gunta tana ɗaga mata hijab ko kallonta batayi ba taci gaba da adduanta,ganin uwar bata da niyan kulata yasata kuka tana sake jan hijab din, hanunta ta ɗaga ta mareta ta tureta gefe tana faɗin "shikenan ni dan na haihu nono na bazai huta ba nima bazan huta,kuka sosai Noor ta fashe dashi ta rarrafa tana so yafita amma ƙofan arufe,kwanciya tayi kasan gun taci gaba da kukanta dan bata kuka sam bazakce da yarinya agidan ba,ganin yadda take kuka kaman zata shiɗe yasata miƙewa jikinta asanyaye ta ƙarasa gun tasa hannu ta ɗauke ta, koda taga itace kanta ta kwantar ajikin ta tana kuka bayan ta take shafawa harta ƙarasa bakin gado,taciro ta miƙa mata saide sam taƙi karɓa kuka takeyi sosai nan hankalin Nanah ya tashi tasan bata kyauta ba,tunda abincinta ne agunta da kyar ta rarrasheta ta karɓa duk saitaji wani iri kuma,koda tagama wasa tashi ga yi mata rana nafarko knan data tage tana wasa da ita,sosai take kyalkyala dariya wayanta taciro ta mata video ta musu hotuna ta mayar,dan yanzu wayan ma sam baya gabanta,haka tayi ta mata wasa har bacci ya ɗauke su agun.......








Yau shekaran Noor ɗaya da wata uku bbu inda bata zuwa da ƙafarta Nanah taso yayeta Ammih tace sai ta shekara ɗaya da wata 8 sosai Nanah taji haushin abun saide bbu yanda zata yi,zaune take a ɗakinta Noor tayi bacci ajikinta bata san meyasa ba yau tunda ta tashi take tunanin Maina num dinsa tayi searching saide takasa dialling ta kashe ta ajiye,still jikinta bai bata ba tasa sake dakkowa tayi dialling har ya kusa tsinkewa akayi picking,saide muryan mace taji jitayi zuciyarta ta buga ƙarfin hali tayi tace "assalamu alaikum "wa'alaiki sallam wake mgna dan Allah?cikin ƙarfin hali "tace dan Allah inaso nayi mgna da Maina ne,Ayyah ya fita school ya manta da wayan ne saide ki kirasa ta ɗayan number sa, "ok tom nagode saide idan bazaki damu ba dan Allah dawa nake mgna? Murmushi tayi tace matarsa ce,Nanah bata gama sauraron ta ba ta kashe wayanta ta ajiye Noor tashi toilet ta soma rera kukanta,ashe karya yake yi dama ba auren nawa zaiyi ba ashe yaudara ta yayi ashe macucine bayida Amana nikam nashiga uku wannan wace irin rayuwa nake ciki tajima tana kukanta agun kafin ta wanke face dinta ta fita ta kwanta agun bacci yayi gaba da ita da tunani kala².




A month later saide shiru bbu ko ɗuriyar Mainah bbu lbrinsa zaune take a parlor tana ba feeding Noor datake ta mata rikici tasha ta sake taciga ba da kukanta har tayi zuciya tace tinda bazata sha ba bari ta mayar da kayanta saide kuma ta dameta da kuka sosai,hakan yasa ta dakko ta ta dubgure mata kai tana faɗin idan zaki sha kisha idan bazaki shaba wlh lst tym da zan baki knan haba kibarni da damuwar da ke damun na,tasata aiko ta karɓa ta fara sha,kaman daga sama taji muryan dako a mafarki tasan me ita muryar da harta koma ga Allah bazata manta da ita ba da ƙamshin turaren da ko bacci taji saita farka,kasa ansawa tayi har ya shigo inda suke batako iya ansa sallaman sa ba haka bata ko ɗaga ido ta kallesa ba ji tayi zuciyarta ta wani bala'in bugawa miƙewa tayi ta cire Noor a nono ta ajiye ta agun ta yi hanyan sama da gudu tana share hawayen dake ƙokarin zubo mata,da ido yabita da kallo yana mamaki kukan da Noor keyine ya dawo dashi hayyacin sa koda ya ɗaga ido ya kalleta ji yayi zuciyan sa ta daina harbawa cak ta tsaya yana kallon Noor dake kuka tana bin Nanah tana blabbing.....




*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝


*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️




*08069224458*
[8/28, 1:13 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥








*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚


*A short story* 💋






*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️








*Marubuciyar👇🏽*






*Cousins ne*


*Aruwan sama* *kaddara tasame*


*Almajiri ko attajiri*


*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽




*Auren kiyayya*








🅿️2️⃣6️⃣🔁2️⃣7️⃣










*Bismillahir rahmanin* *Raheem*










"Kallon Noor yakeyi harta kai stairs ta fara hawa, kuma sai taja ta tsaya dan dama haka takayi idan a sama ne ko ƙasa zatayi ta yawonta,amma daga tafara hawa stairs sai taja ta tsaya har masu aikin gidan sun san halinta ne,saide a ƙarasa da ita.




"Cigabawa tayi da kukanta tsakanin da Allah,sai kuma tym ɗin ya dawo daga tunanin daya keyi,yabi bayanta yasa hannu ya ɗagata ganin bata san shiba yasata sake tsalla ihu,dai² da gangaro wan Ammih dan taji kukan yayi yawa kuma tana ta kiran Nanah shiru.


Baki buɗe Ammih kebin sa da kallo,Noor kam tunda taga Ammih take miƙa mata hannu,jikin Ammih a sanyaye ta karɓa Noor kafin tayi shiru,shikan sa kallon da Ammih ke masa sanda yaji wani iri,ba tare da tace masa komai ba ta juya ta haura sama,jikin sa a sanyaye yabi bayanta ɗakin Nanah tashi shiga,tana faɗin ina kika shiga?" kina ji yarinya sai kuka take kaman bbu kowa a gidan,Nanah kwance take a kan gado tana rusar kukanta mai ɗaci a zuciya,bata ko ɗago ba Ammih ta ƙarasa ta ɗaka mata duka tana faɗin,"idonki biyu nafaɗa miki ki dai na barinta tana wannan kuka mara anfani,miƙe wa Nanah tayi tana share hawayen idonta saide duk yadda taso ta boye ya gagara sbd jan da idonta suka yi,miƙa mata Noor Ammih tayi ta ƙarɓe ta saide koda ta ƙarbe ta,kallon mahaifinta kawai take mata tama kasa ko rarrashin ta kallonta kawai takeyi hawaye na zuba a idonta.




"Wai meye kike kukane?mutuwa akayi miki ne ko yaya? "Kibata Nono saiki kici gaba da kukun da ba zai anfane ki da komai ba,Ammih nakai wa nan ta juya zata fita Salkhan na tsaye ƙofar ɗakin saide ko nuna tasan yana gun bata yi ba zata wuce sa.




"Tsugunawa yayi dai² ƙafarta yana faɗin "ina wuni Ammih? Ko kallon sa batayi ba zata wuce sa,kaman daga sama taji yana faɗin"Ammih nasan nayi laifi kiyi hkri na dawo Ammih bazan sake tafiya nabar ku ba,cak ta tsaya ta juyo tana kallonsa, "Salkhan bbu abinda zan ce maka sai sai ka nuna min ni ba uwarka bace,mena maka Salkhan a rayuwa sako mun ƴa da cikinka a jikinta kace bana ka bane ka barni bani da lfy har gidan ka naje sai labari naji na kabar aiki a garinnan,haba Salkhan meyayi zafi haka gashi Nanah ta haihu ƴa tafito dangi mahaifiyar ka sak,to ko bamu ci arziƙin komai ba yanzu maci arziƙin yar ka kuma takwarar mahaifiyar ka ko?? Tana kaiwa nan tafashe da kuka mai ratsa zuciya guri tane ma ta zauna aƙasa tana faɗin,"ko dayake Salkhan baka da laifi kome kayi dai² ne duk halin da kuka shiga kai da Nanah nice sanadi, "naso kaina naso zuciya nasan bakwa son junan ku na saku Auren ƙiyayya gashi ya haifa mun ɗa mara ido,"dama inata roƙon Allah kafin na kwanta dama na nasaka a ido na nemi alfarman yafiya agunka,Nanah data zubo musu ido tanajin duk abinda Ammih ke faɗa tuni wani sabon kukan ya sake ƙwace mata,dan ko Noor dinma ajiyeta tayi gefe naciga ba da kukanta har tagaji tayi bacci agun, Salkhan dan Allah dan Annabi Muhammad S.A.W kaya femun abinda nayi maka a raywarka na roƙe ka,shikan sa hawayen yakeyi cikin kuka yace nayafe miki Ammih muna yima Allah ma laifi muroke sa kuma ya yafe mana bare mu ƴan Adam,cikin kuka Ammih ta kalli Nanah tace matso nan ta sowa tayi zuwa gun ta zauna a ƙasa kusa da Ammih,cema Salkhan ma ya zauna tayi shima zaman yayi kusa da ita,cikin kuka tace "na haɗa aurenku ne sbd wata manufa ta daban gara nasanar muku ko zaku yafeni ko da mgnar bazata yi muku daɗi ba nasan idan kunji zaku iya yafe mun karna tafi lahira baku yafe mun ba nakasa kwanciyar kabari dan nashiga hakkin ku yayi yawa,"abunda yasa na haɗa ku aure shine sai kuma tayi shiru kuka yaci ƙarfin ta,da sauri Salkhan yace "Ammih nasani ba sai kin faɗa ba wlh naya fe miki,cikin kuka ta ɗago idonta da sukayi jawur tana faɗin"me kasani Salkhan idan da kasani baza ka wai waye ni ba,karka ɗa kai yayi yace "eh nasa ni Ammih kuma nayafe miki,Nanah dai anbarta cikin ruɗani kallon su kawai take da ido,"aa Salkhan baka sani ba gara na faɗa dai kaji shiru yayi bai sake cewa komaiba ba,dan gsky har ransa yana so Nanah taji komai,"Na aura maka Nanah ne sbd mu mallaki dukiyar da mahaifin ka ya bar maka shiyasa duk abinda Nanah takeyi na dage sai ta aure ka duk da kuwa nasan ba kwa son juna,"Auren ƙiyayya bbu kyau haramun ne manzon Allah S.A.W yayi hani da auren dole duk na ture nasa son zuciya ta duk wanda baiji bari ba to zaiga hoho,Nanah kam tunda Ammih ke mgna ji takeyi zuciyarta nasa sake mata ƙuna kuka takeyi sosai har tana shiɗewa,cikin kukan Ammih tace "dan Allah ku yafe ni na ci amanar dana karɓa,cikin kuka Nanah tace "Ammih nayafe miki kuma nayi ma Allah godiya daya sa kika gane kuskuren ki nayafe miki Ammih na,nima ki yafe mun,"Nanah naya fe miki Duniya da Lahira Allah ya yafemu gaba ɗaya,saide ki nemi gafarar Salkhan yanzu da igiyar Auren sa kike bin wani, ko kallon sa batayi ba dan tarasa dalilin daya sa wani sabon tsanan sa takeji bare idan ta kalla Noor duk sai taji bata sonsu,miƙe wa tayi ba tare da tako kalla inda yake ba tafice aɗakin.






"Sun jima agun suna hira shida Ammih tashin Noor da kukan datake yi,ne yasa shi saurin miƙe wa tun kafin Ammih ta miƙe yama kai bakin gadon har ya ɗakko ta saide kukan takeyi sosai ganin bata san shiba,ko da ya miƙa ma Ammih ita sai cewa tayi ita bata da abinda zata bata yakai wa uwarta ita,tana kuka tana miƙa hannunta wa Ammih ya fita da ita.


Ƙasa ya nufa yaɗan rarrashinta saide sam taƙi shiru,idonsa yaketa rarraba wa bbu Nanah bbu dalilinta,Hajara me aiki ce zata wuce tambayan ta yayi ina Nanah,ƙofar baya ta nuna masa da hannun ta,da sauri ya ƙara dan har ransa yake jin kukan Noor cikin sa'a ko zaune take bakin pool tasa ƙafan biyu a cikin pool tana kuka mai cin zuciya,tun kafin ya iso take jin kukan Noor saide ko kanta bata ɗaga ba,har ya ƙaraso inda take shima zama yayi kusa da ita yana miƙa mata Noor da ta miƙo hannun ta duka biyu tana kuka,ko ɗago kai bata yi ba bare ta ƙarbe ta,cikin damuwa da rawar murya yace "please Nanah feed her kinsan ita fa yarinya ce please ya ƙare mgnar kaman zaiyi kuka,idonta da suka kun bura ta ɗago ta kalle sa tana murmushin daya fi kuka ciwo "ai tunda Allah ya kawo ka kuma ka tabbatar da Noor ƴar kace na yaye ta kuma idan ka tashi ka tafi da ƴa ka,kallon mamaki yabita dashi cikin damuwa yace Nanah kin san fa komai ya faru kowa nada laifi so please let by gone be by gone,kinga kukan nan zai sata fever wlh ki kalla yadda tayi wani iri,haba Nanah miƙe wa tayi zata bar gurun tana faɗin "na faɗa maka bana son ganin ku kaida ƴar ka na yayeta ko dole ne,Noor kam har face dinta yayi ja sosai tsabar kukan da takeyi, wucewa tayi ta koma ɗakin ta yana biye da ita,yana zuwa hanyan sama Ammih data ji kukan Noor tafito a ɗakin ta tana faɗin "wai meke damun ta ne har yanzu batayi shiru ba?? Ganin Salkhan da Noor yasata faɗin "baka ga Maman ta bane? Kaman zaiyi kuka ce "taƙi karɓan tane, cikin ɓacin rai Ammih tace"tana ina ne? Ɗakinta ya nuna ma Ammih da hannu da sauri ta ƙarasa ta buɗe ƙofan zaune take bakin gado tayi tagumi tana jin su,"Wai ke dan ubanki baki da hankali ne baki da mutunci ko wlh ki kiyayeni a gidannan zaki ƙarbe ta ko sai kin ji jiki? Miƙa mata Noor Salkhan yayi tasa hannu tana turo baki ta karɓi Noor da tsabar kuka har tayi wani iri,tana karban ta tayi wani ajiyan zuciya gyarata tayi ta fara feeding dinta kaman wacce ta shekara bataci komai ba take sucking saide ajiyan zuciya take tayi,aiko kafin kace me tuni ta sake ta fara dawo da duk wanda ta sha amai takeyi sosai ta ɓata duk jikin Nanah da sauri Salkhan ya ƙara so yana faɗin,"subhanallahi menene kuma Ammih ma ƙara sowa tayi cikin faɗa tana faɗin,"ai na faɗa miki kukan nan nata yayi yawa zai sata zazzaɓi gashi nan ai sai ki san yadda zakiyi da ita,cikin ɓacin rai Ammih tafice.




"Salkhan kam duk ya rikice hanunsa yasa ɗauki Noor daketa faman kuka Nanah ta shige toilet ta canza riga,ko kafin ta fito tuni har ya cire mata rigar jikin ta da wandon daga ita sai pampers wuyanta ya taɓa yana kallon Nanah hankalin sa tashe yace "fever ne Nanah yake damun ta pls kisa hijab muje asibiti,mamaki yaba Nanah yadda duk taga ya rikice hanu tasa ta karɓi Noor tace "please leave my room da daba kasan da ita ba fa sai yanzu ne zaka nuna wani kada mu da lafiyarta, maganar ta sosai ya masa zafi ɗago idonsa yayi yace "Nanah i can't bear such insult from you ni banji zafin abin da kika mun ba keki bin wani ƙato bayan kina da aure nagan ku da ido na,"na yanke hukunci kuma yanzu kina jin haushi na meye wlh Nanah badan naga jinina a jikin yarinyar nan ba bazan karbe ta ba and kuma ina so ki sani ki ajiye duk wani abu ko bbu aure da ƴa a tsakanin mu yayanki ne ni dole ki bani daraja,"Noor kuma nine ubanta dole ki bani mutuncin nan kisa hijab yanzu muje asibiti nace,bbu musu ta ɗauki hijab doguwar riga da sucks kawai tasa mata suka fita zuwa asibitin.....








*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝




*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️






*08069224458*
[8/28, 1:14 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥








*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚


*A short story* 💋






*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️








*Marubuciyar👇🏽*






*Cousins ne*


*Aruwan sama* *kaddara tasame*


*Almajiri ko attajiri*


*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽




*Auren kiyayya*








🅿️2️⃣8️⃣🔁2️⃣9️⃣










**This page is dedicated to my lovely daughter sadeeyah 😂saɗi nuƙu* *nuƙu Allah ya albarkaci rayuwarki* 🥰😍😘










*Bismillahir rahmanin* *Raheem*










A parlor suka tarar da Ammih ta zaune, Salkhan ne yace mata "zasu kai Noor asibiti,"sai kun dawo Allah yabata lfy,duk abinda yasa meta ai laifin uwarta ne,baza'a faɗa mata mgna taji ba gashinan kinsata rashin lfy ai,Ammih na mita har suka fice daga Parlour.






"Tunda suka shiga motan bbu me kula kowa,dan Noor dinma tayi bacci suna fita,Nanah window take kallo Salkhan hankalinsa nakan tuƙi,Ammih kam tunda suka fita kuka takeyi da dana sani,"dubi yaddah suka fita abin sha'awa saide bbu komai, Salkhan kayi babban kuskure ko da nasan laifi nagun na duk abinda yafaru nice sanadi,wlh dukan ku bana tausaya muku yadda nake tausaya wa yar jikata,sosai take kuka da har zuciyanta ta ansa,sai tym ɗin ta tuna da maganin zuciyanta ta miƙe jiki bbu ƙwari ta hau sama.






"Koda suka isa asibitin Salkhan baiko saurari Nanah ba,suna fita yasa hannu yakarɓi Noor dake bacci yasata a kafaɗan sa suka shiga asibitin,tana biye dashi yayi komai suka shiga ganin Dr.






"Cikin mutunci suka gaisa bbu ɓaya lokaci yafara gwaje gwajen sa sannan Noor ta farka,ganin ta hanun Salkhan yasa tafara kuka ga Dr dake taɓa ta ba sanin sa tayi ba tuni ta gauraye ɗakin da kuka,koda kukan nata ba sosai yake fita ba,Dr ne yace Nanah ta ƙarbe ta tasa hannu ta ƙarbe ta kafin tayi shiru,sun ɗan jima kafin yaga ma gwaje gwajen nan yake sanar musu fever ne,magani ya rubuta musu yace akwai pharmacy a asibitin sai su saya,godiya sosai Salkhan yayi masa, murmushi Dr yayi yace kayi ma mom dinta wayo the baby looks exactly like you wani murmushi yayi yana faɗin,"thank you suka fice.






Suna fita ya tsaya ya clearing bill dinsu ya saya maganin suka kama hanya,still bbu wanda ke cewa kowa komai,sai dai Noor data fara rikici tana ɗaga hijab din Nanah,Yi tayi kaman bata san me take nufi ba Noor kam rikici take sosai tana sake jan hijab din Nanah, Salkhan na lura da ita ransa sosai ya ɓaci amma yayi kaman bai gani ba,baiko ankara ba yaji tana faɗin"Wai taya kike so ki sake sha ne bayan dazu wanke ni kikayi da amai,ni bazan baki ba sai mun isa gida,idan kika mun amai anan dame zan wanke? Tana faɗin haka ta sake gyara mata zama,kuka sosai Noor ta fashe dashi,baice mata komaiba jin zuciyar sa na tafa sa guri yane ma yayi parking inda bbu ƙafar mutane sosai,cikin ɓaci da ita kanta tasan ransa ya ɓaci yace,"Nanah kiba Noor abin da take so,wani kallo tabi shi dashi tana faɗin"taya zaka ce nabata abin da take so bayan kana kallo da tasha amai tayi,baiko juyo ba dan kukan Noor din har ransa yake ji,yace "ba mgnarki nake son ji ba oder nabaki ko baki ji me nace bane ki bata abin da take so,yana faɗin hka ya juyo yana kallon ta, ganin yadda har idon sa sukayi wani iri yasa bata ko iya sake mgna ba,tuni ta juya da Noor ta gyara mata kwanciya,ta ɗaga hijab ɗinta tasata ciki a yun wace ta karɓa tafara sucking,harta gama zata juya ta zuwa ɗayan kukan bata ƙoshi ba tafara yi,ta gefen ido ta kalla Salkhan da ya wani ɓata rai,"aa Noor juya ki zanyi sake juyata zuwa ɗayan tayi suna gun harta gama sha tama yi bacci,taci rota a hijab din tana share mata zufan face dinta,saide kaman daga sama taji Salkhan na faɗin,"Ajiye mun ƴata kifi tan mun a mota,jin mgnar tayi kaman daga sama kallon sa tayi tana faɗin "ban gane mekake nufi ba?"Thank God hausa nayi miki ba wani yare ba, Amma tunda baki gane ba barina mai² ta miki nace ki ajiye mun Noor ƴata ki fitan mun a mota,bazan jure kina wulaƙan ta mun ƴa a gabana ba gara muyi nida ke zan iya ɗauka,but bazan iya ɗaukan ko wani wulaƙanci akan Noor ba,mind you Noor ƴata ce

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads