Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 22111 words

Chapter 2 - DANGINA FREE BOOK BY SECRET PEN.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*






STORY &WRITEN




BY


ADAMA UMAR
SECRET PEN




07081940768






LOVE AND ROMANTIC STORY


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI




3️⃣






PAGE THREE


Yauma kaman kullum suna cikin break a daining abunda zai baku shaawa shine harda Nanna ake cin abincin( wata xuciyata tana faɗamin wannan nannar tana da wani matsayi a wannan family),saida kowa ya gama cin abinci Ammi ta kalli nanna batayi magana ba nanna ta fara tattara kwanuka kallon Hafsat Ammi tayi ta ce


Wato Hafsat bazaki cire wannan damuwar a ranki bako kina dqi ganin halin da muke ciki idan kikace bazaki auri Abdulmallik ba kinsan wanine zaizo neman aurenki kuma idan suka nemi yan uwanmu mezqn labarta musu don haka kiyi hakuri da wannan lamari ai auren nan


Waishin Ammi ina yan uwanmu suke ina yan uwan mahaifinmu shidan nasan ya rasu amma ina iyayensa ina yayyensa ina kawunensa ina baffanunsa washin kema Ammi ina naki yan uwan suka shiga,meyasa bazqki gabatar damu a garesu ba karki manta mun fuskanci kalubalem rayuwa kala kala tun muna yara akan gorin asali sannan yanzu ma akan rashin asali zaki aura mun Abdulmallik umma kodai ta hanyar banzw kika samemune


Tass taji saukar mari a kuncinta wanda hakan ya tilasta mata da yin shiru tanakallon Ammi sa hawaye ya wanke mata fuska ,kallon Hafsat Ammo tayi ta ce


Idan kika sake tambayata asalina kona mahafinku wlh ban yafe mikiba


Shiru tayi taji duniyar da take ciki ba nata ba ne domin furucin Ammi ya doketa dukar da kanta tayi tana rushe da kuka Ammi kuwa dakinta ta nufa ta dinga kuka kaman ranta zai fita Nanna ce ta shigo dakin jikinta a sanyaye domin taji duj hirar da tawanzu a tsakaninsu kusa da Ammi ta shigo ta fara rarrashinta kafun ammi ta ɗago kanta ta ce


Dama haka alhakin iyaye yake Nanna nasani ko istigifari bazanyiba Alhakin iyayen mune yake bibiyarmu tundaga kan abunda ya faru da Hafsat nafara gane haka gashi yanzu yara sunzo kuna tambayata ina yan uwanmu da wani baki zan musu bayani taya zan musu bayanin abunda muka aikata nida mahaifinsu ,shin wani hali zasu shiga idan sukaji asalinsu wayyo Allah nanna wlh da rayuwarmu tanada remote dana sarrafa na.maida komai bai faruba


Hawayen dake zuba a fuskar nanna ta share ta ce


Hakane hjy kisani kowa da kalar kaddararsa ki sani wannan itace kaddararki keda alhaji marigayi ,kuyi neman gafarar Allah zai yafe muku sannan tunda kinga yara sunason sani su suwaye ayi hakuri a waiwayi gida domin gudun gori


Haka ta dinga rarrashin Ammi kafun ta fito ta nufi dakin Hafsat ,kqman yadda tayi tinani tana zaune tana rike da hoton julabib tanata kuka karban hoton tayi ta ce


Haba Hafsat yanzu akan wannan magana shine zaki famewa kanki wani ciwon da warke a zuciyqrki


Rungume nanna tayi ta ce


Meyasa Ammi ta dage akan saian auri Abdulmallik wlh banasonsa nafiso in zauna banyi aureba ta hakane zan nunawa julabib soyayya ,wlh idan nai aure kaman naci amanarsa ce




Ba haka bane Hafsat ki sani shi kanshi julabib Allah ne ya bamushi amma ya dauke abunsa kiyi addua Allah yasa son da kikewa julabib yadawo kan Abdulmallik shikenan zaki samu saukin rayuwa


Shin Nanna bakisan abunda ya shiga tsakanina da Abdulmallik bane


Na sani nasan komai bana bukatar karin bayani kidauka kaman wannan abun bai faruba ,ki dauka kaman baayi komaiba,ki daukeshi mijin ƙawarki kawai ki aureshi kije kicigaba da ibadar aurenki ,ki manta da julabib ki manta da wani an halicceshi waishi julabib ki manta kunyi zaman mata da miji


Haba Nanna kina mahaifiyar julabib kike cewa in manta dashi


Kwarai ki manta dashi duk da cewa nina haifeshi amma nace ki mqnta dashi ,akullum idan na kalli julabib nakan tina mahaifinsa amma gashi Allah a daukesa ,nashiga kunci sosai amma da karfin addua Allah yasamun dangana don haka kema ki miƙa alamuranki gurin ubangiji


Hawayenta ta share tayi shiru tana tina rayuwarta da julabib


Flash back
Kwance take akan kirjinsa hannunsa daya akan cikinta ya kalleta ya ce


Baby yanzu zuwa dan lokaci zaki haifa mana baby ko ,wow waya hangoni da baby a hannuna


Juyowa tayi ta shafa gemunsa ta ce


Wlh my bibi koni ina burin Allah ya kaini wannan lokaci kafun Allah ya dau raina


Haba mesa kike fadar haka ai bakisan waye gawar fariba


Hakane bansan waye na farko ba amm da zaa bani zabi zan bada raina ka rayu kaida baby na nasan zaka kula da Ammina da Nannanmu ga baby na amma ni katafi ka barni bakin cikin missing ɗinka ma ya isheni nima na bika


Ah yanzu don na mutu kina nufin kema zaki bini ,gaskiya bakimun adalciba abunda nakeso dake ko bayan raina ki saki ranki kiyi aure kicigaba da walwala ,kiyiwa mijinki biyya kaman yadda kikemun koma fiye da abunda kikemun


Hawayene suka wanke mata fuska ta ce


Pls my bibi mubar magannan nan don wlh bana tinanin koda halinda zan shiga matikar na rasaka


Rungumeta yayi yana share mat hawaye ,haka kawai yakeji bazai rayuwa me tsawo tare sa Hafsat ba ...


Dafata Nanna tayi tai firfigit Ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka hakan ya tabbatarwa da Nanna halin tinanin nata ta shiga ,haka taita rarrashinta har bacci me nauyi ya dauketa Nanna ta fita ta jawo mata kofar .




Haka ta ta shi jiki babu kwari gaba data.ta rasa ya zatayi ta rushe maganar aurenta DA abdulmalik haka Ammi taita rarrashinta akan ta amince da maganar auren ,amma gaba daya batajin zata iyq auren Abdulmallik ,yau ma kaman kullum yasha wanka yazo gidan ya tura baba me gadi ya kirata babu jimawa ya dawo akan tana zuwa ,ammice ta nufi dqkinta ta shaida mata ana sallama da ita haka ta fito da hijab ta nufi hanyar waje Ammi ce ta kira sunanta ta juyo ta ce


Waike Hafsat haka zakina zuwa babu ruwan sha


Shiru tayi kafun tai murmushi ta nufi kitchen ,glass cup me kyau ta dauko ta bule bold ta dumbuli barkwano ta zuba a cup din kafun ta nufi friedge tana zuwa ta zuba exotic a cikin glass cup din ta fita girgiza kai ammi tai ta ce


Hafsat bazakiyi hankali ba


Tana zuwa yaata baza baki yana gyara zaman hularsa baijira ta masa tayiba ya karba ya ce


Godiyq nqke da alama dai na fara samun shiga tunda har tarbata musamman nake samu


bata kulashi ba don tasan neman magana yake ,kallonta yayi ya ce


Anwuni lafiya kawarmu


Bata kulashiba yayi murmushi yana kai kofin bakinsa da sauri yq furzar jin wani zafin barkwano ya ratsa bakinsa da makokoronsa kallonta yayi yqga kaman batasan yanayi ba ya ce


Hafsat mena miki haka ,ashe tsanat da kikemun harta kai haka


Kwarqi tafi hakama kuma ta ninka shi sau dubu sabain ,wlh Abdulmallik idan ka aurenitamkar ka auri tashin hankali ne gidanka da rashin zaman lafiya ,kai bari in fada maka zan iya kasheka kuma in kashe kaina duk akan wannan lamari


Tabbas Hafsat da na dauka abun naki kaman wasane amma tunda maganar ksa ta shigo ciki ai lamari ya baci don haka kiyi hakuri idan kika aureni zakiyi farin ciki marar misaltuwa ,zan maye miki gurbin julabib kai harma na fishi


Wani tsawa ta daka masa ta ce


Karka sake fadan wannan kalma baa halicci wani namiji da zanso sama da julabib ba sannan baa halicci wanda zausoni sama dashiba ,na yarda an haifeni ne da son julabib bq koya nayiba ,kasani babu wata fuska da natsansna gani sama da taka babu wani gunjin sauti dana tsana sama da muryarka babu wata mummunan halitta da banason gani sama da kai don haka ka tattara kabar mana gidan mu tunda gidan bana hadin cinya bane ko


Murmushi yayi ko daya maganganunta basu shigesaba shdai abunda ya sani zata gama bakine daga baya ta dawo soyayyarsa don haka zai iya kokarinsa yaga ya kafa tutarsa a cikin zuciyarta ganin yanda ranta ya baci yasa ya shiga motarsa mai gadi ya bude masa ya bar gidan .


Cikin kuka ta koma cikin gida domin ta tina da abun kaunarta julabib .




Tunda ya koma gida gaba daya jikinsa a mace ita kanta zuwaira ta lura da hakan shiyasa ta ke tambayarsa


Waini dear meya faru ne meke damunka


Kallonta yayi ya ce gaskuya bazan boye miki.ba na janye raga maganar auren Hafsat


What ka janye kuma .......






Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*






STORY &WRITEN




BY


ADAMA UMAR
SECRET PEN




07081940768






LOVE AND ROMANTIC STORY


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI




4️⃣






PAGE THREE


Eh Tabbas na janye domin na gaji da fuskantar walakancin dq takemun nibama walakanciba ki sani duk abunda tamun zan shanye amma bazan juri tana kiran sunan wancan banzan a gaba na ba kuma koda munyi aure saita kira sunansa don ta bakanta mun rai nikuma wbunda bazan jura ba kenqn


Haba honey damq na fada maka dole zaka fuskanci matsalloli kala kala karfa ka manta da babban laifin da kayiwa Hafsat kaine sanadiyar rabatada danta sannan kaine sanadiyar rabata da mijinta haba ko wannan laifin ta kalleka dashi ai bazata yafema cikin saukiba nidan abunda nakeso dakai shine dole ka zamabmai juriya a soyayya ,dole ka jure koma meye sanna kai kokari ka mallaketa ai duk wani qbu da takeyi saboda taga yanzu baa karkashib ikonka take ba amma kana aurenta kagama da wannqn babin


Shiru yayi yana nazarin maganarta tabbas a zancenta akwai kamshin gaskiya amma taya zan fara tunkarar Hafsat da maganar aure haka yayi ta sakawa da warwarewa saukar muryarta a kunnensa ne yasa ya juyo yana sauraron abunda take fada




Nasan tinanin da kake taya zata yadda a fara maganar aurenku ko ,to ba ita zamu tinkara ba Ammi itace makaminmu da ita zamuyi amfani wajen cin nasarar wannan.yakin


Haka taita nuna masa matakan nasara a aurensu har shimq yq yarda suj warware akan zataje ta samu Ammi idan ba matslaa manya su shiga lamarin .


Kaman yadda tayi alkawari hakan ta kasance zqune suke ita da ammi tana shaida mata sakon da Abdulmallik ya turota akan a bashi dama ya turo wakilansa su nema masa auren Hafsat ,Ammi tayi farincikin jin hakqn babu musu ta amince da suturo zuwa anjima zataje ta samu liman suyi magana ,sannan zuwaira ta karisa dakin Hafsat ,kwance ta sameta tanata sakawa da warwara domin taji duk abunda su ammi suka fada kenan yanzu idan tayi sanya haka zaa aura mata wanda bataso anya bazata shiga duniya ba kuwa kowama ya huta to ya ammi zatayi idan ta shiga duniya.wata zuciyar ta tambayeta saikuma wata ta bata amsa da yazatayi kuma ai itama haka tayiwa iyayenta tana cikin wqnan zancen ne zuwaira ta shigo dakin bata kalleta ba balleta mata sannu da zuwa kusa da ita ta zauna ta ce


Haba haba.Hafsat bazaki rungumi kaddara ba ,zaki zauna kiyita zama cikin kunci haba sai kace akanki akw fara meyasa kike hakane


Dallah rufemun baki munafukq ai nasani duk wannan alamari ke kike daɗa taazzarashi wato zaa kawo kudin aurena ko to sai ayi auren mugani wlh ko gawata baa ganiba balle akai cikin gidansa


Subhanallah anya kina cikin hayyacinki kuwa kike irin wannan kalamai ,anya kinsan meyake futowa daga bakinki ,aure fa akace zaa miki ba wani abu ba kiamince da Abdulmallik zakiji dadin zama dashi wlh bashida matsala ko kadan matsalarsa daya kuma ke kanki kinsan ya daina to meya rage dan Allah ina rokonki da ki amince ki yarda


Bangajrta tayi ta fita a dakin ta nufi bangaren Nanna domin ita ta gaji da jin abunda take fada mata


Kaman yadda aka shirya Ammi ta kira aminan mijinta guda biyu ta sanar musu idan babu abunda zasuyi gobe zaazo neman auren hafsat dukkansu sunji dadi sunsawa abun albarka .


Washe gari


Da musalin karfe 6:09 na yamma Ta dawo daga makaranta cikin gajiya.ga shegen yunwa dake ibarta har wani jiri takeji ,gaba daya tayi nadamsr zuwa makaranta don babu abunda ta gane tsabar damuwa ,shigowa falon tayi ta ajiye hakarta tana kallon Ammita ce


ammi sannu da gida


Yauwa sannu yadai karatunne ya dawo daie haka


Eh wlh ammi gaba daya karatun ya bamu wahala


Ok kije gacab abincinki maza ki dauka


Tashi tayi taje ta dauki abincin ta dawo falo har yawunta tsinkewa yake tsabar yunwa ,kusa da ammi ta zauna ta fara cin abincin kallonta qmmi tayi ta ce


Yauwa Hafsat dazu DA hantsi magabatan yaron nan sunzo neman aurenki kuma anbasu.har ansa muku lokaci nan da 2 weeks ga sadakinki ma ankawo


Abincin da takecineya shiga kofofin hancintq aikuwa nan take tari ya sarketa ta fara ba gaggautawa ruwa ammi tabata sannan tarin ya tsagaita gaba daya idonta sun fito waje tsabar wahala kallon Ammi tayi ta kalli kudin ta ce


Ammi wani karya naji kunnuwa na sunamun kaman an kawo kudin aurena naji kince kuma da Abdulmallik


Kwarai ka kuwa kuma auren babu jimawa domin kuba yara bane kuma kunsan juna tunba yauba


Haba.Ammi wannan wani irin tozarcine ,saikace wata kaza zaku daukeni kubada aurena kuma nanda sati biyu saikace auren tattabaru gashi yayana baya gari zanyi aure gaskiya ammi bazan yarda ba


No na kira yayanki shima yana hanya nan da sati daya


Why Ammi meyasa zqki yanke hukunci batare da neman izinina ba kinsan yanzu ni nake da daman nemaw kaina miji fa


Eh kwarai na sani kuma na zaba miki ,wlh Hafsat idan baki maida hankalinki ki nitsu waje dayaba zakiga yadda zamuyi nida ke




Tunda Ammi tai mata maganar aure taji abincin ya fita a akanta cikinta ya toshe ko yunwarma bataji,tashi tayi ta nufi dakinta tai kuka son ronta tana cikin kukw kaman wacce aka mintsina ta firgita ta tashi dauko daya daga cikin akwatunan ta ta fara zuba kaya a ciki saida ta shirya tsaf sannan ta ajiye a cikin drower ta dauko babbar jakarta ta zuba wayoyinta da system da charger saida ta gama hada komai nata ta nufi bandaki tai wanka ta dauro alwala ta fito ta tayar da sallah ,bata tashi akan dardumanba saida ta gabatar da isha sannan ta koma kan gado tana saka tana warwara wata zuciyqrta tana shaida mata abunda take shirinyi ba abu me kyqu bane amma batada mafitar da yawuce haka da tayarda a mata auren dole ya lalata rayuwarta har abada domin matikar aka mata auren nan shi zaikaita har cikin wutan jahannama domin bazata bawa mijin hakkinsa ba kuma bazata masa biyayya ba gwanda kawai tayi iya kokarinta kar ayi auren don matikan akayi auren nan to an lalata mata rayuwa tana cikin wannan tinani taji anyi knowking izinin shigowa ta bayar tana share hawayenta ,Nannace ta shigo tai murmushi irin nasu na manya domin taga hawayen da take gogewa kusa da ita ta zauna tana dafa kafadarta ta ce


Hafsat shin amminki ta sanardake maganar aurenki da akasa nanda kwanaki jalilan


Wani murmushi ta kakalo tayi ta ce


Eh nanna ta fadamun


To wani hukunci kika yanke


Tinanin da nake kenan har yanzu ban yake hukunci ba shawara nakeyi da zuciyata


Kisani ba koda yaushe zuciya take baka shawara mai kyauba ,a wasu lokutan takan baka marasa kyau don haka inaso kiyi shawara da kwakwalwarki bada zuciyarki ba


Hakane Nanna nagode


Shikenan yanzu qbunda nakeso ki tashi kiyi istihara saiki kwanta Dafatan Allah ya nuna miki aurenki dashi alkhairine ko kuma akasin haka


Shikenan Nanna in sha Allah zanyu kokarin yin hakan


Mikewa tayi ta nufi bandakin dake cikin dakin Nanna kuwa harta mike tana kallon jakar da take shakare da kaya bude jakar tayi taga wayoyi d sauran abubuwan bukata da sauri ta.bude drower taga akwati ,yawancin kayanta babu ,jinjina kai tayi ta fita tana zancen zuci ,bayan fitan Nanna hafsat ta fito babu alamar ruwa a fuskarta ta ja jakarta ta dauki wayarta ta fara dannawa .




Gidan yayi shiru babu qlamar mutane da dukkan alamu kowa na gidan yayi bqcci tafiya take cikin sqnɗa da akwatinta akanta sannan ta bude kofar falon a hankali ,motarta ta nufa ta bude boot tq saka kayanta ta jinginq tana karewa gidan kallo wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska ji take kaman ta fasa abunda tayi niyya amma ina zuciyarta ta kekashe bude marfin motar tayi zata rufe taji an rike marfin kofan da sauri ta fito don ganin waye ,zaro ido tayi ganin .........






Share pls


*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*






STORY &WRITEN




BY


ADAMA UMAR
SECRET PEN




07081940768






LOVE AND ROMANTIC STORY


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI




5️⃣








PAGE FOUR


Nanna a tsaye tana rike da marfin kofan fitowa tayi jiki a sanyaye Nanna tasa hannu ta zare key din motan ta kama hannunta suka koma cikin gida bangarenta suka nufa sannan ta zaunar da ita ta ce


Haba hafsat wani kuskure kikeson aikatawa ne ,shin kinaso tarihi ya sake maimaita kansa ne ,kinaso kiyi nadamar da haryau Amminki tana cikinsa meyasa haka meyasa


Wlh Nanna bazan zauna a auramun wannan mutumin ba karki manta da abunda yamunfa kuma yazo yace yana sona na fada masa banasonsa amma duk da haka ya dage saiya auren don haka gwanda in barmusu garin kowamq ya huta Gwanda tarihi ya maimaita kansa


Ba haka sakiyi ba yanzu idan kikw tafi idqn yayanki ya dawo me zamuce masa wani hali kike tinanin zai shiga ,yanzu kiyi hakuri har Allah ya dawo da yayanki lafiya saiki masa bayani yana da hakkin dakatar da auren ba shikenan ba


Shiru tayi tana tinanin maganganun Nanna tabbas a amaganarta akwai kamshin gaskiya don tasan matikar ta fadawa yayanta batason auren nan anfasa shima angama nan take wani kayataccen murmushi ya kamata ta ce


Shikenan Nanna bari zqn jira ba ammi tace yana hanya nanda one week ba
Kwarai yana hanya saiki masa bayani nasan shi zai fahimceki,nasan me Ammi take tsoro shiyasa ta amince da auren nan


Haba Nanna kenan kinq nufin kinsa asalinmu kumq kinsan tarihin su Ammi da Abba


Kwarai nasan komai amma nayiwa mahaifiyarku alkwari bazan taba fadawa wani wannan zance ba matikar ba bukatar hakan ta taso babu yadda aka iya ba ko kuma ita ta amince


Dan Allah Nanna kiban labarin asalinmu daga ina muke mu yan wani

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads