Showing 15001 words to 18000 words out of 22111 words
Chapter 6 - DANGINA FREE BOOK BY SECRET PEN.txt
da zogele ta hanyoyi uku wanda kowanne daga ciki yanada amfani wajen sauƙarda ni'ima nan take saidai abu ɗaya da zogale yake dashi shine ɓata ciki, yakan sanya gudawa a kowanne lokaci shiyasa yakeda muhimmaci kisan abu buyu, kafin ki fara na farko shine kada kisha da yawa na biyu kuma idan kinada ƙaramin ciki wanda be wuce watanni biyar ba kadama kisha, amma dai wani abu kuma daya kamata kisani shine bayan ni'ima dazai baki zai ƙara miki lafya,
hanya ta farko kiyi garin zogale wanda ya bushe a inuwa saiki zuba cokali ɗaya a ruwan zafi ki bari ya jiƙa saiki tace ruwan ki saka masa madara saiki sha,
hanya ta biyu ganyen zaki tafasa da kananfari sai bayan ya tafasa saiki tace ruwan sannan ki saka lefton kisha kamar yanda kike shan shayi,
hanya ta ƙarshe wato ta uku shine ki dafa ganyen saiya dafu saiki yanka masa farar albasa da tumatir kina iya saka masa mai da magi amma banda abu me yaji,
kamar yanda na faɗa asama kowanne daga ciki zakiyi kada kiyi da yawa sannan sai kina tare da miji zakiyi haka kuma ba'a yinsa asaka a firji don yayi saniyi, saidai kina iya sakawa shayin sikari ko zuma ko mazarƙwaila don yayyi zaƙi amma dai ba'aso yayi sanyi
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
1️⃣1️⃣
Washe gari gidan ya tashi shiru babu kowa a falo kowa yana dakinsa sai nanna dataketa zirga akan daining ,da alama karyawa take hadawa ,tsayawa tayi kaman mai tinanin wani abu sai kuma ta juya ta nufi dakin danaga an rubuta rais a jiki ta kwankwasa ,qmsawa yayi da "shigo" babu fargaba ta fada ciki ta sameshi dagashi sai boxer ta lura wannan dabiar suce shida Julabib ,wani murmushi tayi wanda ya karawa fuskarta kyau ta shigo ya juyo ya kalleta ya ce
*Our Nanna kece da safiyar nan "
"Nice mana yaron Nanna nazo na sanar maka karyawanka yana jiranka karyayi sanyi "
"To shikenan Nanna amma dai ke zakiban a bakiko "
Murmushi tayi ta ce
"Duk yacce kakeso yarona "
Harta kama hanaya zata fita saita juyo ta ce
"Yauwa jiya kace na tina maka zamuyi magana "
"Eh tabbas zamuyi magana amma inajin nauyin maganar ne "
Dawowa tayi ta zauna tana tinanin meyake tinanin fada mata haka da yakejin nauyi ,kusa da bakin gadon ta zquna ta ce
"Rais ka daukeni kaman mahaifiya ka fadamun wani abune yake damunka "
"Tabbas nanna inada damuwa a cikin raina amma na rasa wazan fadawa ,shine na yanke hukunci bara na fada miki ko zanaji sanyi a raina ""
Murmushi tayi ta ce
"Tabbas nasan damuwar da yarona yakeyi akan wata ce ,fadamun wacece ta sace zuciyarka"
Murmushi yayi ya ce
"Nanna idan na fada miki bazaki damuba kuma bazaki dauken marar hankaliba "
"Ko kusa bazan maka wannan kallonba saboda ita soyayya babu abunda bata jawowa ,takansa mutum makanta idan idonsa ya rufe akan abu baya taba ganin muninnsa sannan talansa kurumta kome mutum zaiji bazai taba dauka ba so kenan "
"Nanna wata nakeso amma ta girmeni sosai watalil ma ta haifen "
Murmushi tayi ta ce
"Tome a ciki don ta haifeka kota girmeka ,ka manta manzon Allah S A W matarsa khadija irin auren da sukayi ai wannan ba aibu bane "
"Nanna kuma abun shine matar ta daukeni tamkar danta kuma tanamun kallon da ina mata kallon mama ,sai daga baya Allah ya jarabceni da sonta ,bangane so nake mata na.aureba sai yanzu "
Shiru tayi ta ce
"Yoni agun aikin nakune ka hadu da ita har kake gudun kartaki amincewa "
"Ah ah Nanna.,tun lokaci. Da na bude ido nake ganinta ,ta nunamun so irin wanda takewa danta ,ni ndauka da sonta nake da kallon mahaifiya sai yanzu na gane sonki nake Nanna dan Allah bansan da wace manufa zaki fassaraniba amma nidai gaskiyata na fada miki kawai ,ki amunce ki auren "
Wani gigitaccen mari ta daukeshi dashi wanda ita kanta batasan tayi hakanba taya Rais zaice yanasonta wannan wani irin mafarki takeyi ,shin kodai Rais ya fara shaye shayene ,yanzu dai tasan yana da shekara 25 ,ita kuma 45 amma yace ita yakeso ya aura ,innalillahi wa inna illaihirrajiun ,
Shi taketa maimaitawa harta bar dakin ta barshi sake da baki yana kallonta ,dakinta ta wuce ta fashe da kuka ,tana tino Julabib dinta ,tabbas tasan da Julabin yana raye da kofa wasa rais bazai furta mata soba ,kalmar da abakin mutum daya ta sanshi wato Julabib ,ko mijinga mahaifin julabin haka sukai aure bai taba shaida mata yanason ta saidai inyaga ranta ya baci yace mata masoyiya shikenan amma shine yau dan cikinta yake fada mata haka ,ta rushe da kuka.ta kifa kanta akan filo .
Tunda ta fita yaji ciwom fitarta fiye da marin da tayi masa ya gwammace da duka ta mishi ta fada masa abunda yake ranta da yafi masa ,to wai.meye laifinsa don yace yana sonta kuma har yanzu yana sonta kotaki.kotaso
A falo kuma Ammice ta fita ta kalli falon da alama dai Nanna ta fito amma bataji motsinta ba ,kallon dakin Hafsat tayi ta mataa kusa da kofar ta kwankwasa babu jimawa aka bude ta kalleta da rigar wanka da alama daga wanka ta fito ,kallonta tayi ta ce
"Hafsa"
"shiiiiiiii Kice my inlow "
"Dallah nikam ki.saurareni meyasa naga gidan shiru yau kaman ba kowa a ciki "
"Eh Ammi ,wlh yau nayi baccin da najima banyi irinsa ba shiyasa amma ai ganinan kije jiyiwa Brox magana ya fito muyi break ,wannan break din na musamman ne domin an jima baayi irinsa ba a gidanan "
Juyawa tayi da alama dai Hafsat murnar fasa aurenta takeyi ta nufi dakin Rais ta.sameshi yana zaune kaman me tinanin wani abu shigowanta ne ya dawo dashi hayyacinsa ya ce
I"na kwana Ammina kadde harkin fito "
"Eh nafito yanzu fa almost 10 naga baka fito ka karya ba "
"Oh nima ban jima da tashiba amma bari na shirya yanzu ina fitowa "
"Ok" ta fada tana jawo masa kofar ,kama ta juya sai kuma ta kalli dakin Nanna ta nufesa ta murda ,tun daga bakin kofa take jiyo sheshekar kukanta da sauri ta bude dakin ta ahiga tana shiga ta ganta kwance akan filo taje ta zauna kusa da ita tana tambayarta lafiya
Dagowa tayi taga hawaye sun wanke mata fuska abunda ta jima bata ganiba tun bayar rasuwar danta julabib ,a razane ta kalleta ta ce
"Meke damunki Nanna kodai bakida lafiya ne.? "
Kai kawai ta daga mata domib ji take kaman idonta zasu fado taabar sarawar da kanta yakeyi
Da sauri ta fita ta kira driver tace ya dauko mota sannan ta koma dakin Rais take shaida masa babu jimawa sai gasu tare shine da kansa ya rikota aka sata a mota sai asibiti .
"Gaskiya zan fada muku shine matar nan rashin hutu yana damunta sannan jininta yahau amma bada yawaba ,don haka tana bukatar kulawa ka kula da mahaifiyarka da kyau ya fada yana kallon Rais da yayi shiru yana kallon dr "
Fitowa sukai da Nanna da ammi suka shiga mota soja yana driving juyowa yayi ya ce
"Nanna ta ya jikin naki ?"
"Da sauki kawai ta amsa domin yanzu ko hada ido bataso suyi "
Murmuahi yayi ya ce
"Ammi kodai zamuyi Nanna ta aurene ko zaa samu wanda zaina sata farin ciki "
Dakuwa ta masa ta ce
"Idan zaayi saika hada da uwarka "
Juyawa yayi yana dariya.,ita kuma Nanna.kwafa kawai tayi batace dashi komai ba .
Suna dawowa suka sameta a falo da alama waya takeyi ganinsu yasa ta kashe wayar ta nufo gunsu tace
"Lafiya kuwa ammi meke faruwa ?"
Ganin yanayin Nanna yasa ta gane itace bata da lafiya zasu wuce da ita daki Rais yace sam saidai su dawo falo taci wani abu haka suka dawo yaje ya hado tea ya kawo mata ,kin karba tayi ganin zai bata a baki yasa ta karba a kafa kai taanasha a hankali kaman bataso ,sannan aka bata magungunanta tasha.
Waya Rais ya dauka yasa aka turo masa maaikata sojoji suka karbi aikin gidan da nanna takeyi ita kuma aka cigaba da jinyarta ita da ,har yanzu babu wanda yasan maganar da tashiga takanin Nanna da rais ,saidai alakarsu.taja.baya hakan yasa.julabib a matikar damuwa ,yanzum bya zaune yake cikin yaransa kuma abokansa sojoji suna wasa suna dariya ,kaman da wasa sako.maganarsa da Nanna ,babu laifi sun masa.dariya da ihu kafun kowa ya fara bashi shawara wani.ya ce
"Ni a ganina ka tursasa mata ta.aure ka kawai yunda kana da dama."
"No ni aganina kawai ka saceta saita amunce zata aureka ka dawo da ita "
"No ni aganina kawai ka nuna mata zaka.iya mutuwa akanta har fiya fiyan karya kasha "
"Like how ,kaman ya zansha.fiya fiya?"
"Ka saku bottle na fiya fiya.ka.bayar a wanke maka ya fita saika saka olive oil a ciki saika mata kalamai a karshe kace zaka iya kashe kanka ma idan bazata aureka ba ai tanasonka kawai.tana tinanin taya duniya zata kalleta ne "
"Ok haka zaayi but.kai zaka wanke bottle din sannan ka fara sha ”
Dariya sukai dukkansu ........
Tofa ana wata ga wata ,rais fa ya dage ya kuke gani
Shin mijin nanna na raye idan yana raye ya.zaiyi da rais
Shin wani.mataki ammi zata dauka idan taji wannan zancen
Kai wannan lamarin abun dubawa ne.fa
Ina jiran amsoshinku a comment section
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
*STORY &WRITEN*
*BY*
*ADAMA UMAR*
*SECRET PEN*
*07081940768*
*LOVE AND ROMANTIC STORY*
*Ina masu so a tallata musu hajarsu to ga dama ta samu ,duk maiso a tallata miku ko kaya ko magunguna to tuntubi number nan*
07081940768
A SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
Kaman yadda suka samu kwalban fiya fiya aka zuba olive oil a ciki suka bashi ya nufi dakin Nanna tana kwance yaje shiga daga jin muryarsa ta gane shine ya shigo shiyasa ma taki dago kanta kaman tana bacci murmushi yayi don yasan dalilinta nayin hakan yazo kusa da bed side din ya zauna yana kallon fuskanta ,taarguwa tayi hakan yasa ta bude idonta aikuwa suka hada ido ta bata rai ta ce
"Me kakemun a dakina "
Murmushi yayi ya ce
"Laifine don masoyi yazo wajen masoyiyarsa "
Rintse idonta tayi jin abun ya mata banbara kwai ta bude idonta cikin fushi da bacin rai ta ce
"Ka saka idonka a nawa Rais ka kalleni da kyau ,ni a matsayin mahaifiyarka nake domin kasha nonona kaga babu wannan maganar tsakaninmu ,shiyasa kullum nake maka kallon danda na haifa wannan soyayyar da kake ji a kaina ka maidashi soyayyar da da uwa domin bazqn taba zamw.matarka ba har abada "
Tunda ta fara magana yake kallonta yanaji kaman ya daura hannu aka ya tsala ihu , me kunnuwansa suke jiye masa ne me Nanna take nufi kenan soyayyar da yakeji a ransa irin wacce yake yiwa umki ne innalillahi wa inna ilaihirrajiun ,tashi yayi yana gauraya hanya ya nufi dakin Ummi ko sallama baiyiba saida ta tsorita da ganinsa ta ce
"Lafiya Rais ka shigomun daki ko sallama babu "
"Sorry Ammi nazo gunkine "
"Ok i hope lafiya ko "
"Eh lafiya kalau ,dama Yanzu nakejin wata magana wai Nanna ta taba shayar dani "
Murmushi tayi ta ce
"To mene don ta ba shayar dakai din ko zakayi amai din abunda tashayar dakaine "
"No ammi kawai kibani amsata "
"Eh watarana na tafi company na babanku domin yin setteling da maaikata to na barka a gida ,na dauka zan dawo da wuri har yazamana kanata kuka idan kaga zaa bawa julabib mama hakam yasa kawai ta baka kashe saida ka koshi me yake faruwa "
Fita kawai yayi a daki ba tare da ya bata amsa ba ya koma dakinsa yana kuka yana da nasanin abunda ya furtawa nanna ,saida yasha kukansa ya koshi sannan yayi bacci.harya makara sallan azahar .
Haka rayuwa taita tafiya daga Nanna har rais babu wanda yake cikin walwala har ammi taso ta fahimci abunda yake faruwa halan yasa ta kira Rais take tambayarsa meke faruwa ya shaida mata yana shirye shiryen yacce zasu tafi garinsu ammin da abbansa ,saida gabanta ya fadi jin abunda ya fada hawaye suka cika idonta tana tsoron jin mummunan labari game da iyayenta shiyasa bata wauwayi gida ba shinya Mommynta ta kasance bata saniba haka ta dinga ti ani har Rais ya fahimci ta tafi wata duniya ta daban ta tabata ta farga ya ce
"Haba ammi meye rage kuma ,ki godewa da ya kawoki wannan lokacin da ranki ya kamata ku waiwayi gida ammai ki duba Abbanmu shin yana taye ko ya mutu waya sani so yakamata mu waiwayi gida mu sanar musu da halin da ake ciki ,ni kuma na tura letter akam inaso ma fara bincike akan abunda ya sami su daddynmu banma nuna mahaifina bane kuma ina da tabbacin zaa ban daman hakan don haka ya kamata muje musan wani hali kakaninmu suke ciki "
Shiru tayi gaba daya ya kashe mata jiki da abunda yake fada.ta rasa ima zatasa ranta tabbas maganarsa gaskiya ce a kullum mutuwa kara tu karota take dole ta waiwayi gida tauiwa hajiya bayanin abunda ya faru
Kallon Rais tayi ta ce
"Shikenan rais.na baka wuka da nama ka fara shirye shiryen tafiyar namu ,idan kasa rana saika sanarmun don inaso mu dauki formal manager namu "
"Shikenan Ammi bamatsala"
Haka ya sa shirye shiryen tafiyansu gadan gadan yasa nan da kwana uku xaau tafi ,aka fadawa manager shima ya shirya ,da kaman Nanna bazataje ba amma ammi ta matsa mata saida ta shirya zaa tafi da ita .
Bahaushe ya ce rana bata karya saidai uwar diya taji kunya ,yauce ranar tafiyarsu Rais an shirya manyan motoci na alfarma sannan an shiya.motan sojoji.guda shida gaba uku baya uku daga ganinsu kasan a shirye suke ,akwatuna aka dinga fito dasu.ana sawa a mota su Rais kam sai zumudi yake shida Hafsat amma banda ammi dake gabanta yanata faduwa tana cikin firgici shin iyayenta suna rayr ko baffanta ya kashesu shida dansa inuwa sun hau kan karaga sannan tana tsoro ta ina zata fara yiwa hajiya bayanin ina takai mahaifinsu ,gana daya tana cikin firgici hakan ,hafsat ta lura da halin da take ciki hakan yasa take mata hira nan suka daukin hanyar birnin gombe ,tsoron ammi ya kara tsananta lokavin da ta lura sun kama hanyar birnin gombe babu abunda takeyi sai adduoi ,Nanna kuwa ji take inama itace zataje taga iyayenta ,da asalin dangin mijinta ,adduoi ta fara turawa iyayrnta da dukkanin musulmai baki daya ,haka suka dinga tafiya suna wuce garurruwa da kauyuka sun taso karfe 10:00 na safe qmma sub iso cikin gombe da la'asar saboda babu ruwansu da gosilo suna tare da sojoji ,kallon Rais Ammi tayi ta ce
"Rais ya kamata muje mu kama hotel wanda zamu sauka don bamusan wani irin tarba zaa mana "
Murmushi yayi ya dauki wata waya.yayi magana nan sojojin dake gabansu suka sanja akalar motar zuwa wani babban.hotel ,suna zuwa sojojin.suka.shiga suka kama musu daki kafun suzo su musu iso ,saida suka gabatar da Sallah sannan Rais ya daukesu suka dunguma zuwa anguwar ,in banda jiniya babu abunda kakeji amma dake anguwar shiru ne babu ma wanda ya lura dasu ,Numbern gidan ammi ta basu nan motarsu ya faka a bakin gate din gidan ,daya daga cikin sojojin ne ya sauka ya kwankwasa aka bude ,kaman da Nanma wani mutum ne.da.ganinsa ya cika kakkarfa yana ganin sojan ya.sara masa ya kame saida ya amsa sannan ya fito yana karewa tarin motocin kallo ,rais ne ya fito ya ce.
"Ka shiga ka bude mana gate munzo wajen hajiya ce "
"Ok sir "
Kawai yacr ya koma ya zuge gate din gidan nan.suka.danna hancin motarsu cikin gidan da jiniyarsu ,kallon me aikinta hajiya tayi ta ce
"Ke saade kaman karar jiniya nakeji a cikin gidab nan "
"Eh hajiya nima haka kunnuwa na suke jiyemun "
"Maza jeki duba mana idan yan sandane ki tambayesu wa suke nema "
Tashi tayi ta nufi hanyar waje tana bude kofar main falor kawai tayi arba da manyan motoci sojoji sunata fitowa suna kamewa ,shaaninka da dan kauye nan cikinta ya hautsina ta juya a guje ta ce
"Hajiya mun shiga uku zo kiga ba yan sanda bane masu.yakin nanne sukazo mun banu "
"Ah bari in haura sama in taso da Alh.yazo ya ganewa.idonsa watakil bakinsa ne "
Ta dauki sandarta ta fara tafiya ta shiga wata korido ,ganin tsayuwa bazai karbeta ba yasa ta haura sama da gani wata ko wani zata kira.tana zuwa wajen dakin ta fara kwankwasawa da karfin cin tuwo tana kiran
"Aunty Nihad ,aunty Nihad ki bude!! "
A razane budurwar ta tashi ta bude kofar duk da.ba wani kayan kirkine a jikinta ba ta ce
"Meke faruwa ne sa'ade"
"Mun shiga uku wasu ne sukazo da bindigogi "
"What yan fashi.da rana tsaka."
"Ah ba yan fashi bane jamiaine "
"Muje na gani bazan iya da shirmenki ba ."
Atare suka fito falo dasu hajiya sun tsaya sunyi carko carko sun gagara fita ,a waje kuwa snata shan fama da ammi akan ta fito taki ko daga kafanta hakan rais ya rike hannun Hafsat suka nufi gidan duk da suma suna tinanin irin karbar da zaa musu kofan suka tura da yake saade bata rufe nan suka kara zaro ido suna jiran wazai shigo sukaga wani saurayi da wata budurwa sunshigo kansu a kasa ,a hankali ya fara daga kansa ya fara kallonsu tun daga kafarsu yazo har suka hada ido ,zaro ido sukai dukkansu suna toshe baki ,Da sauri ta fara dan gwala sandarta don ta tabbatar da abunda idomta yake gane mata shin mafarkine ko kuwa ,saida tazo deden Rais ta dauki hannunta ta shafa fuskarsa nan taji wani jiri ya dauketa ta nufi kasa da sauri ya riketa su kuma suka yiyo kanta suna kiran sunanta ..........
Tofa muje zuwa meya sumar da yar tsohuwa
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
1️⃣3️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
Salati sukai dikkansu suka nufeta ,Nihal ta daga masa hannu ta karbi mahaifiyarsa tana jijjigata ,saade kam da gudu taje ta dauko ruwa ta kawo aka fara shafawa hajiya ,Alh ne ya dago yana kallon Rais tabbas wannan daga ganinsa jinin Muhammad ne ,da badan yaga wanan da fuskan yarinta bama da yace muhammad ne ,zuciyarsace ta buga lokacin da qata tambaya