Showing 21001 words to 22111 words out of 22111 words
Chapter 8 - DANGINA FREE BOOK BY SECRET PEN.txt
kwari ,Maman ammice ta kira daya daga masu aikinta ta musu iso saida suka tafi ammi da nanna sai kallon juna suke ,ji suke kaman su ruga a guje su bisu amma saboda kunyar iyayensu sukai shiru domin ji suke kaman in suka tafi bazasu dawo ba ,hajiya da ta lura da hakan ta kira sunan ammi ta ce
Me kuke mana anan bazaku tashi kuje wajen mazajenku ba ,me zaku mana anan to maza ku tashi ku tafi
Dama jira suke nan suka tashi cikin jin kunya ,Abbakar yayi gyaran murya ya ce
To nidai hajiys diyar kinnan nakeso kibani zan aura ,zanyi na biyu da ita
Kulle fuskanta Nihal tayi domin dama ta jima da harbo jirkinsa tun daga kallon da yake mata ,Hajiya kam fatan alkhairi kawai tayi musu da sauran jamaan dake falon .
A bangaren su ammi kuwa saida suka shigo part din sannan kowacce ta shiga part din da aka ajiye mijinta a tare suka tura kofan ,Alh muhammad yana zaune bakin gado ya hada kansa da guiwa ,yana ganinta ya taso da sauri ,inda ita kuma ta tsaya daga bakin kofa ta kasa karisowa ,tasowa yayi ya ce
Meyake faruwa ne Aisha ,akwai matsace ,hankalina ya fara tashi da naga baki biyonba kodai kin sake wani aurene
Kuka ta fashe dashi tana mai rungumeshi ta ce
Bazan taba auren wani mutum ba bayan kai na gwammaci na koma ga Allah ban auri kowa ba akan na auri wani ,duk da cewa na maka takaba amma na kasa yarda da ka mutu ,amma na godewa Allah da yabani da daya tamkar ya dubu na gode naka .
A bangaren nannama makamancin tambayoyin da ya mata kenan ciki ya hada mata da ina julabib bata boye masa ba ta sanar masa da komau yayi masa addua kafun su shiga shirya mazajen nasu .
A bangaren Asiya kuwa tunda taji Aisha ta dawo ta tattaro yayanta duka akwai namiji wanda bazai wuce saan Rais ba koma ya fishi da kadan sannan akwai mace wacce itama tana da yara kanana sai kuma yar autarta wacce itama macece budurwa bazata wuce 21 years ba ,cikin farin ciki da murna ta shigo gidan kafarta har hardewa takeyi cikin na juna duk da mahaifinta ya kirata akan idan ta taka gidan bai yafe mata ba amma hakan baisa ta mishi biyayya ba tubda ya kaucewa Allah da mazonsa ,cikin falon ta shigo inda taga wadu dandazon mutane anata hira da sauri kanwar Abbakar ta kariso wajen Maman ammi ta ce
Mama ina yaya take ina take ina yaranta da mijinta jiya munga komai a tv mama
Murmushi mamanta tayi ta juya wajensu Asiya ta ce
Asiya ku shigo mana ,tunda autar asiya ta shigo idonta ya sarkafe a cikin na Rais ko kauda kai batayi ,jin Asiya ta ce
haba suhana me kike kallone haka
Dan dibirbicewa sukai suka fara sosa keya sannan suka nemi wajen zama aka fara hirar yaushe gamo ,suna cikin haka Ammi suka dawo hannu sarkafe a cikin na mazajensu suna dariya da lama wata hirar suke ,suna shigowa Asiya ta tashi da saurinta harda sassarfa taje ta rungume ammi suna kukan rabuwa .
Agurguje pls .
An bawa su Alh muhammad tarihin duk abunda ya faru a bayansu na kokawa sun koka na murna sunyi ,nan aka shiga yiwa Alh bello taaziyar julabib dinsa.
A bangaren abubakar fa soyayya tayi karfi tsakaninsa da nihal ,sannan Rais ma baa barshi a baya ba ya jone da suhana suna shan soyayya ba laifi ya samu karbuwa sosai ,ganin akwai fahimtar juna tsakaninsu yasa akasa surensu nanda sati biyu tunda komai akwai a wadace ,ammice ta fara yiwa amare gyaran jiki kaman ba gobe ,idan aka hadawa Amare tsumi ta debo musu susha domin sunyi alwashin cirewa mazajensu kishirwan shekara da shekaru ,babban abokin Rais ya taso tundaga lagos daurin aurensu yaga Hafsat aikuwa baiyi nauyin bakiba ya kada kuriarsa nan aka hada da nashi auren anata shirye shirye .
A bangaren abdulmalik kuwa yana hasasho abunda zaiyiwa su Hafsat amma ganin abunda ya faru a tv yasa yasha jinin jikinsa ya manta da komai ya rungumi matarsa .
Rana bata karya saidai uwar diya taji.kunya ,yauce ranar daurin auren iyalai guda shida wanda suka kasance cikin farinciki da kaunsr juna anyi komai.cikin soyayya da wasa da kudi tamkar ba gobe anyi duk wani event na sojoji da ya kamata babu wanda aka bari a baya ,bayan an gama biki amare sun sauka a part a gidan Alh Usama kuma sunsa ramar dawowa kano zasu ziyarci kabarin iyayen Alh bello Sannan zaa siyawa ngwaye gida ,shima Alh usama ya ce zaibar bayelsa domin yayi nisa zai zaba zai dawo kano ko gombe ta inda ya yanke.hukuncin zama a gombe anguwar bypass .
Bayan sun dawo kano sun ziyarci iyayen alh bello inda gari ya iso wajen ya biya kudi a kudin aka gina islamiyya a kusa da kabarin nasu ,Zuwaira taji dadin zuwan kawarta gidanta da mijinta da sauran amare inda ta kaga bata shawsrwarin aure yadda zata kama.mijinta dakyau.
Bari mu leka sashin su ammi
To ammi dai.amarci yayi dadi domin dukkanninsu sunyu guzurin ciki a jikinsu ,inda suka tsorata aihuwa da tsufarsu ,sai bobboyewa suke amma ina tuni Mama da hajiya.suka harbo jirginsu daga ganin yadda basason cin abinci sai kayan kqadayi hakan yasa suka ajiyesu suka murna ,sunji kunya kam amma suna farin ciki sa cikin musamman nanna.d yaronta ya rasu ,lokacin da cikinsu yakai hsihuws sukaje aka musu bucking na c section suks tafi ma babu wanda ya sani,ganin baasan mezai faru ba yasa aka kira Mama da hajiya ,sukazo an shiga dasu suna bakin treather saiga Hafsat ta taho daga ganinta bata hayyacinta itada Rais da matarsa da Abakar da Nihal ,tana zuwa ta ce munje gida bakwanan akace duk kuna asibiti meke faruwa nan aka shaida musu take jiri ya kama Hafsat aka riketa sai gado ana musu gwaji aka tabbatar da suna da ciki , anyi aiki cikin
Lnasara an fitowa da Nanna yan biyu mace da namiji ita kuma ammi an fito.mata da namiji an yi murna sosai inda akasha shagali sosai aka maida sunan julabib in kiya .
Bayan wata tara amare suka sunkuto yayansu inda Rais yayiwa Hajiya mai suna ,ita kuma Hafsat ta ce Mama zatasa ,Nihal kuma tasa mai sunan Alh muhammad .
Tammat bi hamdilkah
Ina godiya ga dukkan masoyana da suke a fadin duniya alkhairin Allah ya kaimuku a duk inda kuke ,ina godiya ga Allah da yabani rai da lafiya na karisa wannan littafin.
Albishir gareku masoya
Shin kunsan da sabon littafina mai suna
Hakak dina
Kaman yadda suka sani Alkalamin na dabanne shima salon na dabanne
Ku biyoni domin jin dan dano
Share pls