Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 33516 words

Chapter 10 - ABIN CIKIN KWAI By Ummu-Maheer Miss Green .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

dukana za ki yi uwata?saboda matar yayanki ce shiyasa zaki ce haka ko?wannan Ƙazamar ai ko jika ta ce wallahi sai na faƊi gaskiya,yo aƘwai mai duka na ne?da sauri na ce"a'ah hajiya kaka Allah ya baki haƘuri".




kuƊi naga ta fito dasu masu yawa na ce"Hajiya kaka waƊannan kuƊin fa?au daman su ki ke Ɓoyewa?".da sauri ta ce"ah haba khairat aike nasan bazaki faƊawa kowa ina da kuƊi ba?damanan wannan kuƊin Soja ne ke bani su duk wata dubu talatin ya ke bani duk wata to shine yanzu na Ɗebosu a bankin bankin ya cika shiyasa zan ajje su saboda ga buki ga kuma saukarku tazo shine zan bayar ayimin dubulan da cin-cin ko?".


Dariya sosai na yi sannan na ce"ah lallao hajiya kaka ki ce zamuci daƊi".na faƊi hakan gabana yana dukan uku-uku saboda aduk sanda aka ambaci sunan yaya Bilal sai inji zuciyata tana bugawa sosai.
***




"Kai Captain Ahmad gaskiya ban cika son shiga geton nan na ku ba,saboda wallahi duk motata Ɓaci take".daga cen Ɓangaren aminin Bilal wato Ahmad ya ce"ai kuwa mutumina dolenka kazo tunda dai yau dubiya zakaxo,Gauro kawai kasani ma ko ka sami mata a geton na mu".?


"kau haba captain ta ina kuma ?A haba a wannan geton gaskiya never for ever".dariya Ahmad ya yi sannan ya ce"to magani a Ƙasa dai nan da wasu Ƴan watanni musha biki".


wannan maganar da ya yi kansa ne yaji har ya fara sara masa ya shafa goshinsa yana ajiyar zuciya ciwon marar da ya ke ne yaji yana tsarga masa ya riƘe cikin yana kiran sunan Allah har ya fara jin dai dai.




wata zazzaƘar murya yaji tana ce wa"hmm aisha ni fa wallahi na matsu ranar saukar nan ta yi,don wallahi so na ke kawai in ganni da allon sauka na".


bai san ya aka yi ba ya dawo baya kaƊan,wata kyakkyawar yarinya ya hango fara ce sosai tana da siririn hanci da Ɗan Ƙaramin baki,pink lips ne da ita fuskarta rawn face ne da ita,ga wani kyakkyawan dimple shigen irin na khairat wanda ya Ƙara mata Ƙyau sosai,idanuwanta kamar na mage irin tana jin bacci.






tsayawa ya yi cak da motarsa yaji zuciyarsa ta wani harba masa,sam bai san wani so ba amman ya tabbata yanzu ciwon so ne ya kamasa daga kallo Ɗaya,da sauri jidda taja baya don Ƙur'anin da ta rungume yana son faƊuwa cikin fushi ta Ɗago tana kallon motar Bilal.


A hankali Bilal ya fito daga cikin motarsa idanuwansa na kan jidda Ƙur wacce take sanye cikin green Ɗin hijabinta wanda ya yi matuƘar haska ta.


ta buƊe baki cikin masifa xa ta yi magana,amman me ganin me fitowa daga cikin motar sai ta yi sauri ta mayar da maganar ta,sai dai sukayi kallon Ƙuda yafi na minti goma har sai da Ƙawarta Rabi'ah ta taƁa ta ta ce"ke jidda lafiyarki kuwa".?


Da sauri ta dawo hayyacinta cikin jin kunyar Bilal ta sadda kanta Ƙasa,ya kalli zara-zaran yatsunta waƊanda suka sha jan lalle wanda ya yi mata mugun Ƙyau.


A hankali jidda ta raƁa ta gefe ta wuce da sauri tana murmushi,Ɗan shafa Ƙwantaccen sajensa ya yi sannan ya bi jidda wacce har tasha Ƙwana,ya tsaya da motarsa a dai dai wajenta ya fito cikin muryarsa mai daƊi da zaƘi ya ce"jiddatul-khairi"!.da sauri ta juyo jin muryarsa wacce ta tafi da ita baki Ɗaya,gani take kamar babu wanda ya taƁa faƊin sunanta ya yi daƊi kamar haka".


ganin jidda ta tsaya yasa Rabi'ah ta wuce gaba don har sun fara makara lokaci ya wuce,a zuciyar Rabi'a Tana ji da ma ita ce ta yi wannan gwagwaƁan dacen tunda take bata taƁa ganin namiji hamshaƘi irin wannan ba,kai ko a fina finan nan na indiyawa bata taƁa cin katari da mai aji kuma kyakkyawa irin wannan ba.




kallon jidda ya yi sosai wacce take wasa da Ƴan yatsun hannuwanta take Ɗam wasa dasu ya rungume hannuwansa akan faffaƊan Ƙirjinsa yana murmushi ya ce"sorry jidda na tsare ki kan hanya wanda bai kamata hakan ba,amman ki yi haƘuri nima zuciyata ce ta kasa barina ij haƘura in Ƙyaleki har sai na zo na sameki".


jin haka yasa jidda Ɗan Ɗago fararan idanuwanta farare sol wanda har wani ruwane ya kw taruwa acikinsu suna wani shining oily.


Tuni ya Ƙara mace wa akanta yaji wani shork a jikinsa da kallonta da ya yi,ya ce"jidda ki Ɗago idanuwanki ki kalle ni"?.a Hankali ta fara kallonsa gabanta yana faƊuwa don wani irin mugun Ƙwarji ni ne da Bilal don ba abanza ya yi soja ba.
"Jidda!tun kallon farko naji wani abu a dangane dake amman kuma na kasa tuna meye wannan abun dana ke ji acikin ziciyata,amman yanzu zuciyata ta bani amsa sonki da ƙaunarki sune suka kamani alokaci ɗaya,wanda dukkan wata rai an halacceta da son waninta,Jidda tunda na ke bantaɓa son wata mace ba dai dai da sakon ɗaya idan ba ke ba,jidda ke ce komai nawa ayanzu,ins fatan kema zaki ƙaunace ni kamar yadda na ke sonki".


wata irin kunya ce ta mamaye ta tarasa a wani bigire za ta saka abin,wani nishaɗi da farin ciki take ji mara misaltuwa,ta rufe fuskarta da tafin hannayenta saboda kunyarsa,ko da bata faɗa masa ba wannan shine ya ke nuni da ta yi na'am da zancensa,don haka ya ƙara kallonta a karo na biyu ya ce"idan har ba zaki damu ba ina son muje inga gidanku"?.da sauri ta ɗago kanta ta ce"a'ah da zai yiwu dai ka biyoni kaga gidan,amman idan aka ga na shiga motar namiji bansan irin hukuncin da za ayi min ba".ta faɗi hakan cikin shawaɓa,sosai yaji ta ƙara burgesa arayuwarsa yana masifar son yaga mace tana shawaɓa ba yaga mace tana acting kamar namiji ba.




Haka kuwa akayi kai tsaye ta koma gida tana tafiya cikin takunta kamar tana tausayin ƙasa har suka iso gidan na su,suna zuwa da sauri ta kallesa ta yi rau-rau da idanuwanta ta ce"to yanzu zan wuce makaranta kada ayimin bulala babanmu yana ciki".


tana faɗar hakan da sauri ta yi hanyar islamiyyar tasu tana murmushi,ta daɗe tana jiran wannan ranar taga mijin daya ƙwanta mata.ko a mafarki bata taɓa tunanin Za ta samu miji irin Bilal ba,sai gashi ta samu mijin wuce sa'a,daman ko wani saurayi idan yazo wajenta ta koreshi sai ya ce wai ta fiya iyayi don tana ganinta mai ƙyau,shiyasa take ƙwaɗayi da buri.
Har tasha ƙwana bao daina kallonta ba,yarinya ƙarama amman ta tafi da hankalinsa haka?shi kansa mamaki ya ke ko da awasa bai taɓa tunanin hakan za ta kasance dashi ba koda a nafarkine kuwa.




Wani farin tsohone ya fito daga gidan,kana ganinsa kaga ba fulatani na asali,kamarsu ɗaya sak da ƴarsa ya faɗaɗa fara'arsa ya ƙaraso suka gaisa da Bilal sosai ya ke mamakin ganin wannan kyakkyawan saurayi,wanda kana ganinsa kasan kuɗi sun samu gindin zama ajikinsa.


Ɓoye mamakinsa dai ya yi don wata ƙila ko wani abune ya kawosa.




Cikin jin kunya da nauyin mahaifin jidda ya ce"Baba daman naga jidda ne ina sonta da aure so shine na ce bari in fara zuwa gidansu inyi iso sannan kuma idan an bani izini sai in fara zuwa zance".ya faɗi hakan cikin kunya da sunkuyar da kai.


Sosai dattijon ya yi mamakin jin haka daga gareshi,ya daɗe bai ga yaro mai hankali irin wannan ba,da yawa yawan yaran masu kuɗi basu fiya tarbiyya ba,wani ma sai dai ya yaudari ƴarka ya tafi ba tare dama kasan abinda ya faru ba.





"Yaro naji daɗin maganarka sosai don daman haka akeson neman aure,mutum ya zama jajirtacce kuma mai hankali wanda yasan ya kamata,to yaro ni dai ko daga ganin hankalinka nasan ka fito ne daga gidan mutunci,amman kai ɗan wani gari ne?kuma kai ɗan wani gida ne?".


Cikin nutsuwa Bilal ya ce"to Baba ni dai ɗan asalin garin kano ne anan unguwar rijiyar zaki,wacce take nan ƙasanku,iyayena kuma ƴan asalin bauchi ne garin azare,ni ɗan gidan Alhaji Abdullahi mai ƙwabo ne".


sosai mahaifin jidda ya faɗaɗa fara'arsa ya ce"ah to kace min kai ɗan gidan manya ne?masu kuma dattaku da sanin ya kamata,kai naji daɗi sosai sai dai inyi muku fatan Allah ya haɗa kanku da ƴa ta".






*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*










*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*






1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_


5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_




Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k


*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*




Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.




Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144




Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224


...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....


*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*








*miss green ce👉🏼*
[01/09, 19:38] Badi.at: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚*


📃Littafi na 1








By🪶
*®️Ummu maher(Miss green)🍏🍀*




_*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_


*Wattpad user name*
Rabiatu333


*Arewabooks*
rabiattu0444




Ya ku ƴan uwana mu yawaita addu'ar fita daga gida don neman kariya daga sharrin shaiɗanu.
---------------


25🟩26




. .. . ...Kai tsaye ya wuce gidansu captain,yana isa kai tsaye ya shiga gidan,da kansa yazo ya taresa,Halisa matarsa ta fito suka gaisa harda ɗansa ɗaya wanda sunan Bilal ɗin yaci,Bilal kusan shine hope ɗiin captain ya tsaya masa a komai,shi ne ya nemo masa aiki har yau gashi yana a matsayin captain shiyasa ya ke matuƙar girmama Bilal ɗin,don shi a sahon masu arziƙi masu taimako da gudu zai saka Bilal don mutum ne mai tausayi sosai da kuma son talakawa.


Abinci Halisa ta kawo musu,ruwan shayin dai ya kurɓa wanda yasha coffie sosai don shi arayuwarsa yana bala'in son shayi da coffie suna ɗan taɓa hira captain ya ce"ah mutumina ni fa tunda na ke da kai ban taɓa ganin ranar da naga kana magana kana dariya ba,sai dai inga ka yi murmushi,to meye sirrin A.D? Ko dai ka kamu ne kaga wata ƴar geton namu".?


murmushi ya yi sannan ya kurɓi coffie ɗin sannan ya ce"Captain tabbas ka yi gaskiya,don wallahi na ga wata yarinya wacce ta ƙwantamin sosai a zuciyata".




Dariya sosai captain ya yi sannan ya ce"lallai mutumina wannan wata yarinya ce mai sa'a haka?".


"Hmm captain ni ne dai mai sa'ar don Wallahi yarinyar nan cikin mintina ƙalilan naji ina azabar sonta wanda ban ma san lokacin da ya kamani ba".sosau captain ya ke dariya sannan ya ce"ina ma zan haɗa baki da ita da na ce wallahi kada ta yadda".


dariya sosai Bilal ya yi sannan ya ce"hmm kaga oga maganar ma da na ke maka yanzu ai har na kai maganar wajen mahaifinta,kuma yarinya ta yaba don haka sai ka nemi wata hanyar".


har dukan dining table ɗin captain ya yi sannan ya ce"shege mutumina sharp shooter kenan,ka ce har ka kai magana daga haɗuwa yau"?.


"To zan tsaya ne abuga min ball?ai kai ma kasan ni winner ne akan komai".dariya dukansu sukayi Halisa na ɗaku tana mamakin jin dariyar Bilal haka,duk tsahon tarayyarsu da mijinta bata taɓa ji ya yi dariya ba koda kuwa awaya ne,don mijinta captain yana da ban dariya sosai.




Suna cikin dariyarsu captain ya ce"yauwa A.D ni kuwa ya maganar case ɗinka da Alhaji Damas"?.


ɓata rai sosai Bilal ya yi sannan ya ce"captain mutumin nan ya zarce duk inda ba ka tunani,mutum ne mai mummunan hatsari,yanzu fa wai so ya ke adole gidanmu ya zama mallakinsa,kuma duk akan case ɗinmu dashi ne ya janyo hakan,amman ni nasan ta inda zan ɓullo masa idan ya san wata bai san wata ba".




Yana faɗar hakan ya tashi tsaye ya saka hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya ce"ni zan wuce captain Allah ya ƙara sauƙi".


"Haba mutumina har tafiya?ah to tunda dai ka samu ƴar geto ai dole ka koma gida da wuri"?.dariya sosai Admiral B ya yi sannan ya sanya kyakkyawan glass ɗinsa ba tare da ya ce komai ba ya fita.


Har mota captain ya rakosa sannan ya koma gida.


Har yaje gida tunanin jidda kawai ya ke,yana godewa Allah yau ya samu wacce ya ke so muradin ransa.






Sanda ya sako hancin motarsa muma lokacin muka fito daga cikin gidan,ya wani kallemu ya watsar ya wuce abinsa,na haɗiye wani irin yawu mai zafi.da zanyi da tuni na cire son yaya Bilal araina amman na kasa,kallonsa na ke har ya fito ya wuce sashensa.




Rashida ta dungureni ta ce"to ya wuce sai ki taho mu tafi?".ta faɗi hakan tana hararata,kunya ta kamani muka wuce gaba.




Muna dawowa daga islamiyya kai tsaye na wuce sashen hajiya kaka,ina shiga na tarar da mutane sosai,muna cikin gaisawa sai kuwa hajiya kaka ta ce"inno kin gane wannan kuwa?".


"A'ah gaskiya ban gane taba?kinsan rabona da birni na daɗe tun su khairat suna ƙanana".sai kuwa kaka ta ce"ahaf ai wannan i'ta ce khairat ɗin?".gwalalo idanuwa inno ta yi sannan ta ce"ikon Allah girman ɗan mutum babu wahala yau shekara 17 kenan rabona da garin nan tun sunansu,amman kinga yara sunyi wayo".


ɗan murmushi na yi kawai sai kuwa kaka ta ce"khairat sunzo saukarku ne fa?ga mairo cen don Allah ta zauna a sashenku,tunda ita dai ta dawo nan da zama yanzu,kunga idan tana cikunku za ta ƙara gogewa".kallon wadda aka kira da mero na yi sai kuwa ta ce"hannunki dafatan kina lafiya".nima murmushin na maida mata muka cigaba da hirarmu,na fuskanci mairo aƙwai ƙauyanci sosai akanta.ga ƙiriniya sosai ni kuwa dariya kawai na ke azuciyata don tun yanzu har sun fara faɗa da Hajiya kaka.








****
Su Rashida suna zaune a farlonsu harda mahaifiyarsu sai ga yaya Bilal nan ya shigo,da sauri Su Rashida suka tashi don sunsan karon nasu bai musu ƙyau dashi.


Suna fita hajiya Ruƙayya ta kallesa ta ce lafiya kuwa Bilal".?




Babu abinda ya ɓoye na dangantakarsa da Jidda,har unguwarsu babu abinda ya ɓoye mata.sosai ta yi murna da jin hakan sannan ta ce"to insha Allah kuwa xan gayawa Babanku idan ya dawo,sai ayi bincike sosai don daga jin labarinta mutuniyar kirki ce sai dai yana da ƙyau binciken.
*****


"wallahi khairat atsorace na ke sosai,don gaskiya ni tsoron rikici ne dani ko yaya ya ke?,ni fa har yanzu ban amsawa yaya Aliyu ina sonsa ba?".




kallonta na yi sosai sannan na ce"ke dai kawai ki fito kice min bakya son yaya Aliyu?amman ina ruwanki da anty khadija wanine ya ce kada ta riƙe mijinta da ƙyau".?


Murmushi maryam ta yi sannan ta ce"hmm khairat ko dai ma yaya ne?ai macece ƴar uwata nima kuma bazan so hakan ya faru dani ba".ta faɗi hakan kamar za ta yi kuka.


"Maryam ni dai don Allah ki taimakeni kiso yaya Aliyu,don wallahi ina jin tausayinsa wannan auren da zaiyu shine zai kawo solution ga dukkanin matsalolin da suke faruwa tsakanin yaya Aliyu da anty khadija".


"Khairat bari in fito miki a mutum sosai kinga nan na daɗe inason yaya Aliyu amman ban taɓa nunawa kowa ba,sai dai in shiga ɗaki inyi kuka idan abin ya dameni,amman duk da haka ina jin tsoron abinda zai faru khairat?kin san ku ƴan uwane ni kuma bare ce acikinku to kinga aure na da yaya Aliyu zai iya kawo matsala tsakanina dashi."


"Babu wata matsala da zai kawo?".da sauri muka ɗaga idanuwanmu Rashida ce tsaye akanmu tana murmushi ta samu waje ta zauna ta ce"Maryam haƙiƙa na jima ina jiran wannan ranar tazo da wani ɗan gidanmu zai aure ki maryam,kina da tarbiyya sosai da kuma nasaba mai ƙyau babu namijin da zaiso ya auri macen da take da hali irin na anty khadija.tunda har ya buɗe bakinsa ya ce yana sonki don Allah kada ki bawa maraɗa kunya ki yadda musha biki".ta faɗi hakan tana dariya.


Maryam dai ta kasa ce wa komai,a wani ɓangaren na zuciyarta son yaya Aliyu ne tsan-tsa acikinsa,tsoronta ɗaya anty khadija don ita sam a atsarinta ba zata so ta auri namiji mai mata ba.


Nan dai mukaci gaba da hirarmu akan saukarmu da kuma bikinsu Rashida,anan ne Rashida ke yi mana albishir da Babansu ya nemo mana admission a makaranta,ni ɓangaren law sai kuma Rashida, nadiya,Iman, khalisat,Bara'atu sai kuma maryam aminiyarmu duk harkar lafiya ne amman kowa da nasa ɓangaren.




Ni daman tunda na taso ina masifar son karatun lawyer don ina tausayawa talakawa musamman idan suka shigar da ƙara aka yi biris da abin ko kuma a cuce su,ko kuma fyaɗe da akewa ƙananan yara wanda ayanzu ya zama ruwan dare sai dai Allah ya kawo mana mafita.


Soyayyar A.D da jidda sai daɗa haɓaka take,wani mugun son Bilal ne ya ke damun jidda ko bacci zata yi idan ta rufe idanuwanta shi take gani,ta rasa wani irin love take masa.uwa uba ga irin taimakon da ya ke mata ba kaɗan bane,yanzu haka ya bada kuɗi a ruguje gidansu a sake musu wani,daga haɗuwarta dashi zuwa yanzu ya kashe mata kuɗi yafi a ƙirga,ko a mafarki ita jidda bata taɓa tunanin za ta auri miji irin Bilal ba,haƙiƙa tafi kowacce mace sa'a.ga wani irin mugun kishinsa da ke cin zuciyarsa sai take ji kamar duk ranar da ta ganshi da wata mace za ta iya yin komai akanshi.






****




Ina shiga sashen Hajiya kaka na tarar Mero ta tsaya tana wani muzurai,Hajiya kaka na tsaye da ɗan madoki hannunta,tana bin mero ita kuwa mero sai gwaliya take wa hajiya kaka tana dariya tana mata gwalo tana rufe ido.


Sosai abin ya bani dariya,sai kuwa hajiya kaka ta ƙara biyo mero ji ka ke timm,kaka ta faɗi a tsugunne ta kasance a ƙasa hajiya kaka ta saki kuka ta ce"shegiyar yarinya aljana wallahi na ɗauki masifa tun ba'aje ko ina ba".


ta faɗi hakan tana fashewa da kuka,sosai na tausayawa hajiya kaka na matso na ɗagata sai kuwa mero ta ce"ai wallahi don baki san yadda na taɓa kada megari bane shiyasa,har rawar banjo na sakasu da na saka musu karara ajikinsu,ni fa wallahi ba'a taɓani in ƙyale".ta faɗi hakan tana yi wa hajiya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads