Header Ads
Showing 21001 words to 24000 words out of 33516 words

Chapter 8 - ABIN CIKIN KWAI By Ummu-Maheer Miss Green .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ko ina ƙamshi kuma ko ina tsaf,ga ladabo da biyayya ga haƙuri,shiyasa baka taɓa jin kansu matuƙar har idan ba Hajiya kaka ba ce ta haɗosu,mahaifinmu da kanshi ya ce yafi jin daɗin zama da mahaifiyarmu saboda babu ruwanta ita haka rayuwarta take,kuma duk ita mukayo da rashin son magana Salim ne kawai shegiyar zuciya kamar ta kuturu wannan kuma zuciyar babanmu yayo.






ina gama wankan na fito na shafa maina me shegen ƙamshi da kama jiki sannan na wuce zuwa kitchen shima dai ƙazantar ce fal acikinsa ga abinci nan wanda ba a cinye jiya ba duk kyankyasa sun hau kai,kamar zanyi amai a haka na toshe bakina na gyarasa tsaf na saka air freshner ya hau ƙamshi sannan na shiga tsore na ɗebo dankalin turawa da kayan miya nazo na gyara na yi blnending ɗin kayan miyan sannan na ɗakko nama a fridge na wanke shi tsaf na tafasa shi sannan na ɗakko wata tukunyar daban na zuba mai na soya naman da kayanmiyan sannan na ɗan tsar da ruwa kaɗan na zuba curry da mai ɗanɗano yana tafasa na zuba dankaline wanda na feraye sa na wanke na yankasa a slice amman da kauri sosai saboda kada ya narke na zuba tafarnuwa da ƴar citta.haba sai ga girki ya hau ƙamshi sosai,na buɗe fridge na ciro mango ƙato na zo na wankesa tsaf na cire ɓawon sannan na cire tsokar na saka a blender ta markaɗa fruit yana markaɗuwa na zuba ruwa mai sanyi na faro harda ƙanƙara na ƙara blending sannan na juye na ta ce sa sosai,na juye a jug sannan na zuba suger enouph sosai ya fara ƙamshin mangwaro mai warin gawasa.girkina yana yi na sauke na zuba a babbar kula shima lemon mangwaron na saka sa a fridge sannan na wanke ƙwanukan tsaf na goge kitchen ɗin sannan na fito har lokacin bata tashi ba na yi mamakin mugun baccinta ace tun sanda nazo kusan awa uku mutum yana bacci,na zuba abincina na ci cikin ƙwanciyar hankali nasha lemon mangwaro na ina lumshe ido.sai ga ta ta fito daga ita sai rigar bacci iya guiwa duk gashin kanta a warwatse,na kalleta a fakaice na gaisheta ta amsa da ɗan wani guntun murmushi ta ce"au ashe ma kinzo?daman tunda zai tafi ya ce min kema yau zaki xo saboda bani da lafiya ne".sannu na ce mata kawai na cigaba da shan lemona ina kallo.ta ɗan kalleni duk sai taji kunya ta ce"kai rabonda naji ƙamshi mai daɗi har haka har na manta wallahi,gidan ya yi tsaf wallahi ban iya aikinne saboda wannan ciwon da ya sako ni agaba".ta faɗi hakan tana buɗe wamers na abinci ta ce"ta ce wow so delicious bari inci daman tun jiya banci komai ba duk abinda naci dawowa ya ke".duk zubar da take ance mata ƙala ba sai sannu dana ce mata don ni na tsani mace ƙazama duk sai najo ta fice min araina,to da ta ke ce wa ba tada lafiya ta kasa aiki ita me aikin me ye amfanin ta da baza ta iya yi ba sai wani goge farlo saboda wato shi mutane zaso gani.


buɗe cikinta ta yi sosai taci abinci kamat wata sabuwar mahaukaciya tasha lemon sosai tana gamawa ta ce"kai Khairat kin samu ladana wallahi rabon da naci abinci haka har na manta wallahi".ni dai bance komai ba ko da ta tashi daga baccin ko brush bata yi ba ina kallonta amman wai tazo har ta iya cin abinci gaskiya Yaya Aliyu yana ƙoƙari.






***


"Umma wallahi Alhaji Damas ya tsaya sosai akan wai sai mun sayar masa da gidannan,kin san wannan mutumin yana da hatsari sosai wallahi,shiyasa muke binsa a hankali".


Hajiya kaka ta kalli Abdul malik sannan ta ce"kai ni fa aduniyar nan ina ganin ikon Allah ace mutum ya dinga tsoron mutum?a i'na aka taɓa haka?ashe duk zafin zuciyarka na banza ne?shi dan ubansa ya isa ya karɓi gidan ya siya to wallahi kuce masa inji uwarku ƴar ƙasar uman bai isa yazo ya ce zai wani amshi gida awaje na ba,da a uman ne da banu shakka sai an garƙame shege,ɗan arnan kan dutse kawai".










*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*






1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_


5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_




Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k


*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*




Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.




Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144




Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224


...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....


*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[01/09, 13:44] my no: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚*


📃Littafi na 1








By🪶
*®️Ummu maher(Miss green)🍏*




_*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_


*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------


*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------


masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.


*Sirrinmu*


yawan barin jikinmu awaje shine ya ke saka miyagu shiga jikinmu da kuma rashin addu'ah,Allah yasa mu dace baki ɗaya.
-------------------




19🟨20


. ..dukkaninsu kallon Hajiya kaka suke ta ce"to me ye kuma akr kallona kamar na faɗi ba dai dai ba?shi fa Damas ɗinnan ɗan shege ne ma bashi da uba,asalinsu arnan daji ne tun kakarsa ta wajen uwa,uban dai nasa ne ba'asan inda ya ke ba".ta faɗi hakan tana kallonsu.tabbas haka ne mahafiyarsu ta faɗi gaskiya sai dai mutuminne yana da hatsari sosai.


Wanene Alhaji Damas?


Adamu shine asalin sunansa nahaifiyarsa kuma Sadiya sunanta,asalin Damas ɗin sunansa ya haɗa dana mahaifiyarsa,ya taso da sonta sosai sai dai baiyi rayuwa da ita mai tsayi ba,aka shigo har cikin gida aka kasheta kisan wulaƙanci,sai dai ba kowane ya janyo mata wannan kisan wulaƙancin ba sai ɗanta Damas faɗa ne ya haɗashi da wasu miyagun mutane kuma ya cucesu akan harkar don haka suka ɗauki wannan mummunan matakin,don mutane ne marasa imani sosai tun daga mutuwar mahaifiyarsa shikkenan wani rashin imani yazo mai,kashe mutum awajensa ba kimai bane,kowa yasan yadda arnan daji ke da asiri,don ma a haka mahaifiyarsa ta musulunta kafin ta mutu shine ma yasa ta dawo cikin gari taje zaune gidan haya,tana ƴar sana'ar mai da ƙuli ƙuli dashi take samu take ciyar da ƴaƴanta,yaranta biyu mace dana miji,Ruƙayya da Adam Ruƙayya ita ce ƙarama sai Adam saɓanin Adam bashi da uba,ita kuma Ruƙayya taba da uba,shi Adam tun a garinsu ta haifesa ita kuma Ruƙayya sai bayan ta shigo birni ne ta yi auren ta haifeta auren ma kuma ya mutu.


Bayan mutuwar mahaifiyarsa ya taso cikin ƙuncin rayuwa shi ya ke zuwa ya samowa ƙanwarsa abinci ta kowacce irin hanya haka ya ke zuwa ya samo ya kawo mata,Ruƙayya ta kasance mai ƙyamar mahaifinta ako da yaushe,don wataranma idan ya kawo mata abincin bata ci don tasan ta hanyar daya samo.


Tun abin na Adam bai yi nisa ba har ya yi nisa,babu irin aikin da ba ya yi,shine safarar miyagun abubuwa daga ƙasar nan zuwa wata ƙasar,shine safarar mata daga waccen jaha zuwa wannan kai har ya zama har ƙasar waje,sai a ɗauki yara dag nan ace za'a fita dasu birni aiki amman kuma daga haka bazaka ƙara ganin ɗanka ba,shikkenan kunyi bye bye.


Ganin haka yasa ƙanwarsa Ruƙayya guduwa garin mahaifinta tunda tasan garin,Adam ya yi baƙin cikin barin ƙanwarsa gida don yana sonta sosai,kai tsaye shima yabar unguwar don daman saboda ƙanwarsa ya zauna agidan,don ya yi da ita ta koma gidansa daya ƙera taƙi yadda dole ya ƙyaleta ya cigaba da miyagun aikinsa,aka daina jin ɗuriyarsa a unguwar don daman suma ya fara isarsu,ko da idan ya yi wani kaifin ka kaishi wajen ɗan sanda to fa washe gari za'a sakosa don ya samu masu goya masa baya cikin manyan masu kuɗi na ƙasa baki ɗaya.Ga shi da mugun asiri don ko biyosa akayi ba'a samunsa saboda ɓacewa ya ke.


Wannan shine taƙaitaccen tarihin Alhaji damas.
****


daga zuwa na gidan Anty Khadija gidan ya koma gidan amarya sak saboda tsafta ina tashi da safe babu abinda na ke farawa da na yi sallah na yi azkhar da karatun alqur'ani to ajjewa na ke in fita in gyara gidan tsaf ɗakinta kuma sai bayan ta tashi na ke gyarawa,sannan inyi girki inyi wanka sai dai matar gidan ta fito taci ta koma tana yimin sannu,ni kuwa har mamakinta na ke,wata shegiyar rigar bacci tun ranar da nazo gidan na sameta da ita kusan sati biyu har yanzu bata wanketa ba,kuma me wanke yana zuwa wai sai ta ce mai ya tagi bata da wanki,kuma ga kuɗin me wankin anbata amman tana baƙin cikin fitar da kuɗin,ko da daman yaya Aliyu yasan halinta sai da ya siyo komai na kayan da ake buƙata komai da komai har nama sai da ya saka a fridge don shegen son kuɗine da ita.


Ko da nazo gidan har nan yaya mk ya ke biyoni yazo ya tafi ya barni da tunanin waninsa yaya Bilal don nifa babu namijin da ke cikin ƙwaƙwalwarnan tawa idan ba shi ba,ko da na yi tunanin ciresa araina bai taɓa ciruwa.sam ko kaɗan bana son yaya mk har tausayi ya ke bani yadda duk ya matu akaina,bana son nuna masa bana sonsa ne saboda halinda zai shiga ina dai lallaɓasa ne dai mu rabu lafiya.


Babu yadda baiyi dani ba da in amshi wayar daya kawomin naƙi amsa saboda Baba ya ce baza a bamu waya yanzu ba,haka ya koma da abarsa sai dai tun a fuska naga bai ji daɗi ba don fuskarsa ta canja,na lallaɓashi na bashi haƙuri.muna rabuwa na dawo cikin gidan na sameta tana cin abinci,daman aikin kensn taci abinci ta ƙoshi shine aikinta babu abinda take sai bacci,sai kuwa ta juyo ta ce"wai ni Khairat in tambayeki?"da sauri na ce"ina jin ki anty khadija".


Gyara zamanta ta yi sannan ta ce"wai da gaske yaya mk sonki ya ke"?.ta jeho mun wannan tambayar alokacin da ban shirya ba na ce"eh sona ya ke".na bata amsa nima sai kuwa ta ce"kai ƴan gidan mu ma sai abarsu Bara'atu fa baki ga yadda take sonshi ba,kuma wallahi har soyayya suke amman shine ya komo wajenki?amman ya cika mayaudari".ta faɗi hakan tana kallona.
ɗan murmushi na yi sannan na ce"to ni yanzu Anty khadija meye na wa a ciki?ina shi ya ce yana sona ko?kinga ba ni na ce ina sonsa ba kinga ai ta ƙwana gidan sauƙi ko?soyayyarsu kuma da suke yi da Bara'atu su cigaba da yin soyayyarsu ko kada su cigaba wallahi ba damuna zaiyi ba".ina faɗar hakan na tashi na shige kitchen dan ɗora girki don ni ko san hirar yaya mk ɗinma bana son ayi,ni dai ba ni na ce ina sonsa ba?hasalima ni bana sonsa wallahi ni da zai auri Bara'atu wallahi daɗi xanji don sam bana son in koma gida ya cigaba da zuwa wajena a matsayin saurayi sam bana son hakan,wata dabara ce ta faɗomin na fito na samu Anty khadija har ta fara chat ita da yaya Aliyu sai shagwaɓe mai take wai ya dawo,ni dariya ma abin ya bani da kuma kunya bayan sun gama ne na ce"yauwa Anty khadija don Allah magana na ke son muyi".kallona ta yi sannan ta ce"to ina jinki ya aka yi"?.


"Anty na don Allah so na ke ki faɗawa hajiya kaka soyayyar yaya mk d kuma anty bara'atu".kallona ta yi sosai sannan ta ce"to wai ke ba kya son yaya mk ɗin ne?".
"Eh anty".


ɗan murmushi ta yi sannan ta ce"yo ke wa ki ke so"?.anxo wajen kallonta na yi babu ko kunyar ta na ce"na ce yaya Bilal."


da sauri ta tashi sannan ta ce"ah yarinya gyara zancanki wannan guy ɗin yafi ƙarfinki wallahi kina ganin mutum har mutum kamar shi ya yi kansa mutum mai izza ji-ji da kai uwa uba ƙyau da komai kin san ba fa zai yadda ya soki ba?don nasan duk nasan irin tsanar da ya yi miki sannan ki ce wai shi ki ke so?ni dai shawarar da zan baki ki yi haƙuri ku cigaba da lallaɓawa da yaya mk ɗin ina ganin hakan zai fiye miki".tun kafin ta gama naji wasu hawaye masu mugun zafi suna zubomin,yanxu idan na fuskance ta tana nufin yaya Bilal bazai iya aure na ba,saboda ni mummuna ce kuma baƙa?sosai maganganunta sukayi min ciwo sosai na tashi na tafi ɗakina na faɗa kan gado na fasa wani irin kuka mai cin rai,ciwo sosai na ke ji acikin zuciyata aduk sanda aka danganta ni da yaya Bilal bazai iya rayuwa dani ba yafi ƙarfina,tabbas nasan da hakan ya fi ƙarfina ne sa ba kusa ba,amman kuma ni a duba yadda na ke sonshi mana ayi min adalci.


ta baya na naji an dafa ni na juyo a hankali naga anty khadija ce ta ce"yi haƙuri ABIN CIKIN ƘWAI ta hajiya kaka,ki yi haƙuri kinji ban zata ranki zai ɓaci ba,insha Allah bazan sake ba kinji,ni da ki ke ganina zan tsaya miki har sai na ga kin auri yaya Bilal ɗinki".


Sosai na ji wani farin ciki ya baibaye ni na tashi zaune na rungumeta,ta buga baya na a hankali ta ce"yi shiru daina kuka kinji ta yaya Bilal".ɓoye fuskata na yi a bayanta wai ni kunya.


Tun daga ranar idan yaya mk yazo sai anty khadija ta ce mishi ai ina gidan koyon ɗinki da ta sakani,tun yana daurewa har dai rannan ya ce azuciyarsa zakusan baku da wayo idan kunsan wata baku san wata ba. rannan da ya tashi zuwa sai ya ɗakko Rashida da kuma aminiyata Maryam,wacce duk duniyw ba ni da aminiyar da ta wuce sai Rashida daman mu uku muke rayuwarmu ita maryam anan ƙasan unguwarmu take iyayanta masu matsakaicin ƙarfine ko islamiyayya da mukeyi tare babanmu ke biya mata har skull ɗinda ta yi babanmu ne ya ɗauki nauyinta,ganin dai irin zaman amanar mukeyi da ita tun muna ƙananu ita ta ce bata ra'ayin yin skull ta boarding mu kuma muka zaɓi boading ɗin to tun daga nan ne fa muka ɗan raba jaha saboda sai mun dawo hutu ne muke haɗuwa.
Ina kitchen ina girki kawai sai Naji anyi ihu an rungumeni ta baya,ina juyowa naga Maryam da gudu nima na ɗafeta muna juyi a kitchen ɗin sai kuwa ta ce mu da Rashida ne tana waje a hanya ne taji ciwo,to kinsan Rashida da kafiya yanzu haka da bin bango ta shigo ta hana ko in ɗan taimaka mata"...ai bata ƙarasa faɗar maganar ta ba da gudu na fito don ganin Rashidar to sai dai me Yaya mk na gani yana face ɗi na ya kalleni sosai ya yi dariya sannan ya ce"ah Hajiya me ɗinki ƙaraso mana"?.ya faɗi hakan yana ƴar dariya.


Wata best ce ajikina wacce ta ɗameni sosai sai zanin dana ɗaura da kuma irin hular na ta zaren lilo wadda yare suka fiye amfani da ita musamman a awajen bacci.
Na rasa yadda zanyi gashi na riga dana fito ya gama kallona tsaf,sunkuyar da kaina na yi kamar wata munafuka kawai sai naji maryam ta zuramin hijabin da ta zo dashi da gudu ta koma farlon.


Rashida tazo ta wuce ta kusa dani tana ƴar dariyar mugunta,yadda kasan in shaƙesu haka na ke ji tsabar baƙin ciki,jikina duk a mace na ƙarasa ina kallon ƙasa,na gaishe sa ya amsa sannan ya ce"sannu gimbiya mai koyon ɗinki?Khairat ban taɓa tunanin haka daga gareki ba?banyi tsammanin haka ba?nasan ke mutum ce mai gaskiya hasalima baki iya ƙarya ba?to me yasa ki ke min ƙarya ni?tabbas ko da baki faɗa ba nasan komai Khairat,bakya sona Khairat idan na fahimta kamar dole na yi miki amman ki yi haƙuri don Allah idan na takura miki,zuciyata ce bata yi min adalci akanki son da na ke miki shine ya ɓoye mode ɗin fuskarki gareni,ina son ki fito sosai straight foward ki faɗamin matsayi na agunki don Allah".


kasa ce wa komai na yi sai da yaga ƙwalla ta taru a idanuwa na alamar zanyi masa kuka sannan ya ce"sorry yi haƙuri kinji ban ɗauka wannan maganar za ta ɓata miki rai ba,amman don Allah ki yi haƙuri ki daure ki faɗamin abinda ke ranki saboda kada mu ɓatawa juna lokaci tsakanina da ke".


Cikin siririyar murya ta na ce"yaya Mk ka yi haƙuri amman wallahi bawai bana sonka bane kunyar anty khadija na ke ji shiyasa na ke ce mata ta ce na je koyon ɗinki".ɗan murmushi ya yi sannan ya cs "khairat kenan uwar kunya to shikkenan yanzu dai ayi haƙuri adinga kulani kinga duk yadda na rame saboda tunaninki ko aiki fa bana iya yi a office?sai dai inyi ta rubutu shirme".dariya ya ɗan bani rayuwa kenan shi yana sona baki ɗaya da zuciyarsa ni kuma ina son wanin sa haka.nan dai muka cigaba da hirarmu ya ɗauko wani ƙaton gift a nannaɗe na miƙomin yana murmushi don shi ma'abocin murmushi ne.


Juya abin na yi a hankali sannan na ce"na gode yaya mk Allah ya ƙara arziƙi".ɗan murmushi ya yi yana kallona sannan ya ce"ba komai matata kada kiji komai gobe Baba zai dawo daga tafiya inason in shigar da maganar aurenmu ayi komai a gama".


Ai ban san sanda na zaro idanuwa na ba cikin tsoro,kallona ya yi sosai sannan ya ce"lafiya ki ka tsorata haka?ko kuma tsoron auren ki ke"?.mayar da wani malulun da ya tokare ni na yi sannan na ce"ba komai".daga haka ban ƙara cewa komai ba har muka rabu na koma cikin gidan.har na shiga bai daina kallona ba ya shafa gashin kansa sannan ya ce"khairat ina sonki da yawa Allah ya bani ke na more mata".
Ina komawa ciki suka fara yimin dariya ba babu ma wacce tafi ban haushi irin Maryam na kai mata duka na ce"banza uwar ƙarya kawai".dariya ta yi sosai sannan ta ce"don Allah khairat ki bawa yaya mk dama mana ya fito musha biki?ki manta da wani yaya Bilal".ɗaka mata wani duka mai zafi na yi sannan na ce"aniyarki ta biki insha Allah yaya Bilal zan aura".tare suka haɗa baki wajen ce wa"to Amin tunda kin dage sai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads