Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 33516 words

Chapter 7 - ABIN CIKIN KWAI By Ummu-Maheer Miss Green .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ta haɗamu".?ganin irin mirmisisin da ya yi da idanuwa bata ƙara ce masa komai ba suka cigaba da hirarsu kaka na ɗarsa wani abu azuciyarta.


Ina fitowa na samu wani ɗan lungu na fashe da kuka mai ƙarfin gaske,na yi mai i'sa ta sannan na juya xan tafi sai muka ci karo da yaya Aliyu da Yaya Mukhtar.da mamaki suke kallona sannan suka haɗa bakinsu wajen ce wa"a'ah little sis me kuma ya sameki haka?me ya faru agidan?".saurin goge fuska ta na yi to me zance musu?ce musu zanyi inason yaya Bilal shi kuma yana wulaƙanta ni ko me?no ai abin da kunya.

Ganin bance komai ba suka sakani agaba wai sai na gaya musu abinda ya faru?bakina yana rawa na ce"kukan rabuwa ta na ke yi da Rashida".na faɗi hakan cikin shagwaɓa.dariya sukayi dukansu musamman yaya Aliyu ya ce"to ikon Allah kukan kuma tun yanzu?ai haƙuri zakuyo dukanku don ku daman rayuwar mace ƙanƙanuwa ce daga gidan iyayenta sai gidan miji,don haka ki share hawayenki kinji?"da to na bisu sannan na wuce.


Yaya Mukhtar ya ce"bro ni fa na samu mata agidannan Tun khairat bata kai haka ba na ke matuƙar sonta har yanzu,amman na rasa ta inda zan faɗa mata".?dariya yaya Aliyu ya yi sannan ya ce"bro me gaskiya kada ka yi sakaci kamar yadda na yi akan Rashida ka gabatar mata da kanka ka ga kawai sai a haɗa bikinmu asha biki".ya faɗi hakan yana kallon mukhtar wanda shima shi ya ke kalla.
***


Har na isa sashenmu jikina duk a sanyaye ya ke,ban kula da mutanen da ke farlon ba na yi wuce wa ta sai kuwa naji anty Hamdala ƴar Mama wato uwargidan su maman mu wacce take aure a Abuja ta ce"ikon Allah ita kuma wannan ƴat baƙar yaushe ta fara raina mutane har haka?".mata ce"hmm Hamdala ta gaisheki tana ganin kakarta da uwarta sun ɗaure mata gaba agidannan sai wanda taso ta gani da mutunci a gidannan sannan take gani da gashi,ai kinga gwara mutum ya kama kansa kafin kuma a koma dukanka".cikin jin kunyar maman nawwara wato antyna Hamdala na ce"mmn nawwara ina yini?wallahi ban kula da zuwan ki bane amman don Allah ki yi haƙuri".na kama kunnuwa na alamar ban haƙuri,sai kuwa ta ce"ai ke dai kam Khairat kin shiga ukunki da iya haɗa munafunci yanzu da ki ka saka za'ayi wa su Nadiya auren dole me ye ribarki?baki da wata riba sai ta munafunci da iya haɗi,to wallahi ni dai kada ki yadda gulmarki tazo kaina don ba Hajiya kaka ba ko Hajiya wacece agabanta zanyi maganinki ehe don ni ba kunyar wata tsohuwa na ke ji ba,idan su Baba ita ta haifesu to mu ba'ita ce ta haifemu ba".


Sosai na yi mamakin abinda Anty Hamdala ta faɗa na rasa me yasa iyayensu suka koya musu rashin sanin darajar mutane,Daman Hajiya kaka sun saba yi mata rashin kunyarsu da fitsararsu abin yana yimin ciwo don duk zagin da Hajiya kaka ke yi wa mahaifiyata bai saka ko kaɗan na raina ta ba,shiyasa sam bata bari a cuce ni ko kaɗan sai dai idan bata wajen don takan faɗa ce wa wai ni banyo mai sunan na ta ba,don ni ba mutum ce mai faɗa ba,sai ka yi min abu ban taɓa nuna maka ka yi min ba sai dai inyi kuka in share hawayena ko mama ba ta sanin komai idan ba ni ce na gaya mata ba.
Ban sake ce wa komai ba na wuce ɗaki raina babu daɗi,a rasa me yasa ƴan uwana suka tsaneni haka?ko don suna ganin son da Baba ke nuna min ne oho?ko kuma fifita ni ɗin da kaka ke yi ne?don ita Hajiya kaka babu ruwanta ko agaban waye sai ta nuna min ƙaunar nan daga Allah take.




Mama ta sameni aɗakina lokacin na fito wanka na gaisheta ta ce"yauwa Khairat ɗazu yayanki Aliyu yazo ya ce gobe zakije gidansa Khadija babu lafiya ga shi kuma zaiyi tafiya kinga sai ku zauna a atare".?to na ce mata amman ba don raina yazo ba don sam bana son zuwa gidan babban yayan nawa wanda shine babba awajen mama shine ɗan farin ta,abinda yasa bana son zuwa saboda Khadija aƙwaita da shegen son jiki sannan ba tada jan dangin mijinta ajiki,duk da itama ƴar uwarmu ce don auren dangi a ka yi musu Babanta baba faruku Ƙanine awajen babanmu kuma uwa ɗaya uba ɗaya suke.
Babu yadda na iya washe gari da wuri na haɗa kayana bayan na gama gyara ɗakina harda babban farlonmu duk sai da na gyara sannan na nufi kitchen inda mama take aiki,na samu Nadiya tana cin ayaba sai zubar da ɓawon take,mama kuwa ko kallon ɓangaren Nadiyan bata yi ba,tana ta aikinta na rasa mama wata iriyar macece sam babu ruwanta da wani faɗace faɗa ce rayuwarta so simple ce,babu yadda za ayi inyi wa mahaifiyarsu Nadiya haka don mama bata taɓa bani ƙofar raina wani cikinsu ba,nima ko kallon Nadiyan banyi ba don nasan neman jaraba take na wuce wajen mama,da fara'a na ce"mama aƙwai abinda za'a ƙarasa miki ne?"ɗan murmushi ta yi sannan ta ce"a'ah na gama komai ɗauki abincin Kaka ki kai mata anjima kuma Boy zai zo ya ɗaukeki"?in dai kaji mama ta ce boy to yaya Aliyu take nufi ɗan farin mama don tana matuƙar ji masa kunya don ko hira sosai basu cika yi ba.


Tsaki naji Nadiya ta yi sannan ta fita,nasan sarai dani da mahaifiyata take amman bance komai ba na girgiza kaina na wuce.
Ina zuwa sashen Hajiya kaka na same ta tana kallon labaran safe a tv ɗinta,da fara'a ta amshi basket ɗin kayan karya kumallon na ta sannan ta ce"ABIN CIKIN ƘWAI Lafiya naga kin rame haka ko wanine ya taƁaki yanzu in saƁa masa".


Girgiza mata kaina na yi kafin in bata amsa naji sallamar Yaya Bilal,a take naji gabana ya yi wani mugun faƊuwa don tsabar tsoronshi da na ke ji,hajiya kaka ta kalleni ta daka min harara don tasan abinda na ke wa tsoron.




hajiya kaka ta ce"ke kuma me ye kika wani firgita kamar kinga wani namijin zaki"?.ɗan dai dai ta nutsuwa ta na yi sannan na ce"babu komai kaka bari inje mama za ta aike ni ne".


Hajiya kaka ta ce"hmm kyaji dashi dai da kin gansa sai ki kama wani rarraba idanuwa kamar mujiya yo sojan har wani abu ne da zaki dinga tsoronsa haka?Ni fa kakanku nasha yi masa kuka akan ya kaini barrek Ɗinsu don a tafi filin daga dani saboda rashin tsorona,yo me aka yi aka yi wani soja".


baiyi niyyar dariya ba amman sao da ya yi ya ce"to ke hajiya idan akaje naushi Ɗaya za'ayi miku ki baje awajen".


ni dai raƁewa na yi a gefe kamar wata munafuka ya buga min wani banzan kallo sannan ya ce"ke tashi ki fita ni sa'anki ne da zaki zauna kina kallon bakina ina magana,comon dalla tashi ki fita Ƙazama kawai me shegen kallo kamar mayya".




*Miss green ce*






*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*






1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_


5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_




Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k


*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*




Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.




Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144




Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224


...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....


*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[01/09, 13:40] my no: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚*


📃Littafi na 1








By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*




_*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_


*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------


*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------


masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.












17🟩18


...ina fita kaka ta kalli yaya Bilal ta ce"haba soja na me yasa ka ke damun yarinyar nan ne?ƴar uwarka ce fa?ni dai babu ruwana wallahi kada wataran kazo ka ce kana sonta Allah ko zaka mutu bazan baka ita ba. . ."da sauri ya ce"Allah ya tsare ni,ni kuwa duk matan garin nan sai ij rasa ƴar da na ke so sai wannan mai mugun halin,baƙa ƙirin kamar zunubi,ni dai kada ki ɓata min sauran nisha ɗina ni na yi nan".yana faɗar hakan ya tashi ya fita zuciyarsa fal haushin Khairat,shi fa yau ba zai iya cewa ya taɓa jin yana son wata mace ba ballan tana ma kuma Khairat da ya yi wa muguwar tsana.




"Haba Khairat me yasa kullum na ke gaya miki magana amman kamar a banza ne?shi fa namiji da ki ke ganinsa muddin ki ka cika nuna masa so to tabbas za'a samu matsala don ƙarshe ma sai ya ce ke ce ki ke sonsa,gwara ma ki yi saffa2 don Allah Khairat ki nutsu kisan inda ya ke miki ciwo don gaskiya idan ba haka ba za ki yi nadamar wannan mugun son da ki ke masa,ni dai kinji na gaya miki."


muna cikin wannan hirar ne Arman ya dawo daga makaranta,ya taho da gudu yana dariya ya ce"Sannu da gida Anty ABIN CIKIN ƘWAI".ɗan dukan wasa na kai mishi sannan na ce"wato ka ji hajiya kaka na faƊa min shine kai ma ka koya ko?"ƴar dariya ya yi sannan ya ce"anty yanzu ma Auncle bilal ya bani chocolate kin ganta ma".sai ya fara cirota a basket Ɗinsa na skull.ganin duk mode Ɗina ya canja Maman arman ta ce"kai zo ka wuce uban surutu kaje kaci abinci ka ce mero ta shiryaka zuwa islamiyya".da saurinya ce"umma su Aslamiyya baza su dawo ba auncle dee ya ce idan suka dawo sai ya zane su".


"Idan sun dawo ya kashe su ba sai ya gansu ba ma Aslamiyya ta koma kaduna da zama".da sauri na ce"maman arman daman baza ta dawo ba,amman na yi missing baby soba fa".ƴae dariya ta yi sannan ta ce"ai dole ayi missing Ɗin shegen surutunta da wasa na ke miki jiya abbansu ya ce shi fa bai yadda ta koma cen da zama ba,ƳaƳan na sa guda biyu".dariya na yi sannan muka cigaba da hirarmu tana Ƙara bani shawara akan yadda zan rage son yaya Bilal.abinda bata sani ba shine son yaya Bilal nisa sosai acikin raina son da na tun ina Ƙarama na ke masa sai yanzu rana Ɗaya ace in rabu dashi ko in rage sonsa ai binda ba zai taƁa yiyuwa bane.


ina shiga sashenmu na tarar mama har ta haƊa min kaya na ta ce"haba khairat daga zuwa kuma sai ki zauna"?.ki wuce ki yi wanka ga kayanki nan amman ki tsaya ki yi breakfast yanzu mukhtar ya shigo ya ce zai kaiki gidan".to na ce sannan na tuƁe kayana na faƊa ban Ɗaki na yi wanka na fito banyi wata kwalliya ba don ni ba amabociyar Ƙwalliya ba ce,idan na yi Ƙwalliyar ma bata wuce lipstic da hoda sai Ƙwalli,ruwan liptop nasha babu madara ya buƊa min cikina sannan na je wajen mama mukayi sallama sai ga yaya mukhtar ya shigo yasha shaddarsa mai Ƙyau ya yi Ƙyau sosai.Da kansa ya Ɗaukarmin kayan muka mama tana hanasa amman sai da ya Ɗauka muka fito su iman suna farlo har dasu salimat,kuma daman tunda batun aurensu ya matso naga sun wani jone,daman basu sakani cikin sha'aninsu nima ban shiga,ina ji salimat na ce wa"oh nadiya kuna ganin abinda na ke gani kuwa a cikin gidan nan?Wai yaya mk da girmansa amman ya Ɗakkowa wannan kucakar troley Ɗinta?".taƁe baki nadiya ta yi sannan ta ce"hmm mu fa ana ganinmu Ƴan iska ne amman aƘwai Ƴan bariki ƘwanƘwararru agidan nan don haka ba fa abin mamaki bane don kinga haka don su inyamurai daman haka suke kuma su koyawa ƳaƳan wasu ma".


rintse idanuwa na na yi ina juyosu suka cigaba da shewarsu suna Ƴan gulmarmakinsu na yi wuce wata.
***


tun a mota yaya mk ya cikani da surutu,a zuciyata na ce ah dole ne ka yi surutu tunda kai lawyer ne,ya kalleni sosai sannan ya ce"khairat kin tsayar da wanda ki ke so ne?".with full confidence ya faƊi hakan,wata muguwar kunyarsa naji na sunkuyar da kaina ina wasa da zara zaran yatsuna na,A hankali na ce"a'ah". Gabana yana ta faɗuwa ina jin kunyar ince masa ai yaya Bilal na ke soin gaya masa ko kuwa in yi shiru?.kafin in ƙara magana ya ce"good girl ki ce ko yanzu ia free ki ke?ah to masha Allah ya faɗi hakan yana yimin wani irin kallo mai cike da abubuwa acikinsa,Allah2 na dinga yi in sauka don maganganunsa ƙara tuno min da yaya Bilal suke sunkuyar da kaina kawai na yi har muka zo gidan ban ƙara ce wa komai ba,muna zuwa na fara yunƙurin fita cikin zaƙuwa na ke murɗa murfin amman ya ƙi buɗewa sai kuwa na juyo na kallesa naga yana yimin murmushi na tsura masa idanuwa sosai na mamakin rufe motar,sai yau na kalli yaya mk sosai fari ne ƙal kamar zaka taɓa shi jini ya fito kuma daman kaf ƴan gidanmu haka suke ni ce dai baƙa kuma nima bawai baƙar ce cen ba a'ah da ɗan haske na.


"Khairaty kenan kina tunanin zan barki ki fita ba tare dana gaya miki abinda ya ke damun zuciyata ba?abinda ya daɗe yana damuna kusan shekaru 7 tun kina ƴar ƙaramarki?to yau zan gaya miki in huta da wannan dakon soyayyar dana daɗe ina walagigi dashi".


sai ya ɗan ruƙo hannuna ya damƙe sosai cikin nasa ya kalli ƙwayar idanuwa na ya ce"khairat zuciyata ta kasance tana tare da ke ko da ke ɗin ba kya wajen?zuciyata tana mararin son ganinki ako da yaushe,zuciyata tana ƙaunarki da sonki,ki taimakamin ki yadda mu ƙulla soyayya mai ƙyau da kuma tsafta har ta kaimu ga aure."ya faɗi hakan yana kallona da idanuwansa da sukayi jawur yanzu yanzu".


kasa ce wa komai na yi don maganarsa ta girmi ƙwaƙwalwata ya ce"kinyi shiru khairat yin shirunki dai dai ya ke da rashin amincewarki,wallahi indai baki sona kada ki ƙwari kanki ki faɗa min don arayuwata ina son wadda take sona don mu rayu cikin so da kuma amince wa."
"Yaya Mk ka taɓa ganin wanda ya ke ƙin ɗan uwansa na jini?to bazan taɓa ƙinka ba nima ina sonka kamar yadda ka ke sona. . ."tun kafin in ƙarasa ya kama hannuna ya yi min kiss sannan ya ce"tnx so much khairaty ina ƙaunarki da yawa".idanuwa na ne suka firfito sosai tashin hankali ƙarara akan fuskata ban sake ce wa komai ba har ya buɗemin motar na fito.


A tare muka shiga cikin gidan dashi mai aikinta tana farlo tana goge tile muka shiga,ta gaishemu muka zauna nan ɗinma hirar soyayya ya cigaba da yimin,ni kuwa mamakinsa kawaai na ke daman haka ya ke?don a gida ba zaka taɓa tunanin haka ya ke ba don ko dariya bai cika yi ba,don ko da su Amina ƙannensa bai fiya wani hira ba.azuciyata na ce namiji kenan a harkar soyayya babu babba babu yaro kowa yi ya ke.
Ganin zaman na mu ya yi yawa ga shi har na gaji da hirar yaya mk na ce masa"bari inje ɗakinta ina tunanin bacci take".ya bini da kallo har na shiga ai kuwa baccin take ta ƙudunduna da bargo sai bacci take,ɗakinta duk kaya ko ina ga kayan yaya Aliyu nan daya cire haryanzu suna wajen mamaki sosai abin ya bani daman haka Anty Khadija take da ƙazanta ko kuwa ba abin mamaki bane don mahaifiyarta ma haka take,a hankali na fita daga ɗakin na samesa a farlo na faɗa masa bacci take ya ce"oky babu komai ni zan tafi don office na nan yana jirana".main compound na rakosa sannan na koma.
har na juya sai ya ce"khairat!".cikin wani irin salo kamar shi kaɗai ne ya taɓa kiran sunan na wa da haka a hankali na ƙaraso kusa dashi na ce"ga ni yaya"?.murmushi yayi sannan ya ce"daga yau adaina ce min yaya na fi son azaɓomin suna mai natuƙar daɗi".ɗan murnushi na yi kawai na yi wanda bai kai zuciya ta ba,na sunkuyar da kaina ban ƙara ko da ɗago kaina na kallesa ba don idan na kallesa sai inji kamar Yaya B,na ke ganin a gabana ba wai don kama ba a'ah tsabar son da na ke masa ne sai na ke ganin kamar duk wani namiji tamkar shine.


Ganin bazan ce komai ba sai ya ce"look! khairat ni fa wannan kunyar ta ki cutata kawai take wallahi,ni gaskiya mutum ne mara kunya gaskiya,kinga kuwa dole ne kema ki zama mara kunya don ina son a dinga bani kulawa yadda ya kamata".ɗan murmushi na yi don abin nasa dariya ya fara bani.daga nan mukayi sallama na miƙe na shige gidan har na shiga yana kallona yana bakin motarsa ya shafa sajensa wanda ya ƙwanta luf,wannan kuma gadone na ƴan gidanmu duk wani ɗan gidanmu zaka samesa da saje matuƙar kuwa ya fara girma to har da gemu.


Ina shiga na kalli mai aikinta na ce"bata ce ki ɗora mata komai ba"?.ta ce"eh gaskiya bata ce ba don idan tana bacci har sai ta tashi sannan a ke yi".ɗan taɓe baki a yi sannan na tashi na shiga ɗakin da ke kusa da na ta.wa'iya zubillah ɗakin duk ƙura haka na ajje kayana a waje na cire wanda nazo dasu na yi ɗaurin ƙirji na hau aiki tas-tas na gyara ɗakin sannan na kunna burner ta ƙamshi na shiga bayin ma na wanke shi tsaf na kunna na'urar busar da banɗaki wacce ke cire duk wani bacteria idan da aƙwai.


Ina fitowa na ce"mama iya farlo kawai ta ce ki dinga gyarawa ne"?ta ce"eh wallahi bata bani umarnin gyara ɗakinta ba kawai iya farlo ne,shima ada sai bayan ƙwana biyu sannan na ke sharewa wai bata don ƙura".mamaki sosai abin ya bani na wuce kawai ɗaki na faɗa wanka ina tunanin halin da yaya Aliyu ya ke,sam bai son ƙazanta don bai taso ya samu mamanmu na yi ba,tsaf za ta gyara ko ina har ɗakin Babanmu in dai ranar ƙwananta ne zakaji

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads