Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 22047 words

Chapter 1 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

335

Ads at the middle of Article

TAKOBIN ƊAUKAKA
Littafi na farko
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubuta Littafan Yaƙi
Haƙƙin Mallaka
©SUFI
Shekarar Rubutu
2/3/2021
Website:- arewanovels.com.ng
Phone number :- 08137237071










BABI NA ƊAYA




Saurayi ne kyakkyawa na gaban kwatance ke ta faman tafiya a cikin ƙasaitacciyar kasuwar birnin. sanye yake da tufafi riga da wando da aka sana'anta su da fatar damisa, hatta takalmin dake kafars an yi sa ne da fatar damisar, a hannunshi yana ɗauke da wata doguwar sanda, kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON MAYAƘI. Saboda da yadda ya tara ƙwanji tamkar duwatsu aka cusa mashi a ƙirjinshi.
Babban abin da yakara fito da kyawun sa shine zara-zaran gashin kansa daya zuba izuwa kan kafaɗun sa da kasumbar sa gemun sa baƙaƙe siɗik,
Haka dai saurayin ya cigaba da tafiya a cikin kasuwar babu sassauci,
Lokacin da shafe tsawon rabin Sa'a yana wannan tafiya a dai dai wannan lokaci ne sarauniyar dake mulkin birnin ta fito yawon shaƙatawa tare da dakaru masu tsaron lafiyar mutum dubu biyar.


Duk inda sarauniyar ta durfafa a kasuwar sai kaga jama'a sun da re sun bayan da hanya.


Bakomai yasanaya hakan ba sai domin tsananin tsoron fushin sarauniya lasmirat.


Ana cikin wannan hali ne sarauniyar lasmirat ta hango wannan kyakkyawan saurayi ya tunkaro inda take babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da fuskar sa.


Al'amarin da yayi matuƙar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai


Domin shekaru masu yawa tana fitowa wannan rangadi hakan bai taɓa faruwa ba


Su kuwa dakarun dake bayan ta sai zukatan su suka harzuƙa jikin su ya kama kyarma yana tsuma saboda tsananin fushi.


Kawai sai sarauniyar lasmirat ta daga hannun ta sama tana mai nuni da a tsayar da tafiya


Sannan ta dubi saurayin ta daka masa tsawa cikin fushi tace dashi" yakai wannan saurayi me kake takama dashi da bazaka risina agare ni ba.


Koda jin wannan tambaya daga bakin sarauniyar lasmirat sai saurayin ya kura mata idanu batare da yace da ita uffan ba


Cikin fushi lasmirat ta sake dakama sa tsawa a karo na biyu tare da maimaita tambayar ta.


Kawai sai saurayin ya saki wani tattausar murmushi daya karawa fuskar sa kyawu sannan ya dakamata sarauniyar lasmirat tsawa ya dube ta ya ce


" Yake wannan sarauniya mai takama da abinda bazai dawwa ma agare ta ba kiyi sani cewa bazan taba girmama ki ba.


Domin a halin yanzu abinda na sani kawai shi ne bambancin dake tsakani na dake shine ke ɗiya mace ce Ni kuma namiji, mulkin da kike takama dashi tamkar kumfar kogi ne akoda yaushe za'a iya neman sa a rasa shi,


Kafin saurayin ya gama rufe bakin sa fiye da rabin dakarun sun zare makaman su yunkura izuwa kansa suna ihu da kururuwa mai firgitar wa


Koda ganin hakan sai ya gyara tsayuwar sa gami da sandar dake hannun sa yana mai jiran karasowar dakarun


Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dabaru suka ruga izuwa kan saurayi sai yayi tsammanin dandazon zakoki ne suka farma barewa guda ɗaya, saboda tsananin kwarjini daban tsoron su ,


Yayin da ya rage saura baifi taku uku tsakanin su ba sai kawai akaga saurayin ya dako tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harboshi daga cikin baka yana saman ya sanya sandar sa ya daki kawunan dakaru mutum goma,


Take dakarun suka tsandara ihu sannan suka zube a kasa magashiyan,


Sannan ya dira bisa ƙafafuwan sa a turba cikin gwaninta,


Nan take aka kacame da azababban yaƙi matukar muni ban tsoro daban Al'ajabi.


Dakarun suka wanzu suna kaiwa saurayin sara da suka cikin matukar zafin nama JURIYA DA BAJINTA.


Shi kuwa ya wanzu yana kare hare haren su cikin wani irin baƙin zafin nama, kuma yana makosu da sandar sa daga kan dawakan su suna yin MUGUWAR HALLAKA, Na fa waje ya yamutse da ihu da kururuwar mazaje, karar karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne, gawarwakin dakarun suka watsu a wajen gasu birjik kwance cikin jini.


Sai da aka shafe tsawon sa,a ɗaya ana wannan gumurzun babu sassauci,


Sa'adda sarauniya lasmirat ta lura cewa saurayin ya hallaka fiye da rabin dakarun sai ta cika da matukar mamaki, domin a tarihin masarautar tun a zamanin mahaifin ta bata taɓa samun wanda ya hallaka dakarun gidan sarauta mutum uku ba,


Kuma zuciyar ta ta harzuƙa bisa ganin yadda dakarun ta keyin muguwar hallaka


Duk inda saurayin ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa kasa cikin mawuyacin halin dake tsakanin RAYUWA DA HALAKA


Nan fa dakarun suka ɗimauce bisa ganin iri kisan da saurayi keyi musu,


Amma koda kwarzane ɗaya basu samu nasarar yi masa ba.


Daga can nesa jama'ar kasuwar suna kallon fafatawar da ake yi waɗansu ta tagogin gidajen su suke leken abinda yake faruwa.


Kuma suka cika da mamaki bisa ganin yadda saurayi yazamewa dakarun sarauniyar lasmirat ANNOBA ƊARI wanda a tarihi hakan bai taɓa faruwa ba.


Lokacin da sarauniyar lasmirat ta fahimci cewa idan har aka cigaba da wannan artabu a haka dukkan dakarun ta zasu rasa rayukansu sai kawai ta dakamusu tsawa suka ja da baya sannan ta dako tsalle daga kan dokokin ta tamkar an harbota daga cikin baka ta sanya ƙafafuwan ta biyu ta daki saurayin a kirji da dukkanin karfin ta.


Saboda karfin dukan sai da saurayin ya yi katantanwa sau uku sai ya turje aka sake yin sabon kallon kallo tsakanin lasmirat da saurayin


Lasmirat ta kasance mace mai madaidaicin jiki ba doguwa ce ba gajera ba, tana da kyakkyawar fuska mai ɗauke da fararen idanu dara dara tana da siririn hanci wanda aƙasan sa aka yanka wani ɗan madaidaicin baki, wuyan yana kyawu tamkar na barewa, gashin kanta baƙi ne siɗik mai sheki da ƙyalli,ya zuba har izuwa ƙasan kwankwason taqKirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam bai rankwafa ba, cikin ta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, daga sama ƙugunta ya tsuke daga baya baya kuma ya buɗe yayi tudu sosai, tana da zabga-zabgan cinyoyi, fatar jikin ta farace mai ƙyalli.


Wohoho Hakika duk inda kyawu yake tabbas sarauniyar lasmirat ta kai, domin babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da lasmirat face ya kamu da matukar kaunar ta.


Yayin da aka shafe tsawon dakika talatin ana wannan kallon kallo, sai lasmirat ta zare wata zabgegiyar takobi a damtsen ta kaiwa saurayin wani wawan sara da nufin tsinke masa wuya,


Cikin baƙin zafin nama saurayin ya sunkuya takobin lasmirat ta sari iska,


Kawai sai suka kacame da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA


Ana fara wannan gumurzu ne lasmirat ta fahimci cewa tsananin KARFIN DAMTSEN saurayin ya nunka nata sau biyar gami da zafin nama.


Sai da sa,a ɗaya ta shuɗe ana fafatawa batare ɗayan su ya samu nasarar lakutar jikin ɗan uwan sa ba,


Bisa dole lasmirat ta sake zare wata takobin yazamana ta kai wa saurayin hari da takubba biyu,


Ana Cikin wannan artabu ne saurayin ya shammaci lasmirat ya gabza mata wawan naushi a fuska saboda karfin naushin sai da sarauniyar lasmirat tayi sama tamkar an janye ta kugiya,sannan ta faɗo ƙasa a matukar galabai ce.






***


Bayan gabatar mulkin sarki Hulbaru na birnin Misra anyi wata gagarumar sarauniya da ake yiwa laƙabi da lasmirat bintu kazmal


Lasmirat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance kuma gagarumar basadaukiya,mace mai kamar maza,daɗin daɗawa kuma mashahuriyar attajira ta shara ainun a fagen sanin ilimin tsafi,


A gaba ɗaya nahiyar babu kasa mai karfin tattalin arziki kamar ta ta


Sau tari manyan sarakunan duniya kan kaiwa lasmirat HARIN BAZATO domin mamaye ƙasar ta kuma su mallaketa a matsayin matar aure amma sai abu ya ci tira, domin duk sa'adda aka gwabza yaƙi sai dai sarakunan suyi asarar dakarun yaƙi da dukiya mai tarin yawa bisa dole suka janye aniyar su






***


Lokacin da sarauniya lasmirat ta fara ƙwaɗaituwa da son ɗa namiji sai ta gudanar da bincike bisa halarar tsafin ta domin taga irin namijin da ya dace ta aura


Abinda binciken ya tabbatar mata shine mijin da zata aura shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya


Binciken yakara tabbatar mata da cewa matsawar ta auri wani ɗa namiji ba shi har ta tara dashi tofa zata rasa komai nata da ta mallaka a duniya.


Sa'adda sarauniya lasmirat taga wannan al'amari a cikin halarar tsafin ta sai ta cika da matukar baƙi ciki maral musaltuwa


Taya za'ayi ace sarauniya kamar ni ace na auri wanda yafi kowa talauci a duniya, bayan cewa nafi kowa ne BASARAKE karfin mulki da tarin dukiya a wannan nahiya baki ɗaya.


Tabbas hakan ƙasƙanta daraja ta ne da ƙimata a idanun sauran sarakunan duniya


Kuma idan na auri talaka dukiya ta da mulki na zasu zamo bisa ƙarƙashin ikon sa.


Lokacin da sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai hankalin ta ya sake dugunzuma fiye da ko yaushe kuma ta rasa abinda ke yi mata daɗi,


A wannan lokaci lasmirat na zauna ne a bisa wata ƙasaitacciyar kujera amma sai ta miƙe tsaye ta shiga kai komo a cikin turkar ta.


Daga ƙarshe dai lasmirat ta yanke shawarar ta ziyarci wani boka dake zaune a wani gari dake iyaka da Birnin misra.






****


Lokacin da sarauniya lasmirat ta isa gidan boka Dayyubul-Barmas ta kaɗaita dashi a cikin turakar sa


Nan take ta kwashe labarin abinda ta gani a cikin halarar tsafin ta ta zayyanewa boka Dayyubul-Barmas tun daga farko har ƙarshe, sannan ta ɗora da cewa


Yakai wannan boka mafi girma a halarar tsafi kayi sani cewa Babban burina shi ne na auri mijin da yafi kowa Arziki a duniya sannan ina da burin na rayuwa kamar shekaru dubu biyu domin nazamo nafi dukkanin sarakunan duniya daɗewa a bisa karagar mulki.


Yayin da boka Dayyubul-Barmas yaji irin buƙatar dake tafe da sarauniya lasmirat sai ya jinjina al'amarin a cikin ran sa.


Tsawon daƙika arba'in bai ce uffan ba sai daga bisani ne ya dubi lasmirat yayi gyaran murya yace" ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa hakika kin zomini da al'amari mai girman gaske


Hakika bakaramar hikima kikayi ba da kika bayyana bukatar a gareni domin shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka a cikin sa baza ka kwashe Abin da ke ciki ba,


Kuma kinsan masu iya magana na cewa Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai hango ba, abin da bincike ya tabbatar mini ga me da bayanin ki shi ne.


Matsawar kina son ki fi kowa ne sarki daɗewa abisa karagar mulki kuma ki auri mijin da yafi kowanne kuɗi a duniya to yazama wajibi ki mallaki abubuwa guda uku domin ki samu nasarar samun ruwan koramar matsafi Daryalu


Da farko za,a nemo ruwan kogin ma'ul-hayatu,


Sannan waɗansu zobunan tsafi dake ajiye a kogon fatalwa a can yankin kasashen Larabawa a wani daji da ake yiwa laƙabi da Husumul-kadar


Abu na karshe shi ne kubar miftahul-daryal,


Shi dai wancan ruwa zamu yi amfani dashi ne a lokacin da zamu shiga wani daji kafin mu isa inda koramar boka Daryalu takr, ruwan zai bamu kariya ne daga waɗansu musifu dake dajin,


Su kuwa waɗancan zobuna zamuyi amfani da su ne a lokacin da zamu shiga gidan boka Daryalu rukuni na farko wajen sanya su a hannayen mu,


Domin babu yadda za,ayi mutum ya shiga gidan face ya na ɗauke da waɗannan zobunan sihirin,


Kubar miftahul-daryal kuwa zamu yi amfani da ita ne wajen buɗe gidan boka Daryalu


Dazarar mun samu nasarar ɗebo ruwan koramar kinsha to shi kenan bazaki auri wanda yafi kowa talauci a duniya ba.


Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai dai nan azancen sa sai hankalin sarauniyar lasmirat ya ɗugunzuma ainun


Ta dube sa cikin alamun tsantsar damuwa tace" ya Sarkin bokaye shin taya ya zan mallaki waɗannan abubuwa kafin ajali ya riskeni


Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa


Sannan daga bisani kuma ya fashe da kuka.


Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai ta dube sa ta ce" ya uban bokaye shin ina dalilin wannan dariya,da kuka naka?


Da jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya share hawayen dake sannan ya buɗi baki yace ya shugaba ta abinda ya sanya dariya shi ne bincike ya tabbatar mini dacewa a wannan zamani nine bokan da zan samu ɗaukaka fiye da kowa ne matsafi domin ya cika burin mahaifin mu.


Abinda Ya sa ni kuka kuwa shi wani bakon jarumi zai rushe wannan ɗaukaka tawa ta yadda ko tarihina bata sake tunawa a duniya ba


Kuma wannan jarumi ba wani bane face namiji da zaki aura har ki samu Haihuwa wanda yafi kowa talauci a duniya


Sai dai iyakar bincike ne na kasa gano ainahin a nahiyar da saurayin yake,


Domin jarumin yana yana ɗauke da waɗansu sirrika masu basa kariya,


Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai -dai nan a jawabin sa, sai hawaye suka sake zubo masa,


Nan take Sarauniya lasmirat taji ta kamu da matukar tausayin sa


Dayyubul-Barmas ya cigaba da cewa ya sarauniyar kyawawa kiyi sani cewa bazaki taɓa fin kowane sarki daɗewa abisa karagar mulki ba face kin mallaki wata takobin da ake yi wa laƙabi da TAKOBIN ƊAUKAKA,


A salin TAKOBIN ƊAUKAKA ta wani gagurtaccen mayaki ne ma'abocin addinin musulunci.


Bayan shuɗewar jarumi Hilal ne wani mashahurin matsafin aljani ya sace takobin ya shiga halarar tsafi ta tsawon shekaru arba'in yana sana'anta takobin da sirrikan tsafi


An kira takobin da suna TAKOBIN ƊAUKAKA ne saboda duk jarumin da ya mallake ta zai samu ɗaukaka a duniya


Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya kammala halwar sa sai yaga wani Al amari da ya firgita sa kuma ya ɗimauta sa,


Abinda ya gani shi ne bazai taɓa samun amfani da TAKOBIN ƊAUKAKA ba ajali zai riske sa.


Wani jarumi wanda bai kasance kowan kowa ba shi ne zai mallaki takobin ya lalata sirrikan tsafin dake jikin ta kuma ya ɗaukaka a duniya,


Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya ga wannan al'amari sai ya cika da baƙin ciki


Kawai sai aljani Sautul-Hidar ya ɗauki TAKOBIN ƊAUKAKA ya caka a kirjinsa a saitin ƙahon zuyar sa,


Faruwar hakan ke da wuya sai numfashin sa ya ɗauke komai na jikin sa ya daina motsi ya sandare,take gangar jikin sa ta zagwanye ta zama wani irin ɓakin ruwa mai yauƙi,


Daga bisani sai ruwan ya rikiɗa izuwa waɗansu irin gabza - gabzan samudawan aljanu dukkanin suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro a hannayen sa rike da waɗansu irin makaman yaƙi masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi,


Koda bayyanar aljanun sai wani daga cikin su wanda da alama shi ne shugaban su ya ɗauki TAKOBIN ƊAUKAKA ya sanya ta acikin wata akwatu ta farin gilashi ya ɗauki akwatin da takobin ke ciki ya shiga sanya ta acikin waɗansu akwatin har guda dubu,


Sannan ka sa dakarun aljanun izuwa kowace kusurwa ta gidan domin tabbatar da cikekken tsaro ga takobin


Tun daga wannan rana waɗannan aljanun suke gadin gidan boka Sautul-Hidar dake kan tsaunin lauhul- azwar


Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa duk ɗaya daga cikin wadannan aljanun yana iya kayar bil'adama guda miliyan daya


Ke nan hakan ya nuna cewa aljanun zasu iya yakar duniya baki ɗaya.


Tabbas a halin yanzu tunkarar gidan aljani Sautul-Hidar dai dai yake da mutum ya buɗe taskar ANNOBA DARI


****


Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo daidai nan ajawabin sa.


sai idanun sarauniya lasmirat suka zazzaro kuma tsoro ya kamata, ta shiga damuwa ainun kamar tacewa boka Dayyubul-Barmas ta janye buƙatar ta,


Amma sai ta dube sa cikin karfin hali da ƙi faɗi irin nasu na sarakuna tace" ya uban bokaye shin yanzu yaushe zamu yi wannan gagarumar tafiya ta ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA?


Dayyubul-Barmas ya gyaɗa kai yace"ya sarauniyar kyawawa ai komai ya na hannun ki duk lokacin da kika shirya tafiya a shirye nake,


Koda jin batu sai sarauniya lasmirat tayi godiya a gare sa ta ɗebo dukiya mai mai yawa ta basa


Wannan shi ne cikekken tarihin sarauniya lasmirat,






****






Koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawan saurayin ya sakarwa sarauniya lasmirat dake kwance a ƙasa wani tattausar murmushi


Har saurayin ya juya da nufin da nufin ya cigaba da tafiya a cikin kasuwar, sai yaji alamar motsin tafiya a bayan sa. Koda ya waiga sai yayi arba da ita fuskar cike da annuri ba wata ba ce face sarauniyar lasmirat.


lasmirat ta dube sa tace" yakai wannan kyakkyawan saurayi ma'abocin sadaukantaka idan baza ka damu ba ina bukatar nayi maka waɗansu tambayoyi, kuma ina neman wata alfarma guda ɗaya a wajen ka.


Koda jin wannan batu sai saurayin ya yi murmushi har fararen haƙoran sa suka bayyana ya dubi lasmirat yace" yake wannan sarauniya faɗi duk abinda kike son tambaya ni kuwa zan baki amsar ta dai dai abinda na sani.


Lasmirat ta dubi saurayin da wani irin kallo mai ɗauke da alamar tambaya sannan tace


"Yakai wannan saurayi shin mene ne sunan ka da ma






Abinda Ya Kawo izuwa wannan birni nawa


Alfarmar da nake nema a wajen ka ina so ka biyo ni izuwa gidan sarauta domin ina so mu tattaunawa wata muhimmiyar magana


Yakai wannan jarumi kayi sani cewa kai ne jarumi na farko a rayuwa ta dana taɓa fafata yaƙi da shi har ya samu nasarar kai ni kasa


Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tambayar ta sai saurayin ya dube ta yace


" Ni dai da farko suna na yaslir ibn Hulzal na fito ne daga wata nahiya da ake yiwa laƙabi da Nashmir


Game da Alfarma da kika nema a waje na kuwa bazan amince da ita ba


Sai kin yarda kuma kinyi mini alkawarin cewa zaki dunga daraja kowane ɗan adam,


Ma'ana za ki dai na azabtar da mutane da zaluntarsu,


Sa'adda saurayi yaslir ibn Hulzal yazo nan a zancen sa sai sarauniya lasmirat ta zurfafa izuwa kogin tunani


Sa'adda talakawa da sauran jama'ar kasuwar suka ga yadda sarauniya lasmirat ta ƙasƙanta kanta a gaban saurayin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi domin fiye da shekaru masu yawa hakan bai taɓa faruwa tunda lasmirat ta hau bisa karagar mulki


Daga can sai ta ɗago da kanta da dubi saurayi yaslir tace"na amince da wannan sharaɗi naka yakai wannan jarumi,


Koda gama faɗin hakan sai sarauniyar lasmirat ta yiwa wani badakare inkiya da hannu kamar badakaren yasan abinda take nufi sai kawai ya janyo waɗansu fafaren dawakai ya iso gaban ta ya risina ya rike ta linzamin dokin ɗaya,ta kama ta hau.


Ta na mai yiwa yaslir

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads