Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 22047 words

Chapter 5 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

338

Ads at the middle of Article

nan take tiririn zafin ya sumar da su boka Dayyubul-Barmas.


















Mutumin mai siffa biyu ya bushe da dariyar mugunta bisa ganin wannan gagarumar nasara da ya samu akan su boka Dayyubul-Barmas,


Dariyar tasa ta haddasa girgizawar kogon, a lokaci guda kuma ya tsuke bakin sa tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA kawai sai ya nufi wata kofa a cikin kogon dutsen,


Kwatsam bazato babu tsammani sai mutumin yaji an dankara masa wawan sara a gadon bayan sa,


Saboda karfin saran sai da sai da takobin ta nutse a gadon bayan sa,


Kawai sai ya kwarara ihu tare da waigawa bayan sa domin ya ga wanda ya sareshin.


Ai kuwa yana waigwa sai yayi arba da jarumi yaslir hannun sa riƙe da zaratan takubba masu kaifi da tsinin tsiya,


A dai dai lokacin ne jini yafara kwaranyo wa daga inda yaslir ya sare shi ,


Mutumin ya dakawa yaslir tsawa wanda ta sanya kogon ya amsa da karfi,


Bisa mamaki sai mutumin yaga ko gezau yaslir bai yi ba, al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan,


Domin bai taba dakawa wata halitta tsawa ba face ta ɗimauce,ko ma ta rasa rayuwar ta,


Wani tunani da ya faɗo masa shi ne, taya ya wani makami yayi tasiri akan sa Bayan cewa hakan bai taɓa faruwa ba,


Lallai bakaramin kuskure kayi ba da ka manta da wannan bil,adama,


Sa'adda halittar yazo nan a tunanin sa sai zuciyar sa ta kama tafarfasa tamkar zata kone jikin sa yakama kyarma yana tsuma tamkar mazari,


Kawai sai ya miƙa hannun sa ya ɗauko wannan Gatari nasa Sannan ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan yaslir yana mai ɗauke da su boka Dayyubul-Barmas a ɗaure a jelar sa,


Sa,adda yaslir yaga halittar ya rugo izuwa gare sa cikin mugun tanadi,


Sai kawai ya gyara tsayuwar sa, lokacin da ya rage sauran taku


Sai yaslir ya dako wawan tsalle tamkar an harbo sa daga cikin baka yana saman ya kaiwa halittar sara da takubban sa biyu a kafaɗa,


Bisa sa,a sai gashi ya same Shi har jini na zuba a kafadar tasa


Cikin gwanin ta yaslir ya yi katantanwa a sama sau uku ya dira ƙasa a bisa duga-dugan sa cikin gwanintar yaki,


Sannan suka kacame da azababban artabu mai matukar muni,ban tsoro daban al'ajabi,


Sai da aka shafe tsawon sa,a biyu ana wannan gumurzu babu sassauci,


Tsawon wannan lokaci babu wanda ya samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin sa,


Duk sa'adda mutumin mai siffa biyu yakaiwa yaslir sara inda ya goce duk abinda gatarin ta sauka a kansa sai kaga wajen yayi rami mai zurfi,


Idan akan Dutse ne sai Dutsen yayi bindiga ya tarwatse,


Kafin cikar dakin talatin yaslir yafara galabaita saboda yadda yake zillewa harin mutumin,


A dai dai lokacin ne kafafatun yaslir suka faɗa cikin wani rami a kogon kuma wani dutse ya danne sa,


Wohoho! Wuya mai sa dole, shi kuwa tsoro na iya sawa mutum ya aikata abin da ko a mafarki bai taba tunanin zai iya ba idan yaga bala'o'i,


Koda yaslir yaga halin da yake ciki kuma ya tabbatar da cewa idan har bai yi wani abu ba zai iya rasa rayuwar sa


Sai kwai akaga yaslir ya sanya hannayen sa biyu ya ture Dutsen daya danne sa ta ƙarfin tsiya,kuma ya naushe sa da hannayen sa biyun cikin baƙin zafin nama take dutsen yayi sama tamkar an janye da ƙungiya ya daki fuskar mutumin mai siffa biyu,


Take halittar ya ɗimauce ya gigice yayi jifa da gatarin sa ya sanya hannayen sa biyu akan fuskar sa yana rusa ihu,


Koda yaslir ya duba hannun daya naushi dutsen sai yaga ko ɗan yatsan sa bai karye ba ballantana hannun yayi ciwo,


Sai ya cika da matukar mamaki, kawai ya kama gefen ramin da ya faɗa ya fito waje,


Yana fitowa sai ya zare wata takobin daban a jikin sa ya falfala da azababban gudu zuwa kan halittar ya daka tsalle sama ya soka masa takobin a ƙahon zuciyar sa,


































Nan take mutumin ya kurma wawan ihu sannan ya fadi kasa,yana shure-shuren mutuwa jini ya dunga kwarara da tsartuwa daga kirjin sa.


Kafin wani lokaci komai na jikin sa ya daina motsi alamar rai yayi halin sa,


Take wannan wuta dake ci a cikin wannan akwatu na mutu murus kuma jelar halittar dake daure da su lasmirat ta sake su,


Sakamakon jinin dake zuba daga jikin halittar shi ne yayi sanadiyar farfaɗowar su boka Dayyubul-Barmas,


Sunaila ce ta fara farfaɗowa koda ta buɗe idanuwan ta dake rufe cikin baƙin yanki koda tayi arba da yaslir a tsaye rike da takobi tsirara jikin sa duk ta ɓaci da jinin mutumin mai siffa biyu daya hallaka, sai ta cika da matukar mamaki,


Sannan baka Dayyubul-Barmas, lasmirat suka cika da Mamaki bisa ganin bajintar yaslir.


Bayan kowa ya samu nutsuwa kuma ya sanya wa kansa magani a raunin dake jikin sa,


Sai aka sake ɗungumawa aka fice daga cikin kogon dutsen


Lokacin da Sunaila wacce Ita ce a ƙarshe ta fita sai ƙofar kogon ta mayar da kanta ta rufe tamkar bata taɓa budewa ba,


Haka dai su boka Dayyubul-Barmas suka dunga shiga kogunan dutsen yazamana cewa sun sha ɓakar wahala wajen yaƙar halittun dake ciki


Sai a kogo na biyar ne bayan sun samu nasarar fafata yaƙi da wata SIHIRTACCIYAR mucijiya suka samu nasarar ɗauko zobunan sihiri,


Amma kowannen su ya samu raunuka a jikin sa masu yawan gaske,


Domin sai da su kayi kwana shida suna jinyar jikin su sannan suka fice daga dajin da fitar su suka tarar da aljani Huzmal ya bararraje yana ta sharar barci,


Tabbas Bambancin aljani da bil'adama a bayyane yake yanzu duk tsawon kwanakin da muka shafe a cikin wannan daji Huzmal barci yake yi bai farka ba,


Jaruma Sunaila da yaslir ne sukayi wannan furuci a zukatan su batare da sun bayyana kowa ya ji ba.


Boka Dayyubul-Barmas ya katse shirun daya wanzu ta hanyar zungurar aljani Huzmal da kwagirin tsafin sa dake rike a hannun sa,


Firgit! Huzmal ya ɗago kansa yana mutsittsike idanu cikin magagin barci, yace" Kai wane ne ya katse mini wannan daddaɗan barci da nake yi wanda ban fi daƙiƙa goma da farawa ba,


Koda jin wannan batu sai boka Dayyubul-Barmas ya dakamasa tsawa yace" kai bana son maganar banza yi maza ka ɗauke mu izuwa tsaunin SHAFRAS domin ɗauko kubar miftahul-daryal


Ka sani cewa daga nan izuwa tsaunin SHAFRAS tafiya ce ta tsawon kawanki arba'in bisa ingarmar doki,


Ina so ka kai mu a cikin abinda bai gaza kwanaki uku kacal ba,






















Sa'adda Huzmal yaji wannan batu daga bakin mai gidansa boka Dayyubul-Barmas sai ya wartsake ya dawo cikin hayyacin sa ya dubi Dayyubul-Barmas cikin ladabi ya ce" Ka gafarceni ya shugabana naji dukkan bayanin ka amma ina so nayi maka wata tambaya wai shin kwanaki nawa kuka shafe a cikin wannan daji?


Koda wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas yace " Kwanaki arba'in muka shafe


Huzmal yace "Taɓ ɗi jan amma kuwa in dai haka ne ku bil'adama kuna hakuri da kuƙe yin barci sau ɗaya a rana,


Amma ni gashi na shafe tsawon kwanaki arba'in i na barci amma ji nayi tamkar barcin daƙiƙa goma na yi,


Ya shugabana na rantse da girman halarar tsafin ka inda za,a bani gaba ɗaya kwanakin rayuwar da kowannen ku zai yi a duniya a ace nayi barci iya adadin kwanakin a waje na bai huce kaso ɗaya bisa uku na barcin da na keyi a rana ɗaya ba,


Sa'adda aljani Huzmal yazo nan azancen sa sai mamaki ya turnuƙe yaslir,Sunaila da sarauniya lasmirat har dariya ta kuɓucewa musu,


Huzmal na kammala wannan furuci sai ya shimfiɗe gadon bayan sa kowa ya hau ya zauna


Sannan ya bude manyan fuka fukan sa ya luluƙa izuwa sararin samaniya, cikin matsanancin gudu babu sassauci,


******. *****. ******


A,amarin su tawagar sarki Hamras kuwa, waɗanda ya tura domin su yanko masa gashin kan boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat domin ya samu nasarar mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA kuwa bisa jagorancin aljani Huruful-labarus kuwa


Sun wanzu suna gudu a bisa sararin samaniya domin zartar da umarnin shugaban su,


Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai tsulum suka ga wani ɗan wadan aljani ya bayyana tsulum a gaban su tamkar an jefoshi daga sama,


Aljanin ya na ɗauke da ranƙwalelen kai mai ɗauke da manyan idanu ja jajur.wuyan sa ɗan siririn ne tamkar na barewa, kai bazaka taɓa cewa wuyan nasa zai iya ɗaukar nauyin rafkeken kan nasa ba, yana ɗauke da tafkeken kirji mai ɗauke da curi curin tsoka,


Cikin sa rubdumeme ne tamkar an kifa kwarya, ƙafafuwan sa yan sirara ne tamkar sillan kara, yana ɗauke da wata murtukekiyar jela, Du dudu tsawon sa bai huce kamu ɗaya ba,


Tabbas duk inda muni yake wannan aljani ya cika mummuna, idan kuwa za,a yi gasar muni ta duniya zai iya zama na ɗaya,


Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su aljani Huruful-labarus da aljanin,


Daga can sai Huruful-labarus ya dubi aljanin ya dakamasa tsawa ya dube sa a wulakance yace" yakai wannan ɗan ƙaramin kwaro a cikin aljanun duniya, shin wane ne kai, kuma wane irin rashin sani ne ya kawo ka nan wanen,


Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin naga irin hukuncin daya dace dakai,


Koda jin wannan batu daga bakin aljani Huruful-labarus sai aljanin ya kyalkyale da dariya har da kwalla,


Al'amrin da yayi matukar bawa Huruful-labarus da tawagar sa mamaki kenan kuma ya basu mamaki,


Abin da ya basu mamaki shi ne taya ya wannan aljani da bai huce ɗaya daga cikin su ya maƙure shi ba zai dunga ɓabbaka musu dariya


A lokaci guda ɗan wadan aljanin ya tsuke bakin sa kuma ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da


SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya yace" yaku waɗannan kananan jarumai kuyi sani cewa suna na Sahibul-Muluk,


Kuma Ni ne shugaban yan fashin aljanun wannan nahiya baki ɗaya, Hakika kunyi babban kuskure da har kuka tsaya a gaba na kuke faɗa mini magana amma yanzu zan ganar daku kuren ku,


Koda jin wannan batu sai aljani Huruful-labarus ya fusata ainun ya dakawa yaran sa tsawa su kayi ɗauki kan Aljani Sahibul-Muluk suka ihu da kururuwa mai firgitar wa,


Nan take aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro daban al'ajabi,














Sa'adda da aka yamutse da azababban artabu tsakanin shugaban Yan fashin wadannin aljanun duniya,


Wato aljani Sahibul-Muluk, da tawagar aljani Huruful-labarus,


Sai yaƙin yazamo abin tsoro gami da ban mamak,


Domin kuwa duk irin girma da kwarjinin Huruful-labarus da yaransa sai ya zamo abanza,


Domin kuwa Sahibul-Muluk yazame musu alƙaƙai sun rasa yadda zasu yi dashi,


A inda zaka ga ya taƙarƙare ya ƙirɓawa ɗaya daga cikin su naushi yayi katantanwa sau uku ya faɗo ƙasa tim!


A wasu lokutan idan hannun sa ya naushe su sai dai kaji kashi yayi ƙara ruƙus,


Nan fa ihu da hargowar aljanun ta ci ka dajin baki ɗaya,


Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje sai yayi tsammanin cewa YAKIN DUNIYA ya taso,


Sa'adda da aljani Huruful-labarus dake tsaye a gefe guda ya na kallon artabun da akeyi yaga yadda aljani Sahibul-Muluk yazame wa yaran sa ANNOBA ƊARI,


sai ya cika da matukar mamaki kuma ya fusata ainun,


Abin da ya basa mamakin shine yadda Sahibul-Muluk ke ragargazar dakarun tamkar na'ura ce ke sarrafa shi,


Tabbas wannan shine fa abin da masu iya magana


ke cewa" GABA DA GABANTA


Aljani ya taka wuta"


Koda Huruful-labarus ya lura cewa idan har aka cigaba da wannan yaƙi a haka dakarun nasa zasu iya karewa sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen sa yayi ɗauki kan Aljani Sahibul-Muluk,


Aka ruguntsume da sabon azababban yaƙi, Sahibul-Muluk ya tare sa ya wanzu yana kare hare haren tare da mayar da martani ta hanyar kai bugu da naushi,


Ana cikin wannan yaƙi ne Huruful-labarus ya samu nasarar laftawa Sahibul-Muluk wani sara, jini yayi tsartuwa ya zuba a ƙasa,


Sahibul-Muluk ya kwarara ihu sakamakon tsananin zafida zugin da yaji, cikin zafin nama ya mayar da martani ta hanyar kai wa Huruful-labarus naushi a fuska,


Huruful-labarus ya zille tare da zamewa harin sannan ya sanya takobin sa a karo na biyu ya tsarge Sahibul-Muluk gida biyu, take gangar jikin ta fado ƙasa rikica jini ya kwarara tamakar an buɗe fanfo,


Koda samun wannan nasara sai Huruful-labarus ya ɗaga kansa izuwa sama ai kuwa sai yayi arba da wata yar ƙaramar halitta,


Bata ba ce face Aljani Huzmal ɗauke da su sarauniya lasmirat,


Nan take Huruful-labarus ya busa musu wata irin gagarumar Iska daga bakin sa,


Tsananin karfin iskar ya tashi hankalin duk wata halitta dake rayuwa a dajin, kuma ta sanya fuka-fukin aljani Huzmal na ɓangaren dama ya karye take suka rikito daga sararin samaniya,


Sai suka faɗo a kan tafin hannun Huruful-labarus Huzmal yana mai tsandara ihu sakamakon tsananin raɗaɗin da yaji a fuka fukin sa daya karye,


Sarauniya lasmirat,boka Dayyubul-Barmas, yaslir da Sunaila kuwa sun galabaita ainun domin koda wata gaɓa a jikin su basa iya motsawa,


Cikin matukar farin ciki aljani Huruful-labarus yace" yaku abokan tafiya kuyi sani cewa wani abin farin ciki ya same mu ku sani cewa waɗannan bil'adama da kuka gani akan tafin hannu na sune abinda muka fito nema wato sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas,


Koda gama faɗin hakan sai ya nuna su sarauniya lasmirat da ɗan yatsan sa na hagu take wata igiyar tsafi ta bayyana a ɗaɗɗaure su tamau!


Kawai sai ya jefasu a cikin aljihun rigar sa tamkar ya jefa kwallon goriba,


Kawai sai ya yunƙura ya tashi zuwa sararin samaniya yana tsala gudu yaran sa na biye da shi.


Huruful-labarus da tawagar su ka cigaba da tsala gudu a sararin samaniya ɗauke da su sarauniya lasmirat a cikin aljihun sa,


Sai da suka shafe tsawon dakika ɗari huɗu sannan aljani Huruful-labarus yayi umarni a yada zango


Inda aka yada zangon yakasance daji mai matukar kwarjini daban tsoro,


Yana ɗauke da waɗansu dogayen bishiyu masu siffofin ban tsoro,


Ko iya shirun da wanzu a dajin ya isa ya jefa tsoro a zukatan JARUMAI,


Yayin da aka sauka a cikin dajin sai a kayi turus!


Bakomai akaga ni face wani kyakkyawan saurayi sanye da fararen tufafi zaune bisa wani buzu na fatar damisa ya fuskanci alkibila yana gabatar da wata irin ibada mai ban mamaki,


Nan fa aljani Huruful-labarus da yaran sa suka ƙurawa saurayin idanu cikin tsananin Mamaki,


Abu na farko da ya basu mamaki shi ne taya ya bil'adama guda ɗaya ya shigo wannan daji mai matukar haɗari, alhalin shi bai kasance wani mashahurin matsafi ba,


Wani abu da yafi ɗaure musu kai shi ne menene yasanya da saurayin yayi arba dasu bai firgita ba,


Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan,


Kawai sai suka zuba idanu suna kallon yadda saurayin yake gudanar da ibadar,


Bisa mamaki sai suka ga ashe har ya kammala ibadar tasa ya ɗauki wata jakar fata ya rataya a kafaɗar da ya kunna kai izuwa wani bangare a dajin,


Al'amarin da ya fusata Huruful-labarus kenan yasha gaban saurayin yana mai dakama sa tsawa ya dube sa cikin matukar fushi yace


"Yakai wannan saurayi ma,abocin GAJERAN KWANA,


shin wane ne kai a cikin bokayen duniya da har zaka nuna rashin ladabi a gareni?


Koda jin waɗannan tambayoyi sai saurayin yayi murmushi da ya ƙarawa fuskar sa kwarjini da haiba kawai ya sake kunna kai izuwa dajin batare da ya bawa Huruful-labarus amsar tambayar sa ba


Cikin fushi Huruful-labarus ya kai masa duka da fuka-fukin sa


Kafin dukan yakai saurayin ya ɗaga hannayen sa sama ya karanta waɗansu addu,o,i na musamman ya shafa a fuskar sa,


Kawai sai aka ga wata irin murtukekiyar igiya ta ta ɗaɗɗaure aljani Huruful-labarus da yaransa kuma igiyar tsafin da ta ɗaure su sarauniya lasmirat ta bace ɓat, suka faɗo daga cikin aljihun rigar aljani Huruful-labarus,


Har a wannan lokaci a matukar Galabaice suke boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat kaɗai basu ji jiki sosai ba,


Yayin da saurayin yayi arba da su lasmirat sai ya cika da matukar mamaki.


Lasmirat ta miƙe tsaye da 'ƙyar boka Dayyubul-Barmas yayi koyi da ita, yaslir d Sunaila da aljani Huzmal na zaune dirshen a ƙasa cikin halin galabaita.




Sa,adda lasmirat ta haɗa idanu da saurayin sai taji wani abu ya ɗarsu a zuciyar ta wanda ta kasa Bamban ce ko mene ne a iya tsawon rayuwar ta bata taɓa ganin namiji mai kyawun saurayin ba,


Kallo ne ya wakana a tsakanin su na ɗan wani lokaci lasmirat nayi masa kallo mai ɗauke da alamar tambaya,


Daga can sai lasmirat ta buɗi baki cikin wata irin tattausar murya mai rikita duk wani ɗa namiji cikin annurin fuska ta ce


"Yakai wannan saurayia ma'abocin kwarjini da haiba shin wane ne kai?


Kuma ya akayi ka samu nasarar ceto rayuwar mu a hannun waɗannan aljanu?


Koda jin waɗannan tambayoyi sai saurayin ya zurfafa izuwa kogin tunani da ga bisani ya dubi lasmirat da fararen idanun sa masu haske tamkar madara cikin zazzakar murya yace


"Yake wannan sarauniya ma'abociyar kyawu game da tambayar ki ta farko


Suna na shamsuddin ibn Abbas na baro birnin mu ne domin ɗaukaka kalmar Ubangiji.


Na samu nasara akan waɗannan aljanu ne ta hanyar neman taimakon Ubangiji na ,


Cikin matukar mamaki lasmirat ta sake budar baki a karo na biyu tace" shi wane ne wannan Ubangijin naka?.


Shamsuddin yayi murmushi yace" Ubangijina shi ne wanda ya halicci duniya da abinda ke cikin ta babu abin da ya gagare sa komai yana iko a kansa, shine mai ciyar da tsuntsayen dake cikin duhuwar daji dama kifaye da ke karkashin Teku,


Tsananin duhun dare ko na Teku baya ɓuya gare sa.






Jarumi shamsuddin ya cigaba da jawabin sa bisa tambayar da sarauniya lasmirat ta yi masa,


A inda ya cigaba da cewa Ubangiji shi ne ya wanzu tun babu babu ita kanta,


Bashi da farko ba shi da ƙarshe,


Sa'adda sarauniya lasmirat taji wannan jawabi sai nan take mamaki ya kamu ita da abokan tafiyar ta,


Shiru ne ya wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci daga bisani lasmirat ta matsa daf da inda shamsuddin yake ta yadda suna iya jin numfashin juna ta dube sa tace"yakai shamsuddin ina so ka ɗan bani lokaci zan yi shawara da abokan tafiyata,


Da jin wannan batu sai shamsuddin ya gyaɗa kai


Lasmirat ta matsa kusa da abokan tafiyar ta ta dube su tace" Yaku abokan tafiya ta shin me kuke gani game da wannan baƙon jarumi shamsuddin Ni ina ganin idan muka haɗa tafiyar dashi zai bamu wata gudun mowa ta musamman, domin ku duba fa kuga yadda Ubangijin sa ya bore masa sarrafa aljanu


Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya lasmirat sai boka Dayyubul-Barmas ya dube ta cikin kakkausar murya fuskar sa a murtke tamkar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA,


Yace"ya shugabata kiyi sani cewa ni ashawara ta bazamu haɗa tafiyar mu da wannan baƙon jarumi ba domin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads