Showing 21001 words to 22047 words out of 22047 words
Chapter 8 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt
gurnani mai sanya firgici daban tsoro.
Nanfa aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro yazamana cewa kowa ya gane kuren sa,
Sai da aka wuni cir ana artabu babu sassauci, sannan aka samu nasarar hallaka halittun amma kowa ya samu manyan raunuka a jikin sa
Nan fa yazamana cewa tsananin azabar dasu lasmirat suka sha tasa jikin su yayi sanyi kuma gwiwoyin su sukayi sanyi dukkanin su suka yi nadamar yin wannan tafiya domin wata buata ta jin dain duniya musamman sarauniya lasmirat,
Bisa wannan dalili ne yasanya dukkanin su suka yanke shawarar karbar addinin Musulunci
Bayan sun karbi kalar shahada ne a wajen shamsuddin
Sai shamsuddin ya bayyana wa sarauniya lasmirat cewa dukkanin bayanin da boka Dayyubul-Barmas yayi mata aiki ne. Na bokaye ma,ana sihiri shi kuma sihiri karya ne
Saboda haka imani da tayi da Ubangijin musulunci zai biya mata dukkan bukatun ta kuma muradin ta ya cika na samun aukaka a duniya da ma tsawon rayuwa
A sannanne Sunaila ta cire rawanin dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili arara
Sa, adda kowa ya yi arba da fuskar sulaina sai mamaki ya kamashi ,
Yaslir kuwa bai san sa,adda ya ruga izuwa inda take ba ya kura mata idanu hawaye na zuba daga fuskar sa
Nan take ita ma Sunaila kwalla ta zubo mata
Bakomai ne ya sanya hakan ba sai domin a yanzu ne yaslir ya tabbatar da zargin sa cewa Sunaila ita masoyiyar sa gimbiya salimat
Kawai sai suka rungume juna cikin matukar farin ciki maral musaltuwa gami da tsantsar soyayya hade da shauin juna,
Ana cikin wannan hali ne sai kawai akayi arba da boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum hannun sa rike da wata zabgegiyar takobi ta haske mai matukar kyawu ba wata ba ce takobin ba face TAKOBIN AUKAKA
Abinda basu sani ba shine. A lokacin da yaji dukkan su sun karbi addanin Musulunci sai ya faki idanun su ya bace yaje ya haa kai da sarki Hamras mai gidan su aljani Huruful-labarus, da tsohuwa zahira wacce sarki Hamras ya shiga gidan ta a cikin wannan daji a lokacin da ya fito farautar shamsuddin ,
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su shamsuddin da su boka Dayyubul-Barmas,
A lokaci guda boka Dayyubul-Barmas,sarki Hamras ,tsohuwa zahira suka yi kukan kura suka afkawa shamsuddin da azababban yai mai matukar firgici da tashin hankali,
Dakyar shamsuddin ya hallaka su duka bisa taimakon Ubangiji dukkan su sukayi mutuwar hulakanci
Tabbas da ace mutum yana wannan waje zai ga yadda gawar boka Dayyubul-Barmas ta hulakanta dole ne takaici ya kamasa bisa ganin yadda duk wahalar da boka Dayyubul-Barmas yasha abaya gashi ta tashi a banza yayi mutuwar asara
Tabbas rayuwar kafirci wahala ce kuma arasa ce
Amma shamsuddin yasha wahala tamkar ransa zai fita,
Koda su aljani Huruful-labarus suka ga abinda ya faru da mai gidan su sarki Hamras da kuma irin abubuwan al,ajabi da shamsuddin yayi sai nan take suka bayar da gaskiya da Ubangiji suka amshi kalmar shahada,
Batare bata lokaci ba jarumi shamsuddin ya auki TAKOBIN AUKAKA ya tofa mata Ayatul- kursiyyu take takobin ta canza launi kuma rubutun sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama dake jikin takobin suka fito raau,
Shamsuddin ya dubi su lasmirat yace" waannan sunaye su ne suka bawa su Boka Dayyubul-Barmas nasara akai na har nasha bakar wahala,
Haia duk wanda yayi rigo da kamun kafa da mai sunan wato annabin rahama s,a,w zai samu nasara. A komi nasa koda kuwa kafuri ne Allah zai jinkirin ta masa na wani lokaci kafin na kamashi
Koda jin wannan jawabi daga bakin shamsuddin sai kowa ya sake jin kaunar shugaban halitta ta arsu a zuciyar sa ,
Batare da wani bata lokaci ba su aljani Huzmal suka sake aukar su shamsuddin aka nufi hanyar dazata kai su birnin Misra
Bisa mamaki a wannan lokaci sai su Huzmal suka ga cewa karfin gudun nasu ya karu ainun
Abin da basu sani ba shine sirrin hasken MUSULUNCI ne a tare dasu ya basu karfin gudun
Tsawon kwanaki huu aka auka a wannan lokaci bisa taimakon Ubangijin halitta aka iso birnin Misra
Nan fa waziri ukashat da jama'ar birnin suka fito tarar su sarauniya lasmirat da tawagar ta
Bayan an sauke su an haa liyafar Abinci da abin shaye shaye nau'i daban daban,
Take kowa ya shiga kimtsa cikin sa ana fira cikin nishai
Su ma su Aljani Huzmal sai akawo musu tasu liyafar abisa wadannsu manyan tukwane dake auke da farfesun naman rakuma da shanu
Nan fa suka fara tanar baki suna rafka koma,
Al'amarin da ya sanya har dariya ta subuce wa yaslir da Sunaila kenan bisa ganin aljanu nayin kalace,
Bayan kowa ya samu nutsuwa ne waziri ukashat yakashe labarin abinda yafaru bayan tafiyar lasmirat ya zayyanewa lasmirat daga farko har karshe,
Da abinda yafaru tsakanin su da wannan dodo daya bayyana a fada
Batare da bata lokaci ita lasmirat ta shiga bawa jama'a labarin tafiyar su da abinda yafaru tsakanin su da shamsuddin da abubuwan al,ajabi da ya nuna
Sa,adda jama'a sukaji wannan labari sai suka cika da inkin al'ajabi kuma suka ce tabbas munyi imani da Ubangijin jarumi shamsuddin take sarauniya ta biya kalmar shahada
Dubban miliyoyin jama'ar ta suka amsa,
Sai da aka nako guda shamsuddin na koyar da jama'a yadda ake gudanar da ibada kuma yana jinyar raunukan dake jikin sa
Sannan aka shiga shagalin bikin aurin auren sarauniya lasmirat da shamsuddin, yaslir da Sunaila,
Bai daga sassan duniya sun halarci taron bikin
Akayi shagalin da ba,a taba yin kamar sa ba
Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye ko ina arzikin birnin Misra ya kara bunkasa
Bisa dole sarakunan dake nahiyar suka dunga zuwa da kansu suka karbar addinin Musulunci,
Jarumi shamsuddin yazo sabon Sarki birnin Misra,jarumi yaslir yazamo shugaban majalisar sarki,
Musulunci ya cigaba da bunasa.
Karshe
Alhamdulillah