Showing 15001 words to 18000 words out of 22047 words
Chapter 6 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt
idan baki manta ba acan baya lokacin da kika ziyar ce nagaya miki cewa saurayin da zaki aura har ki samu Haihuwa shine namijin da yafi Kowa talauci a duniya, kuma shine zai hanamu cika burin mu na mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA,
Shin yanzu bakya tsammanin cewa wannan baƙon jarumi shi ne saurayin da zai hana cika muradin mu,
Tabbas jikina ya bani cewa babu wani alkairi a tare da wannan jarumi.
Lokacin da sarauniya lasmirat ta ji wannan batu daga bakin Boka Dayyubul-Barmas sai hankalin ta ya ɗugunzuma ainun ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mai zurfafa cikin kogin tunani,
Abu na farko da ya faɗo mata arai shin yanzu idan wannan baƙon jarumi shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya shin taya ya zata iya cire soyayyar da ta kama zuciyar ta a Lokaci guda,
To wai shin ma boka Dayyubul-Barmas da yake wannan magana yana da tabbacin cewa Wannan baƙon jarumi shine saurayin da zai hana su cimma muradun su na samun TAKOBIN ƊAUKAKA,
Domin haka ai bashi da hujjar dazai zargi baƙon jarumin, haka dai lasmirat ta cigaba da wannan tunani ta saƙa wancan ta kunce wancan,
Daga bisani ne dai sai ta dubi boka Dayyubul-Barmas tace" yakai Dayyubul-Barmas kayi sani cewa babu wata hujja da zata sanya mu janye tafiyar mu da wannan baƙon jarumi ba,
Abu ɗaya ne kawai zai kawo mu janye kuɗirin na mu shine ka gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka ka tabbatar mana da zargin da kake yi,
Sa,adda boka Dayyubul-Barmas ya ji wannan batu daga bakin lasmirat sai ya dubeta yace "ya shugabata kiyi sani cewa da ace wani zai iya taimaka mana da bamu samu nasarar ɗauko zobunan sihiri ba,
Amma masu iya magana na cewa"Ba,a kwacewa yaro garma"
Zanyi duk abinda kika faɗa sai dai duk abin da ya biyo baya kada ki zargi ko a sai kanki,
Koda jin wannan batu sai Hankalin sarauniya lasmirat ya ɗugunzuma ainun hantar cikin ta takaɗa amma sai kawai ta basar ta nufi inda shamsuddin yake tana mai sakar masa tattausar murmushi tace"yakai wannan jarumi ma,abocin kyawu da kwarjini kayi sani cewa na tattauna da abokan tafiya ta kuma dukkan mu mun roki alfarma a wajen ka da kayi mana rakiya izuwa mallako waɗansu abubuwa,
Shamsuddin yayi murmushi yace" Nasan dukkan abinda kuka fito nema wato kubar miftahul-daryal da TAKOBIN ƊAUKAKA tunda kun samu nasarar ɗauko zobunan sihiri a cikin kogon fatalwa,
Dajin wannan batu mamaki ya turnuƙe lasmirat ta dube sa cikin mamaki"ya akayi kasan abubuwan da muka fito nema ya jarumin jarumai
Shamsuddin yayi murmushi yace"ya shugabata idan bazaki manta ba ko a baya na gaya miki cewa ikon Ubangiji na ya huce haka
Hakika Ubangiji na ya bayyana mini dukkan Abin da ya gudana daku a cikin mafarki na.
Sai dai kafin na amince da buƙatar ku tilas ne ku amince da sharudda na guda biyu
Na farko shine duk sa,adda wani abu ya taso na neman taimako sakamakon wata musiba zan zuba muku idanu sai kunyi dukkan abinda zaku yi kun gaza sannan na gwada tawa dubarar,
Sannan idan Ubangiji na ya bani ikon mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA kuyi mini alkawarin cewa za ku ƙarni addinina na Musulunci
Sa,adda sarauniya lasmirat ta ji waɗannan sharuɗɗa daga bakin shamsuddin sai tace"Duka mun amince da wannan sharuɗɗa naka ai biyan buƙata yafi dogon buri,
Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya koma kan buzun sa ya cigaba da gudanar da ibadar sa, lasmirat ta koma wajen abokan tafiyar ta,
Sai da aka kwana biyu a wannan waje aljani Huzmal yayi jinyar Fuka fukan sa su yaslir suka samu karfin jikin su sannan aka cigaba da tafiya
A halin yanzu tafiya ta canza daga tawaga ɗaya zuwa biyu wato sarauniya lasmirat da su aljani Huruful-labarus da jarumi shamsuddin
Maimakon a wannan karon a hau bisa aljani Huzmal sai shamsuddin ya ce kowa ya hau ɗaya daga yaran aljani Huruful-labarus bisa izinin Ubangiji ɗayan su bazai saɓa daga Umarnin da aka yi masa ba,
Da yake a wannan lokaci da aka fara tafiya da hasken rana ne,
Lokacin da duhun dare yafara kawo kai sai shamsuddin yayi umarni aka yada zango
Take aljanu shida dake ɗauke da, yaslir,Sunaila, Dayyubul-Barmas, lasmirat da shamsuddin suka saki manyan fuka fukan su suka sauka a turba,
Ana sauka aka kafa tantuna bayan an kafa ne sarauniya lasmirat ta shiga tanti ɗaya tare da sunaila,
Boka Dayyubul-Barmas da yaslir, shamsuddin sai ya shiga nasa shi kaɗai
Aljani Huzmal yana tsaye bisa bakin kofar tantin su boka Dayyubul-Barmas, su aljani Huruful-labarus kuwa suka karkasu izuwa kowace kusurwa a dajin domin tabbatar da cikekken tsaro,
A cikin tantin sarauniya lasmirat kuwa bayan sun kammala kalaci ita da sunaila,
Sai lasmirat ta kwanta Bisa kan gadon ta domin ta samu rintsawa amma duk sa,adda ta rufe idanun ta sai taga babu abinda take gani face fuskar jarumi shamsuddin yana yi mata murmushi,
A wannan lokaci tuni Sunaila ta fara sharar barci har da minshari,
Haka dai lasmirat takasance a cikin wannan hali har barci yayi awon gaba da ita,
Tabbas lasmirat ta kamu da matsananciyar soyayyar wacce bata taɓa tsammanin zata shiga ba,
Tabbas da ace jarumi shamsuddin zai zaɓeni a matsayin a matsayin abokiyar rayuwar sa
Tabbas zan iya hakura da mulkina dukiya dama komai da mallaka domin na samu soyayyar sa ,
Kamar yadda ya wakana a masauki su lasmirat haka al'amarin yakasance a masaukin su yaslir
Ina da bayan sun kammala kalaci sai boka Dayyubul-Barmas ya zira hannun sa a aljihun rigar sa ya ɗauko madubin tsafin sa ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin sa.
Shi kuwa shamsuddin tun Kafin ya shiga tantin ya ɗaura alwala yana shiga ya dauko dabino da ruwan sa a cikin salka ya ɗan kimtsa cikin sa,
Sannan ya shimfida buzun sa ya shiga gudanar da Sallah, batare da kalli abincin da su lasmirat suka kawo masa ba,
Amma a ɓangaren su aljani Huruful-labarus kuwa suna cikin yin rangadi a tsakanin tantunan ne sai wani ɗaya daga cikin yaransa .mai suna Barbusa ya dubi abokin sa yace "yakai saltir wai yanzu haka zamu zauna muna ji muna gani wannan yaro shamsuddin yana juya mu tamkar yana sarrafa waina (masa) a cikin yanda
Me zai hana bazamu shammace su ba mu hallaka su mu kama gaban mu,
Baka tsoron mai girma Hamras zai aiko da wata musiba ta hallaka mu,
Koda jin wannan batu sai idanuwan saltir suka zazzaro ya dubi saltir cikin alamun tsananin tsoro yace" A kul ɗin ka yakai aboki na kayi sani cewa tun ina yaro karami mahaifina ya gargaɗeni akan irin waɗannan mutane ma'abota addinin musulunci yace a halin yanzu a duniya babu hatsabibai kamar su
Kafin saltir ya gama rufe bakin sa sai kawai su kaji wani sanyi gami daddaɗar iska ta mamaye wajen kafin kace me
Gaba ɗayan su sun bungire kasa sun fara sharar barci har da minshari,
Sarauniya lasmirat, Sunaila da yaslir suma nauyin barcin su ya karu ainun,
Kuma wani irin gurnani mai ban tsoro ya mamaye wajen baki ɗaya.
Sa'adda wannan iska mai ɗan karan daɗi ta bugar dasu aljani Huruful-labarus, tare dasu sarauniya lasmirat suka kama barci mai nauyin gaske kuma wani gurnani na mamaye wajen sai,
Kwatsam bazato babu tsammani sai aljani Hafsul-Habarus ya bayyana a wajen,
Yayin da yayi arba dasu Huruful-labarus sai ya cika da matukar farin ciki kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta,
Sai da yayi dariyar ta ishe sa sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa,
Kawai sai ya miƙa gabza gabzan hannayen sa domin ya ɗauko su aljani Huruful-labarus,
Yayin da rage saura kamu goma hannayen sa su isa sai wani mutum ya bayyana gaban sa tsulum,
Ba wani bane face jarumi shamsuddin,
Hafsul-Habarus ya ja hannayen sa baya ya dubi shamsuddin cikin tsananin fushi yana mai daka masa tsawa mai kama da saukar aradu
Nan take bishiyoyin dake dajin suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, duwatsu suka dunga bindiga suna farfashewa, kuma su lasmirat suka farfaɗo daga dogon barcin da suke yi suka fito daga cikin tantunan su a firgice suna masu zare makaman su,
Sa'adda sarauniya lasmirat, Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila, Huzmal, aljani Huruful-labarus da yaran sa sukayi arba da aljani Hafsul-Habarus sai suka firgice suka zube kasa,
Sunaila, yaslir,da Huzmal suna masu sakin fitsari a wando saboda tsananin firgici,
Shi kansa boka Dayyubul-Barmas a matukar firgice yake,
Nan take a lokaci guda aljani Huruful-labarus ya tsuke bakin sa ya murtuke fuska,
Take komai na dajin ya samu dai dai tuwa
Cikin Wata irin kakkausar murya mai kama da kwaran kwatsa Yace"yakai wannan bil'adama ma'abocin tsaurin idanu shin wane ne kai dazaka hanani zartar da umarnin shugaba mai duniya sarki Hamras,
Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin na ganar dakai kuskuren ka,
Sa'adda shamsuddin yaji wannan batu daga bakin aljani Hafsul-Habarus sai ya yi gyaran murya yace" yakai wannan mushriki makiyin Allah kayi sani cewa babu wani mai daraja face yakasance bawan Ubangijin musulunci mahalicci
Abin da nake so dakai shi ne ka kadaina bautawa wanin Allah ka dawo izuwa TAFARKIN TSIRA,
Wato addanin Musulunci,idan kuwa kaƙi yanzun nan zan roƙi Ubangiji na ya bani nasara na hallaka ka,
Koda jin wannan batu daga bakin shamsuddin sai Hafsul-Habarus ya fusata ainun, idanuwan sa suka kaɗa sukayi jajur!
Saboda fushi har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga kofofin hancinsa,
Kawai sai Hafsul-Habarus ya zare wani makami a jikin sa,
Shi dai makamin yakasance dogo tamkar mashi, daga saman sa kawunan takobi ne guda biyu ɗaya na zarto mai cako-cako ƙasan kuma ya na da siffa irin ta lauje wanda ido bai taɓa gani ba,
Tabbas wannan makami abin tsoro ga dukkan wanda yayi arba da shi,
Sannan ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan shamsuddin,
Koda ganin hakan sai shamsuddin ya dunkule hannayen sa ya ruga kan Hafsul-Habarus aka tari juna aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali da ban tsoro,
Wohoho Hakika gaskiyar masu iya magana da suka ce,
Ranar bikin gwanaye sai wane da wane ne ke fitowa a taka rawa,
Kuma idan ana babbakar Giwa ba,a jin ƙaurin bera
Tabbas fadan da yafi karfin ka sai ka zamo da kallo,
Hakan ne yafaru da su sarauniya lasmirat,
Ba shiri su lasmirat suka rike tsaye suka runtuma da gudu izuwa cikin dajin , suka laɓe a bayan waɗansu bishiyoyi suka hangen artabun da akeyi tsakanin shamsuddin da Aljani Hafsul-Habarus,
Nan take su jarumi shamsuddin suka tashi hankalin duk wata halitta dake dajin ya kama girgiza kasa ta dunga tsagewa tana zaftarewa bishiyoyi na faɗa wa cikin ta, duwatsu suka dinga murginawa kan juna suna karo.
Wani abin mamaki da yafaru shine, duk yawan hare haren da Hafsul-Habarus ke kaiwa shamsuddin yana samun nasarar zillewa koda sau ɗaya makami bai taɓa jikin sa ba,
Idan kuwa shamsuddin ya naushi wata gaɓa a jikin Hafsul-Habarus sai aji ya kwalla kara,.
Bakomai ne yasanya hakan ba sai domin duk sa'adda shamsuddin ya naushe san sai yaji wajen tamakar an ƙonashi da ruwan zafi yana yi masa raɗaɗi da zugin tsiya,
Al'amarinn da yayi matukar bashi mamaki kenan bisa ganin yadda yakasa samun nasara akan shamsuddin,
Shin wannan wane irin jarumi ne da za,ace na kasa samun nasara akansa alhali koda makami bai riƙe ba , amsar tambayar da Hafsul-Habarus ya kasa bawa kansa kenan,
Kawai ya sake zage damtse yana cigaba da kai Hafsul-Habarus miyagun hare haren babu ƙaƙƙautawa,
Daga can nesa su sarauniya lasmirat na hangen artabun da ake yi tsakanin ZARATAN MAYAKAN biyu,
Sa,adda sukaga yadda Hafsul-Habarus ke yakasa samun nasara akan shamsuddin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi kuma suka tabbatar da cewa shamsuddin ya cika jarumin kawarai mai karfin Allah na isa.
Nan take sarauniya lasmirat taji soyayyar jarumi shamsuddin takara shiga zuciyar ta,
Ita kanta Sunaila sai taji a cikin ranta cewa i na ma dai ace masoyin ta yana da jarumataka irin ta shamsuddin
Abin da su duka biyun basu sani ba shine tsananin taimakon Ubangiji ne,
Ke ɗawainiya dashi bayin kansa bane,
Sai da shamsuddin da Hafsul-Habarus suka shafe Tsawon sa,a ɗaya da daƙika ɗari biyar suna ɗauki ba daɗi batare Hafsul-Habarus ya samu nasarar lakutar jikin shamsuddin ba,
Nan fa Hafsul-Habarus ya sake fusata ainun ya haɗa da kai bugu da naushi hannu da kafa
Sa,adda shamsuddin ya fahimci cewa wankin hula zai kaishi dare sai ya cigaba da riƙon Allah a zuciyar sa yana mai cewa,
Ya Ubangiji ka taimaki bawan ka mai rauni akan mushirikin bawan ka. Don matsayin annabin ka,
Ai kuwa yana kammala hakan sai shamsuddin ya taƙarƙare ya ƙirɓawa Hafsul-Habarus naushi a ciki,
Saboda karfin naushin sai da cikin Hafsul-Habarus ya yi ƙara fam fam! Tamkar an daki Tanki,
Ya faɗin ƙasa yana murginawa gami da turmutsutsu Cikin sa yana murɗawa,
Kafin yayi wani yunkurin jarumi shamsuddin ya sake ƙirɓa masa wani wawan naushin a cikin sa, take. Cikin nasa yayi bindiga ya fashe tamkar an buga katuwar ganga, kayan cikin sa suka fito waje jini ya dunga tsartuwa yana feshi yana malala a ƙasa tamkar an balle ƙorama,
Sa,adda su sarauniya lasmirat suka ga irin nasarar da shamsuddin ya samu sai suka fito daga inda suke laɓe suna masu yi masa jinjina suna cewa
G ausheka GOGA SHA YAƘI,
SADAUKIN SADAUKAI
Ciwon idanun kananun kwari
JARMAI SHA YAƘI uban maza DODON MAZAJE
Amma boka Dayyubul-Barmas sai ya murtuke fuska tamkar an aiko masa Da sakon mutuwa,
Kafin su kai inda yake gangar jikin sa ta zagwanye ta narke ruwan ya tsotse a cikin ƙasa,
Suna karasowa sai shamsuddin ya dubesu yace fuskar sa cike da annuri yace " Yakamata kowannen ku yaje ya kwanta a samu ishashshan barcin saboda tafiyar dake gaban su,
Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya juya ya shiga izuwa tantin sa,
Take kowa ya shiga nasa tantin a ka cigaba da barci,
Acan birnin misra kuwa tun daga ranar da sarauniya lasmirat ta tafi izuwa ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA domin ta samu damar ɗebo ruwan ma'ul-diya'u,
Waziri ukashat ya cigaba da tafiyar da sha,anain mulki bisa tsari da adalci,
Wata rana waziri ukashat na zaune a fada,
Wata kyakkyawar budurwa na zaune a gefen sa na dama cikin ado na keta raini ba wata ba ce face gimbiya Hulaifat yar waziri ukashat,
A gefe guda kuma fadawa ne a zazzzaune bisa shimfiɗu na alfarma
fadar ta cika maƙil ana tafiyar da sha,anin mulki,
Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai akaga wani waje ya zabtare a fadar ya rufta izuwa kasa
Kwatsam sai ga wani narkekeken dodo ya fito,
Shi dai wannan dodo yakasance jibgegen basamude ,fuskar sa mummuna ce babu kyan gani
Hannayen sa tafka tafka ne tamkar bishiyar kuka,tafukan kuwa su na da faɗi tamakar faranti, ƙafafuwan sa manya ne tamkar da dutse aka yi su, kirjin sa ya kumburo ya tara kwanji, kofofin hancinsa manya ne idanuwan sa jajawur tamkar garwashi girman kowanne daga cikin su yakai girman lemon zaƙi,
Tabbas wannan dodo ya cika abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face ya firgice
Nan fa yazamana cewa fadar ta kaure da guje-guje gami da ifice-ificen jama'a
Cikin matukar tashin hankali waziri ukashat ya miƙe tsaye zumbur daga kan karagar sa ta mulki yana mai zare zare takobin sa take fadawa da sauran dakarun dake fadar suka yi koyi dashi
Aka fara kallon kallo tsakanin su da dodon,
*****. *****. ****
Kashe gari tunda duku dukun safiya bayan su sarauniya lasmirat sun yi kalaci an kammala shiri tsaf!
Sai kawai kowa ya bisa kan ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus aka cigaba da tafiya domin isa izuwa tsaunin SHAFRAS,
Tafiya kwanaki talatin kaɗai akayi aka iso tsaunin DARUL-SHAFRAS
a iya tsawon wannan tafiya babu abin da ke sanya wa atsayar da tafiya face idan jarumi shamsuddin zai gudanar da ibadar sa,
Inda aka tsaya ɗin yakasance daji ne ma,abocin kwarjini daban tsoro,
Tsakanin su sarauniya lasmirat da inda tsaunin DARUL-SHAFRAS yake ake tazara mai yawa don haka sai suka cika da tsananin mamaki bisa Ganin yadda tsaunin yakasance
Tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance mai matukar tsawo inda ace mutum zai kalle sa daga nesa sai yaga cewa har ya shige cikin gajimare,
Babu wani ɗan itaciya da yayi tsiro a wajen face waɗansu irin duwatsu masu ɗauke da siffofin bil,adama da dodanni masu ban tsoro
Sai da aka shafe tsawon lokaci a cikin wannan hali sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas yayi umarni aka tashi aka nufi tsaunin gadan gadan
Nan fa jarumi shamsuddin ya dunga kallon abubuwan kudirar Ubangiji na halittun sa da tajallin sa iri daban daban,
Yayin da aka sauka a tsaunin sai kowa yasha jinin jikinsa kuma hankalin sa ya ɗugunzuma ainun,
Bakomai ne yasanya su hakan sai bisa ganin yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance
Daga sama tsaunin yakasance mai ɗauke da manyan gine gine da aka yi su da zallar duwatsun wuta kirar mutanen farko mai ɗauke da manyan ɗakuna tamkar akwai wata halitta da ta taɓa rayuwa a wajen
Babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafar sa face akwai ƙasusuwan bil,adama ko wasu sassa na jikin sa yana duk ta lulluɓe su,alamun dake nuna cewa wata halitta ta daɗe bata ziyarci wajen ba,
A wasu lokutan sai kaga mutum an rataye da igiya har ya zagwanye yazamana kwarangwal,
Babu abin da zai firgita Mutum shine yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance shiru tsit tamkar babu wata halitta a cikin sa domin koda yan kananan tsuntsaye babu,
Nan fa hankalin kowa ya ɗugunzuma ainun, amma bisa mamaki sai kaga shamsuddin bai razana ba
Nan fa su duka raya a ransu cewa shin menene yasanya shamsuddin bai razana da ganin kwarjini tsaunin ba,
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan
Boka Dayyubul-Barmas ne ya katse shirun da ya wanzu budar baki sannan yayi ajiyar zuciya ya kawo gwaron numfashi yace
"Yaku abokanan tafiyata kuyi sani cewa mun iso tsaunin DARUL-SHAFRAS inda zamu ɗauki ruwan ma'ul Daryalu,
Sai dai kafin hakan ina san na samar daku waɗansu dokoki
Da farko dole ne kowannen ku ya kiyaye amfani da dukkanin wani abu da danganci sihirin tsafi,
Abu na biyu kuwa shine dole ne kada wani ya shiga wani waje face yasanar dani na basa umarni,
Yana gama faɗin hakan sai ya juya ya dubi shamsuddin fuskar sa babu annuri tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce " yakai shamsuddin kada ka manta alkawarin dake tsakanin mu dakai na fito rayuwar mu a lokacin da wata musiba ta taso mana muka kasa tseratar da kan mu idan har ka gaza ceto rayuwar mu
Tabbas zamu yanke tafiyar mu daki domin hakan ya tabbatar mana cewa Ubangijin ka ya gaza wajen taimakon ka,
Koda jin wannan batu sai jarumi shamsuddin ya yi murmushi yace"Da yardar Annabi mai daraja Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Ubangiji na