Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 22047 words

Chapter 3 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

337

Ads at the middle of Article

haddasa girgizar kasa,






Nan fa bishiyoyi suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, gida je su ka dunga rushewa suna hallaka, ƙasa tana tsagewa dawakai da mahayan su suna rufta wa cikin ta,






Ihun mazaje,mata, tsofaffi gami da yara ya cika dodon kunne,






Sa,adda sarauniya lasmirat taga yadda jama'ar ta ke hallaka sai ta cika da tsananin baƙin ciki maral musaltuwa,






Cikin fushi ta sake dakwa aljanar tsawa a karo na biyu tana mai cewa "yake wannan shu'umar aljana yau duhun ta cika idan har kin isa ki fito muyi fito-na fito na rantse da karagar mulki na sai na ga bayan ki,






Koda jin wannan batu sai aljanar ta tsuke bakin ta komai ya samu dai dai tuwa bishiyoyi suka daina karyewa duwatsu suka daina fashewa kasa ta dai na tsagewa,






Aljanar ta buɗe bakin ta wanda yafi kama da kofar gari cikin murya mai ban tsoro tamkar saukar aradu tace"yake wannan sarauniya kayi sani cewa bakomai ne ya kawo wannan birni naki ba sai domin ya kashe mutanen birnin ki kuma na mallake ki saboda wata muhimmiyar buƙata ta,






Kafin aljanar ta gama rufe bakin ta saurayi yaslir ya tari numfashin ta yana mai daka mata tsawa cikin fushi yace"yake rafkananniyar aljana kuma yar tsakuwa a cikin jerin JARUMAN DUNIYA, kiyi sani cewa karyar ki tasha karya ina mai tabbatar miki dacewa bazaki tsira daga sharrin mu ba,






Sai ki shirya ka maza nan bisa kanki,






Yana gama faɗin hakan ya sakarwa dokin sa linzami yana mai gyara rikon sandar sa cikin hanzari lasmirat ta mara masa baya tana mai ɗaga takobin ta sama,






Sauran dakaru mutum dubu arba'in sukayi koyi dasu






Ana haɗuwa aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali






Domin kafin a haɗu sai da aljanar ta sanya hannu ta ta ɗebi dakaru mutum hamsin har da dawakan su ta watsa a bakin ta ta taunesu tayi kalaci dasu,






Sannan ta afkawa su lasmirat.






Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin shu'umar aljana da su sarauniya lasmirat,






Sai lasmirat da yaslir suka wanzu suna kaiwa aljanar sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA






Duk sa'adda makaman su suka sauka a jikin aljanar sai kaji sun bada kara ƙal ƙal !! Tamakar karfe suka sara






In banda lasmirat da yaslir suna cikin kariyar tsafi da tuni sun hallaka,






Idan aljanar ta kaiwa yaslir da lasmirat hari da hannayen ta, idan suka goce duk abin da hannun ta ya sauka akai sai dai kaga ya tarwatse,idan kuwa a ƙasa ne sai ya haddasa wani rami zurfin gaske,






Take dakaru da dawakan su zasu afka cikin sa suna ihu da kururuwar neman taimako,






Nan fa waje ya cika da ihun mazaje mata da yara da matasa,






Karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne, JINI DA KASA suka cakuɗu, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya,






Lokacin da aka shafe dakika ɗari biyu da sittin ana wannan bakin gumurzu,






Sai ya zama na cewa aljanar ta samu nasarar hallaka dakaru Fiye da dubu shida,






Amma bata samu nasarar koda lakutar jikin su lasmirat ba sai ta cika da matukar mamaki kuma ta fusata ainun,






Abin da ya bata mamaki shi ne ya akayi sarauniya lasmirat da saurayi yaslir suka kasance masu tsananin zafin nama, tabbas yau ta haɗu da takadiran jarumai, hakika rashin wannan nasara ƙasanta darajar ta ne da kimar ta,






Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta canza salon faɗan ta yazamana cewa tana haɗa kai bugu da naushin hannu da ƙafa,






Ai kuwa nan take labari yasha Bambam, domin a halin yanzu daƙyar su yaslir ke iya mayar da martani






Idan ta daki gini ya tarwatse sai kaga duwatsun sun yiwa su lasmirat lugudan duka,






Sai da aka shafe tsawon dakika dari da ɗoriya ana wannan fafatawa,






Ana cikin wannan yaƙi ne aljanar ta kaiwa sarauniya lasmirat da yaslir wawan naushi da nufin yi musu farat ɗaya,






Amma kafin hannun ta yakai gare su sai suka daka tsalle a sama tamkar an harbosu daga cikin baka suka bar kan dawakan su






Sai gashi hannun ya sauka akan dawakan sun tarwatse tamakar an talitse tumatir,






A daidai wannan lokaci ne yaslir da lasmirat suka sauka akan aljanar bisa tsakiyar kanta su shiga kafta mata sara babu sassauci,






Nan fa yazamana sun riki ta aljanar yazamana cewa ta daina kaiwa dakaru hari






Sai dai ƙoƙarin taga ta jefo su yaslir daga kan ta, ana cikin wannan hali ne aljanar ta samu nasarar damƙo su yaslir ta hannun ta ta matse su nan take suka sume sakamakon maƙurewar,






Ashe ta samu nasarar karya ɗan yatsan yaslir, lasmirat kuma ta samu gocewar ƙashi, a hannun ta,






Koda samun wannan gagarumar nasara sai aljanar ta bushe da shu'umar dariya






Sai da tayi dariyar ta ishe ta sannan ta tsuke bakin ta kawai sai ta juya ta nufi kofar fita daga birnin tana mai koɗa kanta gami da yiwa kanta kirari, tana mai cewa






" Saini GAWURTACCIYA uwar hatsabibai,






GUGUWAR YAƘI nake mai share MAYAKA,






ANNOBA ƊARI nake duk wanda ya Kusan ceni zai baƙun ci barzahu,






Ni ne gararriya uwar gagararru,














Haka ta cigaba da yiwa kanta kirarin tana lafiya a cikin birnin,






Duk sa'adda ta ajiye kafarta ɗaya sai dai kaga ƙasa tana girgiza tamkar zata tsage abin da ke saman ta ya faɗa cikin ta






Koda sauran dakarun suka ga abin da yafaru sai suka dunga ɗame kwari da bakan su suna Harbin aljanar






Duk tsananin yawan kibban sai yazamana a banza domin ko gezau batayi ba






Sai dai ma kaga ta sanya hannun ta ɗaya tana karkaɗe kibiyoyin kamar tana kaɗe ganyayyakin bishiya,






Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji aljanar ta kurma wawan ihu kuma ta faɗi ƙasa tim,






Ta saki su sarauniya lasmirat suka faɗo ƙasa babu alamun rai a tare dasu ,






Kuma akaga aljanar ta ɗaga hannayen ta sama tana mai roƙon gafara






Al'amarin da yayi matukar bawa dakarun mamaki kenan, suka rugo izuwa wajen domin su ga abin da ke wakana,






Su na isowa sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya,






Ai kuwa sai su kayi arba da wata kyakkyawar budurwa,






Budurwur takasance dogowa mai matsakaicin kaurin jiki, cikin ta ashafe yake tamkar bata cin komai ba,






Kuma a tsuke yake daga ƙasa, ƙugunta mai faɗi ne yayi tudu sosai, gashin kanta mai tsawo ne ya zuba har izuwa kan kafaɗun ta baƙi ne siɗik tamakar gilashi, a jikin ta tana sanye da tufafi irin na mutanen birnin sun, kanta daure da bakin rawani idanun ta kaɗai ake gani,






A sannanne dakarun suka fahimci cewa wannan bakuwar budurwa ce ta ceci rayuwar su sarauniya lasmirat,






Bakuwar budurwar ta nuna aljanar da ɗan yatsan ta na hagu take aljanar ta ƙame, tamakar gunki, komai na jikin ta ya daina motsi,






Faruwar hakan keda wuya sai budurwur ta taka da ƙafafuwan ta izuwa inda su yaslir ke kwance,






Kawai sai ta buɗe bakin ta ta karanto waɗansu kalamai da ita kaɗai tasan me take faɗa,






Tana gama rufe bakin ta sai aka ga sarauniya lasmirat da saurayi yaslir sun mike tsaye zumbur tamakar babu wani abu da ya same su.






Kafin wani daga cikin su yace uffan, budurwar ta sake nuna aljanar a karo na biyu da ɗan yatsan ta,take ruhin aljanar ya dawo jikin ta, komai nata yana yin motsi,






Budurwur ta buɗi baki cikin wata irin zazzakar murya tamkar ana busa sarewa tace" yake wannan AZZALUMA kiyi sani cewa na yarda zan barki Lafiya kici gaba da rayuwa amma bisa sharaɗin cewa za ki dai na zaluntar al'umma,






Cikin ladabi da ƙan-ƙan da kai aljanar tace Muryar ta na rawa saboda tsoro" Na amince ya shugabata na ɗaukar miki alkawarin cewa bazan kara cutar da wata halitta har abada,






Koda jin wannan batu sai budurwur tayi wa aljanar nuni da ta tafi,






Cikin hanzari aljanar ta miƙe tsaye ta buɗe manyan fuka-fukan ta tashi zuwa sararin samaniya tana mai keta gajimare cikin tsananin gudu keta Sa'a ta ɓace,






Nan fa gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matukar mamaki maral musaltuwa,






Abu na farko da ya basu mamaki shi ne yadda ta ceto rayuwar su sarauniya lasmirat kuma suka warke sumul,






Abin da yafi basu mamaki kuma ya ɗaure musu kai shi ne yadda bakuwar budurwar take sarrafa aljanar tamakar tana juya waina (masa) a tanda,






A ɓangaren sarauniya lasmirat kuwa, mamaki ne ya cika zuciyar ta ta kasa cewa uffan,






Yaslir kuwa yafi kowa mamaki domin ko a mafarki bai taba ganin ya mace mai baiwar sarrafa irin wadannan aljanu ba,


Kawai sai ya ƙurawa budurwur idanu yana nazarin ta, duk da kasancewar fuskar budurwur na rufe da rawani amma idanun ta kaɗai yaslir ya kalla ya fahimci cewa ta nunka sarauniya lasmirat a kyawun sura,






Lasmirat da yaslir suka taka da ƙafafuwan su izuwa inda budurwur take tsaye, suka risina da kawunan su kasa domin girmama wa agare ta,






Sannan lasmirat ta ta dube ta cikin murmushi mai taushi tace"yake wannan basadaukiya mace mai kamar maza shin mene ne labarin ki?






Menene kuma dalilin da ya sanya kika ceci rayuwar mu ni da jama'ar birni na?.






Koda jin waɗannan tambayoyi sai budurwur tayi shiru tana mai nazari,






Daga can sai ta ɗago da kanta ta dubi yaslir, lasmirat tace cikin tattausar murya






" Da farko dai suna na Sunaila na fito daga cikin wata nahiya da ake yiwa da Haurul-zamras,






Abin da ya baro dani daga birnin mu shi ne domin na sadu da waɗansu irin mutane da ake yiwa laƙabi da musulmi,






Babban burina shi ne na sadu da su kuma na karɓi Addinin su domin na samu nasarar ɗaukar fansa akan azzalumin sarki da ya rusa mini farin cikin rayuwa ta,






Wannan nasara da kuka ga na samu na sarrafa wannan aljana ba tsafi ba ne kawai ina neman taimakon Ubangijin ma'abota addanin Musulunci ne,






Sa'adda jaruma Sunaila tazo nan a bayanin ta sai mamaki ta turnuƙe su yaslir,






Sunaila ta ɗora da cewa" Na shigo wannan birni naki ne na ɗan wani lokaci ne domin na bincika ko zan dace na samu irin waɗannan mutane ma'abota addinin Musulunci,






Koda jin wannan batu Daga bakin Sunaila sai lasmirat ta ce"Kada ki samu damuwa yake Sunaila zan baki masauki har zuwa lokacin da za ki sadu da mutane ma'abota addanin Musulunci, domin ba za mu iya biyan ki taimakon da kika yi mini ba,






Koda jin hakan sai sunaila ta cika da matukar farin ciki tace" Godiya nake ya shugabata,






Da jin haka sai lasmirat ta matsa daf da ita ta yadda suna iya jin numfashin juna ta dafa kafaɗun ta tace da ita" yake Sunaila daga yau bana so ki kirani da shugabar ki face abokiyar ki ko Aminiya,






Sa'adda Sunaila ta ji hakan sai ta gyaɗa kai cike da farin ciki,






Cikin hanzari sarauniya lasmirat da yaslir suka juya suka nufi gidan sarauta,jaruma Sunaila na biye da su,






Ana cikin tafiyar ne lasmirat ta lura cewa yaslir yana satar kallon jaruma Sunaila ta wutsiyar idanu,






Nan take taji kishi ya turnuƙe ta, domin ta fahimci cewa yaslir yana yiwa jaruma Sunaila kallon SO ne,






Kawai sai ta jefe sa da wata irin haramta, a lokacin da yake satar kallon,






Take yaslir yaji hantar cikin sa ta kaɗa, kuma kunya ta kama sa ya sunkuyar da kansa ƙasa aka cigaba da tafiya,har aka isa gidan sarauta ɗayan su bai ce uffan ba,






Har zuwa masauki lasmirat da yaslir suka raka jaruma Sunaila,






Sannan kowa ya tafi izuwa bangaren sa,






Lokacin da yaslir ya kwanta a bisa kan gadon sa domin ya huce gajiyar dake tattare dashi, sai barci ya gagare sa,






Duk sa,adda ya runtse idanun sa sai ya yaga fuskar jaruma Sunaila rufe da rawani,






Tana yi masa murmushi, nan take yaji tsananin SO da begen Sunaila ya mamaye zuciyarsa,






Wani abu da ya faɗo masa arai shi ne shin hararar da lasmirat ke yi masa a ɗazu mene ne ma'anar sa shin tana tsananin kishi ne da kallon Sunaila da yayi,






Shin ke nan hakan na nufin ita sarauniya lasmirat ta kamu da matukar kaunar sa kenan?.






Amma yanayin tsayuwa da tafiyar da Sunaila tayi a ɗazu a filin yaƙi iri ɗaya ne sak da na masoyiyar sa gimbiya salimat,






Shin jaruma Sunaila ita ce masoyiyar salimat?






Sa'adda yaslir yazo nan a tunanin sa sai ya shiga cikin tsananin damuwa,






Kuma yaji gaba ɗaya duniyar tayi masa ƙunci, nan take ya ƙudiri aniyar cewa sai yaga fuskar Sunaila kafin tabar wannan birni.






***














































3


Kamar yadda ya wakana ga saurayi yaslir haka al'amarin yakasance ga sarauniya lasmirat,






A inda ita ma barci ya gagare ta,


Abu na farko da ya faɗo mata arai shi ne, shin Mene ne yasanya yaslir zai kamu da soyayyar Sunaila, Alhalin ta nuna alamun so,


Sannan taya zai kamu da son wacce koda fuskar ta bai gani ba,






Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai taji zuciyar ta tayi ƙunci, kuma tasha alwashin cewa sai ta bayyana soyayyar ta ga yaslir a lokacin da suka gudanar da tafiya ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA,


Da ɗebo ruwan ƙoramar boka Daryalu.


Tun da tana so ne tafiyar ta kasance har da jaruma Sunaila za a yi ta,


Daga wannan shawara ne sai ta ɗauko madubin tsafin ta domin gudanar da bincike don irin wainar da ake toyawa a duniya,






***


Acan inda aka fafata yaƙi kuwa dakaru sun shiga aikin su na kwashe gawarwakin jama'a da waɗanda suka samu raunuka aka shiga duba lafiyar su,


Kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai sai aka kunna fitar ice aka cigaba da aiki


Inda ace mutum zai ga yadda ake kwashe gawarwakin jama'a jini na kwaranya sai ya rantse yace a mahauta yake,


Waɗanda suka rasa iyayen su, ya'ya da yan uwa gami da gidaje sai suka shiga rusa kukan baƙin ciki


Domin a iya tsawon wanzuwar birnin Misra ba'a taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba,


Kashe gari tunda duku dukun safiya sarauniya lasmirat ta umarci kuyangi suka shirya nau'ikan kayan abinci da abin shaye shaye da tanɗe tanɗe a bisa wani dogon teburin azurfa, a cikin wata ƙasaitacciyar turaka ta musamman,


Kuyangi na cikin kammala aikace aikace a cikin turakar sai ga sarauniya lasmirat ta shigo,


Cikin ƙayatattun tufafi irin na manyan sarakai,


Koda shigowar ta sai gaba ɗaya kuyangin suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa


Lasmirat ta amshi gaisuwar sannan ta umarci wata kuyanga ta tafi zuwa masaukin su yaslir ta yi musu iso, kuma ta ce tana gayyatar su walima,


Jim kadan da ficewar kuyangar sai ga yaslir ya shigo


Turakar,yana sanye cikin shiga riga da wando na alhariri masu taushi da ƙyalli,


Yana shigowa ya risina ga sarauniya lasmirat sannan yaje ya zauna abisa wata kujera dake fuskantar ta,


Ana cikin wannan hali ne Sunaila ta shigo, ta shigo turakar duk da cewar ta canza tufafin dake jikin ta amma har a wannan lokaci fuskar ta rufe da rawani idanun ta kaɗai ake gani,


Bayan ta miƙa gaisuwa ga lasmirat sai ta zauna a kujerar dake fuskantar lasmirat da yaslir,


Lasmirat ta dubi yaslir da Sunaila tace" yaku waɗannan baki masu daraja a gare ni, kuyi sani cewa na kiraku nan ne domin shirya muku walima bisa taimakon da ku kayi mini,


Wanda bani da abin da zan saka muku dashi


Koda gama faɗin hakan sai sarauniyar lasmirat ta tsiyaya ruwan inibi a cikin yan kananan kofunan zinare guda uku ta miƙawa yaslir da Sunaila kofuna biyu suka karɓa,


Sannan ta ɗauki na uku a hannun ta, kamar hadin baki a lokaci guda suka kai kofunan bakunan su suka shanye ruwan inibi,


Sannan aka shiga hidimar ciye-ciye da tanɗe-tande ana fira cikin nishaɗi,


A cikin firar ne lasmirat ta dubi yaslir tace"In tambaye ka mana ɗazu da ka shigo naga fuskar ka akwai alamun damuwa shin ko me ya kawo hakan,


Yaslir ya shafi sajen sa da gemun sa yace" na ɗan makara ne shi ne ya sanya Ni cikin damuwar,


Koda jin amsar wannan tambaya sai lasmirat tayi murmushi ga yaslir mai ɗauke da alamar tuhuma,


Sannan ta gyaɗa kai cikin gamsuwa,


Al'amarin da sanya yaslir yaji hantar cikin sa ta kaɗa,


Amma sai ya banzatar da abin aka cigaba da ciye-ciye da tanɗe tanɗe kamar babu wani abu.


Bayan kowa ya kimtsa cikin sa an samu nutsuwa kuma shiru ya wanzu,


Sai lasmirat ta dubi yaslir da Sunaila tace"yaku ababan soyuwa a rai na, kuyi sani cewa babbar muhimmiyar maganar da nake so mu tattaunawa Ita ce, ina so ku taimake ni muyi wata gagarumar tafiya tare daku,


Nan take lasmirat ta kashe labarin abinda ya wakana tsakanin ta da boka Dayyubul-Barmas akan batun ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA ta zayyanewa su yaslir da ga farko har karshe,






Sannan ta ɗora dacewa yaku waɗannan baki masu daraja a gare ni kuyi sani cewa idan har kuka taimake ni wajen cika burina






Ina mai tabbatar muku dacewa zan raba kasa uku,dukiya, da komai nawa kowannen ku ya ɗauki ɗaya






Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan azancen ta sai yaslir da Sunaila suka cika da matukar mamaki, kuma suka zurfafa izuwa kogin tunani,






Sannan daga bisani yaslir da Sunaila suka dubi lasmirat Cikin haɗin baki suka ce mun amince da wannan bukata taki ya mai karamci,






Koda jin wannan batu sai sarauniya lasmirat ta cika da matukar farin ciki mara musaltuwa,






Kuma ta labarta musu ranar da zasu gudanar da tafiyarsu,






Ranar da tafiya dajin Husumul-kadar tazo, sarauniya lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi gagarumin shiri,






Suka hau bisa dawakai suka nufi hanyar da zata sadasu da gidan boka Dayyubul-Barmas,






Bayan lasmirat ta bayar da rikon sarautar ta a hannun waziri ukashat,






Kuma waziri ukashat ɗin da sauran al'ummar gari sun yi musu rakiya har zuwa kofar gari,






Lokacin da sarauniya lasmirat suka iso gidan boka Dayyubul-Barmas sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya,






Su kayi cirko- cirko suna masu ƙarewa gidan kallo, shi dai gidan boka Dayyubul-Barmas yakasance ɗan madaidaici da aka ginasa da zallar duwatsun wuta masu ƙyalli, yana da kofa guda ɗaya da akayi ta da zallar karfen jauhari,






Bakomai yasanaya su sarauniya lasmirat suka yi wannan cirko-cirko ba sai bisa ganin Kofar gidan a garƙame, kuma ya na lulluɓe da wata yanar gizo gizo






Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai akaga boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum! a gaban su fuskar sa cike da annuri,






Yana sanye cikin kyawawan tufafi na alfarma,sun yi matukar yi masa kyawu, a hannun sa yana rike da wata isgar tsafi,wacce take canza launi Lokaci zuwa lokaci, wani lokacin ta koma baƙa,shuɗiya ko Koriya,






Lasmirat ta yi murmushi ga boka Dayyubul-Barmas daya ƙarawa fuskar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads