Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 22047 words

Chapter 2 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

336

Ads at the middle of Article

nuni da yau bisa ɗayan dokin take ya kama dokin ya hau


A lokaci guda suka sakarwa dawakan linzami sauran tsirarun dakarun suka mara musu baya a ka cigaba da tafiya,


Jama'a suka bisu da kallo cike da tsananin mamaki






****


A can kololuwar sararin samaniya inda Allah (s,w,t) yayiwa halittu iyaka a nanne sarki Hamras ibn zulaibu ya sanya aka gina masa ƙasaitacciyar fadar sa.


Wacce masana suka tabbatar da cewa babu wata fada data Kaita ƙawatuwa da kayan alatun jin daɗin rayuwar duniya.


Domin an ce sai da bakaken aljanu guda dubu shida suka shafe shekaru goma suna aikin ginin fadar dare da rana babu sassauci.


Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa Sarki Hamras yakasance jinin wata Kabila da ake kira da Banu lahzar.


Waɗanda aka tabbatar dacewa sun mamaye rabin sarakunan duniya,


A rayuwar sarki himras fiye da abu uku, yana matukar adawar ace akwai wani sarki a duniya da ya fisa KARFIN MULKI


Abu na biyu kuma shine ya tsani ma'abota addinin musulunci.


Bakomai yasanaya hakan sai domin mahaifinsa sarki zulaibu ya mutu ne sakamakon kwabza yaki da wani jarumi ma, abocin addinin Musulunci,


Akwai waɗansu muhimman sirrikan tsafi da mahaifin sa zai sanar da shi waɗanda da zarar ya sanar dashi ɗin zai mulki duniya baki ɗaya,


Amma sai ya zamana waccan jarumin ya hallaka sa batare da ya sanar dashi sirrikan tsafin ba,


Abu na karshe da sarki Himras ya tsana shi ne wani gawurtaccen jarumin ma,abocin addinin Musulunci,wanda binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa shine zai kawo karshen mulkin sa a doran kasa.


Lokacin da sarki Himras ya ga cewa a halin yanzu basa da abokan gaba da suka huce ma'abota addinin Musulunci sai ya zurfafa izuwa cikin halarar tsafin sa domin ya gano wata hanya zai bi ya kawar da musulmi kuma ya mulki duniya baki ɗaya,


Abin da bincike ya tabbatar masa shine bazai taɓa cika wannan buri na sa ba face ya mallaki wata tsafaffiyar takobi mai suna TAKOBIN ƊAUKAKA


Amma koda ya mallaki takobin bazai samu nasarar sarrafa takobin ba face ya haɗiye gashin kan waɗansu mutum biyu,


Waɗannan mutum ba wasu ba ne face" sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas,


Sa'adda sarki Hamras yaga gagarumin aikin dake gabansa na mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA, da silin gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat sai ya umarci waɗansu gwarazan dakarun aljanun sa domin su yanko masa gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat


Bisa jagorancin aljani Huruful-labarus.


Aljani Huruful-labarus yakasance GWARZON MAYAKI da masu Bincike suka tabbatar dacewa a jinsin baƙaƙen aljanu babu mai karfin damtsen sa.


Bayan Sarki Hamras ya tura Aljani Huruful-labarus sai ya shiga shiri sai da ya kwana arba'in ya na tsuma kansa da tsumin tsafi, sai ya fito ya shiga izuwa duniya domin mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA.


Al'amarin saurayi yaslir da sarauniya lasmirat kuwa, tafiyar daƙika arba'in kacal suka yi suka iso izuwa gidan sarauta


Gidan sarautar yakasance kasaitacce mai girma da faɗi tamkar gari guda, gaba ɗaya katangun ginin gidan anyi su ne da wani irin farin gilashi


Babu wani BASARAKE ko attajiri dazai yi arba da wannan gidan sarauta face ya Zamo cikekken ɗan ƙauye,


Tsayawa masalta tsaruwar gidan sarautar zai iya zamo wa ƙauyanci sai dai abinda idanu suka gani kawai


Duk inda mutum ya duba bayi ne hade da kuyangi


da barori na kai komo suna hadima


Duk inda sarauniyar lasmirat da saurayi yaslir suka gufta a cikin gidan sarautar sai dai kaga jama'a na zubewa kasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa,


Lokacin da aka iso wani bangare mai ɗauke da manyan falo guda uku haɗe da kewayen wanka, kayan more rayuwa sai


Waɗansu tsala-tsalan kuyangi na kai komo a cikin turakar,


Da sauri wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru hamsin ta rugo izuwa inda sarauniyar lasmirat take ta zube ƙasa bisa gwiwoyin ta ta kwashi gaisuwa


Bakin ta na kyarma kuma kanta a sunkuye tace "me kike da buƙata ya shugaba ta?


Lasmirat ta dube ta tace" yake zarima kiyi sani cewa bakomai nake da bukata ba face ina so wannan baƙo dake tare da ni a basa kulawa da dukkanin wani abu da ya buƙata kiyi sani cewa yana da matukar muhimmanci agareni


Koda jin wannan batu sai zarima ta sake risina wa tace angama ya shugabata bin umarnin ki ai shi ne ibada ta,


Tana gama faɗin hakan ta mike tsaye tana Mai yiwa saurayi yaslir nuni da ya biyo bayan ta


Batare da bata lokaci ba yaslir ya kama linzamin dokin sa ya sauko sannan ya rufa mata baya


Amma koda ya waiga ya haɗa idanu da sarauniya lasmirat sai yaga tana yi masa wani mayataccen kallo mai ɗauke da alamar tambaya.


Cikin hanzari sarauniya lasmirat ta juya taɗa linzamin dokin ta ta nufi bangaren da turakar ta take,


Lokacin da isa sai ta shiga izuwa kewaye ta tsala wanka sannan ta shiga tsaɓa ado tana mai fuskantar wani madubi


Tana cikin wannan hali ne sai ta jiyo motsin tafiya a bayan ta


Koda ta waiga sai tayi arba da shi ba wani bane face wazirin ta mai suna ukashat


Waziri ukashat yakasance dattijo mai yawan shekaru amma duk da hakan babu gajiya a tare da jikin sa,


Yana da kaurin jiki, dogo ne tsaka-tsaki,yana da tarin gemu da ƙasumba fararen sol,


Fuskar sa tana da kwarjini


Ukashat yakasance ɗan uwa a wajen mahaifin lasmirat wato sarki kazmal kuma babban aminin sa, bisa wannan dalili ne yasanya duk abinda lasmirat zata zartar sai ta nemi shawarar waziri ukashat,


Bisa al'ada duk sa'adda waziri ukashat zai gana da sarauniya lasmirat yana sanya ayi masa iso,kuma zai shigo ne fuskar sa cike da annuri


Amma a wannan karon sai ga fuskar sa a murtke babu annuri tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa,


Kawai sai ya zaune a bisa wata kujera dake fuskantar lasmirat ya dube ta cikin tsananin fushi yace" yake lasmirat shin menene yasanaya za ki karrama wanda ya wulakanta ki a gaban talakawa?.


Tabbas hakan zubar da darajar wannan masarauta ta mu ne da muka gada tun iyaye da kakanni,


Shin yanzu da wane irin idanu zamu kalli sauran sarakuna abokan gabar mu?


Wai shin ma bakya tunanin cewa wannan saurayi ɗaya daga cikin abokan gaba ne yayi ɓadda kama domin ya yaudare ki?


Koda jin wannan tambaya daga bakin waziri ukashat sai sarauniya lasmirat ta dube sa a nutse tace"yakai waziri kayi sani cewa ko kaɗan bana taɓa da nasanin karrama wannan saurayi kuma jiki na ya bani cewa tabbas bazai cutar da Ni ba, hakika zai zamo mai amfani a gare ni.


Ukashat ya katse ta ta hanyar ɗaga mata hannu yace " Haƙiƙa ke yarinya ce, tabbatas Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai iya gani ba.


Ban yi mamakin maganar ki domin na fahimci cewa tsananin kauna da soyayyar wannan saurayi ce ta makantar da idanuwan ki, ta sanya har kika manta da burin zuri'armu na kare martabar wannan masarauta,


Koda wannan batu daga bakin ukashat sai sarauniya lasmirat ta fusata ainun ta dakawa matsawa ta dube sa tace" yakai ukashat kayi sani cewa ni nake da ikon bayar da umarni a wannan masarauta don haka abin da naga ya dace shi zan aiwatar,


Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta fice daga cikin turkar ta bar waziri ukashat a zaune


Cikin alamun tsantsar damuwa waziri ya mike tsaye ya fice daga turakar zuciyar sa cike da takaici.


Da shigar saurayi yaslir izuwa cikin turakar, sai ya tarar turakar takasan ce ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin jin daɗin rayuwar duniya.


Gaba ɗaya turakar shimfiɗe take da wani koren kilishi mai taushin gaske,


Bayan yaslir ya fito daga kewayen wanka wani wanzami yayi masa gyaran fuska da saje, sai wata kuyanga ta kawo masa waɗansu fararen tufafi masu taushi ya sanya a jikin sa,


Nan take tsakanin kyawun sa ya fito fili ƙarara, kawai sai ya nufi teburin da aka tanadar masa abinci da abin sha ya shiga kimtsa cikin sa,






Bayan ya kammala ne da yake a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai,


Sai ya kunna fitulun dake turakar ta kaure da haske,


Sannnan ya zauna a bisa kan gadon sa kuma ya zurfafa izuwa kogin tunani,


Yana cikin haka ne sai yaji an turo kofar shigowa turakar


Ai kuwa kofar na buɗewa sai ya yi arba da ita ba wata ba ce face sarauniya lasmirat ta caɓa ado wani irin daddaɗan ƙamshi na tashi daga jikin ta.


Cikin Wata irin tafiya mai ɗaukar hankalin duk wani ɗa namiji,ta nufi wata ƙasaitacciyar kujera dake fuskantar yaslir ta zauna a kan ta,


Cikin annurin fuska ta dubi yaslir tace"yakai yaslir kafin mu kai ga tattaunawa abinda ya taramu anan Yana da kyau ka sanar dani labarin rayuwar ka.


Koda jin wannan tambaya sai idanun yaslir su ka ciki da kwalla ya dubi lasmirat yace" ya sarauniyar kyawu shin ina dalilin son kiji labarin rayuwa ta?


Lasmirat ta numfasa tace"Domin sanin labarin ka ya na da matukar muhimmanci a gareni,


Yaslir ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan yafara dacewa






***




































Kimanin shekaru arba'in baya anyi wani ƙauye da ake kira da suna Darul-Na'am.


Gari ne mai ɗauke da arzikin noma, kiwo, Sarkin dake mulkin kauyen yakasance adali mai tausayin talakawa


Ana kiransa da suna Abu-salimat, Abu-salimat yakasance GWARZON MAYAKI mai tarwatsa maza a filin daga,


Yana da ƴa guda ɗaya kyakkyawa tagaban kwatance ana kiran ta suna salimat ta gaji mahaifin ta a kyawawan halayen mahaifin ta.


Ƙauyen Darul-Na'am na karkashin mulkin wata babbar masarauta da wani kasaitaccen sarki ke mulki mai suna Husnalu ibn kailub,


Sarki Husnalu yakasance GWARZON MATSAFI, kuma mashahurin mayaki, daɗin daɗawa kuma yakasance AZZALUMI nagaban kwatance,


Ƙwace,kashe rayukan al'umma,tare da farauce dukiyoyin su ba a bakin komai yake a wajen sa ba,


A rayuwar sarki Husnalu babu abin da yake tsananin kauna fiye da ɗansa guda ɗaya mai suna Hatmal,


Yarima Hatmal yakasance ɗan lele a wajen sarki Husnalu baya son ɓacin ransa ko kaɗan,


Bisa al'adar Sarki Husnalu duk bayan shekara ɗaya sarakunan dake ƙarƙashin ikon sa kan biya sa haraji na dukiya da adadin ta yakai dinare dubu ɗari tara, gami da kayan amfanin gona da dabbobin ni'ima


Tsakani na da gimbiya salimat akwai soyayya mai karfi, kasancewar mahaifina shi ne wazirin mahaifin ta,tun muna yara ƙanana muke kaunar juna.






****


Wata rana daga cikin ranakun da sarakunan ke kaiwa sarki Husnalu haraji, kamar yadda aka saba duk shekara,


Sai yazamana cewa a wannan shekara anyi tafiyar tare da ni da masoyayi ta gimbiya salimat,


Bayan dukkanin sarakunan sun kammala hallara a fada,


Bayan shiru da ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai aka hango sarki Husnalu da yarima Hatmal sun shigo fadar, suna sanye cikin suturu iri ɗaya hatta takalmin dake kafar su iri ɗaya ne,


Koda jama'a suka hango sarki sai suka miƙe tsaye domin girmama a gare su,


Kai tsaye sarki Husnalu da yarima Hatmal suka huce izuwa inda karagar mulki take suka zauna a tare,






Sannan sauran jama'a suka zauna, batare da bata lokaci ba sarakunan suka dunga tashi daga wajen zaman su suna zuwa gaban na Husnalu suka kwasar gaisuwa sannan su gabatar da harajin su da jama'ar da suka yi musu rakiya






Sarki na farko da ya gabatar da harajin da ana kiransa da suna zulaibu, yana mulkin wani ɗan ƙaramin gari mai suna madinatul-shaswal,






A gaba ɗaya sarakunan da suka hallara a fadar babu wanda yakai zulaibu yawan shekaru da kuma dadewa akan karagar mulki,






Sai da sarakuna biyar suka gabatar da harajin sannan aka iso kan sarki Abu-salimat,






Abu-salimat ya mike tsaye ni da gimbiya salimat muka mara masa baya, dakaru na biye da mu ɗauke da akwatin dinare gami da kayan amfanin gona, har mu ka isa inda karagar mulki take, muka zube ƙasa muka kwashi gaisuwa muna masu sunkuyar da kawunan mu.






Kawai sai waɗansu dakaru daban a fadar suka karɓi wadannan akwatin dinare suka lissafa kuma suka bincike kayan gonar suka tabbatar da ingancin su sannan suka ɗauke suka fice daga fadar,






Ana cikin wannan hali ne na ɗan saci kallon yarima Hatmal ai kuwa sai na ga ya ƙurawa gimbiya salimat idanu yana mai yi mata wani irin kallo daya sanya hantar ciki na ya kaɗa, Ku ma tsoro ya kamani.






Domin kallon da naga Yarima Hatmal na yi mita kallo ne ma nuna kamuwa da soyayya.






Jikina a ssnyaye na mayar da kai na kasa, sannan sarki Husnalu ya Umarce mu da mu fice daga fadar,






Cikin hanzar sarki sarki Abu-salimat ya miƙe tsaye muka rufa masa baya muka fice daga fadar


Fitowar mu keda wuya sai muka fara shirye-shiryen komawa izuwa ƙauyen Darul-Na'am






Bayan an kammala ne muka hau bisa dawakan mu muka fice daga kasar Baitul-sharhal muka nufi hanyar da zata sadamu da ƙauyen Darul-Na'am,






A wannan lokaci sarki Abu-salimat ne akan gaba tare da wani hadimin sa mai suna Haimar suna hirarrakin su cikin nishadi,






Ni da salimat muna hira irin ta masoya, ana cikin wannan hali ne gimbiya salimat ta dube ni tace"ya masoyi na kuma hasken rayuwa ta shin nayi maka wata tambaya mana






Cikin annurin fuska nace faɗi tambayar ki ya abar kauna ta






Salimat tayi ajiyar zuciya ta ce " shin a halin yanzu yaya matsayin soyayya ta yake a zuciyar ka?






Koda jin wannan tambaya sai na tuntsire da dariya na dubi lasmirat nace " shin kina kina tantama ne akan matsayin ki a rai na ko kuea.






A,a kawai ina so naji matsayi na ne






Salimat ta faɗa fuskar ta cike da annuri,.






Murmushi nayi a karo na biyu nace" Ai matsayin ki a waje na tamkar hanta da jini ne domin babu abin da zai raba tsakanin mu face mutuwa,






Salimat tayi murmushin jin daɗi tace " Ni kuwa ka zame mini tamkar numfashi a rayuwa ta,






Nan take mu duka biyun muka fashe da dariyar farin ciki






Ana cikin wannan hali ne muka jiyo alamun takun sawaye a bayan mu,






Cikin firgici muka ja linzamin dawakan mu muka tsaya koda muka wai ga sai muka yi arba da waɗansu ZARATAN DAKARU masu matukar yawa






Shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,






Har mun yunkura zamu zare takubban mu sai sarki Abu-salimat yayi mana nuni da mu dakata






Bisa lura da yayi cewa basu bane dakarun face na sarki Husnalu






Sannu a hankali dakarun suka iso har izuwa inda muke suka yiwa dawakan su Turkiya,


Sarki Abu-salimat ya dubi wani garjejen kato mai kirar samudawan farko wanda da alama shine shugaban dakarun yace dasshi" yakai muraizu shin wane saƙo kuke tafe dashi izuwa gare mu ina fatan dai bamu saɓawa mai girma Husnalu ba,


Sadauki muraizu ya bushe da dariyar mugunta mai kama da kukan jaki daga bisani ya murtuke fuska tamkar an masa da saƙon mutuwa,


Cikin Wata irin kakkausar murya yace" ya kai Abu-salimat kayi sani cewa bakomai ne ke tafe da mu ba sai domin ka bamu yar ka salimat mu Kaita izuwa ga sarki saboda ɗan sa Yarima Hatmal ya kamu da soyayyar ta kuma yana so ne ya aure ta


Cikin matukar kaduwa Abu-salimat ya dubi muraizu a lokacin da idanun sa suka zazzaro yace" shin wace irin maganar banza kake yi yakai muraizu anya kuwa a cikin hankalin ka kake kuwa?


Muraizu ya bushe da dariyar mugunta har ya kusa faɗowa daga kan dokin sa daga bisani ya haɗe rai yace"Tabbas garau nake nasan Abin da nake faɗa ina cikin hayyacina,


A halin yanzu ba neman shawarar ka muke yi ba face zartar da umarnin mai girma Husnalu,


Koda jin wannan batu daga bakin muraizu sai na fusata ainun ya dakamasa tsawa cikin matukar fushi na dube nace " karyar ka tasha karya yakai wannan la'ananne kuma BAKIN AZZALUMI kayi sani cewa karyarka tasha karya baza mu taɓa lamunta da wannan magana taka ba,


Kafin na gama rufe bakina sadauki muraizu ya fusata ainun ya zaro kibbau guda biyar a gadon bayan sa ya ya saka a cikin bakan sa yaja ya ɗame cikin wani irin zafin nama ya harba kibban


Kafin ɗaya daga cikin mu yayi wani yunkuri kibiyoyin guda biyar sun sauka a kan waɗansu jama'ar mu mutum biyar sun faɗi kasa matattu






Mutum biyar ɗin sun kasance dattijawa kuma manyan yan majalisar sarki da muke matukar alfahari dasu a cikin ƙauyen Darul-Na'am


Koda sarki Abu-salimat yayi arba da gawarwakin yan majalisar tasa sai hawayen takaici da bakin ciki suka zubo masa,


**


Lokacin da saurayi yaslir yazo daidai nan a labarin sa sai hawaye suka zubo daga idanun sa,


Al'amarin da ya sanya sarauniya lasmirat ta kamu da matukar tausayin sa kenan.


Har ta buɗi baki da nufin tace wani abu sai kawai suka ga sararin samaniya yayi dubu dunɗim!


Cikin matukar firgici lasmirat da saurayi yaslir suka ruga mike tsaye zumbur suka ruga izuwa wajen turakar, suna fita suka ci karo da Sarkin yaƙi,


Sarkin yaki ya dubesu cikin tashin hankali yace " ya shugabata muna cikin gudanar da ayyukan mu na tsaron kofa kawai sai mu kayi arba da wata gibgegiyar halitta mai matukar muni daban tsoro tana ta hallaka mutane,


Ya shugabata na rantse da karfin mulkin ki babu wata halitta da zata tsira da ga sharrin halittar,


Kafin Sarkin yaki yagama rufe bakin sa sarauniya lasmirat ta tari numfashin sa tace" A yi maza aje a busa ƙahon yaƙi,


Batare da lasmirat ta jira Sarkin yaƙi ya furta wani abu ba ta shige gaba yaslir ya mara mata baya yana mai dogare da sandar sa,


A can cikin gari kuwa halittar ta wanzu tana ta hallaka mutane jama'a suna ta guje-guje da ifice-ifice domin tsira da rayukansu,


Duk inda halittar ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin jama'a birjik kwance a ƙasa cikin jini,


A wasu lokutan ma sai kaga halittar ta sanya hannun ta ta yaye rufin ɗaki ta ɗauko mutum ya na ihu ta sanya a bakin ta ta laƙume tayi loma ɗaya dashi,


Ana cikin wannan hali ne sai aka hango sarauniya lasmirat da saurayi sun rugo wajen a bisa dawakai cikin gagarumar shigar yaƙi suka tsaya cak,


Kawai sai lasmirat ta dakawa halittar tsawa,


Koda halittar taji an dakama tsawa sai ta tsaya cak a waje guda ƙurawa su lasmirat idanu tana mai nazarin su,






Ita dai wannan halitta takasance,shirgegiyar aljani mai matukar tsawo,muni,gami da ban tsoro,






Babu wata halitta da zata yi arba da wannan aljanar face firgici, Saboda matukar munin ta






Duk irin dakewar zuciya irin ta lasmirat da saurayi yaslir sai da tsoro ya ɗarsu a zukatan su,






Dakarun dake bayan su kuwa sai jikin su yakama kyarma yana tsuma tamakar ace kyat su cika wandon su da iska saboda tsananin tsoro,






Sai da aka shafe tsawon dakika talatin a cikin wannan hali ana kallon kallo






Daga can sai aljanar ta bushe da dariyar wanda ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads