Showing 9001 words to 12000 words out of 22047 words
Chapter 4 - TAKOBIN DAUKAKA complete .txt
ta annuri tace"ya abin dogaro na shin ina dalilin rashin bayyanar ka akan lokaci domin gudanar da wannan tafiya tamu?
Dayyubul-Barmas yayi murmushi yace" ya sarauniyar kiyi sani cewa bakomai bane ya sanya ban bayyana akan lokaci ba sai domin na kara gudanar da bincike ne game da tafiyar tamu,
Koda jin wannan batu sai lasmirat tace " ka gafarceni ya uban bokaye,
Dayyubul-Barmas ya tari numfashin ta yace "ba sai kin wahalar da kanki wajen sanar da ni sunayen a bokan tafiyar ki ba,
Yaslir da Sunaila, dukkan su ilimin tsafi ya bayyana mini abin da ya gudana tsakaninsu da su,
Tabbas kin yi tunani mai kyau, domin Sunaila da yaslir zasu yi matukar taimaka wajen wannan tafiya tamu,
Yanzu ina ganin abinda ya kamata mu fara yi shine tafiya domin ɗebo ruwan koramar boka Daryalu, domin hakan shi ne zai bamu damar fuskantar dajin Husumul-kadar,
Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya kwallawa aljanin sa kira sau uku,
Aljanin ya bayyana gaban sa ya kwashi gaisuwa, duk da kasancewar su lasmirat suna da dakakkiyar zuciya sai da suka razana da ganin aljanin,
Aljanin yakasance garjejen kato karfaffan gaske,yana da rafkeken kai tamkar dutse,mai ɗauke da waɗansu manyan idanu jajaye,tamakar kwallon goriba,yana da katon hanci da rafkeken baki, sannan ya da manyan fuka-fukai guda shuda,
Boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljanin cikin nutsuwa yace"yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka ɗauke mu izuwa Husumul-kadar domin ɗauko zobunan sihiri a cikin kogon fatalwa,
Daga nan kuma mu huce izuwa inda ma'ul-diya'u yake mu ɗauko kubar miftahul-daryal,
Yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zaka samu ya ci
Yayin da aljani Huzmal yaji wannan batu sai ya risina ya ce" An gama ya shugabana
Yana gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa boka Dayyubul-Barmas, lasmirat, yaslir da Sunaila suka hau suka zauna
Sannan ya yunkura ya ya tashi sama ya na mai buɗe fuka-fukan sa yana mai keta gajimare, cikin sa wani irin azababban gudu na keta sa'a
Tun da aka fara wannan tafiya babu wanda yace kala har yazamana an shafe tsawon sa,a uku
Ana cikin wannan hali gyangyaɗi ya fara ɗaukar boka Dayyubul-Barmas koda ganin hakan sai dariya ta suɓucewa sarauniya lasmirat wanda ta sanya Dayyubul-Barmas dawo cikin hayyacin lasmirat ta dube sa tace" Haba dodon bokaye ai bai kamata ace irin ku suna suna barci ba,
Koda jin wannan batu sai dariya ta suɓucewa boka Dayyubul-Barmas ya dubi lasmirat yace"Taɓ ɗi jan wannan fa shi ake cewa wai ana wata ga wata Dara ta ci gida ke yanzu wannan gyangyaɗi da nayi shi ne ya baki mamaki, tabbas da ace kin taɓa jin labarin boka shu'umanu da baki yi mini wannan dariya ba,
Wane ne kuma boka shu'umanu?
Lasmirat ta tambaya a ƙagauce,
Dayyubul-Barmas ya ce" boka shu'umanu wani hatsabibin matsafi ne da ya shiga alwar tsafi ta tsawon shekaru uku domin ya karance wani muhimmin littafi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN JARUMTA,
Babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki kundin ya karantasa baki ɗaya face ya mulki duniya,
A daren ranar da boka shu'umanu zai kammala wannan karatun littafi ne wani irin barci mai nauyi ya ɗauke sa
Sa'adda boka Dayyubul-Barmas ya zo nan azancen sa sai mamaki ya kama lasmirat, yaslir da Sunaila,
Lasmirat ta ce" shi kuwa Boka shu'umanu da ya farka daga barcin me ya faru dashi,
Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya ce"Ai wannan tambaya taki labari ne mai tsawo sai dai ki nemi littafi KUNDIN JARUMTA ki karanta,
Lasmirat ta gyaɗa kai aka cigaba da tafiya,
Kwanaki nabin kwanaki,mako nabin mako sai gashi su sarauniya lasmirat sun shafe kwanaki ashirin da uku suna tafiya,
A iya tsawon wannan kawanki babu abinda ke sanyawa a tsayar da tafiya face idan wani daga cikin su zai yi bawali ko kuma lokacin barci yayi,
Ana cikin tafiyar ne saurayi yaslir ya dubi Sunaila yace da ita" ya JARUMAR JARUMAI,
shin mene ne dalilin daya sanya kika ƙi bayyana fuskar ki a garemu?
Koda jin wannan tambaya sai sunailata sunkuyar da kanta ƙasa kamar mai tunanin wani abu,
Daga can sai ta ɗago da kanta ta dubi yaslir tace"Ai wannan rufe fuska tawa yana da matukar muhimmanci agareni anan gaba zaka tabbatar da abinda na faɗa
Idan kuwa har ka na so ne kaga fuskar ta wa to yazama wajibi ka amince da sharudda guda uku
Da farko zaka yanko mini kan riƙeƙƙen zaki da ya shekara arba'in,
Na biyu kuma zaka ceto rayuwar abokan tafiyar mu har sau uku
Abu na karshe shi ne zaka farauto mini damisa guda biyu ka kawosu gare ni,
Sa'adda saurayi yaslir yaji waɗannan sharuddan daga bakin Sunaila sai sai ya shiga nazari.
Abu na farko da ya faɗo masa arai shi ne menene fa'idar waɗannan sharuɗɗa da Sunaila ta gindaya masa,
To amma tun da a halin yanzu bashi da burin da ya huce yaga fuskar Sunaila dola ne ya amince da wannan sharuɗɗa,
Kawai sai yayi gyaran murya ya dubi Sunaila yace" Na amince da wannan sharuɗɗa naki ya JARUMAR JARUMAI
Duk wannan tattaunawa da ake tsakanin yaslir da Sunaila sarauniya lasmirat ta na sauraron su
Koda taji yaslir ya amince da sharuɗɗan jaruma Sunaila domin ya yi arba da fuskar ta kawai
Sai zuciyar ta takama tafarfasa tamkar zata kone kuma tsananin kishi ya turnuƙe ta,
Lallai lokaci yayi da zaki bayyana soyayyar ki ga yaslir domin matsawar yayi arba da fuskar Sunaila
Abin da kike gudu zai fara
Koda jin wannan shawara daga zuriyar ta sai lasmirat sai ta bar abin a ranta
Amma sai wani tunanin ya faɗo mata,shin wai ma me yasa zaki kamu da soyayyar wanda bazai ji kiranki ba,kuma Bayan cewa bashi ne namijin da zaki aura ki samu Haihuwa ba,
Sa'adda tazo nana atunanin ta sai taji zuciyar ta tayi mata ƙunci,
Har lasmirat ta buɗi baki zata ce wani abu sai boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljani Huzmal yace dashi"
Yakai Huzmal ai sai ka sauka a turba domin mun iso dajin Husumul-kadar
Koda jin wannan umarni dai Huzmal ya saki fuka fukan sa ya sauka a turba,
Boka Dayyubul-Barmas ne yafara saukowa sannan lasmirat, yaslir, Sunaila ce a ƙarshe,
Nan fa aka yi arba da dajin Husumul-kadar yakasance mai ɗauke da manyan bishiyoyi masu tsawo tsiya babu duwatsu ko ɗaya a cikin sa face waɗansu manyan koguna guda uku masu ban tsoro,
Wani irin farin hayaƙi ya mamaye dajin baki ɗaya babu alamar haske rana a cikin sa,
Tabbas wannan daji yakasance mai ban tsoro,
Tsawon daƙika arba'in su lasmirat na karewa dajin kallo sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas ya dube su yace" yaku abokan tafiya kuyi sani cewa a cikin wannan daji ne zamu ɗauko zobunan sihiri,
Sai dai ina so kuyi sani cewa wannan daji ne na ɗauke da musibu da bala'o'i da sai mun yi da gaske zamu tsira da rayukan mu,da wannan nake yi mana fatan samun nasara,
Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya shafi sandar tsafin sa take ta rikiɗa izuwa wani ƙaton sungumi
Sai kawai ya kunna kai izuwa cikin dajin yana mai cewa aljani Huzmal sai ka jira mu anan
Lasmirat, yaslir da Sunaila suka mara masa baya,
Tun da aka shiga dajin Husumul-kadar sai da aka shafe tsawon dakika ɗari biyu koda motsin tsuntsaye ba,a ji ba,
Al'amarin da ya ƙara jefa tsoro a zukatan su sarauniya lasmirat kenan.
Lokacin da aka iso inda wannan koguna suke sai aka shiga nazari
Boka Dayyubul-Barmas ya dube su yace" A cikin waɗannan kogunan dutse uku ne zamu ɗauko zobunan sihiri sai dai ba za mu iya gane wanne ne wanda zobunan ke ciki ba,
Karfin shirin tsafi bazai taba tasiri a cikin su face dole mu shiga izuwa kogo na farko ko zamu dace ,
Lasmirat ta dubi Dayyubul-Barmas cikin damuwa tace to mai hana bazamu koma baya ba domin mu gudanar da bincike mu gano kogon da zobunan sihirin ke ajiye a cikin sa,
Dayyubul-Barmas ya ce "Ai bisa sharaɗin wannan daji idan mutum ya shigo baya fita kodai ya samu nasarar ɗauko zobunan sihiri ko kuwa ajali Ya riske shi a ciki,
Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya matsa kusa da kofar kogo na farko ya ɗaga kansa sama ya karanta waɗansu haruffa da aka rubuta da tawadar za'afaran jikin wani allon karfe a saman kogon,
Yana kammala karantawa sai kofar kogon ta buɗe wani irin tiririn bakin hayaƙi ya surnano daga cikin sa,
Boka Dayyubul-Barmas ya tusa kai izuwa ciki, lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi koyi dashi, lokacin da Sunaila wacce ita ce ta karshe ta sanya kafarta ta biyu sai kofar kogon ta mayar da kanta ta rufe ruf
Tamkar bata taɓa budewa ba,
Lokacin da su sarauniya lasmirat suka shiga izuwa cikin wannan kogon dutse na farko a cikin dajin Husumul-kadar,
Sai suka ci-gaba da tafiya a cikin sa suna ganin abubuwan abubuwan al'ajabi kala daban daban,
A wasu lokutan sai suji alamun takun sawaye a bayan su amma dazarar sun waiga sai su ga basu ga komai ba,
Haka dai suka ci-gaba da tafiyar babu sassauci, har yazamana sun shafe tsawon dakika ɗari huɗu batare da an haɗu da wani abu mai cutar wa ba,
Yana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai su lasmirat su kaji wani mahaukacin gurnani ya mamaye kogon dutsen gaba ɗaya ya kama girgiza tamakar zai rugurguje, sannu a hankali wani takun sawaye yafara bayyana,
Kwatsam sai wani mutum ya bayyana tsulum Tamkar an jefoshi daga sama,
Mutumin yakasance narkekeken kato, rabin jikin sa na gwaggwan biri ne, rabin kuma na bil,adama ne,
Yana matukar tsawo tamakar tsauni, yana da tarin kwanji tamkar jikin sa yakasance na dutse,fuskar sa mummuna ce mai matukar kwarjini daban tsoro, mau ɗauke da gashin gemu da ƙasumba buzu buzu babu kyan gani, wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga hancinsa duk sa'adda ya busar da numfashi,
Tabbas wannan mutum ya kasance abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face ya ɗimauce,
Sa'adda su sarauniya lasmirat suka yi arba da mutumin sai suka firgita ainun
Lasmiratda yaslir jikin su yakama kyarma yana tsuma tamkar nazari
Dayyubul-Barmas da Sunaila ne kaɗai basu yi ba amma su ma a matukar razane suke,kawai dai karfin hali ne irin na GWARAZAN MAYAKA
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su lasmirat da
Sai da aka ɗauki wani lokaci ana wannan kallon kallo,
Sai daga bisani ne mutumin ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta wanda ta haddasa girgizar kogon kuma wani ƙara mai kama da aradu ya bayyana,
Bashiri su lasmirat suka sanya hannayen su biyu suka toshe kunnuwan su domin ji sukayi kamar zasu kurman ce,
Sai da narkekeken kato ya tsuke bakin sa sannan komai ya samu dai dai tuwa, kogon ya dai na raurawa,kuma su lasmirat suka dawo hayyacin su kuma har ma suka lura cewa ashe mutumin yana ɗauke da wata gabgegiyar jela wadda akalla tsawon ta yakai kamu arba'in,
Narkekeken katon ya dakama musu tsawa data sanya hantar cikin su ta kaɗa ya dube su cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki yace
"Yaku waɗannan bil'adama ma'abota GAJERAN KWANA shin wane rashin hankali ne ya shigo da ku wannan kogo bayan cewa fiye da shekaru dubu uku babu wata halitta walau mutum ko aljan da taɓa yin wannan ganganci
Sai dai nasan cewa bawai rashin sani ya kawo ku nan ba sai domin kwaɗayin daukar zobunan sihiri
Dake ajiye a ɗaya daga cikin waɗannan kogunan dutse biyar na cikin dajin Husumul-kadar,
Ina mai tabbatar muku dacewa kun tafka babban kuskure da zuciyar ku ta bayyana muku dacewa zaku fita daga wannan daji a raye ɗauke da zobunan sihiri
Kafin mutumin mai siffa biyu yagama rufe bakin sa boka Dayyubul-Barmas ya tari numfashin sa Yana mai dakamasa tsawa yace
"Yakai wannan mummunan halitta kayi sani cewa kwarjini da girman ka bazai bamu tsoro ba
Shin ko ka manta ne cewa karfi a zuciya yake bawai a jiki ba,
uma idan akwai rai to da rabo, kaga kenan akwai yiwuwar samun nasara akan ka kuma har mu ɗauke zobunan sihiri,
Caraf mutumin ya tari numfashin boka Dayyubul-Barmas ya dube sa yana mai bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa,
"Tabbas gaskiya ne maganar ka amma fa kar ka manta cewa masu iya magana na cewa" Alamar karfi tana ga mai ƙiba,
Wani abu ma da baku sani ba shi ne shi kansa matsafi zarratu ibn lauhat da ya sana'anta zubonan sihirin a halin yanzu ba shi da iko dasu ballantana wani bil'adama karan kaɗa miya,
Sannan ma yanzu idan kun samu nasarar hallaka ni taya ya kuke tsammanin zaku tsira daga sauran musibun dake cikin wannan daji,
Bayan cewa ma kuma a cikin ku babu wanda yasan inda zobunan sihiri suke a cikin koguna biyar ɗin,
Koda gama faɗin hakan sai narkekeken katon ya zira hannun sa a cikin wata akwatu ta baƙin ƙarfe da ke kusa dashi a ɗauko wani zabgegen gatari na zallar mulmulallan farin karfe yana sheƙi,walwali da ɗaukar idanu ya yunƙura izuwa inda su sarauniya lasmirat suke tsaye,
Koda ganin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya ɗaga sungumin sa sama yana mai kurma wawan ihu ya ruga izuwa kan halittar,
Yaslir ne ya mara masa baya hannun sa rike da takobi tsirara,
Sunaila da sarauniya lasmirat ta suka ru fa masa baya,
Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Mansur Usman Sufi
Littafanyaki.com.ng
Takobin Daukaka
Book 2 compelet
Littafin Yaki
Mansur Usman Sufi
Ana haɗuwa aka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban tsoro,
Ana fara wannan gumurzu ne su sarauniya lasmirat suka fara gane kuren su,
Domin ƙarfin saran su su duka hudun bai kai ɗaya na mutumin mai siffa biyu ba,
Domin duk sa'adda daya kaiwa ɗaya daga cikin su sara idan ya zillewa harin duk sa'adda gatarin ya sauka a ƙasa sai kaga ya haddasa rami mai tsawon kamu ashirin, idan kuwa akan dutse gatarin ya sauka sai kaga yayi bindiga ya tarwatse
Sai da aka shafe tsawon sa,a ɗaya ana wannan baƙin artabu babu sassauci,
Ana cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗowa mutumin mai siffa biyu,
Abin da ya faɗo masa kuwa shine shin mene ne dalilin da daya sanya ya kasa samun nasara akan waɗannan bil'adama alhalin baya ta ɓa fafata yaƙi da wata halitta a cikin abinda bai gaza dakika goma ba face ya zare mata ruhin ta daga gangar jiki,
Tabbas akwai wani abu Ruwa baya tsami banza
Koda narkekeken katon ya zo nan a tunanin sa sai ya fusata ainun zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,
Kawai sai ya canza salon faɗan sa yazamana cewa ya sake zage damtse wajen kai wa su boka Dayyubul-Barmas miyagun hare haren fiye da ɗazu
Gami da haɗawa da kai mu su naushi da bugu hannu da ƙafa,
Kaico gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ma ta canza
Faruwar canza salon faɗan keda wuya sai mutumin yafara samun nasarar naushin su boka Dayyubul-Barmas,
Yazamana cewa idan ya naushe sun sai kaga sunyi sama tamakar an janye su da ƙugiya sannan daga bisani su faɗo ƙasa tim
Idan fuska ya nausa sai kaga hanci da baki na yoyon jini, idan kuma ajiki yayi naushin sai wajen yayi tsami, jini ya tari,
Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA sai kaga sun mike tsaye zumbur an cigaba da artabu
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje a lokacin da ake wannan artabu yaga yadda su boka Dayyubul-Barmas ke yakin cikin juriya da nacin tsiya
Dola ne ya jinjina musu ya tabbatar dacewa sun cika GWARAZAN MAYAKA masu dakakkiyar zuciya,
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne Sunaila ta kaiwa narkekeken katon hari da takobin ta a hannun sa a lokacin da yake ƙoƙarin tarwatsa mata kai
Bisa sa'a sai gashi takobin ta tayi tasiri a jikin ɗan yatsan sa har jini yayi tsartuwa.
A dai dai lokacin ne sarauniya lasmirat ta samu nasarar laftawa narkekeken katon sara a kafar sa take inda ta sara ɗin ya haddasa wani katon rauni jini yayi tsartuwa gami feshi,
Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniya lasmirat da Sunaila mamaki kenan domin tunda aka fara wannan yaƙi hakan bai faru ba, domin idan takubban su suka sari mutumin sai dai suji tamkar dutse suka sara tartsatsin wuta ne kawai yake tashi gami da kara marar daɗin sauraro,
Sa,adda mutumin mai siffa biyu naga raunuka biyu a jikin sa kuma dukkanninsu suna zubar da jini sai kawai yayi wurgi da gatarin sa gefe guda ya takarkare ya kwarara wawan ihu wanda ya mamaye kogon dutsen kuma ya haddasa wata yar ƙaramar girgizar ƙasa,
Kafin ɗaya daga cikin su yayi wani yunkuri mutumin mai siffa biyu ya shammace su ya gabza musu wawan naushi a fuska cikin zafin nama a lokaci guda su duka huɗun suka zube kasa magashiyan numfashin su na fita sama
Kawai sai ya wurgila jelar sa izuwa inda suke kwance,take ya samu nasarar kanannaɗo boka Dayyubul-Barmas, Sunaila da lasmirat da jelar sa,
Nan take suka fara gani dishi- dishi sakamakon naushin da mutum yayi musu kuma suka ji tamkar ƙasusuwan jikin su zasu karye, saboda yadda jelar tayi kanannade su tayi musu ɗaurin Hunhun goro,
Sa,adda Sunaila ta duba taga babu yaslir sai tace a ranta shin ina yaslir ya shiga ko kuwa ya rasa rayuwar sa ne?
Amma idan har yana raye wannan itace damar sa ta farko dazai ceci rayuwar mu ɗaya daga cikin sharuddan da zai bi har ya samu nasarar ganin fuskata,
Abin da Sunaila bata sani ba shi ne lokacin da mutumin ya kanannaɗo su da jelar sa yaslir ya gangara izuwa wani rani dake tsakiyar kogon dutsen,
Lokacin da boka Dayyubul-Barmas ya ga irin mummunan halin da suke ciki sai ya shiga ƙoƙarin ceto rayuwar ta karfin sihiri,amma shiru kakeji malam ya ci shirwa,
Koda mutumin mai siffa biyu yaga cewa Boka Dayyubul-Barmas na ƙoƙarin cewa rayuwar abokan tafiyar ta karfin sihiri sai ya sake bushewa da dariyar mugunta har da kyakyatawa,
Ya shiga koɗa kansa yana yiwa kansa kirari yana mai cewa
"" Nine gagarau uban gagararru
Guguwa nake maganin karmami
Wutar bala'i mai tada hankalin duniya,
Mutum dubu kalacen dafe,aljanu dubu goma kalacen yamma""
Kammala yiwa kansa kirarin keda wuya sai kawai ya yi nuni da ɗanyatsan sa na hagu izuwa ga wannan akwatin bakin karfe daya ɗauko gatarin sa a ciki,
Take wata irin gagarumar wuta ta bayyana a cikin akwatin tamkar dama can akwai ta,
Kawai sai ya juyar da jelar sa izuwa inda akwatin take,