Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 68622 words

Chapter 2 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

1128

Ads at the middle of Article

4 zata shagon abinci gashi this whole drama yabata mata lokaci, da kyar ya iya ya lallaba yafito daga bolan sai amai duk wani abu dayaci saida ya amayar dashi sai kakkabe jikinshi yake yadago zai mika mata gyalenta daidai tanashan kwana harta tafi, he wanted to say thank u dudda she’s a crazy wicked girl tana zubamai dirt tana murmushi but she helped him, hannunshi yakai aljihunshi yataba but baiji wayanshi ba kuma baisan a ina ta fadi ba wlh kuma shi bazai duba bolan nan ba, daidai wani cleaner na gunguro nashi bolan dasauri yace “please bani aron wayanka nakira” binshi yayi da kallo ganin kaman ba lafiya yasa yabashi wayanshi Munir yakira kafin yayi magana yace “Munir kazo ka daukeni a airport pls karka fadama kowa kana zuwa katambayi wajen zuba bola ina wajen” kafin yayi magana ya katse wayan yabama yaron yazauna awajen kawai feeling terribly sick kusan 1hr yana wajen jikinshi yadau mugun zafi ga tsigan jikinshi na tashi kaman zai mutu yana zaune ahaka yaji ance. “Riyad” dasauri yadago kanshi da gudu gudu sauri sauri Munir yataho wajen yace “what happened to you like this? Wat are you doing here? Why are you so dirty”? Tashi yayi yana kokarin yima Riyad magana yace “someone tried to kill m…..” kawai ya sume da kyar Munir yasamu wani cleaner yazo kawo datti shima aka tayashi daukanshi suka tafi mota aka sashi sai gida bayan yakira Mom akira Dr.


Tawani special secret gate Munir yabiyo aka budemai already ga mutane tsaitsaye Gwaggo (Mai Babban daki) gawata black beauty mata dake sanye da hijab mai dan kiba (Mom), Wambai, Waziri, Kabeer da su Halilu, Ibrahim da Shuaibu, Baffa Mujitapa dukansu suna wajen da family Dr nasu, yayi parking agurguje Munir duk sukai wajen fashewa da kuka Mom tayi tace “what happen to yarona Munir? Wakeson kashemin shi daga shigowanshi garin nan? How did they even know ya shigo? Gwaggo jini a hannunshi look, Doctor do something” Mom tai maganan tana kama hannunshi ashe wukan ta yankeshi dazu, atare dukansu mazan suka ciccibeshi zuwa wani dabkareren flat na Mom Gwaggo tace “meya sameshi haka Munir? Jibi jikinshi? Meya faru Munir”? Dasauri Munir yace “Gwaggo nima bansani ba but kaman he was attacked ne, yana kokarin fadamin wai ana kokarin kasheshi ya sume ba wayanshi taredashi, shi babu akwati, akusa dashi, awajen bola naganshi da bag pack yana mota dawani dan kwali black, kafin yafadamin komi kuma yasuma” gam Mom tarike hannunshi har daki kan wani taskeken gado aka kwantar dashi Dr yashiga dubashi yanda skin nashi da fatanshi keyin wani bororo dahar wani motsi suke yasa yace “a chanzamai kayan jikin nan nashi maza, ku goggogemai jiki with clean towel, allergy ke damunshi, he’s allergic to dirt da kazanta right from small, kuyi sauri pls” fita kowa yayi daga dakin akabar Munir da Mom, Waziri da sauran duk suka zauna a falo yace “wazai attacking yaro daga durowan shi kasan nan?” Anatse Wambai yace “call the police I think sai anbincika airport din maybe ta CCTV za’a gani” faduwa gaban Kabeer yayi amman yadaure yaranshi always do a clean job he hope bazasu kwofasashi ba, fitowa Munir yayi yace “Dr an gama” dukansu komawa ciki sukayi Kabeer sai tsaki yake aranshi shida yakeso kowa yaji haushinshi amman jibi yanda kowa ke nan nan dashi, attention yakoma kanshi ma infact, skin nashi gabaki daya yakoma so red, drip akamai fixing da allurai ciki Dr yakalli Mom datafi kowa damuwa adakin yace “anjima kadan zai farfado don’t worry” dan murmushi tayi tareda gyadamai kai Waziri yace “ki zauna dashi” Gwaggo tace “nima ina nan kome za’a kawomai kowa zaizo yadubashi saina ganshi inga uban waye keso ya cutar mini da jika, bangama kukan mutuwan d’ana ba yanzu halakamin jika za’ayi wlh jinina yasha karfin kowa” kallon Munir Mom tayi ahankali tace “thank you Munir” gyadamata kai yayi yawuce yafita daga dakin hakan yarage daga Gwaggo sai ita, dafata Gwaggo tayi tace “ki tsare yaron nan ki dage da addu’a akanshi, tun ranan da aka haifi Riyad akace yanada taurari masu kyau kuma babban mutum ne shi, kiduba kigani yaran marigayi maza shidda amman shi kadai akeso ahalaka tun yanzu kenan bama asan waye zai gaji kujeran sarautan ba kenan amman so ake akasheshi balle kuma ace shine zai gaji sarautan ki tashi tsaye Maryama, saikin tashi tsaye, kinyi zaman gidan nan basai na fadamiki hadarorin dake cikinsa ba, inde kalubale ne yanzu Riyad yafara gani, idan kuma yazama Sarki yadinga ganin kalubale iri iri kenan har abada, ki tsare yaron nan, kizama idanunshi kunnuwanshi uwa uba kizama inuwarsa dakuma lullubinsa” gyadama Gwaggo kai Mom tayi takama hannun Riyad tarike gam tana kallonshi tace “Gwaggo meya musu Riyad dako zaman gidan nan baiso, na tabbata baimason ya gaji kujeran nan, dan bata gabanshi” Gwaggo tace “kwarai” Mom tace “shi kadai Allah yabani, shi kadai gareni, Riyad kadai Allah yabani yau ana kokarin rabani dashi” kankame hannunshi tayi tace “Gwaggo zan iya zuwa bangon duniya sabida Riyad! Kuma nayi alkawari duk Wanda yace zai cutar da yarona saidai yafara dani dan daga yanzu zan zama shamaki tsakanin Riyad da komi na duniyan nan, zan zama inuwa hazo zan lullubeshi nakuma kareshi daga duk wata hari” sosai Gwaggo take kallonsu sai kawai tai murmushi tadauki charbi ta tacigaba da ja itama bini bini tana tofama yaron addu’a aka.




JOIN GROUP DANAKE POSTING NOVEL DIN NAN




https://chat.whatsapp.com/CrKHphXCxK09RvYbrO1cCU
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: 💫 SANYI DA ZAFI 💫




EPISODE 3️⃣






✍🏻M SHAKUR


WHEN WAS THE LAST TIME KIKA SAYI SABON PANT?🤭 TALK TRUE


BRA DINKI SUN KOMA RUWAN KASA TSABAGEN SAWA KULLUM😒


TO IDAN NACE YAU NAKAWO MIKI HABISHMA UNDERWEARS FA👙💃 SUNA SAIDA PANTS, BRAS, NURSING BRA, MATERNITY GOWNS, NO LEAKAGE PANTS NA PERIOD, KAYAN BACCI DA SAURANSU🔥
SUNADA MOST AFFORDABLE KAYA GA VERY CHEAP DELIVERY NATIONWIDE GO AND BUY NOWWWW!!!


https://www.tiktok.com/@habismaunderwears?_t=8lzVAMnAhgk&_r=1


4 daidai tashiga wani babban kanti na abinci irin local restaurant din nan, wata katuwar mata dake zaune a tsakiyan shagon kan kujera ga lalitan uban kudi a hannunta tana kirgawa ne ta kalleta tace “Allah yasoki baki latti ba” batace komiba kai tsaye tace “ina wuni Maman Miwa” batare data amsaba tace “nidai je ga wanke wanken ki chan na jiranki” bata damu da yanda tamata maganan ba dudda akwai mutane a shagon sunacin abinci tace “bari nai salla naje nayi” bata jira amsanta ba tawuce ciki chan bayan gidan shagon bayi taje tacire kayan jikinta tafito da dogon riga na abayan dake jakanta tana neman gyalen ta tuna tabawa mutumin nan tsayawa tayi chak sai kawai taja gajeren tsakiya saurin datake tazo nan yasa ta manta bata amsaba, karamin farin hijabin tasaka ta dauro alwala tafito tasami waje tai salla sannan ta cire hijabin tasa kan igiya fari ne batason ruwan wanke wanke ko mai ya bata mata taje gaban makwarara, ga wanke wanke zaka dauka na gidan biki ne ga manya manyan tukunyan abinci, omo ta dauka ta tara ruwa abaho dukta kawo sannan ta dauki wayanta kirar vivo duk taci screen tasaka earpiece ta danna waka ta soke wayan aljihun dogon rigan tashigayin wanke wanken da sauri sauri dan tanada kuzari sosai batada kasala ko son jiki.
Wata yar budurwa ce tazo wajen ganinta tana wanke wanke tana waka kasa kasa like zero worries dinnan yasa ta harareta tajuya tafito tadawo cikin shagon tazo gaban mahaifiyarta dahar lokacin take kirga kudi tace “wai Mama Yar gidan HIV dinchan kikesa take mana wanke wanke har yanzu banace ki sallameta ba gashi gashi abinda ake cewa ita da Mamanta sunada shi” batare da maman ta kalletaba tace “koyar gidan kanjamau ce ba HIV ba ina ruwana ko kinada wanda zaki samo dazatamin wanke wanken nan ta share ko’ina har zuwa katon shagon nan akan dubu biyu kullum aduk fadin garin kanon nan?” Baki yarinyar tabude zatai magana Maman Miwa tace “kinga ki kyaleni fa, nagadai nace kiyi aikin nan bayi zakiyi ba” dasauri yarinyar tace “Mama ni kyamanta nakeji wlh, sunada HIV tana mana wanke wanke” dasauri Maman Miwa tace “wai sau nawa zan gayamiki Maman ta kedashi ba itaba yarinyar datake karatun likita, to koma tanadashi me ruwana nagadai ciwon nan ajini yake kuma baya kwarara acikin ruwan wanke wanke ko? Miwa dan Allah ki barni na kirga kudin nan kinatasa ina mance abinda na kirga” tsaki yarinyar tayi tawuce tafita daga shagon cikeda bacin rai.
Kafin 1hr tagama wanke wanken nan tass, tukunyoyin har bayansu ta wanke kal sai kyalli suke ta share ko’ina tashigo shagoma ta share tsaf tai mopping lokacin biyarda rabi sannan takoma baya tasa hijabinta tadauko jakanta ta goya abaya tafito tazo gaban Maman Miwa tace “nagama” kallonta Maman Miwa tayi tace “ohh kudinki ko”? Gyadamata kai tayi, kudin hannunta Maman Miwa tashiga kirgawa taciro 10k tabata tace “gashi na litinin zuwa yau juma’a” murmushi tayi for the first time dan gaskiya she hardly smile kaganta tana murmushi ko dariya to sai in tana tareda Mamanta, takirga kudin tass dubu goma chip chip tace “nagode Allah yabiyaki” tajuya tawuce kallo Maman Miwa tabita dashi ance duk muguntan ka kaji an maka wani addu’an saikaji ranka ya sosu harta fita waje Maman Miwa tace “Rasheeda!” Dasauri yarinyar tajuyo jin an kirata, komawa cikin shagon tayi tace “na’am gani” kallon sales girl dinta Maman Miwa tayi tace “samata shinkafa da tuwo a takeaway takaima Mamanta” wani kalan murmushi tayi dayasa wani hot dimples suka lotsa a kumatunta Ya Allah! She looks damn beautiful dasauri tace “nagode sosai, nagode nagode” Maman Miwa sai kallonta take dan wlh today is the first time in almost 3months data fara musu aiki take ganinta tana murmushi, yarinyar kam badai kyauba, ta tabbata badan cutan su ba da tuni wani babban Alhaji ya aure ta, kawomata abincin akai a leda ta amsa wannan karan saida ta duka tace “nagode sosai Maman Miwa” murmushi Maman Miwa tamata tace “sai Allah yakaimu gobe” gyadamata kai tayi tafice Maman Miwa tabita da kallo wani zubin she wants to be wicked amman kuma indai kai ba shaidan bane u can’t be wicked to this girl cus zata maka aiki tsakani ga Allah dabazaka taba ganin abinda zakai complain akai ba, wanke wanke take maka tsaf, tai shara tai moping kaga ko ina na kyalli, banda haka daidai da tsinke bata taba sata a shagon ba wlh ko kwayar magi bai taba bataba dudda ko basudashi, kowa ya tsaneta kowa kyaranta yake sabida Mamanta but if u look at it ciwo nakan kowa, zata gudu tabar mahaifiyarta ne sabida tabada HIV? No, ba HIV ba ko HIVVV uwarta kedashi uwarta ce, dudda ma taji labari ance mai kudi mahaifiyarta ta aura but taje tai fasikanci tasamo HIV yakorota yace cikin ma ba nasa bane, hmmm tasauke ijiyan zuciya tace “Allah ya kyauta dai”.


Tafiyan datayi zaiyi nisan tafiyan inda zakaje kabiya 200 ko 300 kan adaidaita sahu amman akafa tai tafiyan nan tana shiga layinsu ta tsaya gaban wani chemist ta kirga 6500 tabashi tace “ga kudin maganin nagode” karba yayi yace “an dawo daga aikin Rashy” gyadamai kai tayi batace komiba ya karbi kudin yana kokarin kirgawa daidai ta juyo zata fito wasu maza guda biyu na zuwa wajen daya daga cikinsu yakalli mai shagon yace “kai Bala nagaya maka idan kana bari yarinyar nan na shigowa shagon ka bazaka taba yin ciniki ba ni nama fasa sayan abinda nazo saya mtswww yawa kake wlh gaye” yajuya harya fara tafiya Rasheeda tace “ko dabba yafi jahilin namiji mara ilimi daraja tirr, adaije makaranta akaro ilimi katon banza” chak saurayin ya tsaya saikuma ya juyo yanuna kanshi yana kallonta kur itama Rashida ke kallonshi yace “dani kike”? Dasauri Mai chemist din Bala yazagayo yana daga marfin kanta yafito yace “badakai takeba Rashida tafi gida kudin sun cika nagode” wani kalan kallo tama mai chemist din tace “akanme zakace badashi nakeba Bala? Inba dashi nakeba waye yamaka kama da jahili awajen nan”? Wani tahowa gayen yayi azuciye zai daketa yace “zan sumar dake wlh ke” dasauri Bala yatareshi yace “me haka kai Sani dukan mace zakayi”? Wani kalan dariyan daru Rasheeda tayi tasauke jakanta dake goye abayanta ta ijiye ledan abincin hannunta duka akasa tanuna kanta tace “nizaka daka?” Tasake dariyan keta tace “billahillazi yauka tabani saidai uwarka ta haifo wani zan gwada maka ni dakake gani kaman maza dari ce anan, try me I will make sure namaka abinda baxaka so ka karabin hanyan danake bi ba” tai maganan azuciye cike da fushi da masifa da rashin tsoro, dasauri Bala mai chemist yakalli abokin Sani yace “please rikeshi ku tafi dan Allah Kamal” kamashi abokin yayi yace “muje Bros shareta pls ba riba a fada da mace” Rasheeda tace “kasan Jahili baida ilimin sanin hakan wannan dahar yanzu ake raba shayin safe dashi agida” haba wani kalan fizge kanshi yayi yakawo mata duka da duka karfinshi kaucewa Rashida tayi da sauri yasami bango batai wata wataba ta daga kujeran dake wajen na zaman mutum plastic chair ne ta rapkamai a fuska kafan kujeran ya yakushi bakinshi haba bakinshi sai jini ganin jini abakinshi yayo kururuwa zaiyo kanta da sauri abokinshi da Bala mai chemist suka rikeshi, itama Rasheeda cikeda fitina ba tsoro azuciye tace “ku sakeshi yazo bakaga komiba duk bakin dazai kokarin bullying dina wlh saina fasa bakin, kai kayi kadan kahanani sakewa agarin nan sabida ka ganka namiji, akan wani dalili zaku hanani sakat bazan iya zuwa nasai abubu? Shaguna nawa nadena zuwa na layin nan? Wannan danake zuwa yanzu shima kuce ban isaba sabida wani dalilin ku na banza da wofi, cuta nakan kowa, babu wanda yasan karshen shi, yes Mamana nada HIV and so what? Kubi duniya a sannu kai kanka bakafi karfin kasami cutan ba dakiki kawai mahaukaci, katon banza wanda ake gutsurama buredi agidansu har yau akasa dashi da kannenshi sabida baida zuciyan nema, kar Allah yasa ka kara zuwa shagon siyan abu, jahili kawai” cika shagon akayi da mutane sabida yanda Rashida ke zubamai zagi shikuma yana kokawa dasu Bala asakeshi ya daketa ganin yanda ta fasamai baki, cikin taron mutanen wani dan tsoho ya leko ganinta sai kawai ya shigo cikin shagon yakai hannu ya karbe kujeran ya ijiye gaisheshi mutanen wajen sukahau yi. “Barka da yamma Baba Liman” cikeda hikima na manya ya dubi Sani yace “ayakuri Sani, kekuma wuce mutafi” hannunta yakama yace “wuce mutafi” batai musu ba akumbure cikeda taurin kai tace “ni jakata” sakinta yayi yana kallonta taduka tadauki jakanta ta goya abaya da ledan abincin tarike a hannu tana nishi kaman kirjinta zai fashe sabida fushi saikuma ta dago azuciye dan tanada naci wani zubin kaman mayya, takalli uban mazan dake wajen duk ana kallonta tace “Baba Liman kagayama yan anguwan nan su kiyayeni nida mahaifiyata, bamu shiga gidan kowaba munyi sata, Mama harni baya shiga gidajensu sabida yanda kowa ya kyamace mu, bamu rokesu kudi ba, banzo nacema kowa yabani kaza zankai mahaifiyata asibiti ba dan haka su fita daga rayuwata dana mahaifiyata Baba, sufita na gayamusu, I am enough for Mamana! ni kadai zan iya kula da ita, nayi girma kuma Alhamdulillah inada karfin yimata komi kowa yafita harkana, ban nemi fadan kowaba ban shiga hurumin kowaba dan haka duk wanda yashigo tawa koshi waye wlh sai inda karfina yakare kagaya musu Baba Liman” tayi maganan with a sound warning, ahankali tsohon yace “ya isa!” wucewa tayi fuuuuu tafice daga shagon kowa na wajen jikinshi yayi sanyi wani dakeda shago kusada na chemist yakalli yaron yace “kudaina abinda kukeyi mutanen nan ba akanku suke zaune ba, wlh Allah zai iya saka musu, shidai cuta nakan kowa, yau dauka fasikanci matan tayi tasamu Allah masani amman ina mai tabbatar muku, gulma, keta, rashin mutunci da sa’ido da menene menene kukema matan da yarta kadai ya kore zunubansu” anatse Baba Liman yace “muji tsoron Allah, mun kyamaci mutanen nan shi kadai ya isa wlh kudena takura musu kar Allah yakamaku, kar Allah yakamaku” yawuce shima yatafi, dasauri Bala yace “nima kada ka kara zuwan mini shagona kaje wani chemist din” tsaki Sani yayi yace “ka dinga shiganmata ko zaka mutu iyayyenka dai damuka sani bazasu taba barinka auren tijararriyan yarinyar me kanjamau dinchan ba” yayi maganan yana ficewa dağa shagon abokinsa na binsa.


Gidansu na wajajen karshen layin, wani dan karamin gidane sosai ciki da falo daya ne sai bayi ba kitchen a tsakar gidan suke girki, ko’ina kal kal agidan, maida kofan tayi tarufe tasa sakata tasauke ijiyan zuciya sannan tai murmushi dan bataso Mama tagane ranta yabaci daganan zaure tai shouting “Mamaaaaa, Mama nadawo” tai ciki da gudu labule ta daga Maman na zaune kan dadduma kaganta kamansu daya sak da Rasheeda itama tanada haske but ba kaman Rasheeda ba, batada kiba ko kadan ta rame ta bushe sosai, duka duka bazata wuce 40 ba but she looks kaman wacce ta tsufa, tana zaune kan dadduma tanajan charbi, ijiye kayan hannunta Rasheeda tayi saikuma tai tagumi tana leka fuskan Mama tace “Mama kiyi sauri kigama kimin sannu da zuwa niii” tafadi a shagwabe, hannu Ammi tasa ta shafe addu’an datakeyi sannan tajuyo kawai saita kama kunnenta ta saman hijabin jikinta tace “dan kaniyanki ba alwala yakamata kiyo ba kizo kiyi salla ba” dariya sosai tayi tana yarfe hannu tace “wayyooo kunnina Mama zai cire” sakin kunnin Mama tayi tana murmushi looking so happy tace “imaza to jekiyo alwala kafin lokacin magrib yafice baki salla ba” tashi tayi tafito tsakar gida alwala tayi tadawo tai salla kusada Mama sannan tadauki jakanta tabude taciro kudin tasa a hannun Mama tace “Maman Miwa tabiyani, hotel din nan gobe suma zasu biyani kuma manager tace nakawo zanen tagani idan na iya sosai zasu saya” karban kudin Mama tayi tana kallo tana murmushi Rashida tashiga fito da abincin tace “nabiya nabawa Abdul kudinshi Mama ga abinci Maman Miwa tace nakawo miki” bubbude komi tayi ta tashi tafita dasauri tadauko ruwa a bowl tadawo tazauna takama hannun Ammi tasa aruwan tace “wanke hannun muci” wanke hannunta Ammi tayi ta ijiye kudin agefe ta gutsuro

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads