Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 68622 words

Chapter 9 - Sanyi Da Zafi By Maman Shakur.txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

1133

Ads at the middle of Article

Riyad? Me ka nema wajen Haleematu karasa? Dan kunnen waye tell me now”? Tunda yake baitaba jin Mom ta batamai rai irin na yau ba kanshi ya nuna yanama Mom wani irin kallo yace “Mom I’m your Son, kin sanni sama da kowa a duniyan nan, Mom yanzu akazo aka cemiki ina neman mata bazaki iya shedana ba? Do I look like ina neman Mata? Ni?” Harga Allah tun Riyad na yaro bai taso dason Mata ba, ko kallonsu bayayi hasalima kunya suke bashi amman dai cikeda kafiya dason nunama Haleema she own her Son tace “how do you want me to trust me bayan matarka taga dan kunne akayan dakasa jiya and kadawo very late eh? Look at the way the poor thing is crying” tanuna Haleematu dake wani irin mummunan kuka tace “ko kadan banso kayi hurting yarinyar nan cus she’s a good gurl, tadaukeni mahaifiyarta, Babanta yataka rawan gani sosai wajen zamanka sarki, he’s the one blocking all kulle kulle da akeyi yanzu daka zama sarki” “did I ask him to do anything for me?” Riyad yayi maganan da karfi da saida Mom tabude idanunta cikeda mamaki ta kalleshi, yau Riyad ya daga mata murya haka? Agaban matarshi, cikeda mamaki tace “Nikake dayama Murya Riyad?” Cikin fushi sosai yace “Mom abinda kikemin is totally wrong, sabida Haleema tace inabin mata saikizo ki yarda da maganan ta kinamin fada agabanta baki san danki ba? You’re not allowing me to be the man in my marriage, nagaji I can’t continue with this marriage because of Babanta kikasa ya nemamin sarki dagayau…….” da sauri Haleematu ta taso tana kuka sosai afirgice kawai ta zube agabanshi tarike kafanshi tace “dan Allah kayakuri wlh nasan bakabin mata bansan menakeyi ba danaga dan kunnen saisa nakira Mom” fizge kafanshi yayi yakalli Mom yace “dagayau tell her bata babu this side I forbid her from coming to my side, duk sanda nake bukatanta zan nemeta!” Rushewa da kuka sosai Haleematou tayi takama kafan Mom tace “Mom do something, dan Allah kimai magana ya yakuri, bazan karaba”
Yakalli yanda Haleema ke rokon Mom ya cije baki ya kalli Mom din dake kallonshi mamaki yagama kasheta yace “and for your question Mom” sai kawai yadaga mata kafanshi yanuna mata tafin kafan inda dan kunnen ya shiga yace “nataka dan kunnen nan akasa ya shigan min kafa, na cire zan yarda ganin ina cikin premises kar wani yaje yataka yasa nasa a pocket with the hope nafito i will trash it but I forgot” ya maida kafanshi ya ijiye yace “I don’t want the sarauta ki nemo wani kibashi, I need a break” yana maganan yabi ta gefensu yawuce dagashi sai jallabiyan jikinshi yanda ranshi yabaci ko waya bai daukaba Mom tajuya tabiyoshi dasauri ganin ahaka zai fita tace “Riyad, Riyad” hannu yasa yabude kofa azuciye yafito key motar compound nashi na wajen Munir hakan yasa yayi gate yafice fadawa zasumai kirari ya buga musu tsawa “leave me alone!” Kawai yawuce fuuuuuuuu shi kadai yana tafiya a bala’in zuciye kawai yawuce side din su Munir bude kofa yayi azuciye key daya hango akan table yawuce kaman zaki yadauka daidai Ammi na lekowa daga kitchen ganin shi yadau key dinta ranshi abace yasa tai shiru daidai yabude kofa yafice parking space nasu yaje yana danna key wani jeep yayi kara motar Ammi ce direct yawuce yabude ya shiga yanda ya danna horn zakasan ba lafiya aka budemai key yawuce yafita.




Kusan yaune rana na farko da Mom take ganin serious fushin Riyad haka, and for him to provoke like this that means abinda yafadi gaskiya ne babu matan dayake nema, hankalinta yatashi sosai, wayanta dake hannunta ta daga zata kirashi saitaga wayanshi akan gado kawai cike da takaici takalli Haleema dake kuka tace “you are not sure of something akan wani dalili da rashin hankali zaki tafka shirmen nan eh Halimatu? Jibi abinda kika jawo yanzu? Bakisan idan mai hakuri yayi fushi yafi zama worst ba? Jibi yanda yafita ko wanka baiyiba bai dauki wayanshi ba tsabagen bacinrai, sabida kinga dan kunne in this pocket mesa zaki assuming mata yakebi”? Cikin kuka Halimatu tace “Mami kishi ne yarufeni I can’t share mijina with anybody wlh, kiyakuri Mom kiyafemin dan Allah” dan tsukin takaici Mom tayi tace “naji is not your fault nima daban biyemiki ba nasan waye Riyad, yana tashen samartaka ma beyi neman mata ba sai yanzu, tashi kitafi side naki zansa azo agyara dakinshi lemme handle the situation” Kama hannun Mom Haleema tayi tace “Mom kinsan baya tsallake maganan ki, please kice yayi hakuri karyayi fushi dani koya chanzamin fuska” “naji tafi” Alkyabban tadauko tasaka tawuce tafita daga side din, Mom itama tafito ta tafi sauro da idanu takira babban bafaden gate din yataho da sauri ya zube yace “an gaida Mai Babban daki matan da darajanta yakai…..” Mom bata bari ya karasa maganan ba cikin whispering yace “inada aiki for you Sarki baida lafiya bazai iya fitowa ba shine abinda zaka sanar kaida yaranka bansan kowa yasan Sarki bayanan, zakaga babban sakon tukuici kai haka” Gyadamata Kai yayi yace “angama me Babban daki” juyawa Mom tayi takoma ciki takira Dr su kaman da gaske, kazo gida by 10 duba Riyad”.
**






1 dot tagama da hospital wanda a outpatient department group nasu yake tareda wani consultant na pediatrics, she’s happy sosai yanda itada Bilal da crew dinsa na yanmata basa group daya, salla tawuce tafarayi a masallaci sannan ta linke lab coat nata tasa a bagpack tawuce tafito daga mosque din tagoya jakan abaya tasa takalmi tafito Keke napep ta tare zuwa hotel, sauka tayi tabiyashi ta shiga ciki ko kallon receptionist wajen batayiba as usual changing room tawuce tashiga cire kayan jikinta tayi ta saka dark blue dogon wandon da light blue shirt mai botur tundaga kasan rigan har sama wajajen wuya, farin fatan jikinta ya haska kayan sosai kaman dan ita akai uniform din, clean baby hijab nata farı ta dauka ta saka wanda yarufe mata kirji sannan tasa takalminta, fitowa tayi zuwa office din Madam tai knocking akace mata ta shigo, shiga tayi tace “good afternoon” “Afternoon Rashida oya ga card din jeki goge office din maza maza, ki dauko kayan gyaran office din a store” karban katin tayi tace “okay” fitowa tayi tawuce store tahada duka abubuwan dazatai amfani dashi sannan tawuce elevator zuwa 5th floor tayi corridor office din, manna katin tayi kofan yayi kara sannan ta tura kofan ahankali hakanan kawai taji gabanta yafadi ga office din yayi mahaukacin sanyi kaman kankara AC a kunne, ahankali ta shiga tareda maida kofan tarufe cikin yar muryanta tace “wayyoo sanyi” dasauri tawuce wajen kashe AC ta kashe tanabin office din da kallo alamun an shigo dama jiya ance Oga yazo lokacin da zata tafi saisa ya shigo office dinshi kenan, a aljihunta tasa hannu ta zaro yar wayanta ta makala earpiece din a kunnenta ta danna wakan Araina Grande mai suna Into You, sannan takoma wajen kofa tadauko kayan ayyukanta tawuce bayi ta tara ruwa tafara bin wakan tafito tadauki handglove black na aiki tazura a hannu tadauki brush din share kura tafara aikinta tana waka……










Ko manager shi batasan yana nan ba babu wanda yasani sabida yanda yazo da jallabiya he looks like normal guest yawuce direct elevator, tunda yazo yake kwance dazun nan ne ma ya iya tashi yayi zuhur yakoma ya kwanta though ba bacci yakeba but ya lumshe idanu kawai having moment of peace, tunda aka bude kofan office din aka shigo yaji, sai chan kuma yaji murya mai bala’in zaki tace wayyoo sanyi, saikuma ga same muryan tafara waka tana aikace aikace dake making sound, shi kadai yace “is she some sort of DJ ko wata Artist?” Cus muryanta dadi bata missing ko harafi daya, kaman tana performing a stage, chan kuma kawai saiya tashi zaune sabida ta kunna vacuum cleaner bayajin muryan nata da kyau kaman da, karan vacuum cleaner yafi muryanta kara, ahankali yataso yataka zuwa wajen kofan hannunshi yakai ahankali zai kama handle na kofan yabude kofan sai kawai yaji yafasa cus baimason aganshi amman kuma saiya tsaya chak awajen yanajin the way she’s singing din cus takashe machine din yanzu tana bin wakan Into your arms na Witty Lowry, God! Her voice is captivating kawai yaji yakasa matsawa.






Daukan bucket na mop din tayi a hannu tarike vacuum cleaner shima a dayan hannun ta tako zuwa gaban dakin sabida tagama da office sai uwardakan before wanke bayuka, juyar da fusknata tayi tana ijiye vacuum cleaner akasa still holding on to the bucket na mop takai free hand din tabude kofan ahankali fuskanta na kallon side din tana rera waka tadawo da hannun tana kokarin daukan vacuum cleaner back danta shigo tunda tabude kofan…






Tunda tabude kofan yayi setting eyes nashi chak akanta yana kallonta tundaga kan pink crocs din dake kafanta dayay finding nasu so funny, dogon dark blue wandonta dabai kamata ba at all kusan ma yaso yamata yawa ya kalla, zuwa navy blue rigan dashi ma bai kamata ba zuwa farin hijab din jikinta that looks extremely neat da side na face nata da he could see sajenta da dan gashinta baki sidik daya leko, daidai tadaga vacuum cleaner ta juyo da kanta kawai taga dogon farin mutum da farin jallabiya ajikinshi ya tsaya chak kaman gunki yazuba hannu a aljihun jallabiyan yana kallonta batada tsoro but saida ta tsorata tayi baya da sauri ganin namiji hakan yasa cord (wayan) vacuum cleaner ya kwasheta jikake timmm tafadi akasa ruwa mopping din hannunta ya kware mata daga ciki zuwa wando, zaro ido tayi atsorace tace “wayyoo Allah na” tai maza maza ta tashi tama rasa mezatayi arude tace “I am sorry” ganin kaman ba ghost bane maybe shine me hotel din takai hannu tana kakkabe jikinta da cinyanta da sauri chan ta lura da aljihuta ajike dasauri tace “Innalillahi wayana” hannu tasa a aljihun taciro wayanta ta cisge earpiece din tashiga tattaba wayan baya haske tace “innalillahi Innalillahi” bude wayan tayi da sauri taciro battery ta huhure wayan sannan tawuce table dagudu ta ijiye wayan awajen danya bushe sannan tajuyo tama kasa kallonshi taduka tana daukan mop tace “sorry i will clean everything yanzu” chak yake kallonta dan yana ganin full fuskanta ya ganeta the girl from the airport! The feisty gurl! Yarinyar daya dade yana nema to reward her for saving his life….


GOGAN NAMU BATA GANESHI BA? KODAI IDONANE💃🤨
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: 💫 SANYI DA ZAFI 💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE 1️⃣2️⃣
Bucket na moping din tadauka da gudu tawuce bathroom na office din ta tara wani ruwa ta taho da sauri jikinta duk rawa yake zata fara mopping ruwan kunfan kasan jikinta duk yana tsiyaya kaman daga sama taji sassanyar muryanshi yace “stop!” Dasauri tadago manyan fararen idanunta ta kalleshi, hada ido tasakeyi dashi for the second time da sauri ta dauke kai aranta tace “sai shegen kallon mata mtsww” fitowa daga dakin yayi ahankali, cikeda tsantsan kulawa yace “step aside” dasauri ta matsa gefe ga mamakinta sai kawai taga ya tsugunna yadauki bucket na mop din ya matsar gefe da vacuum cleaner, yashiga nannade carpet din na tsakiyan office din yadaga yadauka yawuce wajen kofa yabude yafitar dashi ya ijiye bakin kofan nan yashigo yasameta tana kokari fara mopping wajen cikin kwantacciyan murya yace “go and change” dan kallon daga kasan riganta har zuwa crocs na kafanta tayi dake tsiyaya tace “karka damu I can do it banda wani uniform, zai bushe ai” yanda take kallon jikinta tana maganan yake kallo with her voice dake piercing kunnuwa sabida dadinsu, calmly yace “go take them off kisa kayan gida” kawai dan tasan office din mai hotel dinnan ne, sannan shita gani cikin offive din so dole tai assuming shine mai hotel din banda haka data gayamai me ruwanshi da yanda zatai aikinta yabarta tayi abinta tagama mana ha’a, sai gwadamata yanda zatayi yake, sai kawai tawuce kofa batare datace komiba tana zare handglove din, tabude kofa tafita yabita da kallo kafin kawai yazaga yazauna kan kujeranshi na office yayi shiru.






Changing room dinsu tawuce ta chanza kayan tasaka doguwan rigan atampanta brown ne da milk just straight gown babu wani ado ajiki, dan kwalin kayan ta daura aka sannan ta zari gyalenta brown ta yafa daya kara haskata hasken fatanta yayi bau aciki, ta kwashi kayan bayinsu na staff ta shiga ta dauraye kayan ta wanke cinyanta da kafanta da takalmin tama wanke fuskanta kawai gaba daya hakan yasa tai wani haske mai kyau dinnan na bayan ka wanke fuska, tawuce baya ta shanya kayan sannan tafito tana tafiya da sauri sauri sabida tasamu tai sauran ayyukanta tabar office dinshi, tashiga elevator zuwa 5th floor tawuce office din kofan office din ta bude ahankali tashigo tunda ta bude office din ya kafamata ido, the first time daya ganta uniform ne jikinta, yauma haka yanzu ne yafara ganinta da kayan gida, kasa dauke idanunshi yayi akanta, ta taho direct cikin office din batare data kalli wajen dayake bama, zubamata idanu yayi yana kara tantancewa itace dai wannan mara kunyan ta airport, bai cika manta face ba idan yasan mutum, hade fuska tayi batacemai komiba dan jikinta yabata kallonta ake, tadauki moping stick din tafara moping wajen ahankali tana gamawa tadan juyo ta kalleshi karaf suka dake hada ido dauke kai tayi tace “zan iya shiga dakin na gyara”? “Yes” ya amsa calmly hakan yasa kwai ta shiga ta sharo tai arranging bed din dataga ba’a gyare ba, ta wanke bathroom din, kusan 5min tayi sannan tafito tawuce bayin nan office ta gyara shi in 3min sannan tafito tai arranging abubuwan datai amfani dasu tafita dasu waje sannan tadawo tazo gaban table dinshi tasa hannunta tana kwasan wayanta na wajen yanabin white long fingers dinta da kallo that looks so feminine, ahankali yace “wat is your name?” Batare data kalleshi ba tace “Rashida Almustapha” tana maganan tajuya dasauri zata wuce kaman daga sama yace “is your back hurting you naga kin fadi tabaya”? “No it’s not” tabashi amsa atakaice tacigaba da tafiya da sauri bataso yayi wani maganan kuma, hartakai kofa tasa hannu zata bude yace “Rasheedahhh!” Wlh batasan meya faru ba hakanan gabanta yafadi chak ta tsaya takasa motsi sabida yanda yakira sunanta, kawai she felt something strange in her dayasa dasauri tajuyo ta kalleshi sake hada ido tayi dashi saikuma ta dauke kai tace “na’am” kusan 30secs yayi shiru saichan ahankali yace “Thank You” Da sauri ta kalleshi zatace thank you for wat saikuma ta tuna maybe na gyaran ne hakan yasa ta gyadamai kai kawai tama kasa magana sabida yanda heart nata yafara racing tajuya tafito dasauri ta kwashi komi tawuce kasa ta maida komi store tawuce taje dakunan dazata chanza duvet nasu takai washing machine takai sannan tahau gyara Allah yasota bata hadu da Madam ba balle ta tambayeta ya akayi tasa kayan gida ba.






Wuraren 6 tafito daga hotel din sai fama take da wayanta dayaki kunnuwa sai cire battery tana maidawa take sabida ya kunnu yaki kunnuwa, ga jakanta goye abayanta. “Hi Rashy” Aisha receptionist dake night zuwanta kenan tai waving nata tana murmushi awkwardly tadaga hannunta saikuma ta maida ta gyada mata kai kawai tawuce tafito waje tana hure huren waya, Munir da Riyad na tsaye awaje wannan karan ya chanza kaya zuwa jumper na milk yadi suna magan kaman daga sama ya hangota tafito tana hura wayanta, yanda hankalinshi da attention nashi yatafi wajenta saida Munir yajuya dasauri dan yaga meyake kallo haka ganin wacce yake kallo wacce kallo daya yamata she looks like worker nasu not guest yasa yace “who is she?” Batare daya dauke kanshi daga kallonta ba yace “my savior” dasauri Munir yadauke kanshi daga kallonta ya kalleshi dasauri yace “kaman ya your savior?” Yana kallonta yace “the girl that saved me from those goons a airport” dasauri Munir yajuya ya kalleta yace “wow the clearner damuka dade muna nema wat a small world ashe anan hotel namu take aiki, but did you tell her”? Girgixamai kai yayi daidai tasha kwanan layin yadauke kanshi yace “No bangayamata” Munir yace “why?” mota yashiga yace “bata ganeni ba” tada motan Munir yayi yace “ai da saika gayamata, How will you reward her yanzu?” Kai tsaye yace “I will ask her kome takeso arayuwa i will grant her any wish take da shi she’s part of the reason I’m alive today” murmushi Munir yayi yace “wat got you so angry today?” Yatsine fuska yayi yace “I don’t wanna talk about it” ahankali Munir yace “to mutafi gida? Mom tasa an sanar bakada lafiya just to manage situation din harda kiran Dr, tace na tabbatar mun dawo gida tare” hannunshi yasa yasauke glass na window ya lumshe idanu bai sake cewa komi ba, ganin baison magana yasa yace “azumi saura 7days fa bakai approving fund na kayan abincin daza’a rabama al umma da ma’aikatan ka ba” dan ijiyan zuciya yayi yace “i forgot bani file din da pen lemme sign” ahankali Munir yace “bari mukai i will give u yana file dake back seat.
JOIN GROUP DANAKE POSTING


https://chat.whatsapp.com/Ckm5Bo7CcqR1NYkgT0HEvR
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: 💫 SANYI DA ZAFI 💫






✍🏻M SHAKUR




EPISODE 1️⃣3️⃣


Gida tashiga around magrib agurguje tai alwala tashigo ciki Mama nakan dadduma hakan yasa ta tsaya kusada ita ta kabbatar sallan.


Tana idarwa cikeda damuwa tace “Mama ruwa yashiga wayana taki aiki wlh” tai maganan tana jawo jakanta taciro wayan cikeda damuwa itama Mama tace “garin yaya meya sameta?” Cikin damuwa tana kara huhhure wayan tace “faduwa nayi ruwa ya kwaromin shine ruwan yataba har wayan” dasauri Mama tasa hannu ta karbi wayan itama tana huhhura duk wani huji na wayan ta maida battery din kozata kunnu amman bata kunnu ba hakan yasa ta tashi tawuce chan wajen yan kayan abincinsu tabude ledan shinkafa tasa wayan ta zuba shinkafa akai tace “bari mugani kozata kunnu idan bata kunnu ba saina tattara kudin dake wajena kije ki sayo wata wayan dashi, kina bukatan waya kodan school, Allah kiyaye bakiji ciwo bako”? Gyadama Mama kai tayi tace “banji ciwo ba” Mama

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads