Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 24174 words

Chapter 2 - Hatsabibiya Jiddah hausa novels .txt

Ads the beginning of article before Image

JIDDA   

02 Jun 2024

344

Ads at the middle of Article

kitafi gida duk sanda mijinki ya dawo kindawo kuyi sulhu tinda de aure be mutu ba.


Salma cikin kuka Tace banda kowa sai kakata, itama kuma ta rasu satin chan yanzu bansan yah zanyi ba."


Salis ya numfasa, yace "haka de zakiyi hakuri kisamu wani gu kizauna kafin yadawo .


Salma de kuka take sosai na dana sanin zuwanta gidan Saude take, da bata zo ba da haka bata faru ba.😰


futa tayi dan babu yadda ta iya dole taje ta roki alfarma gun Mai Gari taxauna gidansa kafin mujinta yadawo .


Saude kuwa aranta take kiyasta abunda zatawa jidderh inde ta dawo gida.


Mlm Kabiru kuwa babu bakin magana illar juyawa da yayi ya nufi kofar gida.


Salis ne yashiga cikin d'akinsu ya samu oga da yayi shiru yanajin duk abunda ke faruwa cikin gidan


Yace "Oga yarinyar nan ba mahaukaciya bace, hatsabibiya ce wlh dan tafi bom hatsari nafara tsoron zaman gidan.


Kamal Yace "ni abun ya dauremin kai ayya bata da aljanu kuwa? dan abu nata mutum baze iya ba."


Salis ne yayi murmushi yace "wlh mutum ce, sai de hatsarinta yafi gashin kanta yawa.


Kamal Yace "Allah ya kyauta amma gaskiya Ubanta beyi sa'ar yarinya ba, da a'lama ma tsoronta yake."


Salis ne ya saka dariya Yace dole aji tsoranta, tinda ba kasan mai zata kulla maka ba.




Jidderh kuwa tana ganin futowar Mama Tabawa tabi ta baya gida ta buya dan batasan ya suka kaya ba .


Sai da ta shiga gida tukum Jidderh ta futo tashiga gida e'tama


Saude na zaune tana jiran Jidderh dan taci alwashin yi mata dokan mutuwa ya'u,


to Jidderh ma akwai abu A ranta dan ganin Saude ya sata sauya fuska d'aki ta shiga ta dauko sabuwar wuka tana kyali, tayi murmushi tace "Saude gidan nan ko na ubanki ne sai kinfuta ya'u tinda baki tafi ba to zakiga tsiya yanzu ."


Bata gama tunani ba Saude ta shigo d'akin da bulalarta hannu ta dokan Jidderh,


Ganin wuka hannu Jidderh yasata tsorata amma bata nunawa jidderh ba,


bulalar ta d'aga zata zuba mata jidderh kuwa ta dauki wukar ta yanka hannunta da kanta Ihu ta saka mai furgitarwa wanda kusan yan layin duk sunji ihun,

A zabure Saude taja baya ta fasa doka, Jidderh kuwa wullawa Saude wukar tayi ta zauna gun tana kur ma Ihu ga kuma jini yana ta zuba ahannun nata ,


Saude kuwa ta rike wuka tana kallan Jidderh kafin tayi wani abu tini gidan yacika da jama'a


Salis kuwa da Mlm Kabiru har bigewa suke jin ihun yana tashi na futar hankali,


Ganin Jidderh kwance cikin jini ga kuma Saude da wuka ahannunta hakan yadaure musu kai sosai.


mutane suka fara shigowa d'akin dan gani da e'donsu,


har wannan lokacin kuwa Saude na rike da wuka A hannunta ga kuma Jidderh rike da hannunta yana jini bata dena Ihu ba.


Salati kowa yafara agun ana tsinewa Saude ta yanka yar mujinta sabida kishi 😱


Mutane kowa da abunda yake fadi kan Saude .


Saude kuwa bata cewa komai dan gani take kamar mafarki ne abun


Salis ne ya daukota Yace "muje Baba mukaita asibiti.


Ni bazani asibiti ba, bina zatayi ta sheni cewa tayi sai takashe Baba na ni kuma yanzu shine tazo ta fara da kaina, kubarni takashe ni da takashe uba na da ransa."🤔


Mlm Kabiru Yace Saude ni zaki kashe? har zaki iya daukar wuka kiyanka Jidderh saura ni kenan?


bBazan dauki haka ba kije Gidanku na ........🤬


*jidderh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️




*HATSABIBIYA JIDDERH*👯🏼‍♀️


*na jidderh*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...




🅿️4️⃣




.......Salis Yace "dan girman Allah Haba kabari tukum muje mu dawo, sai musam mafuta.

Jidderh Tace "wlh Baba wannan bakon munafikine, Ina Saude ta samu sabuwar wuka? inba shi ya bata ba. bak'insu d'aya shiyaba ta wukar bayan ka tafi sallah."
takarshe maganar cikin Ihu


Salis be san sanda ya saki Jidderh daga rikon da ya mata ba, duk jikinsa rawa yake lalle yarinyar nan tacika dalibar shedan, da akwai sama da shed'en ma to da tabbs zece malamar shed'en ce 😃


Mlm Kabiru yayi shiru na wani lokaci Yace "haka ne kuma mgnrki, dan bamu da sabuwar wuka A gidan nan, amma zanyi binkice nagani waye ya bawa Saude wukar nan, inkuwa da hannunka ciki to koto ce zata ra bamu da ku.
Ya kama hannu Jidderh Yace "mutafi chamis hannun yadena jini .


Mutane kuwa kowa zagin Saude yake yana tsine mata albarka.


Salis kuwa kasa motsi yayi ya kuma kasa tunanin komai dan yarinyar ta gama dashi sosai .


Amma babu komai yayi alkawarin temaka mata ko Allah yasa ta nutsu,


D'akinsu ya koma jiki duk yayi sanyi


Kamal yace "naga ya maka wlh nan ba gida ba ne, gida sai kace koto daga wannan shari'ar sai wannan, haba kawai mukama haya zefi .


Salis Yace "Gaskiya kam, kuma naga shago kofar gidan nan mu tambaya na waye mubiya kawai muzuba kayanmu ciki tinda muna da kayan abunci, amma cikin gidan nan kuwa yafi karfinmu inde zama ne."


Kamal Yace "Wai yan kewa tayi?"


Salis yace "Ni fa ban yarda da Saude ce ta yanka ta ba, kawai yarinyar nan akwai wata A kasa, ba banza take wannan abubuwan ba."


Kamal Yace "Allah ya kyauta, amma na tsani yarinyar wlh tin farkon had'uwarmu na tsaneta.


Salis ne yayi dariya Yace "lalle Jidderh ta baka wuya Oga.


Ni makaranta nakesan sata naga kamar bata zuwa makaranta.


Kamal Yace "tab, aikuwa na tausayawa malamai makarantar wlh, dan wlh yarinyar nan tafi bom illah taje makaranta kuwa sai Abunda yakaru."


Nan de su kaci gaba da tautaunawa yadda zasu bar gidan batare da Mlm Kabiru ya zargesu ba.




Bayan su Jidderh sun dawo daga chamis Mlm Kabiru yashiga gun su Kamal dan ganin hannun nasa


Salis Yace "ya hannun Jidderh kuwa Baba?


"Da sauki anmata dinkima tana cikin gida.


Yace "Allah ya bata lafiya, Amma Baba Jidderh tana zuwa makaranta kuwa? cewar Salis


Mlm Kabiru Yace "A~ a bata zuwa, da tana zuwa Allo amma yanzu ta dena zuwa .


Salis ya numfasa, Yace "To Baba da zaka yarda da munsata makaranta, na kega yafi mata wannan yawo acikin gari.

Kamal ne ya katse shi Yace "kace zaka sata makaranta ba zamu sata ba.


Mlm Kabiru Yace "Babu komai yaro na gode sosai daga zuwa aiki sai kuma wahala kala ~kala.


Salis Yace "Babu komai Baba Ai yiwa kaine, ba musan mai zata zama ba nan gaba.


Mlm Kabiru Yace "hakane ngd sosai yaro."


Nan ya shafawa kamal maganinsa ya musu sallama ya nufi gun Saude


Kamal Yace "Wai kana tunanin yarinyar nan karatu zatayi, har kake cewa zata zama wani abu? to wlh zata zama abu amma agidan mahaukata.😳


Salis Yace "haba Oga."


katseshi yayi Yace "Mubar mgnr dan natsani mgnr yarinyar wlh. cewar Kamal


Mlm Kabiru Yace "Ina Saude take? futo munafuka ai ban barki ba zan hukuntaki.


Saude futowa tayi jiki duk yayi sanyi Tace "gani.


Yace wlh duk abunda Jidderh zatayi nan gaba kar ki kuma mata mgn, balle fad'a babu ke babu ita kinjide koh.?


Tace "Naji kayi hakuri ."


Tashi kiban gu." cewar Mlm Kabiru


Duk abunda A keyi Jidderh na jinsu ta kuma yi alkawarin Saude bazata kuma sati cikin gidan ba.


Bayan kwana uku Salis duk wani shiri na makaranta ya gama dashi komai ya siya mata, yayi da Kamal ya kejin kamar ya kashe Salis dan haushi


Ya'u take mondey tin shida na safe Jidderh ta shirya take jiran Salis ya futo su tafi dan ji take kamar zata aljanna dan murna.


7:30 Salis ya futo Yace "Mutafi toh.


Sallama taje tayiwa Babanta sannan ta futo kafin ta fito ma tini Salis yashiga mota yana jiranta, tana zuwa itama tashiga cikin zumud'i zataje makaranta kuma amota za'akai ta.


Cikin minti ashiri sukazo makarantar kasancewar ta prvt ce makaranta shiyasa suka nufi office din shugaban makarantar


Sallama Salis yayi suka shiga


Amsa musu akayi daga ciki


Zama Salis yayi A kujerar da aka tanada sabida bak'i


Bayan sun gaisa ne Salis yake gabatar da abunda ya kawosu .


"Ok,


Babu matsala kajira nanda minti goma shugaban zezo yakusa k'arasowa cewar wani Mlm dake kyara takadur offincen din.


"Babu matsala." cewar Salis


Jidderh kuwa tunawa take ina tasan wannan malamin? tabbs tasan shi amma ta manta inda ta sanshi amma zata tuna ynz 🤔


Cikin minti uku ta tuna shine ya ganta suna fad'a ya rabasu taki rabuwa yace mata shed'aniya, lalle ya'u ze gane shed'aniya ce e'ta.


Wayar Salis ce tayi k'ara dauko ta yayi domin ganin mai kiran, ganin sunan dady ya sashi mikewa yafita waje domin suyi mgn cikin nutsuwa.


Ganin futar Salis yasa Jidderh cire shijab dinta ta ajeye gefe


Ganin abunda takeyi yace "kee lafiyar kuwa ?


Cikin kuka Tace wani abu ne cikin rigata dan Allah dobamin 😱


Ganin zata cire rigar yasa shi saurin k'arasawa gunta ya kama rigar da nufe zai zagewa ko abun cikin rigar yafadu kasa


turo kofar akayi wanda yasa Jidderh yin Ihu "Wayyo yamin fyade, wayyo ya kasheni. Ihu take kan gari ya gari


Shugabar makarantar ne da Salis suka shigo ganin abunda ke faruwa yasa shugaban futasa Yace Allah ya tona maka asiri daman abunda kakeyi kenan? to na ko......😰




*jidderh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️


*HATSABIBIYA JIDDERH*👯🏼‍♀️


*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


*godiya mara iyaka ga masoya wanan book din*🥰


*kunnu na min so wanda bansan taya zan nuna farin ciki ba amma ina alfahari da ku masoya duk inda kuke*


*banda kamar ku*

zeee md
mts basakkwace 😘
fulanin gilr😍
ak abubakar😾
ammin siyama 👸
shalele 🥳
maman abdullahi😗
khadija ibrahim😚
aeesha jos☺️
jamila ibrahim😘


*yasee kuna da yawan gaske amma muhadu* *pege gaba*



🅿️5️⃣




..... Yace "Na koreka, daga ya'u ka barmin makaranta ta, masu b'a tawa makarantu suna. ya fadi cikin bacin rai.


Yace "dan girman Allah kayi hakuri, wlh karya tamin ni ban mata haka da sunan fyade ba.


"Bansan jin komai futa kawai kaban gu.


Duk yadda Salis yaso k'arya tawa shugaban makarantar be yarda ba, Cewarsa ai gani yayi ba gaya masa A kayi ba.


Haka malamin yafuta yana jimamin abunda yasameshi, beda aikin komai sai wannan koyarwa da e'ta yake temakon kansa, amma yanzu gashi ankoresa beda zabi illa yadauki kaddara da tazo masa da safiyar litinin.


Salis Yace "dauki shijab dinki kisa.

cikin kar~karwa ta dauko ta saka tana share hawaye na makirci.


Shugaban makarantar Yace "kiyi hakuri kinji, nan gaba duk wanda ya kuma miki haka cikin malamai kizo kifad'an ko waye ni kuma zan hukun tashi dan bazasu b'atamin makaranta ba.


"To, shine abunda Jidderh ta ce


Komai da ya kamata Salis yayi ya gama harma an bawa Jiddeeh class sabida batayi premary ba, A kasa ta cikin Aji shida dan ta koyi wasu abubuwan kafin tashiga Js one,


Salis ya barota cikin makaranta ya koma gida


Zuwansa gida Mlm Kabiru yana shirin futowa ze tafi kasuwa,


Nan suka Gaisa yake she damasa Jidda yabarta cikin makaranta. gdy ss Mlm Kabiru ya masa sannan suka rabu.


Cikin gida yashiga ya samu Kamal Yace "Oga yade najika shiru?


Yace "Babu komai su Momy wai sun taho, sai da nace musu karsuzo amma yanxu suke cemin suna hanya.
ya k'arshe cikin damuwa


Salis Yace "To meye ciki dan sunzo sunga lafiyarka, haba dan Allah kabar wanna maganar."


Kamal ne ya numfasa, Yace "kasan de irin zaman da mukeyi cikin gidannan, kullum fada da tashin hankali, ga d'alibar shed'an cikin gida, ga Ubanta besan lefinta, ga Saude ba hankali, yadda naji tana ruwan ashar nasan bamai hankali bace.


Dariya sosai Salis yayi Yace "Tabb, har suna ka basu kenan?


Nan suka ci gaba da shirarsu yadda zasu tari Momy idan ta k'araso.




Karfe biyu da rabi motar su Momy ta tsaya kofar gidan Malam Kabiru dan gidan ba boyyaye ba ne, kowa yasansa suna tambaya wani yaro yashiga motar ya kawosu ,


Salis ne ya futo ya musu sannu da zuwa ya musu Iso zuwa cikin gidan


Ganin bak'uwar fuska yasa Saude sakin jikinta ta tarbesu cikin mutumci, da kulawa,


Nan ta basu taburma suka zauna ta kawo musu ruwa


Bayan sun Gaisa Salis Yace "Mama Saude wannan Itace mahaifiyar Oga sunanta Hajiya Binta.


"Allah sarki,
Cewar Saude Sannu da zuwa Hajiya, ya hanya? da sauran yara?.


Hajiya Binta Tace "hanya Alhadul,
yara kuwa banda ko d'aya Kamal shine kawai d'a na gashinan gidanku."


"Allah sarki, Sannu da zuwa.


Suna cikin haka saiga Jidderh tayi Sallama, tin daga kofar gida da taga Mota Tace "ko suwaye sukazo? bari na sauya tafiya.


Cikin nutsuwa ta k'araso gunsu, Mamaki ne ya kama Salis,


Saude kuwa sakar baki tayi tana kallan Ikon Allah jidderh da sallama? lalle yarinyar nan ba mutum bace.


Tinda Hajiya Binta taga Jidderh, take raya Abubuwa da yawa cikin raita. Addua'r ta d'aya Allah yasa yar gidan ce,


Jidderh ganin kallan da suke mata yasa ta zuwa gun Hajiya Binta ta durgusa Tace "Ina wuni Umma, kunzo lafiya?"


Hajiya Binta cikin farin ciki tace "Lafiya, yah makaranta?.


Jidderh Tace "Alhdul.


Mama Saude na dawo, Yah Salis ya jikin Kawu Kamal?.


Cikin sargewar murya Yace "Sannu da zuwa Jidderh, ya karatu?.


Alhdul Yaya Salis


Saude kuwa kasa magana tayi,


Hajiya Binta kuwa tace na ga gida babu abunda zesa nabar Jidderh ta kubucewa Kamal, yarinya mai hankali, da tunani, Uwa Uba kyau Allah ya mata kyau na futar hankali.


D'aki Jidderh ta shiga ta cire kayanta ta sauya wani ta futo harda daukar buta za tayi sallah 🤔


Sallah tayi ta futo Tace "Mama Saude kin gama abunci kuwa? yunwa nakeji sosai."

Hajiya Binta Tace "Salis dauko kula cikin mota na ta howa da Kamal A bunsa takai masa suci tare. 😳




*jidderh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*


©🎆


*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


*KUYIMIN AFUWA PEGE 4 NE NA MANTA NASA 5*
*ZAN TAFI TASHI HAKA SABIDA WASU BAZASU GANE BA INNASA 5 HA'ILAU*🙏


*banda bakin godiya gareku ina jin dadin comment sosai*🥰kuna *da yawa gruop ~gruop amma duk ina mika gaisuwa gareku masoya jidderh*🥰🥰🥰


*hatsabibiya jidderh*
*banda bakin godiya gareku*🙏


*MTS BASAKKWACE* 😍 *ku na daban ne*


*my class fant*🙏🙏🙏


*yan matan zamani*
🥰🥰🥰🥰🥰🥰


*yasee kuna da yawa sosai muhadu pege gaba*




🅿️6️⃣


......Cikin mamaki Salis Yace "Hajiya kamarya, suci tare kuma?.


Hajiya Binta Tace "kayi yadda nace, bansan musu ."


Jikinsa duk yayi sanyi haka ya juya yaje mota yadauko fulas din da tace ya dauko ya dawo,


"Jidderh tashi maza kibi yayanki kuci abunci, da kamal kinji.


cewar Hajiya Binta ta fadi tana murmushi,


Cikin nutsuwa Jidderh ta mik'e ta saka takalminta ta nufi d'akinsu Kamal,


Saude kuwa, mamaki ya kasa barinta ta kasa koda magana.


Hajiya Binta Tace "Amma jidderh akwai hankali, sabanin yaran mu na Abuja masu rawar kai, basa ganin girman kowa sai abunda suke so."


Saude Tace "hmm, gaskiya ne Jidderh akwai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads