Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 24174 words

Chapter 3 - Hatsabibiya Jiddah hausa novels .txt

Ads the beginning of article before Image

JIDDA   

02 Jun 2024

346

Ads at the middle of Article

babban hankali kuwa gareta, Inaga za tafi nachen.😃


"Sosai kuwa, Inaga had'i yarinya ga kyau, ga nutsuwa, samun irinsu ai sai antona a wannan lokacin. cewar Hajiya Binta


"Hmm." cewar Saude




Jidderh kuwa tana shiga d'akin, gun fulas din ta nufa.
Kamal ya buga mata tsawa, Yace "ki na da hankali kuwa? ko sallama babu kishigo kamar raguma zaki dauki fulas.


Murmushi tayi Tace "Yi hakuri Kawu Kamal matar waje ce, tace nazo na dauka indan ka koshi.


Salis ya shiga maganar Yace "Kayi hakuri Oga, Inaga da gaske Hajiya ce ta turo ta.


"Dallah yimin shiru, taje ta cewa Hajiyar bazan ba yarba, Ai ni takawo wa to na hana."


Cewar Kamal yana huci.


Futa Jidderh tayi ba tare da tace masa komai ba.


Hajiya Binta ganin Jidderh yasa ta saurin tambayarta "lafiya?


Jidderh cikin hawaye Tace Kawu Kamal ne yace "Wai ko kee baki isa ki sashi yaci ynz ba sai anjima. gashi yunwa nakeji tafadi tana kuka sosai .


Zabura Hajiya Binta tayi Tace "muje shidin banza zeja da ni.


D'akin suka koma cikin fada tace "Kamal kasanni de ko? to wlh kabini sannu in kuma kaki na b'ata maka .


Salis Yace "Hjiya kiyi hakuri, kinga Oga yanxu halin da yake abi komai asannu.


"Zanbi, amma sai yabini cikin sannu nima ya sanni yasan halina, ya kuma san mai zanyi, dan haka ya bude fulas din ynz suci yunwa takeji". daga haka ta juya tabar musu d'akin cikin fishi


Salis ne ya dauki wani filet din da suke cin Abunci ya mikawa Jidderh yace "bude ki zuba wanda ze miki kici, shi ba yajin yunwa yanxu


"Banda matsala da yunwarsa, fatana ciki na ya dauka. in na koshi ya shekara beci ba, baya gaba na cikina na sani ba nashi ba."


Kamal da ya keji tabkar ya kashe Jidderh dan tsanarta da yayi, dan ya mata tsana wanda besan taya ze fasalta ba. amma zasu gamu zata gane kuranta fatansa Allah ya basa lafiya.


Budi fulas din tayi taga dambun nama sai kamshi yake, ta zuba cikin filet din tayi waje ba tare da tace musu kala ba.


Gaban Saude taje ta zauna Hhajiya Tace "ya kika futo nan kuma?


Cewar Hajiya Binta


"Lah Umma kunyar Kawu Kamal na keji, bana cin abunci gabansa. "
Cewar Jidderh


Hajiya Binta ta ke taji san Jidderh ya kuma shigarta ta nasan mace mai kunya mai kare martabarta ta yah mace.


Jidderh tayi murmushin mugunta, ganin saude sai had'iyar yawu take, Tace "Mama Saude ga danbun nama babu damar ci, tinda bakisan nama bakyaci. gaskiya likitoti shegune, gashi yanzu sun hanaki cin nama sai zogale da tuwu shima banda miyar kifi."


Saude Tace "Ni kuma?"


Hajiya Binta ta karbin zanchen Tace "Allah sarki, sannu Saude haka likitoti suke su hanaka abunda kakeso.


bari Salis yashigo da guntun kaya sai yaje ya siyu miki buhun zogale tinda naga sun zama yan gari.
Saude babu bakin magana sai tseniwa Jidderh ta take a zuciyarta


"Salis zonan.


cewar Hajiya Binta


Cikin sauri ya k'araso yace "Gani Hajiya.


"Jeka but na mota kashigo da kayan abunci nazo dashi.


"To. shine abunda yafurta ya fita


bayan ya shigo da komai da tazo musu da shi, yace "Nagama Hajiya.


Tace Zo kaje kasuwa kasiyuwa Saude zogale.


"Zogale kuma hajiya? cewar Salis


"Eh, ba tacin nama da kifi, sai zogale, sai tuwu. ta fadi tana mika masa kudin


Mamaki ya kama Salis yaga kullum suka siyu sai sun ba ta, kuma tana ci amma yanzu kuma taya ya zama ta tena ci? lalle akwai wata akasa.


karbar kudin yayi bata re da yace komai ba,


Futarsa kuwa tayi dede da zuwan Mlm Kbr bayan sun gaisa yake ce masa Hajiya mahaifiyar Kamal ce tazo tana cikin gida, yan zuma kasuwa ta aike sa. Cewar Salis


"Ayya, sannunta da zuwa, amma baku kyauta ba, da kunce zata zo aida anmata abunci .
cewar Mlm Kabiru


"lah babu komai Baba, ai gida ne. cewar Salis


Mlm Kabiru Yace "shikenan bari nashiga gidan, sai kadawo.


Mlm Kabiru ya shiga cikin gida cikin sakin fuska ganin kayan abunci kamar ya bude shago ya sa shi k'arasawa cikin sauri .

Gaisa wa sukayi da Hajiya Binta cikin sakin fuska da kuma mutumta juna, take tambayarsa ya mai jiki?


"Da sauki, cewar Mlm Kabiru


Hajiya Binta ta masa godiya sosai Tace ga kayan abunci nan babu yawa."


Mlm Kabiru Yace "haba Hajiya wannan ai yafi karfin ace babu yawa. nagode sosai Allah yabar kauna.


Saude na gefe ta kasa magana.




Jidderh kuwa tashige d'aki tinda ta gama cinye naman tayi gaba abunta .


Hajiya Binta ta numfasa, Tace Mlm ina neman alfarma, naga Iri Inaso dan girman Allah kar kace A ~a


Mlm Kabru Yace "To Hajiya Iri kuma na me?


Cikin murmushi Tace Inasan had'a Kamal da Jidderh au...........🤬




*jidderh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️


HATSABIBIYA JIDDERH

NA JIDDERH


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️7️⃣


...."Inasan had'asu aure, dan harga Allah Jidderh tamin, na yaba da hankalinta da kuma nutsuwarta, ga kuma kamun kai.😳


Mlm Kabiru da tinda ta fara magana yayi shiru har ta kai karshe, A zuciyarsa kuwa mamaki yake wai ya'u A na yaba Jidderh, wanda ko shi baze ya beta haka ba, dan Jidderh ta bashi wahala fiye da tunani ko ma yace har yanzu yana sha begama ba.


Hajiya Binta ta katse masa tunani tace "kar ka damu da kuruciyarta, ba ina nufin ayi auran yanzu ba ne, A~ a ina nufinde munkama tin yanzu zan dau nauyin karatunta da komai nata har lokaci yayi."


Mlm Kabiru yayi murmushi yace "Hajiya duk ba naki bane, kinsan alkawari dole kafin mutum yadauka yayi na zari kansa. bazan miki alkawarin Jidderh ba amma Insha Allahu ina mai tabbatar miki da cewa Jidderh inde raban kamal ce ze samu, sabida halin rayuwa kar nace na basa kuma shi yana da wache yakeso, kinga mun shiga rayuwar yaro, amma idan muka bari zuwa lokacin to Insha Allahu babu matsala gareni."


Hajiya Binta taji dadin maganar Mlm Kabiru sosai ta kuma yaba da girmansa, dan duk maganar da ya gaya mata gaskiya ne, amma tayiwa kanta alkawarin sai kamal ya auri Jidderh


Mlm Kabiru Yace "Hajiya baki gayan komai naku ba? gashi kuma anzama d'aya ynz.


murmushi tayi Tace "lah babu komai.


suna na Hajiya Binta ni yar asalin garin guru ce, mahaifina attajirin mai kudine Alhaji Adamu Nera, mu uku ne gunsa ni ce ta fari sai kannaina guda biyu daya na muji sunansa Muha'd dayar kuma mace mai suna Khadija,


Nayi karatu sosai ta fannin jinya harma na fara aiki awani asibiti da yake cikin garin FMC,
anan muka hadu da Baban Kamal shiyama ciki yake aiki,
muka fara soyayya cikin Ikon Allah manya suka shiga ciki suka tsada magana d'aya.


sunan mahaifin Kamal Dr Fahat Abdullahi mutumin kirki ne, mai hakuri, da juriya kan aikinsa.


bayan munyi aure dashi bamu samu haihuwa da wuri ba, sai da mukayi shekara tara sannan na samu cikin Kamal nasha wuya sosai kafin na haihu lokacin haihuwa da yayi sai aikin akamin aka cire Kamal sannan likitoti suka tabbatar mana da cewa nadena haihuwa har abada.
munyi kuka mai yawan gaske dan munasan yara sosai,


haka muka hakura muka dauki kaddara muke renon Kamal cikin so da kaunar juna.


Bayan Kamal ya gama primary ne muka daukeshi muka kaishi kasar waje domin yayi katunsa achan, yayi secundery school ya ci gaba har ya gama karatunsa yasamu aiki
sannan ya dawo mahaifinsa ya gina masa wani babban asibiti yake aiki ciki.


lokaci daya ciwan ciki ya kama mahaifinsa wato Dr Fahat kafin muje asibiti har rai yayi halinsa.


munyi kuka sosai na rashin mahaifin kamal


bayan anyi arba'in kowa ya watse Kamal ya koma bakin aikinsa
nima kuma nakoma asibitin mahaifin Kamal nake kula dashi.


ko wannan karayar ta kamal kan hanya ne wata mota tashigo musu ze tafi gun aiki,
Kamal ya karye dayan kuma ya mutu munyi aikin asibiti amma daurin beyu ba, kullum jiya I'yau shine wani abokin aikina yace muzo nan insha Allahu za'adace."

Ni kuma lokacin inada wani aiki mai muhimmanci, shine nace sutaho nazo daga baya. ta karshe maganar cikin damuwa na tunawa da rayuwar bayanta.


Mlm Kabiru ya numfasa, Yace "Allah yajikan musulmi, yasa mutuwa hutuce garesu ameeee.


"Ameeeee. cewar Hajiya Binta


dawowar Salis ta katse musu shirarsu


Ganinsa da buhun zogale ba karamin mamaki yayi ba dan bega a'lamun wahala tare dasu ba.


Yace "Salis mai kuma zakayi da zogale har buhu guda?" cewar Mlm Kabiru


kafin yayi magana Jidderh Tace "Abunci Mama Saude ne. shi zata koma ci, inji likita."


Mlm Kabiru Mamaki yaci kasa ya'ushe Saude tayi jinya har Akadaurata kan zogale besani ba."


Jidderh Tace "Baba meye abun mamaki? tinda kasan abuncin tane zogale, safe, rana, dare, kasan batacin shinkafa, balle taliya, tinda siga ne da e'ta, yanxu goriba kawai zaka siya mata tinda Umma ta siya mata zogale gashinan buhu guda.


Hajiya Binta tace.....😍


JIDDERH CE


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️


*HATSABIBIYA JIDDEERH*


NA JIDDERH


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️8️⃣


......Hajiya binta Tace "Allah sarki Saude, gaskiya kinga rayuwa A ce mutum ta koma kamar karfe, baya cin abunci irin na mutane. bari asiyu miki goribar ai bansan haka ba ne kan jinyar taki ."


Saude kuwa da futowarta daga d'aki taji Jiddeerh na shirya mata karya yasa ta cewa "Kee!! jidderh Uban waye yagaya miki an hanani cin taliya? da shinkafa?" ta fadi cikin masifa dan tagane shirin Jidderh so take Hajiya ta hanata cin shinkafar da suka kawo musu da taliya.


Jidderh ganin Saude ta gano nufinta sai ta sauya hanya cikin kissa tace "yanzu Mama Saude har haushe aka kawo miki rubutun? amma har kin koma haukar. hajiya kiyi hakuri Saude tinda tayi wannan jinyar shikenan kanta ya samu matsala, da daureta akeyi yanzu ne aka nemar mata magani amma duk da haka wani lokaci zakiji tana ta zanche marar kai to bata cikin hayyacinta."


ba Saude ba, har Mlm saida yayi mamakin maganar Jidderh lalle Jiddeer ta wuce tunanin mutum sai de Allah ayya ba auran ze mata ba ya huta da masifa, yarinya k'arama da hatsabibanci kala ~kala tab."


Hajiya Tace "Ayya gaskiya Mlm Kabiru ka dage sosai kan Saude, inba haka ba abun ze zama babba.


Jidderh tace "Aida har ance masa ma ...
Saude ta chafe zanchen, Tace "Ance masa uwarki, ko ance masa Ubanki, shegiya tsinarniya jinin masifa, kara nayi haukan ta gaskiya da kina dauran ta karya da makirci irin ta Uwarki."


Hajiya Binta tayi baya dan ta tsorata sosai da Saude ta kuma yarda cewa bata da hankali, mgnr jidderh gaskiya ce.


Mlm Kabiru yace "Saude wuce kitafi d'akinki zanzo muyi mgn.


Saude tace "Ai duk lefinka ne, yarinya tayi duk abunda tayi niya ba zakayi magana ba, ta fadi tana juyawa ta koma d'akinta


Mlm Kabiru yaji mgnrt sosai amma shi abunda yake tunani yasa baya daukar mataki kanta besan mai zata kulla masa ba, dan ta masa ya gani, ya kuma san ko yanzu yashiga gonarta to zata kulla masa makirci 😳


Hajiya Binta ce ta katse shi Tace "kaje kayi sallah Mlm bayi mgn anjima."


"To. shine abunda ya furta ya futa jiki duk yayi sanyi


Jidderh tace "Umma kinga ni ba baya so na. kullum haka sukemin cikin gidan nan sabida uwata bata gidan sun koreta sun barni. Saude tana min azaba duk sanda jikinta ya tashi duka takewa Baba tazo kaina kuma." takarshe cikin kukan makirci.


*kuyi hakuri network yana ban matsala gashi banda chaji in nasamu chaji zaku jini zuwa dare insha allahu*💛


*jidderh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️






*HATSABIBIYA JIDDERH*👯🏼‍♀️


*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️9️⃣


......Hajiya binta take taji tausayin yarinyar ya kama ta.~ ta kuma yi alkawarin dauketa cikin gidan ko ta halin yaya.


Kamal Yace "Hajiya ba tasan gidan da tazo ba, yafi kabari tashin hankali. dan da ka kwana da hatsabibiyar nan, k'ar_ ahad'a ka da gawa kasan gawa ce, amma ita da ranta tafi gawa illah."


Salis dariya yayi sosai Yace "tabb, akwai matsala fa Oga, Allah de ya kare kawai .


"Kamar ya matsala? ta ka shirya wani makircin koh."


"Hmm! yafi nada k'ulluwa, dan na da sai wanda yashiga shirginta, na yanzu kuwa ta had'a da wanche ba tasan wace ita ba.
cewar Salis


Kamal Yace "su suka sani, Allh ~allah nake nawarke nayi gaba nabar wannan masifar ta gidan nan."


dariya sosai Salis yayi dan yasan Kamal be gane nufin saba shiyasa yace haka, amma shikam ya gano nufin hajiya kan Jidderh


Kamal yace "yade Salis?"


Yace "Babu komai Oga, in tuna gida ne kawai nayi missing na gida.


Murmushi Kamal yayi yace "Insha Allahu bazamu jima ba zamu tafi.
nan suka ci gaba da shirarsu cikin kwanciyar hankali.


Washe Gari Jidderh ta gama komai na shirin makaranta ta fito ta gaida Hajiy Binta ta mata sallama zata tafi.
har ta futa Hajiya Binta tace "Jidderh kin karya ne zaki tafi school?.


duk da ba tasan meye scholl ba, sai tashirya makirci tace "lah bata bani abunci, daman haka nake wuni da yinwa wani lokacinma na kwana haka."


Hajiya Binta ta kuma tausayawa Jidderh har raita Tace "kiyi hakuri kinji, watarana sai labari ga wannan kisai abu kici A makaranta naga lokaci ya kure da anyi abunci kinci."


Ganin nera dubu uku sabi yasa Jidderh murna Tace "Nagode Hajiya, Allah ya bawa kawu Kamal lafiya."


"Ameeee."


cewar Hajiya Binta taji dadin addu'arta, ashe ta damu da shi haka Allah ka cikamin burina na had'a Jiddeerh da Kamal."


Duk abunda sukeyi akunnan Mlm Kabiru da ya fito domin sugaisa da Hajiya Binta, jin maganar Jidderh ya sashi tsayawa yaji abunda suke fadi.


Futa kofar gida yayi yake na zarin rayuwarsa ta baya mai cike da farin ciki, kafin zuwan wata kaddara mai karfi wache ta sauyasa har yazama haka .


jin motsi bayansa yasa shi juyawa dan ganin waye
"Baba na tafi makaranta, wache Yaya Salis ya sani, wai besan gani na haka nayi girman da yanzu na gama premary, amma ba a sani ba kullum ina fama da allo kamar almajira.


Zanje kuma gidan su Inna Sahura na gayawa Fatima tazo murokeshi yasa ta e'tama, kar muyi biyu ~babu ~babu karatun babu gatan Uba. dan k'ara ni ma akan Ita da ba kasan da zamanta aduniya ba."


Daga haka ta juya ba tare da tajira amsar saba.

Mlm Kabiru yaja numfashi, yace "Rayuwa kenan.


komai kiyi Jidderh zaki dena, Fatima kuma Insha Allahu ni zan sata makaranta ba wani ba.


Jidderh kuwa kafin taje makaranta taje gidan Inna Sahura wato mahaifiyarta .


Ganin Jidderh cikin kayan makaranta ba k'aramin mamaki sukayi ba .


Fatima Tace "Jidderh ya'u she Baba ya saki makaranta? ya barni kamar ba yar saba."

Jidderh Tace....


Tabb, wato Jidderh su biyu ne kenan."


*Muje zuwa*


*jiddeerh ce*🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️






*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️1️⃣0️⃣


.......Jidderh Tace "kema kinsan ba Baba bane yasani, sai de wani ya samu makaranta amma ba shiba. da ze samu ya barmu har munkusa aure babu Arabi, babu Boko, babu karatun Sallah, balle na Alwala."
ta karshe mgn cikin wani yanayi.


Sahura tace "Oho ni Sahura, wato Jidderh ba zaki sauya daga futsarannan take ba ko? kullum kina girma amma babu hankali atare da kee! to yanzu waye ya saki makarantar? tinda ba Kabiru bane."


"Wani

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads