Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 24174 words

Chapter 6 - Hatsabibiya Jiddah hausa novels .txt

Ads the beginning of article before Image

JIDDA   

02 Jun 2024

351

Ads at the middle of Article

taji haushi


batayi magana ba sai kallonsu da take da e'do dan gani take kamar mafarki


tana tsaye gun Saude ta tsaya gabanta tace "kalleni da kyau na shigo kisawa raiki sai kinfita, amma ba kwana kusa ba sai nagama azabtar da kee tukum zaki fita batare da kinshirya ba." daga haka ta juya suka kaita d'akinta


Sahura kuwa kasa motsi tayi gun sai hawaye dake zuba e'donta na azaba.




bayan kowa ya watse nashigo ko takan Sahura banbiba nashiga d'akin amarya saida safe na fito cikin kwanciyar hankali nayi shirin shago na futa batare da naje gun Sahura ba.




bayan wasu watanni lamarin gida fa yazama sai addu'a domin komai ya lalace Saude ta hargitsa komai, Sahura tazama abar tausayi .


Ni kuwa banda bakin magana Saude ce da komai cikin gidan.


dede da kayan sawar Saude Sahura ke mata,komai ruwa, da rana, haka zata wuni tana aiki kuma baxata bata abunci ba,fatima haka zata tai ta kuka amma saude bazata ba abunci ba saide ta gaji da kuka tayi barci a haka.


amma ban tab'a magana ba 😥😔


*jiddderh ce*




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...




🅿️2️⃣1️⃣


........Kamar kullum ya'uma Sahura sai faman wanki take ga kuma Fatima na kuka nashigo gidan .


Banbi takan Sahura ba d'aki na shiga nasamu Saude barci ma take abunta .


kasancewar Fatima ta fara tafiya yasa ta zuwa d'akin takama kafata tana kuka wanda nasan yunwa takeji😢


wani Uban asahr Saude tayi ta tashi tace "har kinfara zuwarmin d'akin roko? yar maroka, zanyi makaninki. A gabana ta dauko ashana ta kunna takama hannun Fatima ta saka yarinya ta saka kuka mai furgitarwa dalilin konewar da tayi Sahura cikin sauri ta nufo d'akin Saude jin kukun Fatima.


"Wlh kika shigo sai na kasheta." Saude ta fadi cikin bacin rai


Sahura da taji haka sai tasaka kuka ta bar gun .


nikuwa ina zaune ko gizau banba.


haka Fatima azaba tasata ta suma agun, Saude ta dauko logo ta shafa mata ahannunta tsananin axabar loko yasa Fatima tashi daga suman da tayi.




Saude ta dauketa ta cillota waje Sahura taje ta gudu ta dauketa ganin konar yasa ta gigicewa amma babu halin fita ta kaita gun magani tinda bata da kudi .




haka Sahura taci gaba da zaman azaba a bangare biyu ta guna tasha ta gun Saude kuwa abun yayi muni da yawa.


Tinda Saude tashigo gidan bana kwana d'akin Sahura, kullum muna tare da Saude kasancewarta mace mai tsananin sha'awa.


Bayan wasu lokota da Sahura ta kama rashin lafiya mai tsanani wanda yasa bata iya tashi balle tayi aiki, Saude taje ta sameta har d'akin ta mata dokan kawu wuka har ta karyata hannunta ta dauko logo ta shafe mata jikinta dashi tabarta, ta kuma kama Fatima da daureta cikin gado ta kullesu.


kusan sati guda suna cikin wanna hali babu wanda yasani harma Fatima ta suma.


matar Dan Asali tazo domin doba mai sunanta tayi sallama yafi goma Saude na zaune bata amsa ba.


haka yasata shigewa d'akin Sahura ganinsa rufe tayi mamaki sosai har ta juye sai kuma takeji nishi cikin dakin,


torawa tayi cikin firgici taga Sahura ta haihu yar kwace cikin jini da a'lama yanzu ta haihu ga kuma Fatima daure .


"Ihu ta saka take jama'a suka shigo ganin lafiya kuwa ?


A bunda mutane suka tarar shine ya tsorata su aka fito da Fatima da take sume Sahura ma kamar gawa, jaririya kuwa bata numfashi .


mutane suka temaka aka kaisu Asibiti su dukk aka basu gado.


mutane sai tsinimin albarka suke, Saude kuwa cewa suke zatayi fin hakama domin halinta ne.
sai da su Sahura sukayi wata guda A asibiti dan Asali na kula dasu, ba tare da ko sannu naje na musu ba .


har aka sallamesu daga Dan Asali sai matarsa sune tsaye kan Sahura da Fatima.
Dan Asali yasawa yarinya sunan mamata wato Hauwa Kulu jidderh.


bayan wata biyar Sahura na gidan Dan Asali babu ruwa na dasu.


watara na Dan Asali yazo ya sameni yace "na bashi takardar ?.


Babu musu nace "ai najima da sakinta na saketa saki biyu."


Yace "babu damuwa kahadan komai nawa zanzo muyi lissafi.





*jidderh ce*




*HATSABIBIYA JIDDERH*

*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️2️⃣2️⃣


.......Bayan kwana biyu Dan Asali ya dawo ya sameni yace "Nazo muyi lissafi inkana da lokaci?"


nace "Babu damuwa .


lissafi muka fara abu mafi girma shine duk kudin babu nawa ciki muncinye, duk kudinsa ne ya rage shima be cikaba.


yace "Ngd sosai da halakcin da kamin Kabiru, duk da bangani lefinka sharrin asiri ne wanda nake ganin lefin kane, domin kai kayi sake da addu'a har komai ya lalace, kazabi matarka da mu kaje ina kuma guje maka ranar dana sani wache bata da amfani gareka.


wata K'awar Saude ce tazo zata shiga gidan jin mgnr da muke ta tsaya


tace "Ai Dan Asali kar ka bata bakinka domin wlh Saude bata aure Mlm Kabiru ba sai da ta gama dashi, ta asirce shi beda katabus na mgn komai zatayi, shiyasa kaga ya koma dolo besan Saude ba, ya kai kansa gareta duk mazan da take aura kudinsu take kwashewa ta daura musu hauka ta gudu shine mujinta na goma bamusan ya zata kaya ba gaba.


"Tabb, Dan Asali yace "kara da nazo da wuri kenan? da komai sai yakare to Kabiru kai Allah ya daurawa bani ba, dan haka sai anjima kar kuma naganka kofar shagona."
daga haka ya juya


Saude duk tanajin mgnrmu da K'awarta dan haka ta fito ta kamata da kokuwa da kyal aka rabasu tana maka mata ashar haka suka rabu babu dadi.


Sahura kuwa tasamu lafiya harma ta gama iddarta, tana kula da yaranta cikin kulawa .




Bayan shekara goma sha biyar Abubuwa da yawa sun faru, wanda fadin munisu abun yayi yawa sosai na aikata kuskure wanda bazan iya kyarawa ba.




Sahura kuwa I'yayanta sun samu labarin komai Dan Asali ya bata gida yace su zauna da yaranta zena kula dasu.


Fatima da Jiddaerh suna da banbancin hali yayi da fatima ta zama mai hakuri, da kawaici, bata fiye mgn ba haka bata fiye rigima ba.


Jidderh kuwa duk ta had'a wanna abubuwan da na lissafa, bata yafiya bata mantuwa, bata bari abun abu duk k'arancinsa sai ta rama ko bayan shekara ne zata rama shi.

Jidderh bata fiye shiga safgar mutum ba, amma karka shiga ta ~ta domin haduwar bazatayi kyauba, tana da salo daban ~daban na yaki domin daukar fansa, bata barwa yaro ko babba inde ka tabata haka take bata sake da ramuwa.


Suna zaune gun Sahura taga komai Dan Asali ke musu kuma ance Ubnasu yana raye be mutu ba, haka yasa ta tsare mahaifiyarta da tambaya ina nake? labarin komai Sahura ta bata dan haka Jidderh tayi alkawarin daukar fansa tashirya kayanta tsaf tadawo gida na da zama tace gidan Ubanta ta dawo bata barwa kowa domin zuciyata fansa ciki.


Tinda Jidderh ta dawo gidan ya zama babu lafiya kullum cikin fada da tashin hankali yake yayi da Saude take neman hanyar kashe Jidderh domin yanzu e'tace damuwarta.




Wannan atakaice kenan, Hajiya na garjarta miki sabida lokaci.
cewar Mlm Kabiry yana share hawaye




Hajiya Binta ta numfasa, tace "Allah ya kyauta, insha Allahu za musan makama kuma zan temaka maka, karka damu kowanna bawa da kaddararsa, Jidderh kuma inaga zan tafi da e'ta chan nasata makarantar kwana kafin ta gama Insha Allahu komai ya dedeta .


Mlm Kabiru yace "Ayya zan yarda kuwa kitafi da Jidderh tin yanzu?"


murmushi tayi tace "karkadamu babu wanda zesan maganar auran, har sai nagama komai .


yace to "A ya take kenan yanzu?"


zan dauketa matsayin zatayi karatu gabana inta gama zan dawo da e'ta gabanku kafin nan Sahura zata huce intaga halakcin da muka mutaba zata yarda da auran.


Mlm Kabiru yace hakane kuma,domin damuwa Sahura, yanzu yaushe zaki tafi kenan? bansan kowa yasan zata bar garin nan."


Tace "Gobe Insh Allahu karfe 6:00 zamu tafi zance ta shirya zata rakani hanya sai mutafi kawai .


yace "hakan yayi ngd sosai yadda kikamin allah yamiki .


"Ameeeeee suka furta tare.


Washe gari Hajiya ta shirya tsab tacewa jidderh "tashi kirakani hanya zantafi .


tashi tayi ta shirya tace "Na gama Hajiya."


futowa sukayi sukayiwa Saude sallama tana daga kwance kafa ta kumbura


Mlm Kabiru har mota ya rakasu yana musu Allah ya kiyaye hanya, jikinsa duk yayi sanyi hawaye nabin kuncinsa.


suka hau mota hajiya taja sai tafiya


Ganin sunyi tafiya mai nisa yasa Jidderh tambayr Hajiya ina zasu ne haka sunbar garinsu?


hajiya tace "makaranta zankai ki, ko bakiso?"


Shiru jidderh tayi 👌🏽




*jidderrh ce*




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...




🅿️2️⃣3️⃣


....Sannu~ sannu bata hana zuwa sai de adad'e ba ajeba.


karfe 12:00dede su Jidderh suka shiga garin Abuja yayi da jidderh duk ta tsore gani take kamar Hajiya yan kata za tayi.


bata gama tunaninba taga Hajiya ta tsaya gaban wani gida aljannar duniya, tin kai kashiga kasan ba na talaka ba ne.
Hon tayi mai gadi ya bude mata suka shiga paking tayi ta fito ta cewa jidderh "fito munzo, kisaki jikinki kinji y'ata."


Murmushin dole Jidderh tayi tasan abun bazeyuba akawota nan ace ta nutsu babu wannan mgnr.
cikin gida suka shiga "Wow mai karatu gidan ya hadu iyakar haduwa babu karya ciki .


Hajiya tace wa "Jidderh zauna bari nayiwa masu aiki mgn su kawo mana abunci.


Zama Jidderh tayi cikin raita kuwa cewa take Allah ka had'amu da wannan dan jin kai, nayi maganinsa, ashe nan ne gidansu shiyasa yakejin kaisa kamar sarki, Mtss


Hajiya ta fito tare da wasu masu aiki guda biyu dauke da abunci suka aje samn table sukayi gaba.


Abunci Jidderh taci ta koshi duk da cikin raita mamakin abunci take dan yamata dadi sosai kuma bata taba cin irinsa ba.


Ranar asabar Hajiya ta gama komai na Jidderh na makaranta cewarta ba tasan ta zauna har su had'u da Kamal, besan ma ta dawo ba, da yazo




Karfe 11:00 hajiya da kanta takai Jidderh makarantar kwana ta ~ta garin Yola, ankarbi jidderh cikin kulawa da mutumci kusan kudi babu abunda baze sakaba inde dashi hannuka


Fada sosai Hajiya tayiwa Jidderh sannan ta barta sukayi sallama ta juna kowa zuciyarsa babu dadi kamar karsu rabu sukeji.


Wani malami ne ya karaso gunta yace "yi hakuri Hauwa, da haka kowa yazo yasa ba, ga wata bakuwa e'tama yanzu tazo kun zama abokai daga ya'u, kuma e'tama Jss two ne class nata."


Murmushi Jidderh tayi tace "Ngd mlm.


d'ayar ce ta k'araso tace "Suna na Maimuna Isah, kefa?"


Jidderh tace "Hauwa M Kabiru.


Murmushi suka yiwa juna, sannan kowace tadau kayanta dan kaisu inda aka basu.



Dawowar Hajiya Binta kuwa yayi dede da shigowar tawagar mutane masu sanar da daurin auran Kamal da Beby


Ganinsu ba k'aramin mamaki Hajiya tayi ba, tace "lafiya kuwa gidan nawa?


Wani polis din ya karaso yace "Mai girma gwamana ne yace muzo mu shedawa d'anki andaura auransa da y'arsa Beby, bisa amincewarsa da kuma wakilansa wato dangin Dr Fahat kenan.


"Aure? cewar Hajiya Binta


"Aure kuwa harma andaura yanzu haka. cewar wani mutum na gefansu


"To ina aka taba aure babu sanin Uwa?"


Tinda bake ce mujinba ba kuma yarda ki muke nema ba, Ai mgn ta kare, Kamal yana son Beby E'tama tana son sa, dan haka aure ya dauru sai anjima.


Daga haka ya juya ya barta cikin tashin hankali


yadda taji maganar kamar saukar akaradu, jiri ne yake neman daukarta tana shirin faduwa, haka kuwa yayi dede ta shigowar Kamal cikin sauri ya karasa paking yayi yafito aguje ya rumgumeta ta fada jikinsa.


*jiddderh ce*




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...




🅿️2️⃣4️⃣




.......Cikin sauri ya kamata ya rumgume cikin firgice yace "momy lafiya kuwa ?"


"lafiya. shine abunda Momy ta furta


kamata yayi yace "zaki Iya tafiya mushiga cikin gida ko nadauke ki?.


"kama ni de, nataka zefi."


kamata yayi yakaita har fallow ya bata ruwa tasha ta basa kofin


shiru yayi domin ya tsorata sosai d kallan da Hajiya kemai


cikin hada mgana yace "Hajiya..


daga masa hannu tayi tace "bansan jin komai daga gareka, kabarni akauye kataho kai mai zuciya? daga maganar wasa har kadauka gaske kataho baka tunanin wani abu ya sameni kataho."


Bayan kataho ashe soyayya kadawo kuka fara, harda yar gwamna. to Alhdul aure kayi ba sani ba shawara, Allah yasayya Alkhari ya baku zaman lfy ngd ss da halakcin da kamin amatsayina na Uwa." ta karshe cikin hawaye


"Dan Allah kiyi hakuri Hajiya wlh komai ya faru bisa ....


k'ara katseshi tayi tace "bisa mai? bisa rashin hankali, Ina ruwa na auranka, ban Isa ka gayan bane, ko banda matsayin da zaka gayan zakayi aure?


shiru yayi kansa gaba d'aya yadau chaji yarasa ina zeska kansa ya huta, yana ji daman ya mutu kowa ya huta.


cikin tsawa tace "Tashi kaban gu, yanzu nan ban bukatar komai gunka, aure kayi daman kana da gida shine gadararka to ban bukatar ganinta cikin gida na kuxauna gidanku.


kuka yasa sosai yace "Hajiya dan Allah ki tsaya ki saurareni wlh banyi haka da ganganba sai dan sira da rayuwarmu pls Hajiya.


yakarshe cikin kuka


E'tama kukan takeyi sosai domin abun ya dake ta sosai yanzu mai zata cewa Mlm Kabiru kenan ?


ya katseta yace "Wlh bansan yarinyar kawai bala'i ne yasa ta nace min lalle sai ni zata aura pls Momy.


Cikin zabura tace "Da Ubanwa ya kaika gunta? har ta ganka tace tana sonka, A hoto, ko jarida, ko A walkiya taga anhasko ka kamata kyau? aikin banza kawai.
cewar Hajiya


Nan Kamal ya bawa Hajiya labarin komai da yafaru bayan dawowarsa har daurin auran da komai .


Abun ya daure mata kai daman ana haka lalle mulki ba wasa ba.


tace "Shikenan zamuyi mgn daga baya.


yace "Pls Momy dan girman Allah kiyafemin kidena fishi dani.


sai ya bata tausayi sosai Uwa da d'a tace babu komai .


*jidderh ce*




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...




🅿️2️⃣5️⃣


......Tashi yayi jiki duk yayi sanyi, yana tuna irin wulakancin da zewa Beby, dan seya koya mata hankali ya tabbatar mata da ba komai kudi kesiya ba.


da haka ya samu ya nufi d'akinsa ya kwanta be jima da kwanciya ba abokaisa suka zo suka mata cha suna masa korafi, aka daura aure babu daga hannu sai de sugani a tauraruwa ana haska gun daurin aure.


shide be musu magana ba dan haushi suke bashi sani ne basuyi ba.
Salis ne yace "Oga anshirya dener fa karfe 2:00pm zasu fara .


shide Kamal beyi magana ba, da e'do kawai yake binsu dashi babu bakin mgn gunsa yanzu.


wani Anas daga ciki ya dafa Kamal yac "Am sorry, aboki muna da labarin komai amma kadau haka amatsayin kaddara kowa da kalar tasa yadda take xuwa,


kar haka yasa ka wulakanta musu y'ah kasan abun bazeyi kyau ba, domin Beby sangartanciya ce, kasan cewar ta e'ta d'aya gun I'yayanta dan haka ka kula sosai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads