Showing 18001 words to 21000 words out of 24174 words
Chapter 7 - Hatsabibiya Jiddah hausa novels .txt
da rayuwarka.
"Kayi hakuri da duk wani hukuncin da mahaifinta ze yanke kan ka, kabishi sannu ~sannu tinda yarinyar tana sanka watarana sai labari komai ze zama tarihi."
Nura ne ya karbi zanche yace "Duk maganarka gaskiya ce, Kamal kayi hakuri da mulkin mallaka da aka maka na auran dole kayi addu'a Allah yasa alkhari ne cikinsa.
duk jikinsa yayi sanyi amma beji ze'Iya kaunar Beby har abada, dan zuciyarsa bata gareta sam bata tsarinsa bata burgesa, Uwa Uba cin mutumcin da Ubanta ya masa ya kuma tsanarta araisa.
Nura yace "Pls Kamal kadena yawan tunani, kashare kawai komai ze huce kashirya mutafi gun dener tasu naga lokaci ya kusa.
"Banji zan Iya futa, kaina ke ciwo kuje kawai in zaku. cewar Kamal
Anas yace "shikenan babu damuwa, zamu wakilceka. dan yaga yanayin da Kamal ke ciki abun atausaya masa ne.
Karfe 2:00 pm dede suka karasa gun dener gurin ya hadu karshen had'uwa ankashe kudi sosai maza da mata gun abun ba'a mgana, wasu angayyace su wasu kuma gulma ta kawo su.
karasa gun sunkayi yayi da Dj yasauya kid'an zuwa na abokai Ango Anas ne yacewa Dj ya bada labarin Ango besamu damar zuwa ba sbd bejin dadi jikinsa.
nan Dj ya bada shalar Ango babu lafiya,
K'ida ne ya cigaba da tashi yawancin yaran gun yaran manya ne masu ji da kansu.
Amarya nagani ta nufo gun su Anas cikin wata shegiyar riga wache e'ta da babu duk d'aya, ammata meaup na tashin hankali kan yasha gashin kanti ta kara dashi .
Babu sallama domin hakan yazama kamar al'adarta,
cikin yanka tace "yaran Oga ina honey?"
Salis yace "beda lafiya besamu zuwa ba."
"karya ne, lafiyarsa kalau kawai kace baze zeso ba, wannan jinkai nasa bazan dauka ba,MTSSS."
Anas abun yamai ciwo yace "kee kina da hankaki kuwa? har kin Isa mumuki karya wawiya kawai, kinyi wata shiga kamar arniya, kinga mun muki kama da yaranki ne?"
Tas!! Tas!! Tas!! kakeji ta daukesa da mari har uku ajere take hankali jama'a yayu kansu.
tashi Anas yayi ze rama Salis ya rike masa hannu ganin wanda suka zagayesu da bunduga.
tace "barshi yajawa kansa masifa, barshi yasiyawa kansa mutuwa be shirya ba, barshi yajawa danginsa tashin hankali. kutafi da shi har sai na ne meshi Beby ta bada umarnin kama Anas
kama Anas sukayi suka sashi mota sukaja babu wanda yasan inda zasu kaishi
haka su Salis suka bargun cikin tashin hankali mai tsanani
Su kuwa su Beby rawa suka ci gaba dayi cewarta tinda andaura auran bata da damuwa da zuwansa ko rashin zuwansa.
*JIDDERH CE*🖊️🖊️
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️2️⃣6️⃣
......Su salis ne suke bawa Kamal labarin abunda ya faru, cikin tsantsar bacin rai ya dauko wayarsa ze kirata ashe beda nomberta🤔
Salis ne ya lura da abunda yake nema yasa shi cewa nombert kake nema? ina da e'ta.
wayar Kamal ya mika masa domin yadda yakeji kansa baze e'ya daukar nomber ba .
bayan ya gama sawa ne ya danna call sannan ya mika masa wayar
daga wa tayi cikin kissa tace "Honey shi....
"Dallah malama tsaya ina kikai min aboki?"
magana zata kuma yakatseta yace "Wlh kika yarda abu ya sameshi wlh sai kinrena kanki wawiya kawai."
Salis ne yace "Haba Oga, ya muna cikin wata kuma kasa mushiga wata, bayan kasan wace Beby kaima baka fi karfin ta sa akama kaba.
kashe wayar yayi zuciyarsa na masa zafi da k'una, key yadauka ze futa
Salis yace "Wlh Oga bazaka futa cikin wannan hali ba, taya zakaje gunta yanzu kaima ta saka su kamaka, muyi biyu babu kaga mubi komai asannu inaga haka shine dede .
Kamal zama yayi bakin gado zuciyarsa na masa zafi
Ita kuwa Beby dariya tayi mai isarta tace Kmal zan kyara ka, wlh zakasha mamaki wace Beby cikin kissa zan juyaka san raina, kai nawa ne ni d'aya babu wata mace bayan ni, daga ni sai mutuwa bana had'a san abu da wani sai de abarmin, dan bansan duk abund yazama biyu ne aduniya, kai na keso kaima kuma dole kasoni ta hanyar izzata da kissata.babu mace aduniya da ta esa na bata kai sai naga katshen rayuwarta,ko waye ubanta cikin duniya,dole tabarmin kai kamal,beby e'ta d'aya ce gun i'yayanta dole gun mujinta ma tazama tilo shalele, murmushi tayi domin abun yamata dadi sosai😊
wata kawarta tace ta karaso gun tace "Beby kinmin dede abunda kakayi yanzu, kinga zezo gareki da bukatar ki sakar masa abokinsa, ke kuma kice a ~a har sai yabaki hakuri tukum.
"hhhhh Zuly kenan, nima haka ce tasani kamani sa domin tarko na saka masa mai wuyar bullewa garesa,mune muke siyar da kissa ga wasu balle mu dole yayi biyayya gareni."
yan zuma yakirani kinga nafara samun nasara kansa tin yanzu daga haka ze gane shayi ruwa ne .
zuly tace "haka nakesanki tawan, ya maganar kayan kyara kuwa fatan kingama da fanninsu .?
hhhhh "haba Zuly kinsan yadda nakesan Kamal kuwa? ai dole nayi kyara gudun matsala nayi kyara ciki da waje banda matsala .
dariya suka saka lokaci guda magani zuly ta dauko cikin jakarta tace "sha wannan yanzu kiga ikon Allah zakiban labari da kanki.
karba tayi tace "nagode, take ta shanye duk ta jefar da jarkar agun tace "Ngd k'awata.
kirane yashigo wayarta ganin sunan my Dady yasata saurin dauka
"Dady." ta fadi babu sallama
daga daya bangaran yace "Beby yakamata azo yanzu akaiki fa, dare yayi kimasa waya yazo kutafi yanzu tafiyar gangawa tasame ni yanzu .
"To, Dady amma ba kace gida zaka bamu ba ?
"Eh Beby amma ki kirashi yazo sai kizaba gidansa, ko gidan da zanbaku ?"
"Ok Dady zan zauna gidansa inyaso nagunka nake zuwa hutawa ciki.
"Ok, hakan yayi kyau ki hanzarta kiransa yazo.
daga haka yakashe wayarsa
Ihu ta saka cikin farin ciki ta rumgume Zuly tace "bari nakira Honey yazo dady na kiransa."
JIDDERH KUWA..🖊️🖊️🖊️
........*jidderh ce*
*na gaji*😢😢
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️2️⃣7️⃣
.......Cikin kwanciyar hankali Jidderh ta saki jikinta da Maimuna sun saba sosai tsakaninsu, karatu kuwa babu lefi suna dauka fiye da tunanin mutum.
zaune suke suna shira Maimuna tace "Inasan zama Dr yana burgini sosai.
Dariya Jidderh tayi tace "zaki Iya, inde kinsa kaiki komai dan maida kaine inde zaka saka kaika tofa zaka iya komeye.
"hakane, amma ke mai kikesan zama nan gaba?"
cewra Maimuna
"Eto bana ce ba, sai naga zuwa lokacin tukum, amma yanzu ina Jss two ina ni ina lissafin shekara sama da goma nan gaba koma na mutu kafin lokacin ."
cewra Jidderh
Dariya Maimuna tayi tace "lalle yanxu kinasan mutuwa nan kusa? nide gaskiya banso, nafisan sai naga karshen boko tukum, dan ina da buri da yawa cikin raina.
"Kowa yana da buri sai de na wani yafi na wani, banda wani buri gaba na yanzu sai abunda ke gaba na shine nasara ta.
Amma duk da haka bana ce bansan zama wani abu arayuwa ba, tinda bakasan mai gobe zata haifar ba.
cewar Jidderh
Maimuna tace "Nide ko aure banji zanyi kwana kusa gaskiya, mu gidanmu basa aure da wuri sai munfara aiki tukum, wata ma saitayi fin shekara uku tana aiki sannan tayi aure nima kuma ina da burin haka gaskiya.
"Hhhh lalle fa aure manya, aishi lokaci garesa inde yazo bashi da makawa sai anyi .
cewra Jidderh
haka de shirar tasu take kasancewa duk lokacin da suka zauna yayin da Maimuna kewa Jidderh kallon bata waye ba, Jidderh kuwa ke mata kallan sakarya dan bataso tasan halinta yanzu sai ankwana biyu tukum dan taga sai ta kyarata tukum zata rage rawar kai .
Wayarsa ce tayi k'ara yaga mai kiran nomber da yakira ce ake kiransa da e'ta banza yayi da e'ta har tagama wani kiran ya kuma shigowa
Salis yakai hannu ya dauka yace "Pls Oga kubar duk wata jayayya da Beby ka nutsu kace tasa asakeshi dan bata da kai naga a'lama.
Nura ne yace "nima haka nagani, pls kayi hakuri kamata magana tinda gidanka zatazo ai da sauki sai ka kyarata dede gwargwato, har ta koma hayyacinta. Anjima fa ankawota tana kasanka ikon ka kabata lokaci ta gama haukarta lokacin kadai tashigo hannu.
"Tabbs maganarsu gaskiya ce anjima zata zo gidansa ze kuwa yi maganinta sai tayi da tasani nashiga rayuwarsa da tayi beshirya ba.
Beby kuwa jin adauka tana "Hello, Hello, jin ba'ayi mgn ba yasa takashe.
kiransa yashigo wayarta wani Ihu ta saki duk fallow saida ya dauka kowa kallanta yafara yana tunanin lafiya kuwa?
dauka tayi tace "Hello Honey Dady yana kiranka."
"Ok, shine abunda ya furta
tace "yace kazo yanzu tafiya ce ta sameshi yanzu."
yace "lafiya yake kirana?"
murmushi tayi tace "Lafiya yace kazo mutafi, shine maganar.
yace "Ok babu damuwa ganin nan zuwa."
yakashe wayar dan dauriya yayi har yamata magana haka
Nura yace "ko kaifa Oga kabita sannu har ta bamu shi sai ka kyarata san ranka."
tashi yayi yace "Ina zuwa bari naje gun Momy nadawo."
Momy na zaune tana tunanin wanna aure nafi karfi amma ta mukawa Allah lamarinsa komai mukaddari ne Allah yabasu zaman lafiya kuma bazata gaya masa ko da wasa maganar auran Jidderh ba, har sai ya kawo kansa da kansa gareta tukum zata yarda zata ci gaba da kula da jidderh har kamal ya durgusa mata yana rokon soyayyarta."
sallamarsa ce ta katse mata tunaninta
Amsawa tayi ta kyara zamanta kallo d'aya ta masa taga duk ya rame lokaci guda har baki yayi na wahala.
zama yayi kusa da e'ta yace "Momy dan Allah kiyi hakuri kan auran nan pls momy."
tace "Kamal mgn ta wuce babu komai Allah yasayya alkhari cikinsa, aure da mutuwa duk lokaci garesu da yayi to babu makawa sai yafaru kaide ka kula musu da y'arsu amana."
yace "Ngd Momy nan ya kwashe komai ya gaya mata har kiran da ta masa .
Momy ta numfasa lokaci guda ta saki murmushi tace "kayi hakuri zatayi hankali nam gava amma kafin ku zauna gidanku kafara kawota nan gidan tukum, muzauna na wani lokaci daga baya sai kutare gidanku hakan zefi nakega.
"duk yadda kikace Momy." cewar Kamal
"katashi kaje kashirya katafi da wuri karsu gaji, Allah ya maka albarka amma kasan yadda kayi ta bada yarannan.
ta fadi babu a'lamun damuwa gareta sai farin ciki .
"To Momy bari na tafi ya fadi yana mikewa zuciyarsa kuwa mamakin saukarta lokaci guda yayi amma yabari kan ta hakura ne kawai .
ya futa zuciyarsa wasai domin baci rai Momy shine damuwarsa, ba auran Beby ba, yasan wahala zatasha gunsa ba dadi ba.
momy kuwa yana futa tasaka dariya sai da tayi san ranta sannan tace "Beby kike ko wah? hmm!! zaku gamu da maikyara ki, jidderh e'ta ce dede kishi da keee, zan kuma zuba muku e'do naga karshen Izzarki, naga mulkin Ubanki? naga kudin bayan auran mai kuma ze siya miki."
kingamu da dede kee harma tafiki hatsabibanci, zanga zaman naku guri d'aya kafin ku koma gidanku dole tafara kyaramin keee tukum."
*JIDDERH CE*💗
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*💗
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️2️⃣8️⃣
.........Duk wani shiri da Kamal zeyi yashirya tsaf, kai kace daman yashirya auran, farar shadda yasaka amma tamasa kyau sosai jikinsa kamshin ke tashi ta ko ina jikinsa.
yace "Mutafi to, na gama."
dariya Salis yasaka yace "Oga Angon Beby, wanna shiga haka ai saita haukace.
"Daman mahaukaciya ce, bawai saita gannin ba. Kamal yafadi yana shirin fita
futowa sukayi su dukkansu daga bangaran suka nufi gun paking domin daukar motocinsu.
Sun shiga mota Salis da Nura, sai Kamal tasa motar daban dan shi ze dauko Amarya.
kiran Momy yayi yace "Yatafi tasaka akyara bangaren kafin su dawo.
"To, tace Allah ya kaika lafiya ya tsare sharrin karfe.
"Ameee. ya furta sanna ya kashe wayarsa yana murmushin jin dadi yadda Momy tasauko kamar ba e'ta ba.
Momy kuwa bayan gama wayarsu take ta kira masu aiki ta gaya musu abunda zasuyi cikin kankanin lokaci takeso su had'a.
"To shine abunda suka furta suka juya domin aikatawa.
cikin lokacin kadai suka gama komai kasan cewar daman akyare yake kawai de sun k'ara ne kan nada amma Kamal akwai tsafta sosai.
"mungama hajiya. suka furta
"Sannunku Allah yashi albarka yabar zaman tare." Momy tace
Ameeeee, dan sunajin dadin addu'arta garesu shiyasa suke ganin girmanta fiye da tunani.
Hon sukayi mai gadi yazo ya walgale kofa cikin sauri
Gun paking suka nufa suka aje motocinsu suka futo
Salis yace "Allah ya isa kudin talakawa, kana ganin gidan kasan hakkin wasu ne.
dariya Nura yayi yace "baka taba zuwa bane? ai yana irinsu sukai ashari asani na.
"Ashari fa? lalle lahira za'a kai mata kaya.
cewar Salis
shide kamal bece ko ba sai wayarsa da yadauko yakira Beby
bugu daya ta dauka "honey kazo ne? tafadi cikin kashe murya
yace "gani harabar gidanku.
"Ok gani nan zuwa. ta furta cikin saurin
kashe wayar yayi sanna ya kalli gidan dare ne amma tamkar rana sabida haske ko ina matakan tsaro ne, da bindiga hannusu ga kuma ya mata da samari da suke shige da fice cikin gidan, lalle mai mulki yana hutawarsa, Allah sarki talaka amfaninsa sai lokacin zabe da angama yamaza bola.
Cikin sauri ta fito babu mayafi kanta takaraso gunsu babu sallama ta kama hannunsa cikin kashe murya tace "Muje Honey.
kasa magana yayi kunya ta rufesa tinda yake babu mace da ta taba rike hannunsa sai Beby mari ze kai mata
Nura yace "Muje kawai Am sorry."
Beby kuwa ko ajikinta haka ta kama hannunsa har fallow Dadynt duk haka ta ratsa mutanan dake fallow ta kaisa.
"Wow fallow ya hadu iyakar haduwa, zaune yake kan wata kujera ta alfarma yadaura daya kan daya fuskarnan babu walwla
"Beby tace "dady gashi yazo."
"Ok jeki zamuyi magana. yafadi cikin murmushi
Kiss tawa Kamal sannan ta futa tana murmushi
kyaran murya yayi yace "kajini d kyau Beby tafi karfinka, kaddara ce tasata aureka amma banga abunta takeso gunka ba,baka da komai sai jin kai.
ka kula da rayuwarta batasan takura, bata kuma magana biyu komai takeso shi ake mata.
"kar ka bari tayi kuka da kai domin bazakaji dadi ba.
batasan kishiya ko sunanta batasan ji, ko a wasa balle a gaske daga e'ta karufe aure har abada.
"batasan kulle ko ina tana da ikon futa taje babu takura cikin rayuwarta.
e'ta daya ce guna, dole taxama d'aya gareka.
"ka kula da lafiyarta da komai nata na rayuwa.
batasan saka e'do cikin rayuwarta komai tayi dede tayi.
kajini koh?"
kamal abun yabasa haushi amma sai yadaure yace "Naji
sai magnr gida tace gidanka zata zauna da nabata gida amma tace a~ a ?
Kamal yace "babu damuwa, nima inadashi amma bankarasa part nawa zai kaita kafin nagama, tace ta yarda."
"Ok, tinda ta yarda babu damuwa, amma cikin gudan naku ku nawa ne?
Kamar bazeyi magana ba, sai kuma yace ni da Momy ne.
"Ok, Ka gaya mata ta kula da Beby fiye da yadda zata kula da kanta,danrayuwar Beby tafi rayuwarku amfani guna, banda takura nima nan bantakura taba balle ku.
duk yadda kamal yaso daurewa abun yanaso yafi karfinsa
yace "zamu iya tafiya yanxu ka gama?"
"Eh kuje kawai zan tura maka sauran daga baya akwai maganar abuncin da takeci.
ya furta cikin gadara
tashi kamal yayi ya fito
*JIDDERH CE*💗
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826