Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 24174 words

Chapter 4 - Hatsabibiya Jiddah hausa novels .txt

Ads the beginning of article before Image

JIDDA   

02 Jun 2024

347

Ads at the middle of Article

bak'i ne suka zo gun Baba kyara, shine suka sani.
yanzu ma Mamarsu ce taban wannan kudi nasai Abunci."
ta fadi tana mika mata kudin dubu ukun

Mamaki ya kama Sahura da Fatima lalle koma suwa ye suka zo to suna da hali, inba haka ba waye ze baka kyautar dubu uku awannan lokaci sai wanda yake dashi.


Jidderh Tace "sauri nake Fatima ki karbi kudin kije kasuwa ki yanko kayan makaranta irin nawa zan kawo miki wani kudi da zaki shiga makarantarmu, insha Allahu."
daga haka ta fita bata jira mgnr su ba


"Allah ya shirya. shine abunda Sahura tace domin tasan wace Jidderh tin tana jaririya kuma har yanzu bata sauya ba.

Murna Fatima tashiga yi ta kuma kara san yar uwarta ta har raita, duk da jininsu be hadu ba, dan halin ya banbanta sosai tsakaninsu.




tayi lattati sosai sanda tashiga makarantar har malamai sun shiga cikin Aji kowa ya fara abunda ya kawoshi


Ajinsu ta nufa tayi sallama malamin da ke Ajin ya amsa yana k'are mata kallo

Yace "daga ina haka, sai yanzu kikazo?


Tace "Baba na ne beda lafiya.


cikin tausayawa yace "Ayya sannu, wuce ki zauna Allah yabashi lafiya."


haka de ta wuni cikin makaranta har aka tashi tana tunanin mai kuma zata tarar inta koma


kamar kullum haka tayi sallama cikin gidan ta samu Saude na girki Hajiya Binta kuwa barci take


Tsaki tayi Tace "wlh da nasan barci take ba zanyi sallama ba, dan banga wache zanwa sallama ba.
Saude Tace "tinda ni kafira ce ai ba zakimin sallama ba, Shegiyar Tsinanniya, Insha Allahu zaki gamu da duniya sai ta juyaki, munafuka."


"Hhhhh Au da kee Saude wai musulma ce? tbb, wlh ko da wasa karma ki kira kanki musulma. zagi kuma duk kinsan wanda kikewa."


Salis jin sun fara ya futo yace "Jiddeerh meye haka daga dawowarki har kun fara?


Mama Saude dan Allah kidena biye mata tinda de bazata barmiki ba kinsa ni kema .


Jin Hajiya Binta ta farka tana salati yasa Jidderh cewa "Yaya Salis ya jikin Kawu Kamal kuwa?


Salis ya yi mamaki dan yariyar tafi karfinsa yace "da sauki sosai.


"Ayya Allah ya bashi lafiya, na matso naga ya warke wlh amma mutum kullum yana zaune gu d'aya ai babu dadi. ta karshe cikin kissa


Hajiya Binta tace "Jidderh Allah ya miki Albarka, yadda kike kulawa da lafiyar mujinki tin yanzu nagode sosai da kulawa.


cikin had'a baki Saude da Salis suka ce mujinta kuma Hajiya?"


Kwarai kuwa na nemar masa Auran Jidderh harma mahaifinta ya bamu.cewar Hajiya Binta


daga d'aki Kamal yana jin duk abunda suke fadi yana ji cikin zabura da kid'imewa


yace ........




*JIDDERH CE*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*
©


*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️1️⃣1️⃣


.....Cikin sauri Salis ya tarin Kamal ta hanyar rufe masa baki dan yasan abun bazeyi kyau ba, dan Kamal yadda ya tsani Jidderh komai ze iya furtawa, yayin da Hajiya ma zata zartar da hukunci cikin fishi.


Hajiya Binta tace "Jidderh maza je kiyi sallah kizo muci abunci kinji."


"To. shine abunda Jidderh ta furta jiki duk yayi sanyi dan taji girman abun har rainta


Saude kuwa har raita taji ciwan Jidderh zata auri mai kudi, kuma tadau alkawarin inde da ranta auran nan bazeyu ba, dan so take Jidderh tasha wahalar rayuwa ta futa hayyacinta tukum za taji dadi .


Bayan tayi sallah jiki duk yayi sanyi sukaci abunci da Hajiya Binta wanda da kanta ta girka abunta dan bata yarda da girkin Saude ba. taga kiyayyar jidderh cikin e'donta ynz .


Hajiya Binta tace "ki gama kirakani kasuwa naga yadda take.
"To. Jidderh tace


Bayan sun gama Jidderh ta shiga ta shirya cikin wata atamfa riga da siket nan girmanta ya kuma futowa kamar ba yar sha hudu zuwa sha biyar ba,
dan Jidderh akwai sura sosai shiyasa zaka mata kallan tafi Fatima kuma fatima ce Babba.


futowa tayi ta cewa "Hajiya na gama mutafi .


duk da atamfar ba sabuwa bace amma ta mata kyau sosai da sosai Jajiya tace "Masha Allahu Jidderh kinyi kyau san barka.


dariya kawai jidderh tayi dan kunyar hajiya takeji babu yadda zatayi ne kawai


futowa zukayi suka hau mota Hajiya ke tukawa Jidderh kuma na nuna mata hanya


Cikin zabura Kamal ya hankad'a Salis yace "meye haka salis?
Salis yace "Oga mubi komai asannu, kayi hakuri kabi Hajiya yadda takeso, kin binta kasan me ze biyu baya .


Kamal Yace "wlh ko zan mutu ya'u ynz zanbar garin nan. babu wanda ya isa yamin auran dole auran ma da d'alibar shedan ballazagar yariya tace wai tamin kamu ?.


Salis yace "haba Oga, tafiya ynz kuma pls dan Allah kayi hakuri kawarke tukum mutafi, cikin kwanciyar hankali .


Oga rai A bace yace "Salis wlh na kuma minti uku A Agarin nan mutuwa zanyi, tashi mutafi. yafadi yana shirin mikewa amma ya kasa


Tsorata sosai Salis yayi yace "Oga..


Be karasa ba Kamal ya da kamasa tsawa yace "Kamani kafin sudawo muntafi inyaso ta zauna ita agarin .


haka Salis ya kama Oga ya futa dashi zuciyarsa sam babu dadi.


Cikin Ikon Allah har ya sashi mota babu Saude nan ya dawo ya kwashe komai nasu yasa mota sannan yaja suka bar garin cikin wani yanayi


Hajiya kuwa kasuwa suka shiga tayiwa jidderh siyayyar kaya masu yawa na sawa harda shijabai da takalma ta kashe mata kudi masu yawan gaske sannan suka nufi gida


zuwansu yayi dede da zuwan Mlm Kabiru daga kasuwa


futowa sukayi daga cikin motar Jidderh tadau kayan ta shiga gida dasu


Mlm Kabiru tsayawa yayi suka gaisa da Hajiya Binta suka shiga cikin gida tare


Mlm Kabiru ya nufi d'akinsu Kamal amma da mamaki babu kowa ciki har kayan babu


"Saude!! Saude!! Saude!! Mlm Kabiru yake kwallamata kira


futowa tayi daga d'akin da a'lama barci take


yace "Ina yaran nan suka tafi ?"


"Suwa fa? cewar Saude


Su Kamal da Salis naga ba kowa cikin d'akin har kayansu babu shi." cewar Mlm Kabiru


Saude ta dafe girji tace "wlh bansani ba, ni barci nake.


Hajiya Binta tace "Mlm muyi magana man awaje.

"To.
shine abunda Mlm Kabiru yace jiki duk yayi sanyi.


waje suka futa tace "dan Allah da Annabi kamin alfarma d'aya kaban auran Jidderh yanzu. amma ba tafiya zanyi da e'ta ba, anan zan barta kar kace a ~a Mlm katemakamin .


Mlm Kabiru yace "lafiya kuwa Hajiya aure da yamma babu wanda yasani?


Tace "zasu sani in lokaci yayi, durkusawa tayi agun tana makiya kan ya yarda adaura yanzu.

Ganin girmanta yasa Mlm Kabiru ya yarda da auran yanzu amma da sharadin bazasu tafi ba har sai yagawa mahaifiyarta tukum .


Hajiya Binta tace "komai daga baya ne, Inde anyi auran shikenan .


Mlm Kabiru yace "daman sallahr la'asar za ayi bari bayan ankidar adaura auran sai muje dake gidan mahaifitarta ki gaya mata komai da bakin ki dan itama tana hakkin kanta.


Godiya sosai Hajiya Binta tayi ta dauko kudi dubu dari tace "Ga sadaki, ta dauko dubu goma tace asiyi alewa da goro adaura auran dashi."


Mlm Kabiru yayi godiya ya karba ya tafi yana tunanin abunda yasa Kamal suka tafi besani ba.

komai Mlm Kabiru yasiyu na daurin aure ya taho dashi masallaci


Bayan anyi sallahr la 'asar ne liman ya sheda auran Hauwa M kabir da Kamal Alhaji Fahat, bisa sadaki nera dubu dari chef.


mamaki kowa yafara ganin babu damar tambaya yasa kowa rike gulmarsa ya yayi gaba


*jiddeerh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️1️⃣2️⃣


........Mlm Kabiru ya dawo cikin gida cikin farga ba da kuma darurar yadda zasu kwashe da Sahura mahaifiyar jidderh.

Hajiya Binta ta tareshi dan hankalita be kwanta ba, so take taji andaura auran sannan burinta ze cika.


Tace "yah Mlm Kabiru angama komai.?

Klm Kabiru yace "Angama.


duk abunda sukeyi tsakar gida sukeyi, amma daga Jidderh har Saude babu wanda ya gane abunda suke nufi da maganar tasu.


Hajiya Binta godiya tashiga yi babu sausauci har ta bawa Mlm Kabiru tausayi .


Saude taji gabanta ya fadi rass! tace "Mlm lafiya kuwa naga hajiya sai murna take? ko angano inda su kamal suke ?"


Mlm Kabiru yace "lafiya kalau sai alkhari, su Kamal kuwa an samesu shine godiyar da takeyi .


Jidderh kuwa aranta take cewa daman ya mutu, mai shegen jikan masifa,da farar fuskarsa.
Ni wlh da za'aban wuka na kashe mutu d'aya a duniya to da shi zankashe na tsani mutum mai girman kai mtsss.


Mgnr Hajiya Binta ce ta dawo da e'ta daga tunaninta


"Mlm muje gidan muji ta bakinta, dan gobe na kesan tafiya gida .


"Hakane kuma hajiya mutafi to.


futowa sukayi suka hau motar Hajiya Binta domin zuwa gidansu Sahura


Suna futa Saude tace "Mtsss A sara, su Mlm anga masu kudi har wani biyayya yake mata, Allah yasa masu yankai kaine.


"HHhhhhhh Jidderh tayi dry Tace "danma munsan asalin komai tin kina budurwa nake da tarihinki, har yawan gidan Gala, da Gidan barasa nasani, har auran Salele nasani, san zuciya yasa aka futo daga gidan Salele sabida beda abun hannu aka auri mai kudi sai kuma gashi an aura kuma kudin ya kare daman da farar kafa akashigo.


"La~La~La Jidderh wlh sai na karyaki agidan nan dan Ubanki, waye ya gaya miki wannan maganar? shegeya marar kunya.


ta nufo Jidderh gadan~ gadan zata daketa Jidderh tasa kafa ba tare da Saude ta kula ba ta harde ta Tim, ta fadi ashe akwai tabarya kuma kanta ta fadi kafar tayi k'ara da a'lama karaya ta samu


Ihu Saude tasa wanda lokaci d'aya sukayi da Jidderh


take akafara shigowa jin Ihu biyu lokaci guda


"Lafiya kuwa? ake tambayar Jiddderh ganin Saude rike da kafarta tana cigaba da Ihu wayyo kafarta, wayyo kafarta.


Jidderh tace "Mama Saude ce zata dake ni kuma bata kula ba ta fadi. ta karshe cikin kuka


mamaki kowa yafara yana jinjina bakin halin Saude


Jidderh tace "Sannu mama Saude bari na doba kafar ko kinji ciwo.


zuwa wannan lokaci Saude bata gane na kanta balle bakin magana


mutane sai tsine mata suke wasu kuwa cewa suke Jidderh karta kulata, ta barta agun tinda e'ta muguwa ce makira.


Jiddeeeerh tace.......




*jiddderh ceeee*🙋‍♀️


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️


*HATSABIBIYA JIDDERH*

*NA JIDDERH*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️1️⃣3️⃣




......Jidderh Tace "baka biye ta mutum, bari nagani Allah yasa bataji ciwo ba.


takarshe tana share hawaye na kissa


"Allah yasa ta karye gida tara😱 cewar wata mata dake bayan Jidderh tinda e'ta muguwa ce azzalima, mai bakin hali sai kace kanki kad'ai ake zama da yar muji amma kidauki bakin hali kinsawa ranki.


Jidderh bata ce kala ba, takai hannunta kan kafar ta danna da karfi saida Saude tasaki k'ara da futsari atake .


Tace "Sannu Mama Saude, naga kamar kinji ciwo bari Baba yazo ya doba yagani ko targad'ene. amma da magani d'akinsa bari nadauko na samiki koh zakiji dama ~dama.


tashi tayi ta shiga d'akin domin dauko maganin


mutanan gun kowa ganin Imanin Jidderh suke da kuma hankalinta


futa sukeyi d'aya bayan d'aya cewarsu babu amfanin tsayawa tinda mugunta zatayi ta fada kanta. sai Allah yakara suke mata.


loko ta dauko ad'akin Mlm Kabiru ta fito ganin babu kowa sai Saude ta saki murmushi tace "haka nakeso.


gun Saude tazo ta kama kafar tashafa mata loko guda A kafarta, Saude Ihu take Ihu take sosai babu wanda ya kuma zuwa gunta balle yatausaya mata


Jidderh kuwa sai da ta gama tace "kitina da, tarihi ne ya maimaita kansa,ynz wasan ze fara ni jidderh sai na baki mamaki.


ta juya ta barta gun ta suma




Klm Kabiru kuwa bayan yakai Hajiya gidansu Sahura yace "kishiga tana ciki kimata mgn, ni ina kofar gida .


Hajiya Binta tace "to, babu damuwa bari nashiga.
sallama tayi Fatima dake wanki ta amsa mata cikin sakin fuska ta mata iso zuwa cikin d'akin Sahura


kallon kama takewa Fatima da Jidderh tace "kenan su biyu ne yaran nan ?


Sahura ce ta katseta Tace "sannu da zuwa, zauna man .


"Lah babu komai, da mutum mukazo yana kofar gida.


cewar Hajiya Binta


"Lah mai yasa baze shigoba, nida ba aure gareni ba balle nace mujin ya hana. fatima jekice yashigo cikin gida


cewar Sahura


"To, bari nasaka shijab dina."

Shijab ta dauko duk Hajiya Binta na binta da kallon tukuma


Fatima ta fito kofar gida e'do biyu sukayi da Mlm Kabiru


da gudu ta juya gida tana kuka tace.......




*Jiddderh ce*


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️




*HATSABIBIYA JIDDERH*


*NA JIDDERH BEAUTY*




*naji dadi sosai yadda kuka damu da lafiyata ngd ss allah yabar kauna*🥰🥰🥰


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*


_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826


بسم الله الرحمن الرحيم...


🅿️1️⃣4️⃣




.......Cikin kuka Fatima tace "Umma Ba..Ba...Ba...


A zabure Sahura tace "waye ba kuma? kinshigo kamar ankoroki .


Hajiya Binta Abun yadaure mata kai sosai tace "kinga wani mutum a waje yanzu?


cikin kuka Fatima tace "Eh.


Hajiya Binta tace "Ikon Allah shikike gudu ko wani kika gani daban?


Fatima bata ce komai ba, sai gabanta da yake faduwa ga kuma kuka bata dena ba.


Sahura ganin kamar bacin lokaci ne yasa ta fita daga komeye takewa kuka
kofar gidan ta futa daman da shijab jikinta inda Fatima ta barsa tsaye nan ta sameshi amma ya juyar da kaisa gefe duniya yanzu ta masa zafi A ce yarsa ce ke gudunsa kamar taga kura? lalle duniya abar tsoroce kaguji aikata abunda ze zame maka dana sani gaba.


duk da juyarwa bayansa hakan besa Sahura kasa ganesa ba, amma sabida ta tabbatar yasa yasa taje gusa dashi tace
"lafiya mlm?


firgit Mlm ya dawo daga duniyar tunani jin murya da harya manta rabon da yajita.


kasa mgn yayi sai hawaye da ke zuba e'donsa .


Sahura tace "tare kuke da matar da take ciki? ko kowa tafiyarsa daban?


d'aga kai yayi babu bakin mgn
juyawa Sahura tayi cikin gidan raita yana mata zafi tana tuna kalaman Mlm Kabiru na karshe gareta.


Hajiya Binta na zaune inda take ta rasa tunanin mai zatayi kan wannan labari sai ganin Sahura tayi ta shigo rai abace kamar ba e'ta ce ke dariya ba.


tace "bewar Allah tare kuke d na kofar gida?


Hajiya Binta tace "eh, tare muke lafiyade ko?


Sahura tace "kusan ba haka ba, tashi ki futarmin A gida, ya gaya miki lfy ko akasin haka"


Hajiya Binta tace "haba bewar Allah nifa bakuwa ce, be kamata nashiga rikincinku ba, kiyi hakuri ki saurare ni muyi mgn ta fahimta.


"Babu abunda zata saurara, yanzu kije gunsa ya karasa miki lbr da bakinsa.


Jin mgn A bayansu yasa su jiyawa dan ganin mai mgnr dan basuyi tunanin shigowar wani ba.


Jidderh ce tsaye ko d'ar babu A fuskarta balle tsoro ko dana sani.


Hajiya Binta tace "Jiddderh kece da wannan mgnr ko baki da lafiya.


"Ras nake,


Hajiya babu abunda nasha sai ruwan randa balle kice banda hankali, kan Uwata babu abunda zan saurara dan haka ki koma garesa yabaki lbr abunda ya shuga Abaya."


Hajiya Binta jiki duk yayi sanyi haka ta juya ta nufi kofar gida jiki babu karfi.
amma cikin rainta mamakin Jidderh take ayya kuwa bata da iska?
gaskiya Jidderh bazata mata haka ba, saide ko aljanu gareta sune suka mata futsara ba jidderh ba .🤔


da haka taji zuciyarta ta mata sanyi


Mlm Kabiru na zaune yarasa mai yake masa dadi yanzu


jin sallamar Hajiya Binta yasa shi mekewa yana goge hawayen dake kan fuskanrsa


yace "kinfito mutafi ?"


Hajiya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads