Showing 12001 words to 15000 words out of 24174 words
Chapter 5 - Hatsabibiya Jiddah hausa novels .txt
Binta tace "Eh, amma inasan idan munje gida kaban lbr rayuwarka ta baya gaba d'aya.
shiru yayi yana nazari yace "babu komai Allah ya kaimu lfy.
mota suka shiga tajah sai gida
bayan sunje sunci Abunci sunyi sallah suka shiga d'akin Mlm Kabiru suka zauna
Mlm Kabiru ya numfasa, yace zan baki lbr komai amma dan Allah karki gujeni ko kijuyan baya kidauka haka shine kaddarata."
Hajiya Binta tace "babu komai, muje zuwa."
*Nima jidderh na zaune danjin farkon labarin* 📃
*jidderh ce*🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH BEAUTY*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
1️⃣5️⃣
.......Mlm Kabiru ya kyara zama yace "Hajiya baya ban aikata mai kyau ba, duk da akwai makirci na mata da kuma aikin asiri amma duk da haka da nima da nawa laifi, ni na bada dama shedan yamin jagora na aikata kuskure, san zuciya yajani na aikata abu mara akyau wanda baze kyaru kwana kusa ba".
Hajiya Binta tayi shiru dan gaba daya kalamansa yasa jikinta yayi sanyi, shikuwa mai ya aikata haka mai muni da baya san tuna baya.
Ta ja dogun numfashi tace "babu komai Mlm Kabiru kadauke ni tabbakar yar uwarka ta jini wache zan riki maka sirinka zan kuma temakeka ta kowache hanya Insha Allahu
Mlm Kabiru yaji dadi har raisa duk da be tunanin b'arnar sa zata kyaru kwana kusa, amma hakan be hanasa murmushi dole ba.
*️⃣*️⃣*️⃣
"Oga yade tinda muka baru garin chan duk ka sauya?"
cewar Salis
"Hmm, nima bansan meye ba, amma de gaba na yana yawan faduwa, ga shi Hajiya taki dawowa.
Kamal ya furta cikin sanyi rai
magana Salis zeyi amma ganin wache ta nu fosu yasa yayi shiru
wata budurwa nagani ta nufosu irin yan matan nan ne wanda suka amsa sunansu yan mata tayi shiga ta alfarma jan yadi ne jikinta amma fa dinkin ya kamata sosai, kamar ta motsa ya farke ga wani takalmi mai tsani kafarta, fusakar tasha meaup ga uban gilas a e'donsa ta hadu iya haduwa karasowa tayi gun cikin yanka da kararraya tazo kusa da Kamal ta tsaya ko sallama babu cikin yanka tace "Honey ya jikin naka ?"
Banza yayi da e'ta ya juyar da kai sabida sam d'abiun ta basa burgesa, amma kamarta ace ba tasan matsayin sallama ba tirr da wata rayuwar.
Tace "yaran Oga mai ke damunsa ne tinda kuka dawo naga duk ya sauya?.
ta fadi tana juyawa garesa
Salis Yace "babu komai Beby kinsan har yanzu jikin da saura, kibashi hutu tukum inaga hakan zefi amma yanzu yana bukatar hutu sosai.
Tace "hutu wanna kala? bayan Dady yace yana dawowa za'a mana aure, yanxu tinda ya dawo ai shikenan banjin auran ze haura two week nan gaba."
Kamal yace "kee kina da hankali kuwa? wa zaki aura two week din?" yafadi cikin tsawa
kallo sa tayi e'do cikin e'do tace "Kamal Dr Fahat zan aura, nan da two week kasawa raika Beby bata rasa abunda takeso, kaina ke so kuma kai zan aura kashirya kafin lokacin."
daga haka ta juya bata jira amsar saba
Salis yaja ajiyar zuciya yace "Oga kayi hakuri kawai ka aure yarinyar nan, kar haka ya baka matsala kasan waye Ubanta komai ze e'ya kanka."
Cikin zabura Kamal yace "Ubanta Uba na ne? be e'sa ya sani na auran mara tarbiya ba."
In kuwa yayi gangancin haka wlh zeyi dana sani gaba .
"Duk da haka Oga kasan Ubanta de Gwamna yake nema, wanda muke tunanin shi za'abawa kujerar kayi nazari de gudun afkuwar matsala. cewar Salis
"Mtssss.." shine abunda ya furta
*muhadu anjima*
*jidderh ce*🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️1️⃣6️⃣
........salis yace "oga kenan, duk yadda kadau abun ba yafi haka wlh, yarinyar nan sai kabi a hankula da ubanta domin kasan waye shi."
"wai ni duk mazan duniya sun k'arene da sai ni zan bawa yarsa? ni sam bata cikin matan da nake da ra'ayin aura kaga kuwa dole su hakura subarni da abunda ke damuna ayanzu。"
wasu motoci ne suka nufisu gusan guda goma jere wanda kana kaninsu kasan ba kalar talaka bane, dede gun su kamal motocin sukayi paking
sojoji ne suka fara fitowa sai yan sanda da kuma sauran masu tsaran lafiyar na ciki
jeruwa sukayi suka zagaye gun su kamal ya zama suna tsakiyar su
salis banda zufa babu abunda yake yi yayi da kamal ko ajikinsa
kusan minti goma da zuwansu sanna aka bude motar kafarsa yasako kasa "wow takalmin ya hadu kasan kudi yayi kuka jiki fitowa yayi yasha wata danyar shadda mai tsadar gaske mai karatu ku raya yadda shadda gwamna zata kasance. 👌🏽
Cikin kissa ya fito fuskar nan daure babu a'lamu fara'a garesa, kallo d'aya zaka masa kaga tsantsar kama da sukayi da Beby
tafiya yake kamar besan takawa kasan gwamna da jin kai haka ya tako har zuwa gun Kamal da yake zaune kamar gunki yana kallansa
Salis kuwa kusan suma yayi da tsoro dan beta b'a ganin gwamna ba sai ya'u
Cikin gadara ya musu wani banzan kallo kamar yaga kashi ya juyar da kai
Sanna ya juye ya kuma kallansu A zuciyarsa kusa cewa yayi "Babu lefi yaran yana da kamala, amma duk da haka banga abunda Beby ta gani ta nace ba? har take neman haukacewa kan wanan yaran. "Mtsss. shine abunda ya furta afili
Yace "kai ne Beby takeso ko? bude kunne kajini Beby bata furta tana san abu face ta samu, duk wuyarsa duk saukinsa.
dan haka na yanke hukunci ka gayawa manyaka ranar Asabar daurin aure, da two week nace yanzu tafiya tasame ni ta gaggawa dan haka ya'u muna Alhamis, Asabar ne daurin aure .
sannan bana bukatar komai gunku har gida da komai na aure na yafe,bana mgn biyu nariga da na yanke hukunci kan haka.
har ya juya sai kuma ya dawo yace "ban gaya maka tame ba 8:30 am shine lokacin da na kesan auran ya kasance ba ka da zab'i sai hukunci na."
yana fadi haka yajuya bejira amsar su ba ya juya ya koma motarsa
mota suka bude mai yashiga suma suka shiga suka barsu gun
Salis ya numfasa, yace "Tabb, akwai aiki kenan .
*mukoma labarin mlm kabiru muji yadda takaya*
*jidderh ce*🖊️🖊️🖊️🖊️
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️1️⃣7️⃣
.........Mlm kabiru yace "kamar yadda kika sani suna na Kabiru ni haifanfan garin Wudil ne A wata unguwa mai suna kofar Yamma .
Nayi makarantar Allo cikin aminci da kuma kwanciyar hankali har nasamu na sauke Alkur ani mai girma
mahaifina malamin makarantar Allo ne malami ne sosai wanda yayi linkaya cikin ilimin addini, mu tara ne gun mahifina duk kanmu uwar mu daya ubanmu d'aya,
Ni ne babba sai kuma kannena mata biyar maza uku
sunan mahaifina Mlm Abdullahi mai tafsiri mutum ne mai tarin almajirai yan gari da kuma na wajan gari
bayan shekara shida mahaifina ya bani tawa makarantar da kuma almajirai ya ware ni kenan, kofar gidan su Sahura shine yazama gun zama na domin bishiya ce babban A kofar gidan
bayan wasu watanni soyayya mai karfi tashiga tsakanina da Sahura har manya sun shiga maganar ansa ranar aure kasancewar kowa yasan kowa tinda unguwa daya ce
Sannu ~sannu bata hana zuwa har lokacin aure yayi cikin ikon Allah Sahura ta zama mata ta kasancewar banda wata sana'a lokacin sai wannan karatu komai mahaifina ne yamin shi har gida yaban shine aka sa Sahura ciki
bayan wasu watanni muna zaune lafiya da Sahura lokacin harma ta samu cikin Fatima
wani lokaci da bazan manta da shiba muna zaune da Sahura k'anina yashigo cikin firgice yace "Nazo Mlm beda lfy.
cikin sauri na tashi na fita kafin muje rai yayi halinsa nayi kuka sosai amma babu yadda zamuyi haka aka masa sitira akaje aka bunne
bayan wata hudu da rasuwar Mlm lokacin Sahura haihuwa ko yau ko gobe kanne na suka tada rikicin gado dole aka raba gado kowa yadau nasa, gidan da muke ciki harda shi aka raba bansamu daki guda ba
dole mutashi domin sunce siyarwa zasuyi
sunkimin lamuni har Sahura ta haihu daga karshe kwana uku suka bani na bar gidan
Ranar ta uku ne muka had'a kayanmu duk muka kwashe nace Sahura takai gidansu ajiya zamuyi tafiya insha Allahu zamu dawo mu dauka
haka akayi cikin ikon allah muka baro garin wudil akwai abokina wanda mukayi karatu da shi yace min yana nan gari duk sanda natashi kai masa ziyara naje kawai dan haka ban b'ata lokaci ba muka hau mota sai Birniwa cikin Allah muka sauka lafiya
bayan munsauka na tambaye wani "dan allah kasan dan Asali?
yace "na Sanshi, gidansa zakuje?
cikin farin ciki nace "Eh,
yakira yaro yace "kuje ya kaiku."
*jidderh ce*💞💞💞💞
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
*Group na jummai one &two kumin afuwa wuta ke ban mtsala*amma zakujini insha allahu*💓💓💓💓
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️1️⃣8️⃣
......Yaran ya shige gaba mukuma muna bayansa ba wata doguwar tafiya mukayi ba muje gidansa
"Nace wa yaran shiga kace ana sallama da mai gidan." yaran yashiga ya gayi abunda na gaya masa
tare suka fito da Dan Asali gani na ba karamin murna yayi ba game da mamaki .
Cikin Gida ya mana iso muka shiga matarsa ta karbesu cikin mutumci da kulawa .
Bayan munhuta na ke bawa Dan Asali labarin komai da ya faru dan banda shakku kansa nasan ze temakamin
Ya Numfasa, yace "Allah ya kyauta, ya rabamu da sharrin zuciya, Inba zuciya da shed'an ba waye ze tozarta nasa? Uwa d'aya Uba d'aya .
amma yanzu tinda haka ta kasance sai kazauna anan gidan tinda muna da d'akin da ba komai cikinsa sai A kyara shi kashiga ciki har ta sauka kai kuma sai kana bina shago daman ni d'aya ne in bananan rufewa nake amma tinda kazo shikenan."
Godiya na masa sosai haka Sahura ta masa godiya bisa karamcin da ya mana.
Bayan wata guda Sahura ta haihu ta haifi y'arta mace wache taci sunan matar Dan Asali wato Fatima anyi komai na suna yadda al'adar garin take Sahura tana samun kulawa sosai gun Fatima
ta fanni na kuwa harkar kasuwa kullum budewa take fiye da tunanin mutum,
Bayan shekara guda komai ya tafi dede domin nima har gidan nan nasiya wanda har yanzu muke ciki
Sahura ta koma ciki suke rayuwarsu cikin farin ciki sa y'arta.
Wata rana ina zaune shago sai ga wasu mata guda biyu sunzo siyan kaya
kallo daya na musu zuciyata ta buga amma haka na kawar
d'ayar ce tace min "suna na Saude kaifa?
nayi murmushi nace "Kabiru suna na."
cikin yanga irin da yan duniya tace "sannu Mlm Kabiru amma nan shagon kane koh? naga kullum kaine gun."
nace "A~ a na mai Gidana ne baya zama shiyasa kike gani na kullum.
"Ayya sannu."
d'ayar ce tace "bamu kayanmu mutafi kun tsaya kuna shira."
kayansu na basu sukamin sallama suka tafi
tin daga wanna rana kullum sai Saude tazomin shira ko da siyayya ko babu haka zata zo ta zauna guna, tin bana kulata har yazama nasaki jiki da e'ta muna shira sosai.
bayan wasu watanni munshagu sosai Saude harma abunci take kawomin daga gidansu mu wuni muna shira babu ruwanta
duk hakuri irin na Sahura har ta gaji ta fara tambayata "Ina nake zama yanzu bana dawowa da wuri kamar da?"
*jidderh ce*
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️1️⃣9️⃣
......Nace mata aiki ne yakemin yawa A shago shiyasa baki gani na dawuri."
kasan cewar ban tab'a mata karya ba yasa ta yarda tace "Allah yashige gaba.
nace "Ameeee."
haka rayuwamu da Saude ta cigaba da tafiya
watara na muna zaune ta ke tambayata zan Iya auran ta kuwa?"
nace "haba Saude ina naga kudin auranki duk da baki gayan ke budurwa bace ko bazawara? duk zamanmu da ke."
dariya tayi tace "Ni bazawara ce, mujina ya mutu. takarshe cikin kuka
nace "Ayya allah ya masa rahama yasa ya huta ameeee."
"Amma mai yasa kikeso na aure ki, bayan kinsan inada mata harma da yarinya guda daya?
dariya tayi tace "Ai babu komai ai kishiya abokiyar zama ce, d'a kuma na kowa ne banda matsala da su, ko ba y'arka bace yar matar kace ai nariketa amana balle yarka ta cikinka ."
naji dadi sosai yadda ta nuna soyayyrta ga Fatima ta kuma cire kishi duk da ba kowache mace kisan mai mata ba.
tace "yade ko ban maka ba, naga kashiga tunani?
Murmushi nayi nace "haba Saude waye zece be sanki, bayan komai na jan hankali Allah ya baki. amma mubi komai asannu zanyi shawara da Sahura duk yada ake ciki zakijini."
take ta sauya fuska tace "Daman tace ne kai bansani ba, kamar ka amma har anshanyeka komai sai ka gaya mata gaskiya da sake."
take naji bansan bacin raita nace "kiyi hakuri gaya mata ne bakyaso to insha Allahu bazan gaya mata har sai andaura auran taji daga baya kidena kuka kinji .
Saude tace "Naji amma kasan auran baze dau lokaci ba, tinda de mu ba yara bane, balle mutsaya shiririta musaka wata guda ayi kowa ya huta .
nayi jim Nace "shikenan Allah ya kaimu lokacin, mukaci gaba da shirarmu har dare.
Bayan sati guda ta faruwar haka nasamu Dan Asali nake gaya masa aure zan k'ara yace "Aure kuma Mlm tin yanzu, ayya bakayi sauri ba ?"
Nace "A~ a ai ba yarinya bace, bazawara ce mujinta ne ya mutu harma mun dedeta dubu talatin zanbata kudin komai da komai .
Dan Asali yace "ba kudinba Mlm Kabiru kuna zaune lafiya da matarka kaje ka auro bala'i ka kawo gida, ta rabaka da matarka kuma bata rike maka y'ar kaba."
nace "duk munyi maganar da e'ta babu matsala insha Allahu."
yace "shikenan tinda ka dage, kaide ba yaro bane, kana da hankali da kuma ilimi dan haka kaji tsoran Allah ka kula da matarka."
*jidderh ce*🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
*HATSABIBIYA JIDDERH*
*NA JIDDERH*
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
🅿️2️⃣0️⃣
..........Komai na shirin aure mungama shi batare da Sahura tasan wani abu ba.
ana gobe daurin aure nazo da masu kyara domin suyiwa amarya fanti kamar yadda a'lada take
Sahura tace min "Mlm kudi kasamu ne naga kamar...?"
"kamar me? na katseta cikin hasala domin yanzu bata burgeni haushi take ban shiyasa ko magana bata fiye hadamu da e'ta ba: tin safe nake futa ban shigowa sai tayi barci.
tace "Allah ya baka hakuri Mlm."
daga haka bata ce komai ba ta koma d'akinta
Bayan angama na sallami masu aiki nima na futa na koma shago
Ranar jumma'a bayan ansauko a amasallaci aka daura aure na da Saude yayi da wasu suke mamaki wasu kuma suke cewa na daukarwa kaina kaya, dan bansan wace ba shiyasa na aura, duk ban kawo komai kaina ba gani nake bakin ciki sukemin .
bayan anyi sallahr insha'I yan kawo amarya sukazo da komai nata na jere
Sahura na cikin d'aki takejin kuda na tashi cikin gidanta cikin sauri nafito dan gani da e'donta, gud'a ake tayi kinsan taran mata balle da kishiya cikin gidan dole suyi dan