Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 22111 words

Chapter 1 - DANGINA FREE BOOK BY SECRET PEN.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article


DANGINA
*[AKA RABANI DASU]*






STORY &WRITEN




BY


ADAMA UMAR
SECRET PEN




07081940768






LOVE AND ROMANTIC STORY


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI




1️⃣


PAGE ONE


Zaune suke a falon kuna ganinsu kunsan suna tattauna abu mai mahimmanci ,yatsunra yana sarke a cikin na yar uwarta ta sake kallonta ta ce


Dan.Allah Hafsat ki amince da buƙata ta dan Allah bamuda wata mafita da yawuce haka babu abunda zamuyi mu goge lqifinmu a gareki saita wannan hanya pls ki taimaka


Kwarai Hafsat abunda zuwaira take faɗa miki gaskiya ne na roƙeki nima gani na durkushe akan guiwowina dan Allah ki amince da buƙatar mu


Fisge hannunta tayi daga yatsun yar uwartata sannan ta dauki jakarta ta kallesu kawai ta fita a gidan cikin hanzari sunanta suke kira amma ina ko juyowa batayi ba balle kuma ta sauraresu ,kallon zuwaira yayi ya ce


Mucigaba da jarrabawa insha Allah wataran zata amince kinsan sai mun mata uzuri yanzu tana cikin wani hali ,harna rasa da wacce irin fuska zan kalli hafsat wlh ,amma mucigaba da kokartawa insha Allah wataran zata amince


Hawayen dake zuba daga fuskarta ta goge ta ce


Haba hafsat kibani dama kibani dama mana mu goge babban tabon da muka miki ,ki amince mu cireki a cikin kuncin da kike ciki da bakin ciki


Tafaɗa tana kqra rushewq da kuka


Rungumota jikinsa yayi yana ban baki .


A banagaren hafsat kuwa Allah ne kawai ya kaita gida lafiya tana zuwq tayi park na motarta sannan ta fito ta nufi ciki gida ,tana shigowa ta hadu da amminta tana zaune tana karatuna alquran ta zare glass ɗin idonta ta kalleta ta ce


Wai hafsa lafiyarki kuwa ,gaba ɗaya yanayinki ya sanja wai me yake damun kine




Kwanciya tayi a kafadun wannan dattijuwa kana ganinta kasan mahaifiyartace ta ce


Wlh ammi na rasa ya zanyi dq zuwaira gaba day tasani a gaba akan wannan kudiri na ta nikuma nama rasa ta ina zan fara amincewa kai bazan ma faraba domin wlh ita da kanta zatayi nadamar faruwar wannan kudiri nata


Ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce


Gaskiya Hafsat bazan boye miki ba ,kinsan nidai mahaifiyar kice ,bazan baki shawarar da bata gari ba ,a ganinq kuma a abunda ya dace ni kaina ina mai baki shawarar da ki amince da bukatar zuwaira da mijinta wannan itace mafita a gareki


Zubur ta tashi daga kan kafaɗarta ta kalleta Ta fara magana


Haba Ammi kema haka zaki fada,yanzu kina daya daga cikin mutanen da zasu goyi bqyan wannan lamari ,gaskiya Ammi tunda kince shawara ba umarni ba gaskiya bazan yadda da wannan kudirin ba .


Tanq gamq faɗar haka tq tashi da hanzari ta haura sama ,Ammi tq maida glass ɗinta tq ce


Yaro yarone Allah ya ganar dake kamqn yadda ya nunqmun faidar hakan .




Yau tana da lecture around 8:00 shiyasa ta tashi ta shirya da wuri ko break batayi ba haka tayiwq Ammi bankwana ta fita tana zuwa makaranta ta nufi hall taji ankira sunanta a hankali ta juyo ta kalli me siran sunan ta ,dafe goshinta tayi ganin zuwairace ta kira sunanta ,agogon hannu ta ta kalla taga batada lokqcin bqtawa aikuwa ta wuce ta shiga hall ɗin batare da ta tsaya ba,wuri ta nema ta zauna tana jiran su gama lecture ta fito suyi magana don yau babu wanda zai rabata da hafsat matikar bata amince da kudirinta ba ,To abangaren Hafsat ma haka gaba daya tinani ta tsaya yi akan maganganun da ake mata ita gaba ɗaya kanta ya kulle kuma kwakwalwarta ta toshe bata hango abunda ake faɗa ba ganin tinanin bqzai kaita ko inaba shiyasa ta kwatsar da zancen ta maida hankali akan karatunta ,gqba daya lecture ta dau zafi shiyasa gaba ɗaya a gajiye ta fito amma me tana fitowa tayi karo da zuwaira tana jiranta kallonta takeyi kafun tai magana ta kariso inda take ta ce




Dan Allah Hafsat bazan gajiya ba bazan karaya ba sannan bazan haura ba matikar baki yadda da kudirna ba ,mena miki meyasa cike tsanata kumq kike ƙyamata ,shin guduna kikeyi


Ohooo haba zuwqirq meya kawo maganar nan da zakice ina kyamqrki yaushe mukayi dake inq gudunki kawai don naki amincewa da kudurinki shiyasa zaki yanke mun danyen hukunci haka gaskiya kiyu hakuri ,karki manta yadda muka taso dake tamkar yan uwa kudubq irin shakuwa da kaunar dake tsakaninmu kisani inaso ya daure harga yayanmu ,amma ki sani matikar kudirinki ya cika zai iya zama sanadiyar tarwatsewar muamalarmu ,hakan zai dawo gaba mai tsanani a tsakaninmu kuma harga yayanmu ,inqso ki bari Allah ya zaɓamun duk abunda ya dace dani a rayuwata dan Allah karkiyiwa Alla shishigi


Shiru tayi gaba dayata rasa me zata faɗawa kawartata hakan yasa ta fashe da kuka ta ce


Da kinsan alkhairin da nake hangowa da baki faɗi wannan zantuttuka ba


Shin wani irin alkhairi kika hango wanda ni nakasa hangowa pls allow me to rest banason damuwa


Bata jira me zatace ba ta nufi parking space tashiga motarta tayi gidq ,jiki a sanyaye zuwaira tabar makarantar tana nazqrin shin taya zata fara bullowa da kawar tata ta amince da ita .


Tana zuwa gida bata tsaya bata lokaiba ta wuce daining domin wata azababbiyar yunwa da take damunta serving ɗin kanta ta fara sanna tafara cin abincinta hannu baka hannu kwarya ,tana cin qbinci sai hoton lokqcin rayuwarta ta baya ya fara dawo mata ,tana tina yadda ta kasance da walwala da nishaɗi da farin ciki amma yanzu ya zama tarihi ,ture abincij tayi domin saitaji duk abincin ya ginsheta ,tashi tayi ta nufi dakinta ta ajiye hakarta ta kalli wayarta na ƙara ,dauka ta duba tsaki tayi ganin sunan my besty ya bayyana ɓaro ɓaro ,jifa da wayar tayi akan gadon kafun ta fara rage kayan jikinta ta faɗa bandaki ,tana shiga ta tsaya kallon kanta a madubi tana duba shin ta kara ƙiba kota rage shin tumbinta ya karu koya ragu wannan ta kasance dabiarta ce saida ta gama karewa jikinta kallo sannan ta fara wankan ,tana gamawa ta fito daure da alwala ta dauko wata doguwar riga ta zura ta tada Sallah ,tana tayar da sallah saiga Ammi ta shigo da waya a hannunta ,kara wayar tayi a kunnenta ta ce


Ayyah zuwaira sallah take shiyasa bata ɗaga kiranki ba amma idan ta idar zan hadaku


Shikenan Ammin na gode


Saida ta idar da sallah sannan tai afduointa ta shafa tasawa kofarta kry ta kwanta a lafiyayyen gadonta tana kulle idonta tana sauraron bugun xuviyarta da alama bacci takeso ya dauketa ,wayarta ce ta fara ruri da alamar neman agaji tsaki tayi kibata duba ba tasan wace me kira shiyasa ta dauko wayartasata a silent ta maids kanta ta kwanta har bacci ya dauketa .


Ba ita ta farka ba sai misalin ƙarfe 3:00 na rana aikuwa a gurguje ta tashi tayi wanka Hafsat kenan sarkin tsafta haka take kaman wata agwagwa.kullum cikin wanka take ,bata fitoba saida ta dauro alwala sannan tafito ta shirya ta nufi falo ,tqna fita ta tarar da Ammi tadan mike kan sofer maakaciyarsu nanna tana mata tausa karisowa tayi ta rungume Ammin ta ce


Kai ammi yau nasha wahala gaskiya shiyasa dana dawo ban nemiki ba


Na sani kuma naje dakinki a rufe nasan bacci kike abunda nakeso dake ki tashi ki dauko mayafinki inaso ki kaini anguwa


Shikenan Ammi amma bazamu jirq mu gabatar da sallar laasar ba saimu fita


Shikenan bari inje indauro alwala saura minti 5


Tashi tayi ta nufi dakinta ,kallon.Nanna tayi.macece mai dan shekaru don a ƙalla zatakai shekara 40 gashi tanada nitsuwa ga ilimi ita kanta tashi tayi taga Ammi da Nanna domin batai aure bama me gadin gidan aka aura mata sannan ya rasu ya tafi ya barta da yaro daya tilo dagananbata sake aure ba ko zancen aure Ammin tayi tayi harta gaji ,ajiyar zuciya tayi tace


Nanna dan akwai abunda nakeso in tambayeki kinga.dai ke babbace watakil kema ki hango abunda na kasa hangowa


Jinjina kai tayi ta ce


Ina jinki hafsatu


Kaman yadda kika sani Zuwaira ƙawata tace kuma...


Kiran sallah ne ya katseta ta ce.


Kibari hjy nanna idan muka.dawo nida Ammi zanzo har dakinki inbaki labari bari inje inyi sallah


Shikenan to Allah ya dawo daku lafiya


Tafaɗa tana mikewa itama ta.nufi dakinta ,bayan sun idar da sallah kowacce ta fito da shirin fita sannan suka shiga mota suka fita a gidan ,suna ciki tafiya Hafsat ta kalli Ammi ta ce


Ammi wai ina zamuje ne sai tafiya mukeyi


Murmushi ammi tayi ta ce


Gidan zuwaira.


Fuskarta babu alamar wasa ,hakqn yasa Hafsat tadan haɗe rai ta cigaba da.drinving,dede kofar gidan taja tai parking Ammi ta kalleta ta ce


Me kike nufi kina nufin bazaki shiga ciki bane kome


Gaskiya Ammi ni bazani ba.kije ki kawa...


Bata karisaba.kawai taji saukar mari kan kuncinta ta dafe.ta juyo a mamakance tana kallon Ammi.










Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*






STORY &WRITEN




BY


ADAMA UMAR
SECRET PEN




07081940768






LOVE AND ROMANTIC STORY


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI




2️⃣










PAGE TWO


tabbas Ammi tana.wasa da yara amma tanada zafi.kuma ga zuciya macece tsayayya akan yayanta duk da ta.kasance ita ta rainesu amma hakan baisa tarbiyyarsu ta lalaceba ,batayi magana ba ta buɗe marfin motar ta fita aikuwa Hafsat ta rufa mata baya domin taga babu alamar wasa alamarin Ammi .


Zaune suke a falon dukkansu suna kan rug itq kuma Ammi tana kan kujera ta gyara glass ɗinta ta fara magana kamar haka


Wato Abdulmallik komai ya faru mu daukeshi mu kaddarine daga Allah dan adam bazai taɓa maka qbunda Allah bai maka ba ,mu sani komai ya faru a cikin duniyar nan dama alƙalami ya rigada ya rubutashi don haka komai ya samemu karmuce wane ne ya mana ,Allah ne kawai yake iya yin yadda yaso da bawa saidai wani ya zama sila ,wanda shima a sanadiyar wannan silan zai gane ya shiga wata jarrabawa ce ,kusani dukkan mu musulmaine don haka bazamu taaya ɓatawa kanmu lokaciba mu yafewa juna komai ya faru ya wuce har abada banason daya daga cikinku ya kara kallon dan uwansa da abunda ya faru ,kuma naju dadin hukuncin da zuwaira kika yanke hakan ya nuna kinada kaifin tinani don haka inaso dukkanmu mu taru.mu rufawa juna asiri abun mun nan yazamana tuwona maina


Tunda ta fara magana Hafsat take hawaye tasan ba wani abu Ammi take ba.illa ta yarda ta amince da Abdulmallik amma anya zata iya aurensa kuwa shin dawani ido zatana kallonsa tabon daya mata bazai taɓa gogewa ba don haka bazai yiwu ma ta fara haɗa inuwar wre dashi ba.,saida Ammi ta gama koro zance sannan suka mata godiya ta tisa hafsat a gaba suka nufi hanyar gida ,a hanya take faɗa mata ta sani kozata rayu kozata mutu sai andaura aurenta da Abdulmallik don haka idan zata saki ranta ma ta sake ta amince dashi kuma tana gama makaramta zaayi aurensu nan da 6 month ,maganar ta doketa gaskiya me Ammi take nufi ,Ammu tana nufin zqta mata auren dole gaskuya bazwu yiwuba sannan zatai iya kokarinta na ganin ta cusa tsanarta a zuciyar Abdulmallik da matarsa zuwaira.


Suna komawa gida ta nufi dakinta tasa kuka ra rufe ,kukq kawai take me cin bataso ta tin rayuwarta ta baya amma y zame mata dole matikar zatana ganin Abdulmallik dole ta tina da wannan banzar rayuwar tanq cikin haka saitaji wayarta tana ruri tana dubawa ta saki wani kayataccen murmushi ta dauka wani kuka ne ya kubuce mata ta ce


My derling bro


Tq faɗa tanq fashewa da kuka ..


Rarrashinta yq fara domin ta saba mishi shagwaɓa duk lokacin da yakirata ,saida yasha aikin rarrashi sannan ta hakurayake tambayarta me yake damunta kaman zata fada masa abunda yake damunta saikuma tayi tinani zata iya tayar masa da hankali.shiyasa ta hakura ta boye masa domin tasan kalar zuciyar yayanta zai iya daukqr mummunan mataki wanda zai kaita ga shiga fushin ammi hira suka taba kadan sannan yakashe wayar ,sai taji sassauci aranta ba kaman daba .


Suna zaune a falo suna dan taba hira duk da ba sosai Hafsat take responed ba gaba daya kwakwalwarta ta cushe ta rasa taya zata bullowa wannan alamari kaman daga sama taji karar shigowar sako wayarta tana zudewa taga zuwairq ce ta.mata sako kamat haka


Gaskiya.kawata naji dadi sosai kuma na gode miki da kika amince da auren Abdulmallik bansan da wani baki zan miki godiya ba ki shitya yau.Abdulmallik zqizo kudan fita don ku kara fahimtar juna


Tsaki tayi wanda ita kanta batasan.tayi tsakinba mamaki take da alajabin wai wacr irin zuciya ce a kirjin kawar tata anya zuwaira tanada zuciya kuwa ,taya zata fara zaman kishi da zuwaira tabbas tasan tanada kishi bazata.duba wai don zuwaira kawarta bace babu damuwarta yanzu zqta.keta mata.rash in mutumci indqi akan abunda zuciyarta take sone amma qi batason Abdulmallik shit as take gamin bazata taɓa yarda ya zamo mijinta ba.kaman yadda ya cusa mata bakin ciki itama saita cusa masa koda kuwa zai mutu ne bazata taba.amincewa va ,haka taita zancen zuci har Ammi ta lura.da condition ɗin da take ciki sunanta ta kira cikin sanyin murya ta ce


Yanzu Hafsat bazaki cire damuwa a xuciyarki ba kenan kindinga ririta wannan maganar haba meyasa kikeso kija da ikon Allah kisani komai ya faru dake kaddara ce ta ubangiji babu wanda ya isa yayi miki abunda Allah bai miki ba don.haka ina mai. baki shawara ida zqku saki jiki ku fahimci juna to kisaki idan kuma zaki tsaya lusaranci ga fili ga mai doki bazan sakr shiga wannan maganar ba kinsan dai hukuncin da na yanke


Hawayen dake zuba a idonta ta share ta tashi ta nufi dakinta tai kuka saida ta koshi wani bacci ya dauketa ,kqman daga sama taji ana knowking kaman bazata budeba kawai ta mike ta bude Ammi ta gani tsaye tana binta da kallo ta ce


Kinsan kina da bako shine zakizo kihau bacci to maza ki tashi yana jiranki yanzu ki fito


Daga mata kai kawai tayi ta maida marfin kofan ta rufe ,dq badon fishin mahaifiya balai bane a gareta da wlh bazata fita ba amma babu yadda zatayi dole ta bishi ,ba wani shiri tayiba ta fito rike da mayafinta a hannunta ko sallama bata yiwa Ammiba ta fita a gidan ,yana jingine a jikin motarsa yana waina makullin motar kallo daya tayi masa ta dauke kai tazo taja ta tsaya batayi magana ,murmushi yayi ya ce


Barka da wannan lokaci hjy Hafsat ,kinfito lafiya duk cewa kin shanyani zaman jiranki amma banga kin jima ba domin na jima ina kallon kifa domin inga takunki mai jan hanka


Hannu ta daga masa ta ce


Wlh Abdulmallik wlh dabadan Ammiba kayi kaɗan in fito wai don kazo saidai kazo ja gaji da zuwa ka tafi ,kasani bana sonka kuma bazan taɓa sonka ba ,kaine namiji na fako dana tsana a rayuwata ina mai baka shawar kaje ka samu Ammi kace ka fasa aurena karmuzo munayi nadama nan gaba




Murmushi yayi ya ce


Shin bakisan kiyayya tana iya komawa soyayya ba kuma soyayya tana iya komawa kiyayya ,don haka a shirya nake domin na karbi kowanni irin hukunci daga gareki ,nasani Hafsat kowani mataki kika dauka a kaina bazaki huceba domi nasan na kuntata miki na bakanta miki gwargwadon iyaka amma ina neman yafiyarki kuma ina menan gafarrarki kiyi hakuri ki bani dama in bayyana miki soyayya ,ki bani dama in goge tabon dana miki ,ki bani dama pls kibani dama


Tsaki kawai tayi ba tare da tabashi amsa ba wannan Shi ake kira da ihu bayan hari wannan shi ake cewa nade taburman kunya Allah ya hana ramar da gari zai wayeta kalli Abdulmallik a matsayin mijinta da takalli wannan ranar gwanda ta mutu inyaso akai masa gawarta cikin gidansa ,tana cikin wannan zancen zuci taji ya ce


to shikenan tunda yanzu haushina akeji shikenan yanzu kizo muje inkaiki shopping ,pls kibani dama in kyautata miki koda sau dayane


Waye ni kasani bakada dukiyar da zaka sayeni da ita wlh ,badai ni kace kanason gani a matsayin mataba to kashirya duj ranar da natare a gidanka to bakinciki kunci da takaici ka shirya dasu keda kun kulla abota mai karfi ,don kaga tafiyata idan ka gama tsayuwa zaka iya tafiya .


Tana bude kofar sukayi ido hudu da Ammi tana zaune ta zuba mata idon ka da kanta tayi ta magana tace


Harkunje siyayyan ne
Shiru tayi ta fara inda inda tace


Zakije ku tafine kokuma sai nadauki mataki akanki


Batayi magana ba ta juya tana fita takallesa ya juya babu shiri ta shiga bayan motar ta zauna kallonta yayi baiyi magana a yaja motar suka bar gidan ,wani babban mall ya kaita ya ce ta zabi duk abunda takeso bata kulashiba ta shiga ta fara dauko kayayyaki komai hannunta ya dauka akai saida ta dauka saida ta cikq basket guda biyu har suka euce kata sannan sukazo akayi bill suna fita ta tara almajirai d mata ta fara rabamusu saida ta karar dasu tas sannan ta juyo ta kalleshi tai tsaki ta nufi bakin titi aikuwa hakan yayi daidai da zuwan me nafef ta shiga saida ta kusa isa gida ta tsaya a wani dan karamin provision ta siyi kayan ciye ciye ta mishi trnf ta wayarta sanan ta nufi gida tana zuwa ta ajiye Ammi kayan ta nufi dakinta .




Gaba daya tanajin haushin kanta meyasa ta bishi suka fita ai wanan kaman taci amanar julabib ne shin idan ranar alƙiyama ta hadu a julabib mezata ce masa shin ta lalata qljannar daya bata ,ce masa zqtayi tayi aure akan nasa me hakan yake nufi wayyo Allah wlh ko duniya zata tsaneta bazata auri Abdulmallik ba haka ta wuni kuka gaba daya tana cikin damuwar da babu mai fahimtarta babu wanda zai fahimci halin da take ci




Nifa fans tambayoyina sunfi nqku


Shin meyasa Ammi ta dage akan auren nan duk da yarta bataso


Shin wani abune Abdulmallik yayiwa hafsat data tsaneshi


Shin waye julabib


Shin waye yayanta kuma yana ina


Shin abunda zuwaira takeson hadawa bazai dameta ba kuma kundaiji furcin hafsat


Shin wace Nanna kuma waye danta


Ku biyoni akwai sarkakiya me yawa wanda ni kadai nasan yazan warwareta .


Share

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads