Showing 1 words to 3000 words out of 45461 words
Chapter 1 - NISFUL HAYAT Book Complete by Mimi queen.txt
NISFUL HAYAT.
Story & written ✍
Sadeeya Isah (Mimi queen).
MANAZARTA*
WRITERS ASSOCIATION
Sadaukarwa ga.
My twin sis (Drmeenert Umar usman)
Alherin Allah yasameki duk inda kike.
Bawanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani._
_Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata_🤷♀️
Bismillahir rahmanir raheem.
______________________
Nagodema Allah daya bani ikon fara book dinnan yanda nafara lafiya Allah kabani ikon gamawa lafiya.
Allah kabamu ikon amfani da gargadin dake Cikin book dinnan kuskuren dake ciki Allah kabamu ikon watsi dasu.
Marubuciyar.
RAYUWA SAI DA KE (Endless love).
LABARINA (True love).
BARRISTER SHULAIFAT.
SON ZUCIYA (Biased).
And now on NISFUL HAYAT.```
Allah bamu ikon amfana amin ya Allah..
Page 1&2.
Kasar Agadas
Gidan masarautan cike yake makil da mutane dan har bama ka iya kutsawa cikin fadan.
Sojojine tako ina kewaye da gun, motocine gasunan birjik sun cika parking area na masarautan, yayinda wani buzu yafito daga cikin fadan nade da rawani da alama masarautan na buzayene,
Sanarwa yafara akan ayi hakuri an kusa daura auren.
Mamaki nafara dama daurin aurene yatara wa'innan dandazan manyan mutanen dan inna gani da kyau harda sojojin America dana kasashe da dama a gun ga manya manyan mutane daga kasashe da dama.
Kutsa kaina nayi cikin fadan dan gano daurin auren waye akeyi haka.
Da kyar nasamu na kutsa kai ciki.
Mutanen da suke ciki bazasu fi mutanen ashirin da biyarba badda fadawan da sojojin dake gurin.
Ido nafara bin mutanen dake cikin fadan dan gano shin waye Angon nan.
Sarkin buzaye na zaune bisa kujeran sarautan shi ta hannun hagunshi kam wani farin buzune dogo yasha kayan buzaye da nadin su da alama yanada alaqa da bikin kusa dashi wani wani babban mutum ne cikin shigan manyan kaya blue Riga da malummalum kallo daya zaka mishi kafahimci ba Karamin mutum bane naira ta zauna.
ta gefensu wani buzu ne rike da carbi yasha nadi da alama liman ne.
Wani irin addababban kamshine yacika fadan wanda da sauri nayi duba izuwa gefen daman me martaba wanda daganan nakejin kamshin.
Ya Salaam.......
Seda alkalami yafadi kasa.
Wasu hadaddun gayune su biyu sunsha fararen shaddansu wanda idan badan kasan suba seka rantse twins ne, dan sunyi bala'in kama indai ba kalura da en wasu banbanci dake tsakanin suba.
Kyawawane na ajin karshe kuma en hutu nasawa agaban jarida.
Sedai daya yafi daya haske sannan daya yanada cute one side dimple dayan kuma kallo daya zaka mishi kaga manyance a tare dashi domin shine babba yayinda be kai dayan fara'aba, sedai kusan girmansu daya suna bala'in kama sosai dogayene sunada lulu eyes, da dogon hanci ga dan karamin baki, kwantaccen suma.
Huuuu In short dai sun hadu.
Cute Murmushi _AADIL_ yake saki kasa kasa wanda yake haddasa lotsawan kumatunshi , juyawa yayi yana kallon dan uwanshi kafin a hankali ya shafi kwantaccen sumarshi kasa kasa cikin zazzaqar muryanshi Yace. "Bid wai ba za'a daura bane...."
Murmushin shima Aabid yayi tareda fadin. "Mekakeci nabaka na zuba......."
Be rufe bakiba yaji ance '
"Waaliyan angwaye dana amare su matso kusa".
Abie mahaifinsu Aabid da Aadil dake zaune gefen me martaba kusa da baban amare yatashi a matsayin waliyin su ya karisa gaban fada.
Wannan buzun dake gefen me martaba da alama shine mahaifin amaren yayi duba ga kaninshi dake can gefe alaman yaje da sauri kanin nashi ya isa kusa da mahaifinsu Aadid.
Kasa dakai Aabid yayi yanajin wani irin mugun dadin dabe taba jiba yau ze mallaki _AYSHER,_ a matsayin mata.
Shima kasa dakai Aadil yayi shima yana tunanin wani abu a ranshi.
Ko minti goma ba'ayiba sukaji Anfara sanarwa.
```An daura auren AABID ABUBAKAR DA ZARAH ABDULLAHI dakuma AADIL ABUBAKAR TAREDA AMARYARSA AYSHER ABDULLAHI bisa sadaki naira dubu dari```
Da sauri dukkansu suka dago, danjin shin dagaskene abinda kunninsu yaji mushi, still abinda me sanarwan yasake furtawa kenan har sau uku dan a tunaninsu ko kuskure yayi amma garas sukaji ya maimaita kuma ba wanda yamai gyara, kenan auren ya dauru ba tantama.
Tuni jibi yahau ketowa Aadil danme za'a canza daurin auren bayan kowa yasan cewa shi Zarah ze aura Aabid kuma Aysher.
Hada ido sukayi sukayi saurin kauda kai ido Aadil yazubama Abie ganin ko a jikinshi se fara'a yakewa mutane.
Kasa yayi da kai yana saqa abubuwa da yawa a ranshi, Aabid ko kanshine yahau juya mishi yayi saurin sa hannu ya tarbe kan nashi.
Nan aka hau rabon abubuwan tabawa so ake ayi musu murna amma ganin dukkansu yanda sukayi kasa dakai yasa aka rabu dasu,
Se around two sannan fada tafara raguwa mutane sun fara tafiya wa'inda suke kasar waje suka fara shirin komawa.
Da kyar Aabid da idonshi ya kada yayi jajir ya iya fitowa sukayi sallama da mutane Aadil kam yashiga mutane.
Suma basu jimaba suda jama'arsu suka nufi airport domin dama daurin aurene yakawosu kasar Agadas yayinda zuciyoyin biyu suke a jagule....
Azman plane suka shiga zuwa bauchi.
Bauchi
Gidan cike yake makil. Abunka da gidan biki nan sun hada nasu kan nan sun had'a magana ake kasa kasa akan canjin auren da akai.
Tun anayi kasa kasa har maganan tafito abinku da gidan biki kuma taron mata tuni kowa ya dauka.
Da gudu Amira tayi cikin daki,
. "Ummi....Ummi...gayican anata magana kan canjin auren su aunty zarah da akai..."
Wacce aka kira da ummin da alama itace mahaifiyan Aysher da Zarah kuma kallo guda zaka mata kagane yar bararojice ma'ana mutanen Agadas kyakykyawace fara sol ga gashi har gadon baya.
Da sauri ta tashi. "Innalillah Allahsa beje kunninsu Zarah ba...." duban kanwarta tayi dake gefe wacce da alama itama yar bararoji ce tace. "Iyatu inasu Aysher? . "
"Suna dakinsu ana shiryasu...."
Da sauri Ummi tayi waje, dakinsu ta nufa.
Tun daga bakin kofa take jiyo kukansu anata basu hakuri.
Da sauri ta shige.
Kyakykyawar budurwace zaune gefen gadon cikin shigen atampha tayi kyau sosai kannan badan kwali gashin yasha gyara, duk da chocolate colorce hakan be hana bayyanuwar shekin da fatanta yakeba saboda taci gyara, kunsan dai buzaye.
Tanada manyan egg eyes da dan karamin baki tanada dogon hanci kuma doguwace.
Kuka take sosai mutanen gurin na lallashinta duk ta 'bata make up din da aka mata
Ido mami ta zubama zarah asanyaye tace. "Ya isa ki dena kuka zarahna".
Aysher dake kwance kan gado ta rufe fuska yalayalan sumarta kadai ake gani ita ko sautin kukan natama ba'aji jin muryan mami yasata tashi da sauri tareda fadawa jikin mami tafashe da kuka.
Ido na zubama Aysher suna matukar kama da zarah sedai Aysher farace sol dan fatanta har pink pink takeyi sannan tafi zarah kyau kuma tanada dimple dan dukda kuka take hakan be hanasu lotsawa ba, sedai kallo daya zaka musu kafahimci Zarah itace babban sannan kyakywawan en bararojine.
Shafa sumarta ummi ta shiga yi a hankali tace.."Ya isa my Aysher. "
dan karamin pink bakinta ta bude wanda zaku zaci spoon baya shiga cikin sweet voice dinta data rine da kuka tace. "Ummi taya zan rayu da shi ummi taya zanyi rayuwa dashi....ummi Aadil ko magana bana iya mishi bana iya magana dashi taya..........."
Kukane ya kufce mata.
Kaman a tsikari zarah ta mike tana kallon Ummi.
. "Ummi Aabid Aysher yakeso taya za'a bashi ni mutumin dako magana be taba hadamuba Aysher yakeso gaskiya Ummi bazan iya rayuwa dashi ba tsoronshi nakeji..."
Fadawa jikin ummi tayi tasaki kuka.
Shiru ummi tayi tana shafa kansu a hankali ta dubi buzuwa me gyaran amaren.
"Meyasa bakima Aysher kyalliyaba. "?
"Ita tace bataso abar mata face dinta shiyasa nabari dan naga her beauty is ready made ko batai make up ba. "
Dagosu Ummi tayi tana share musu hawayen.
"Yanzu dai kigyarawa zarah kyalliyanta sannan ayiwa Aysherna kyalliya me kyau anjima za'a zo a daukesu......."
Kuka me karfi Aysher tasa dan harma yafi nada da sauri ummi tafice dan bazata iya daurewaba.
Tana fita taga baffansu yadawo daga Agadas daurin aure da sauri tayi dakinshi.
. "Haba baffa taya wannan abun yafaru yanzu gashi an canza auren
Kunsa yaran nan a damuwa sunmaqi tsayawa a shiryasu ko meye dalilin yin canjin bayan kowa yasan Aysher ta Aabid ne meyasa akaba Aadil akaba Aabid zarah. "
Dan Jim yayi kafin a hankali yace. "Jeki Kiramin su...."
Da sauri tafice, koda taje ta tadda sunki yarda a musu kyalliya se kuka suke da kyar suka biyota.
Ido baffa ya zuba musu kafin a hankali yace. "Fateemah..." dago kai zarah tayi a hankali tace. "Na'am. "
. "Fateema kece babba sekinyi shiru zamu samu kanuwarki tayi. "
Share fuska tayi a hankali. "Nayi baffa. "
Yace. "Yawwa to Shatu kema kiyi. "
A hankali dukkansu sukayi shiru.
". Shatu, fateema kuyi hakuri ku karbi abinda Allah yashirya dama haka Allah ya tsara kuskuren ba daga mu bane daga madaurin auren ne kuma haka Allah ya tsara dan haka ku karbi zabinshi......"
Nasiha yashiga musu me ratsa jiki.
A hankali zarah ta dago cikin kuka. "Amma baffa....."
Da sauri ya katseta. "Banasan jin amma indai na isa daku banasan jin komai ku karbi wannan auren hannu bibbiyu banasan jin wani magana domin yanzu Aadil da Aabid mazajen kune ku musu biyayya inkuka saba musu kuda ubangiji,
Allahsa muku albarka a auren insha Allah se kunga riban biyayya Allah muku albarka...."
Duban ummi yayi. "Maza maidasu a musu kwalliyan...."
Ba musu suka miqe se Aysher ce da har lokacin hawaye ke zuba a idonta.
***
Impossible Abie impossible ni Aysher nakeso taya za'a bani zarah......"
Abie da suke zaune bisa kujera shida mami mahaifiyarsu yadubi Aabid dake magana tareda maida kanshi ga Aadil dakanshi ke kasa bece komaiba.
"Sons kuskuren banamu bane su can fadan haka suka dauka sunsha babban shize auri babban shiyasa mukuma muka tafi a haka saboda kaga masarautane kuma an tara mutane za'a zamu basu kunya, kuyi hakuri ku karbesu a matsayin matanku ai naga da zarah da Aysher duk dayane saboda abu daya yayisu....."
Da sauri Aabid yace. "Abie ba daya bane Aysher tafi zarah kyau kuma ita farace Abie ni banmasan baqar mace banasan ta banasan zarah I hate her....ni sakinta zanyi domin ko an kawomin ita bazataji dadiba shima se bro yasaki Ayshet shikenen se a canza auren a boye......"
Abie ne yadaka mishi tsawa. "Are yhu mad kasan me kake fadi kuwa....Aabid bazaka maidani karamin mutumba bayan munyi magana da nace mun amsa auren a haka yanzu kuma kazo kacanzani to idan har kasaki zarah bada miyau naba, kawai in kanaso mu daidaita dakai ka amshi zarah matsayin mata shikenen a hankali zaku koyi san junanku......"
Aadil da kanshi ke kasa yadago da sauri tareda laluban aljihu yasaka hannu ya lalubo Inhelan shi yayi sauri shaqa saboda numfashinshi dake sama sama, domin yanada ciwan Asma me zafi tun yana yaro.
Seda ya shaqa sosai sannan ya dago, mami da Abie sukace. "Sannu...."
Kai ya daga kafin a hankali yace. "Abie kayi hakuri akoda yaushe mu masu muku biyayyane mun amsa kuma insha Allah bazamu baka kunyaba......"
Harara Aabid ya watsa mishi tareda yin hanyan fita cikin fushi da sauri shima yatashi yabi bayanshi......
Yanzu aka fara.
Karku manta kuna tareda ni wacce nasaba suburbudo muku novels. (Mimi).
Comment and share.
2022-06-10, 5:19 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*
*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
_____________________________________
_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._
Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
3&4.
Around takwas na dare jerin gwanayen motocin daukan amare ya iso Unguwan nasu na Magaji cortex,
Su Aysher sunsha kuka sannan sunsha nasiha da kyar suka shiga motocin, zuwa unguwar sarakuna gidan granny (kakar su Aadil).
Tun daga inda sukai parking har zuwa cikin gidan carpet ne aka shimfida mawa amare yayinda suke takawa ana musu feshin turare da naira har cikin gidan.
Duk da granny ita kadaice agidan hakan be hana gidan haduwaba ko wata amaryar albarka.
part na musamman aka ware masu da yan uwansu, nan maid suka hau jero musu ababen tabawa tareda abincina masu yawa.
Aysher dake zaune kan kujera tashi tayi da sauri tayi bedroom din.
Ido suka bita dashi dukkansu harda Zarah da idonta yabi ya kumbura.
Toilet tafada tayi saurin tasa kofan toilet din key, ta jingina da kofan tasa kuka.
Yanzu shikenen an rabata da Umminta da Amira an hadata da wanda be santa duk da kam tasan Aadil yafi Aabid saukin kai ammadai komeye Aabid shike santa Aadil zarah keso......
Seda taji iyatu na buga kofan tana fadin. "Bazaki budeba...." sannan tayi saurin kunna famfoo ta wanke fuskarta tareda bude kofan.
Ido iyatu ta tsura mata kaman me nazarin gano wani abu, da sauri ta kwauce tareda karisawa gefen bed ta zauna.
daidai lokacin zarah ta shigo tareda fara cire bangles din dake hannunta da suke kara mata nauyi,
Ido Aysher tabi zarah dashi tana dad'a tausaya musu.
Iyatune tadubi Aysher "oh ke bazaki tashi ki rage kwalliyan jikinkiba jira kike in cire miki...."
Tashi tayi a hankali tafara zame sarka da dan kunnin, "Zara kinci abinci ko".
Girgiza kai tayi. "Banajin yunwa...."
Ta dubi Aysher. "Kefa... "
Shiru tayi hakan yasa cikin fada iyatu tace. "Kajimin ja'iran yara duk kun hada baki kunasan kusani magana to tun muna mu uku ku ci abincin dan bazaku kwananmin da yunwaba salan kurame aure aiba cutarwa bane da cutarwane da baffanku baze auri yar uwataba harya rabota da kasartaba kuma kuna ganinsu suna zaune lafiya toda aure cutar wanefa, yara bazaku gane gata muka mukuba senan gaba lokacin kun farajin dadin auren......"
Raurau Aysher tayi da ido zatai kuka, harara Iyatu ta watsa mata. "Duk wanda ya sake min kuka sena fasamai baki, bari inje inkawo muku abinci kuma dole kuci, kuci ku kwanta anan ku biyu mu an bamu wani part daban mu kwanta kafin gobe mu sadaku da dakin mazajenku danma kunji dadi kunsamu gidan hutu......"
Haka ta fice tana mitan.
Abinci ta kawo musu, ta tasasu a gaba sukaci kadan da kyar seda suka gama suka kwanta sannan ta musu sallama ta fice.
Ranan dukkansu juyi kadai suka dingayi haka a bangaren Aadil da Aabid.
********
Washe gari.
Tunda wuri granny tasa aka killacesu Aysher ana musu wani irin hadi na musamman wanka ake musu da madara da turare ba'a yarda a je part din, kuka kam Aysher tayishi kaman ba gobe zarah ce ma ta tsagaita da nata.
Karfe hudu na yamma aka shirya taron wa'azi a babban dakin taro na Hajiya Rash dake Bauchi .An shirya wajan ya kawatu sossai, yara matasa aka samu sukai shigar yoruba kowace tasha murjani ta tamke kugu tamkar ahlin emeka su goma shabiyu ne suka saka Aysher a tsakiya suna tafe suna watsa mata wani hadin turare mai hade da furani sunai mata kirari.
Itama Zarah mutane Sha biyun ne suka sakata a tsakiya ana mata irin abinda akayiwa Aysher.
Har zuwa tsakiyar dakin taron wanda ya kawatu da shimfidu kilisai da tum-tum tamkar diyoyin sarauta.
Aysher sanye take cikin wani rantsatsan swice kalar blue light, an mata head pink kafarta flate shoe shima pink sai mayafi da aka lulluba mata kalar azurfa mai ratsin golden.
Fuskarta ta kawatu matuka,sai sheki take
Zara kam nata shigen red ne se head black dukkansu sun hadu ainun.
Malama Maryam jafar Mahmud Adam ce ta bud’e taro da addu’a ta soma lacture kan biyayyar aure.
_”Bisimillahir-rahmanir rahim yake kawata yata yayyata kakkata, da duk wata mace dake wannan waje. Inaso ki bude kunnuwanki ki ssurarreni,shin kina cikin sahun mata nagari? Idan ma bakya ciki saurarreni domin zama abar alfaharin mijinki in kuma kina ciki kikara kaimi. WACECE MACE TAGARI?.Mace tagari itace takan yi kokaarin tazamar wa mijinta aljannarsa ce, batason taga gazawarta a idanunsa,don haka takan yi farin ciki idan taga murmushinsa takan damu matuka in taga fushinsa koda badaita yake ba.Bata jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa batare da almubazzaranci ba, itace amintacciyar abokin shawararsa, mai iya rike masa sirri, bata yarda wani yasani ko waye kuwa, sannan ga taimako._
_Mace a kullum mai sanyaya raice ba mai jiran a sanyaya mata ba, farin cikin maigidanta shi ne nata, komai yabata takan gode, ga fadin yi haquri kamar nunfashinta.Tana fama da baqin ciki amma tayi dariya,tanajin zafin abin da mijin yayi mata amma tayi tunanin yadda zata faranta masa rai._
_Aure sunna ce da Annabawan Allah duk sukayi,ya kamata mugaya matansu suka zauna dasu ???Bai dace ba kowane mutum ya riqa jin matsolinki da mijinki, sai in abin yafi qarfinki.Mace tagari mijinta shine komai, koda bai iya soyayya ba.Bata zama a gabansa ko gefensa saida yardarsa,takan cika da ladabi aduk inda yake, takan nuna masa qauna sosai ta gaskiya ce ko qirqira ce kawai.Idan zai fita qafarsa qafarta, idan taji ya shigo ta tarbo shi cikin fara’a da annushuwa, nan da nan tafesa turare ta shafawa lallenta mai yafito sosai ta danyi kwaskwarima, ta canja murya tareda yawan murmushi da fari.Idan zai fita addu’a, in yadawo godiya da murna dafarin ciki._
_Asma’u bnt Kharijatul Furaziy take cewa ‘yarta ranar budar kanta cewa:ke cewa ‘yarta ranar budar kanta cewa:”Yanzu fa kinfita daga sheqar da aka kyankkyashe zuwa shimfidar da baki santa ba, da abokin tare da baki san shiba, ki zamar masa qasa sai ya zamar miki sama, kizamar masa shimfida zai zama miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai zama miki bawa, kar ki nace wajen neman abubuwa domin karya gujeki, kar kiyi nisa dashi domin karya manta dake, idan ya matso, ki kusance shi, idan yaja jiki, kema ki dan ja da baya, amma ki kiyaye hancinsa da kunnensa da idonsa, karya shinshini komai a wurinki sai qamshi, kar yaji komai sai kyakkyawan abu, kar yaga komai sai wanda zai burge shi.Girki, mahalin kwanciyya girmama danginsa mahaifiyarsa haka abokansa.Tattalin kayansa tare da kilace masa su, kula da damuwarsa insha Allahu zai yi farin ciki dake”_.
Bayan