Showing 24001 words to 27000 words out of 45461 words
Chapter 9 - NISFUL HAYAT Book Complete by Mimi queen.txt
bugawa da karfi, Aabid kam yana tsaye idanshi a kanta yakasa motsawa tana kwance jikin aysher da taketa kuka, lumshe ido yayi, yana godewa Allah,
Duban Aadil yayi. "Dil yanzu ka shirya mana tafiya India yanzu zamu kai Zarah..."
Bece dashi komaiba yafice, gun sojojin da suka zagaye hospital din yayi yana tambayansu abinda ya faru, fadamai sukayi suka kara da fadin. "Kuma mun duba kaf garin Abuja da Minna basu dan har abujan mukaje sun gudu.... "
Aabid da yaji duk abinda suke fadawa Aadil dan fitowanshi kenan yace. "A kama gaba daya danginta in ita ba'a sametaba a daure uwarta da ubanta they will pay on it...."
Da sauri Aadil ya dubeshi. "Abi komai a hankali Bid zamu kamata insha Allah amma aiba danginta suka mana laifiba itane dan haka zamu sameta insha Allah duk inda tashiga da kawar nata....."
Huci Aabid yasaki, tareda dun'kule hannu, indai jamima ta shigo hannunshi sena jahannama yafita jin dadi shikadai yasan hukuncin daze mata,
Daidai lokacin jerin motocin da suka dauko Mami suka shigo asibitin domin Aadil ya fada musu tun a jirgi, da gudu tafito tana tambayan "Zarah. "
Kanta sukayi dukkansu amma ina hankali tashe take tambayan Zarah, Aadil ne yace. "Mami tana ciki ansa mata oxygen..."
Da sauri tace. "Me? ai daganan airport zamu wuce dan India zamu kaita baza'a dubata a Nigeria ba... "
Da gudu tayi ciki duk sukabi bayanta, ta tausayawa Aysher ainun ganin halin da take ciki hakan yasa ta sauke damuwanta ta fara lallashinta,
Basu jimaba aka gama komai a Private jet din Abie zasu tafi, Mami cewa tayi, daga ita se aabid zasu tafi, Aysher najin haka tafara kuka sosai hakan yasa Mami tace, to su tafi da ita.
Oxygen na hancinta a motan asibitin aka nufi airport da ita, Aysher na gefenta ko kadan taki matsawa oxygen din dake aiki kadaine ze tabbatar maka tana da rai,
Suna zuwa aka shiga da ita jirgin, Aysher ko sallama batama Aadil ba tabi bayan Zarah, rungume juna Aadil sukayi da aabid nan, Mami, Aabid, da Aysher suka nufi India, aka bar Aadil da Amira da shima a ranan ze bi flight din 6 ya kaita bauchi.
Inajin dadin comments dinku masu 'karamin kwarin gwiwwa, nagode sosai masoyana masoyan Aadil, Aysher, Aabid da Zarah dan naga yanzu kunfara san Aabid,
Kuyi hakuri da wannan ina fama da ciwan hakorine kwana biyu shiyasa manage 🙏.
Taku Mimi ✍️.
2022-07-02, 7:46 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*
*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa
_____________________________________
_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._
Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
31&32.
Yau kwanan su Biyu a India.
Anaba Zarah kulawa na musamman amma har lokacin bata farfadoba domin ta fada Comma,
Har lokacin ba'a yarda a shiga inda take ta glass suke hangota tana kwance manne da oxygen,
A wani babban gida suke zaune domin ba'a bari a kwana a asibitin wanda daya daga cikin gidajen Abie ne na kasan domin yanada gidaje ako wani kasashe saboda becika san zaman Nigeria ba saboda Mami ne yasa ya hakura domin ba kasar datafiso daga Saudia se kasarta Nigeria,
Aysher ta wani rame sosai cikin kwana biyu domin damuwan datasa a ranta Mami ne ke matsa mata hakan yasa takecin abinci, Aabid kam hummm Mami rasa yanda zatayi dashi tayi hakan yasa ta matsa Aadil yazo,
kwanansu uku a kasar Aadil, baffa, Ummi, Abie, matar uncle sulayman (kanin Abie) da uncle din da granny sukazo.
Dukkansu ba wanda be tausaya ganin halin da Zarah ke cikiba har lokacin ba'a ba kowa daman ganintaba, hakan yasa suka koma gida,
Duk an zazzauna a main falo kowa yayi jigum jigum, Aysher kanta nakan cinyan Mami, se hakuri Mami takeba su ummi tana cewa zata samu lafiya suyi hakuri.
Abie ne ya dubi Aabid da kallo guda zaka mishi ka gane yana cikin damuwa yace. "Wai Bid meye hadinka da yarinyar datawa Zarah haka...? "
Da sauri Aadil yace. "Colleague din shine Abie sunyi karatu a kasar London..
Granny ne tace. "Dan sunyi karatu sekawai tayi kokarin kashe mishi mata..? "
Aadil yace. "Yarinyar tana sanshine shikuma baya santa shiyasa...."
Huci uncle ya saki. "Yanzu dai duk abinda ze faru ya faru sedai muyi fatan Allah tsare gaba Allah bayyana Sipers din su amsa hukuncin doka..."
Daga ummi har baffa ba wanda yayi magana, sun jima sannan kowa ya tafi masaukinsu domin kam babban gidane kowa da part dinsu Aysher suna tareda Mami da Ummi Aabid kuma da Aadil baffa da Abie .
Kwanansu biyu sukace zasu koma,
Tunda Aadil sukazo be samu sun ke'be da Aysher ba,
Yau yaci sa'a yana shiga part din mami tana saukowa daga sama, da sauri ta juya zata koma hakan yasa yayi saurin karisawa ya fizgota,
Fuskanta ya kamo yana shirin magana tausayin yanda takoma yakeji yana tausayinta ita da dan uwanshi ainun se yanzu ya fahimta zarah nada mahimmanci a rayuwan ko wannen su, ganin yanda ya fizgota kaman ze 'ballata yasata da sauri ta fashe da kuka domin dama a wuya take,
Rungumeta yayi tsam a jikinshi jin yanda take kuka kaman ze maidata ciki,
Ijiyar zuciya tafara saukewa ita kanta tayi missing mijinta sosai shima ijiyar zuciyan ya hau saukewa, seda yaji ta dena kukan sannan ya rabata da jikinshi yana kallon fuskarta, juyawa tayi zata gudu da sauri ya riqo hannunta. "My Shatuuu...."
Dago daradaran idanunta da sukayi su'bu su'bu tayi ta daurasu akanshi domin sunan is so special to her, a sanyaye yana lumshe ido yace. "Do you missed me..? "
Daga kai tayi a hankali.
"Banga alamaba gashinan kina guduna..."
shiru tayi tana kallon kasa, yayi jim "Ai tare zamu tafi 'kafana kafanki.."
Da sauri ta dago tahau girgiza kai idanta daff da hawaye. "A'a niba inda zani Ya Aadil....please...
Ta fashe da kuka, rungumota yayi. "Yi shiru Cutie wasafa nake miki nima ai badani za'a komaba saboda u and Bid are not with me kuma u oll my life kona koma i can't do with out yhu Guys zan zauna anan tare dake da Aabid harse Zarahnmu ta samu sauqi mukoma gaba dayanmu.....Kinji dadi..? "
Daga kai tayi da sauri tana kara shigewa jikinshi.
Harda Mami za'a koma amma granny zata zauna, Aysher taci kuka sosai dasu Mami da Ummi zasu tafi da kyar suka lallasheta suka tafi sunce ai zasu dawo, anan Aysher kejin labarin Abie ya fito takaran Shugaban qasar Nigeria 🇳🇬 domin ya riqe governor.
Karfe hudu dukkansu suka nufi asibitin akabar granny a gidan da masu aiki.
Suna isa doctor ke sheda musu za'a iya fara shiga ganinta har rige rige akeyi tsakanin Aabid da Aysher, rungumeta Aabid yayi dukda tana kwance har lokacin ba'a cire mata oxygen ba kuka yake sosai gani yake dukshi yaja mata, Aysher ma kuka takeyi da kyar Aadil yasa Aabid yasaki Zarah, basu jimaba likitan yadawo yace su fita lokaci ya kare.
Tun daga wannan rana kullum a asibitin Aabid yake uni, Aadil ne ke kai mishi abinci domin granny ta hana aysher zuwa kwana biyu dan jikinta ba dadi sosai.
Tana kwance a falo ya dawo se kyarman sanyi takeyi, cire jacket din dake saman jikinshi yayi a hankali ya karisa yadagota ta fado jikinshi ya saka mata tareda shafa wuyanta jin yanda jikinta yayi rau.
"Cutie bakida lafiya muje asibiti kinki magungunanma bacin granny bazaki shaba... "
Runtse idanunta da suka mata nauyi tayi. "Yar uwata nakesan gani I missed her..."
Ta fada tareda zubo da kwalla, "okey zamuje amma sekin yarda in munje zaki yarda adubaki tukun.. "
Da sauri ta daga kai, tashi yayi yahau sama ya dauko mata doguwar riga yadawo ya saka mata ya yafa mata gyale ya riqeta suka fice.
Seda suka fara biyawa sukaga doctor ya duba jikin Aysher yaso a mata allura domin zazzabine ya mata mugun kamu amma ta maqale hakan yasa Aadil yace abarshi kawai, magunguna ya rubuta musu daganan suka biya pharmacy suka siya suka nufi ward din da Zarah take.
Tun daga bakin ward din sukejin muryan Aabid. "Mekika musu Zarah tashi ki fadamin mekika musu suka miki haka tashi ki fadamin ni mijinkine zanbi miki hakkinki duk se sun raina kansu nayi alkawari...
Shiga sukayi yana zaune ya ramqe hannunta se sambatu yake,
Gaba dayansu tausayinshi sukeji ba kadanba yakusa fara zaucewa akan Zarah mutumin da yake miskili da wuya kaga dariyarshi balle kukanshi amma akan Zarah yayi kuka sosai.
Seda Aadil ya taboshi sannan yasan sunzo zunbur ya miqe, "Dil dan Allah karoki Dr su barni na dinga kwana da matana Dil my heart is painful me please Dil.....
Yafashe da wani irin kuka, ba aysher da take maceba hatta Aadil seda jikinshi yayi sanyi domin tunda yake be taba ganin Aabid yayi kuka hakaba.
Da kyar da ban baki doctor ya yarda shima dan aabid ne amma dokan asibitin kenan.
Fad'a granny tayi akan me za'a dinga barinshi be isaba yadinga dawowa, hakan yasa da kyar Abie ya lallasheta ta yarda shima din seda ya fada mata irin damuwan dazasu jefashi insuka hanashi sannan ta bari dan tanasan jikokinta sosai.
Mimi ✍️.
2022-07-03, 11:32 a.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*
*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa
_____________________________________
_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._
Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
33&34.
Yau watan Zarah Uku chir a babban asibitin India.
Yana zaune gefenta ya kura mata ido yau hakanan yakejin wani irin natsuwa na daban, lokacin kusan biyu na dare amma yakasa bacci se kallon Zarahnshi yakeyi ji yake kaman ita ta tashi shiya amsan mata ciwon,
Zuwa lokacin an cire mata oxygen sedai bata farfadoba har lokacin.
Kanshi ya daura a hannunta yana fidda hawaye na tausayin halin da take ciki, ji yayi kaman hannun nata ya fara motsawa da sauri ya dago yazuba mata ido ganin tafara motsi seso take ta bude ido, da sauri ya janyota jikinshi yana fadin. "Alhamdulillah alhamdulillah Allah nagode maka...."
Hawayene yafara bin kuncinshi,
Zarah da sama sama taji alamun mutum sedai bata tantanceba saboda yanda takejinta kaman ba'a duniyaba, a hankali ta bude kananun idanunta da suka jima a kulle, ta daurasu kan Aabid dayake rungume da ita, a hankali kaman zatai kuka dan jikinta ba dadi sosai tace. "wanka nakeso inyi banajin dadi jikina so pain me......
Tafadi tareda fashewa da kuka,
Jikinshi har rawa yakeyi ya tashi ya dauke ta ya shiga bayin da ita, ba yanda ta iya tanaji tana gani batada daman hanawa haka Aabid ya tu'beta ya mata wanka daganan ya nadota a towel kaman baby ya fito da ita ya kwantar saman bed, nan danan bacci ya dauke ta dan tadanji dadin jikinta wankan daya mata.
Tsaye yayi ya zuba mata ido shikadai yasan irin farin cikin dayake ciki yau, kwanciya yayi akan gadon kusa da ita gaba daya ya janyota jikinshi ya rungume jiyake kaman ya maidata ciki a haka wani baccin da rabon da yayi irinshi yafi wata uku yayi awon gaba dashi.
Koda ya tashi da Asbah tanata baccin be tashetaba ya shiga bayi yayi Alwala yafito ya kabbara sallah bayan ya sallame yakoma gadon ya rungumota domin wani nutsuwa yakeji in tana jikinshi, a haka wani baccin ya kara daukanshi....
Dukkansu bacci sukeyi shi baccin gajiyane da rashin samun bacci kwana biyu ita kuma na rashin lafiya,
Har wajen 11 lokacin su Aadil da Aysher sukazo asibitin,
Gaba dayansu tsaye sukayi ganin yanda Aabid ya rungume Zarah kan kirjinshi kaman ze cinyeta ita kuma gata daga ita se towel daya fara kwancewa, cikin rashin fahimta Aysher tadubi Aadil. "Zarah ta farfadone....?
Bata rufe bakiba taga Zarah tafara motsawa tanaso ta kwace a jikin aabid, daidai lokacin ya bude ido jin tanaso ta kwace ido ya zuba mata har lokacin be saketaba kuma bata dena kwacewaba dukda ba karfi a jikinta,
Cikin farin ciki aysher tace."La sister.....
Da gudu ta ruga hakan yasa yayi saurin sakinta dan besanma suna gurinba tareda sa bedsheet ya rufe mata jiki, rungume juna sukayi dukkansu sukasa kuka, fuskan zarah Aysher ta riko. "Sister u leave me alone kusan wata uku kin sani a damuwa.... "
Ta kara fashewa da kuka, Zarah ta kasa furta komai se kuka itama takeyi ganin haka yasa da sauri Aabid yaja hannun Aadil sukayi waje,
Wani babban boutique shop sukaje Aabid yayima Zarah siyayyan kayayyaki masu yawa daganan suka koma asibitin,
Doctor suka shedawa ta farfado sannan suka koma gurinta, lokacin duk sun dena kukan Aysher naba zarah Tea a baki a hankali tana sha suka shigo kallo guda zarah tayiwa Aabid ta dauke kai,
ijiye kayan yayi yana duban aysher. "Sister inta gama ga kayanan tazabi daya tasa.... "
"Toh. " Aysher ta furta, Aadil ne ya dubi zarah. "Auntyna ya karfin jikin gaba daya kinsamu a damuwa. "
Murmushi tayi tana kallon Aadil. "Ayya kuyi hakuri ai yanzu na tashi.."
Daidai lokacin doctor ya shigo yana fadin. "Wow a suprice patient daga tashi harta fara magana.. "
Aabid ne yace please doctor yadan basu guri ashiryata seya dawo ya dubata, fita sukayi dukkansu akabar Zarah da Aysher, ita ta zaban ma zarah wani gown tasaka mata daganan tamusu magana doctor ya shigo,
Dubata yayi yafadi irin abincin da zata dingaci yace inta dage dashan magunguna ko sati bazata karaba za'a sallameta.
Aadil ne ya matsawa Aabid da kyar sannan suka je gida yayi wanka ya canza kaya ya bude ciki yaci abinci, granny tayi murna koda zasu koma tare suka koma da ita.
Mami ma dasu ummi sunyi murna sosai, sunso suzo amma granny tace su bari da an sallamesu zasuje US in sukayi kwana biyu zasu dawo Nigeria hakan yasa suka hakura amma Mami sunayin video call suna ganin lafiyanta haka Ummi suna yi a wayan shattima kuma sunyi murna ganin yanda Zarah take samun sauki sosai.
Yau kwanan Zarah takwas da tashi ta samu sauki sosai ta warke sumul har wani kiba tayi hakan yasa aka sallameta,
Aabid yanda Zarah ke nuna ko in kula akanshi yana sashi yaji wani iri,
Yaso ace ya kwana yau tare da ita amma granny tace tare zasu kwana ba yanda ya iya hakanan ya hakura suka kwana tareda Aadil wanda shima maraicin rashin Aysher yake ya kudurci suna komawa US seya samu nutsuwa a jikinta,
Yaune suka dira a US wanda sojojin coast guard su suka zo airport suka daukeso har gidan Aadil,
Gaba dayansu sun yaba da kyan gidan ainun, suna zaune sun sukaga an fara haska labaran Nigeria wanda Abie shiya cinye zaben Shugaban kasar Nigeria da akayi, dukkansu ba wanda beyi murnaba nan suka dauki waya suka kira su Mami se murna suke musu,
Da dare yayi har Aysher tashiga daki Aadil na niyyan binta granny ta dubi Zarah. "Fateematul zarah tashi kije ku kwana tareda yar uwarki...."
Tashi tayi a sanyaye tabi bayan aysher, Aabid ido ya bita dashi ji yake kaman yasa kuka, dakin Aadil ya nufa yafara safa da marwa, tunanin halin da Zarah take nuna mishi yakeyi anya ze iya daurewa,
Drower din Aadil ya janyo wani diary ya gani a jiki an rubuta _Life Story_
Dauka yayi tareda budewa rubutun Aadil ne wanda yafara da.
```My life, my happiness farkon haduwarmu mun hadune a mafarki My Shatuuu my life my everything.....```
Nan ya dingi karantawa kanshine ya dauke diff da yakai inda Aadil ke cewa ```My brother is everything to me ba abinda bazan iya sadaukarwa saboda shiba, duk da inasan ta sosai haka na hakura zuciyata takasa hakura harna kamu da heart disease but at the end dayike Allah kadai yasan alkharin dake tsakanin mu na mallaki farin cikina my dream partner my shatuuu wacce nima nine dream partner dinta.....```
Hawayene yafara bin kuncin Aabid harya kai karshe, his brother is a gifting from Allah to him, his brother is not like such of all brothers he is special.
Magunguna ya gani da yawa na ciwan zuciya, besan sanda yasa kuka ba. "Why Dil...why Dil...."
Daidai lokacin Aadil ya turo kofan ya shigo, turus yaja ya tsaya ganin diary a hannun Aadil ga magungunanshi a gefe, kasa furta komai yayi domin yasan yanzu Aabid yasan komai danma mantawa yayi be 'kona diary dinba,
Ido Aabid yabi Aadil dashi cikin tuhuma yace. "Why are you staying far from me Dil why....Dil why.....come toward me Dil come Dil u are my life...."
Kuka yasaki da sauri Aadil ya karisa ya rungume Aabid shima besan sanda yasaki kukanba,
"Why Dil meyasa zakamin haka Dil..."
Dagowa yayi tareda pointing zuciyan Aadil yana fadin. "Dil saboda ni ka kamu da heart disease sabodani Dil meyasa tun farko ka boyemin baka fadamin cewa Aysher itace yarinyar mafarkin kaba haba Dil meye bazan iya sacrificing saboda kaiba u be everything to me more Dil why...."
Cikin kuka Aadil yace. "Am very sorry Bid kasani bayin kaina bane hakan it's Allah's chance bid am sorry nayi hakan ne saboda banasan damuwanka kana dauke da Liver cancer brother am sorry...."
Murmushi me ciwo aabid yayi. "Be kamata ka lura da wannanba har ka daurawa kanka damuwa domin ni najawa kaina Dil I tows everything maybe shiyasa Allah ya jarabceni da abubuwa da dama domin na aikata laifika a baya..."
Rungume shi Aadil ya sakeyi sosai.
Dagowa Aabid yayi. "Have yhu take ur medicine today..? "
Daga kai yayi, cikin kulawa aabid yace. "Please Dil be endure domin in wani abu yasameka bazan taba yafewa kainaba..."
Murmushi Aadil yayi. "Bid kaima dai da fatan kanashan