Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 45461 words

Chapter 5 - NISFUL HAYAT Book Complete by Mimi queen.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

taho tafara kwara amai amai take sosai seda ta amayar da tea din da Pepe chicken din duka dukda haka bata dena kakarinba kuka tafara harda hawaye, Aabid na zaune duk abinda take yana kallonta ko a jikinshi, ganin tafara kuka yasa ya d'auke kai jini yaga yafara biyowa ta cikin bakin nata, da sauri ya mi'ke cikin kyankyami ya shige ciki, itako aman jini sosai take dan babu komai a cikinta hakan yasa jinin fitowa,


Wanka ya sillo ya fito harya fada gado ya lumshe ido halin da zarah take ciki ya fad'o mishi , dan karamin tsaki yaja, da sauri wata zuciyan ta tunatar dashi jinin daya gani daga bakinta.


Waya ya janyo ya kira doctor dinshi, doctor merry, "yes Lieutenant.... " da sauri yace. "Please doctor come over I have an emergency in my house...."
Tace. "Really, am on my way. " katse wayan yayi, hakanan yaji ya damu tashi yayi zaune,
ba'a jimaba yaji horn alamun Dr ta kariso se lokacin ya samu yakoma ya kwanta.




Dr na hawa sama a falo taci Karo da Zarah kwance a kasan tiles ta galabaita sosai a rud'e ta daga zarah tayi cikin daki da ita, first aid tafara bama zarah, daganan tasa mata drip ta mata allura, tamata allurai nan da nan bacci ya dauke Zarah.




Taku.


Mimi queen ✍.
2022-06-21, 7:05 a.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*


*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._

Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*




17&18.




Sanyin Asbahn dake shigowa ta windon glass din shiya farkar da Aadil daga baccin da yake, dagowa yayi a hankali daga cinyan Aysher yana jujjuya kai ido ya zuba mata ganin kanta na hannun kujeran baccin ta takeyi kaman ba abinda ke ranta, besan sanda ya saki murmushi ba yana dad'a kallon fuskarta yanajin dadin temakon data mishi hakanan yaji yanajin wani abu game da ita a cikin ranshi yaji dadin abinda ta mishi Ainun,


Tashi yayi a hankali tareda dagata kaman wata er baby yayi bedroom dinta da ita, kan bed dinta da yake a gyare ya direta tareda shigewa bathroom dinta, Alwala ya d'auro ya a bayin dakinta ya fito,


A kwance ya barta yafice ya nufi wani masallaci dake anguwan domin akwai musulmai kadan a Unguwan hakan yasa wani balarabe yake musu jam'i,


Ya fita ba jimawa Aysher ta farka tashi tayi tana mamakin ganinta a dakinta, bayi ta shiga tayi fitsari ta canza pad sakamakon tana al'ada duk da bewani 'baciba domin Aysher ba gwanan jini bace In jini yazo befi yamata kwana daya biyuba ya dauke,


Dawowa tayi ta canza kaya tasaka wata shimi iya cinya ta koma bacci dan wani bacci takeji sosai.




Karfe bakwai na safe Aadil ya dawo gidan domin yaje morning jogging, hakanan yaji yanaso ya kuma ganinta, hakan yasa ya nufi dakinta,


Tana kwance ta canza shige hulan net din dake kanta ya zame hakan ya bayyanar da tulun gashinta dayake a dunkule guri guda ta musu kitso daya, abinka da bararoji ga gashin nan masha Allah dan yakai cinyanta, pink lips dinta daseka rantse ta shafa pink jan baki yana dauke da murmushi lumshe ido yayi, yanabin fararen santala santalan cinyoyinta da suke a waje, besan sanda ya nad'e hannuba yana dad'a kallon kyawawan suranta, ganin ta dan motsa yasa da sauri ya fice dan beso takamashi yana kallonta.




****
Allah sarki Zarah baiwar Allah.


Koda ta farka drip din ya kare tashi tayi da kyar ta zare drip din ta nufi bayi, wanka tayi tafito da kyar tana daddafe bango doguwan rigan abaya ta zira a hankali ta nufi waje,


Breakfast tayi takoma daki akan bedside table taga magungunan da Dr merry ta ijiye mata da yanda zatai amfani dasu, Eva water ta dauko a fridge ta sha magungunan,


Dukda bata hayyacinta ta iya tuna sanda Dr tazo, mamaki take ko waya kirata,
"Kodai aabid ne?
da sauri wata zuciyan tace. "Banzan me mugun halin shinema.


Lumshe ido tayi hawaye nabin idanun nata, tasan Aysher tayi dacen miji amma ita tasan haka nata kaddaran yazo.




****
Yau watansu Aysher dasu Zarah uku cir da tafiya.


Hakan yasa mami ta matsa mawa su Aabid akan su kawo mata yaranta tagansu.






Tun dare Aadil ya fad'awa Aysher akan ta shirya gobe zasu tafi bauchi, hakan yasa ta shirya kayanta tun daren se murna take zataje taga Umminta da Amira, a daren Aadil yakai Aysher babban mall tayi mawa su ummi, amira siyayyan kayan America.




Zarah kam seda safe Aabid yake fada mata ta shirya zasu je bauchi, hakan yasa ta fara shiryawa se murna itama takeyi.




*****


Yau tun safe gidan mami aketa shirye shirye na isowan su Aadil, abincina kala da kala mami tasa ake shiryama yarannata,


Karfe daya, Aadil yakirasu yace sun iso, hakan yasa mami da bodyguard suka nufi bauchi airport dan tarbosu.




Wannan karan Ayshet bata wani firgitaba nashiga jirgi domin wannan shine Karo na biyu, mami na zuwa suna fitowa rungume Aysher mami tayi tana farin cikin ganin yanda Aysher tayi haske tayi 'kiba hakan ya nuna mata ruwan US ya amsa Aysher.


Daure fuska Aadil yayi ganin mami taja Aysher mota kota kanshi bata biba, motan bayan nasu bodyguard suka bud'e mishi ya shiga nan suka nufi gida,


Suna isa suka fiffito se lokacin mami ta fara waige waige. "Wai Son ina kakene....? "
Zunb'uro baki yayi. "Mami se yanzu zaki nemeni bayan a airport kota kaina baki biba. "


Fuskarshi ta shafa "Haba taya zakace haka kasan u are my heartbeat and ur brother is my Breath...."


Murmushi yayi. "Dat my super human. "


Hannunshi dana Aysher ta riko suka nufi cikin gidan,
Abincina mami tasa aka jera musu kala da kala, kadan Aysher taci haka Aadil dan sunci abinci a jirgi,


Wajen two Aabid ya kira sun iso, duban mami yayi. "Ni kadai zanje airport in daukosu mami." a sanyaye Aysher tace. "Mami nima zanje. " dan she's eager to taga sister dinta,
Da sauri mami tace. "No baki huta daga long journey dakukai ba dukda tafiyan jirgine akwai gajiya karda kije ki wahalar min da jika........


Ruwan dake bakin Aadil ne yayi sauri furzarwa jin abinda mami tace.....


Da sauri yace. "Mekikace mami? "
Gyada kai tayi "yep I know you heard me right, abinda kaji shi nace. "


Mikewa yayi cikin basarwa ya dauki car key a kan table "ni mami bari inje in dawo. "


A hankali mami ta dubi Aysher data sunkuyar da kai cikin rad'a tace. "Baza kima mijinki rakiyaba.? "
A hankali ta tashi tabi bayanshi, har yakai bakin mota jin ana binshi yasashi juyawa, da sauri ta tsaya, da gira ya mata alama da lafiya?, dan zunb'uro baki tayi. "Mamine tace in rakoka...."


Dan Murmushi ya saki "ke kikace mata kinada ciki.? "
A rude ta dago. "Ni, yaushe kuma A'ina? "


hannayenshi yayi holding a kirji tareda fadin. "Na miki tambaya daya kinmin uku tambayanki nayi amsa nake jira. "


Maida kanta kasa tayi kaman zatai kuka
"Allah ya Aadil bani bace, bansanma sanda akai magananba. "
Murmushi yasaki "fadamin gaskiya kodai so kike ki samu...? "
A zabure ta dago sedai suna had'a ido ta fashe da kuka tareda juyawa ta shige flat din, Murmushi yayi ya girgiza kai daga Magana se kuka gaskiya zeyi fama, car din ya bude yashiga ya nufi airport.




Aadil na ganin Aabid suka rungume juna, Aadil dan kallon zarah yayi data rame cikin sakin fuska yace. "Matar yaya ya hanya ya kuma zaman jirgi.? " Murmushi tayi. "Lafiya klau ya Aadil. "


a sanyaye ya fada trying to make her feel free dashi,
Duban aabid yayi. "Leutenant Aabid am very surprise muda muke outside country mun riga en 9ja isowa. "
Murmushi Aabid yayi. "Ai bamu fito da wuriba. "


Mota suka shiga suka nufi gida, Aysher na haduwa da Zarah suka rungume juna sukasa kuka, mami tayi mamakin ganin zarah ta rame hakan yasa taita tambayansu bawani matsala duk sukace bakomai, koda Abie yadawo yayi murna sosai da ganinsu nan gaba dayansu suka had'u sukai dinner tare,


Bayan sun gama mami tace Aabid da Aadil su dauki su Aysher su kaisu gidansu su kwana, murna sosai sukayi nan suka dauko kayansu, Aabid badan yasoba hakanan sukaje tare.




Suna ganin ummi dukkansu suka rungumeta sukasa kuka, ummi datun safe da suka fada mata suna hanya ta musu girki me rai da lafiya da kyar tarabasu da jikinta nan ta fito falo gunsu Aadil da suke fira da shattima, seda duk suka gaisa da baffa sannan suka wuce.


Gaba dayansu sun daura kansu kan cinyan ummi nan Aysher ta tashi ta dingi fito musu da tsaraban data musu harda Zarah, baffa da kuma Ya shattima,


Zarah kam komawa tayi ta langwa'bar da kai cinyan ummi domin itakam ba abinda ta kawo musu, hawayene yafara bin idonta jin yanda Aysher ke basu labarin US domin ita kam tun randa sukaje Minna tashiga gida bata sake fitaba se yau,


Waya Aysher ta ciro ta nuna musu Partyn da sukai na sojoji a jirgin ruwa domin kam khaleesat ta turo mata ta WhatsApp, dariya ummi da Amira suka dingiyi abun ya burgesu matu'ka.


Ummi jin zarah shiru ta d'agota sosai hankalinta ya tashi ganin zarah na kuka sosai, itama haka Aysher mi'kama amira wayan sukayi tayi falo da gudu, dukkansu suka dago zarah hankali tashe,
Ummi tambaya take. "Kinada wani matsalane 'yata meke faruwa me Aabid din yake miki."


Wa'azin sheik Ali Isah fantami ta tuna, Wanda yake fadin _Ki zama mace me sirri tsakaninki da mijinki karki zama me fallasa sirrinki koga iyayenkine ko kizama me kai 'karan mijinki idan kuka samu sa'bani domin fa koda wata rana kun shirya sufa magabatanki bazasu ta'ba mantawaba hakan zesa su dinga ganin shi da tabo_


Hakan yasata cikin kuka tace"ummi ku gafarceni ni ba abinda na kawo muku " tsaki ummi taja "shine abin kuka.? "
Aysher ne tace. "Ummi karya takeyi bashi bane sis Kodai bakida lafiya ne.? " girgiza kai tayi. "Ummi nayi kewan kune sosai amma ni lafiyana kalau.."


Rungume ta ummi tayi cikin rashin gamsuwa, ijiyan zuciya zarah tahau saki jinta jikin ummi aysher ma daura kanta tayi a cinyan ummi..







Har Mami ta kwanta Aadil ya shigo da kaman baze tambayaba se kuma yace "Mami wai kwana nawa su Aysher zasuyi a gidan su.? "


Dan Jim tayi "ku barsu suyi sati daya kunga sun jima basuga Ummin suba...ko be makaba.? "


Sosa kai yayi domin harya fara kewan Aysher yace. "Eh yayi amma Mami ai hutun one week dukkanmu muka dauka. "
Tace" ai shikenan kaga ana gobe zaku tafi se kuje ku kaisu gidan granny su kwana washe gari seku wuce inaga shikenan. "


Cikin rashin annashuwa yace. "Ok as u said bestmom. "
Ficewa yayi jiki a sanyaye murmushi Mami tayi danta gama gano Aadil.




Taku.
Mimi ✍️.
2022-06-21, 9:10 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*


*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._

Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*


Allah ubangiji ya jikanki Auntyna it's exactly 50 days without u today, Allah yakai haske kabarinki Maryam ya raya twins din da kika bari (Muhammad da Abubakar), bazan taba mantawa da 23 Ramadan ba wanda yayi daidai da 24 April ranan zagayowan haihuwata yanzu yazama ranar 'kunci a garemu Allah ubangiji yasa kina kyakykyawan matsayi yar uwata halinki na gari ya biki.


Amin ya Allah 🤲.




19&20.




A cikin sati dayan dasu aysher sukai a gidan su sun samu natsuwa sosai, tun ana gobe zasu tafi zarah ta dingi kuka domin ta tsani zama da Aabid gaba daya haka aysher itama ta dingi kuka.




Aadil ne kadai yazo daukansu,


Yana zaune a falo idanshi nakan bedroom din Aysher kadai yakesan gani dan yayi wani irin kewanta, Shattima dake gefe yace. "Kayi hakuri yanzu zasu fito. " kai ya gyada,


Nan Shattima ya dingi janshi da fira, sakin jiki yayi suka dingi fira,




Zarah ce tafara fitowa idanun nan a kunbure tanajan katon trolley dinta da sauri ya dauke kai, Shattima ne yace. "Ke ina Ayshern take...? "


Kan ta bashi amsa, ummi ta fito tana fadin. "Shattima narasa yanda zanyi da Aysher ta rungume amira taki sakinta se kuka take..."


Shattima ne ya mike da sauri yayi dakin, shiru Aadil yayi a hankali yace. "Ummi...."


Ummi da take tsananin jin kunyanshi a sanyaye ta amsa.


"Ummi dan Allah ina rokon alfarma abamu amira mu tafi da ita Indai ba damuwa. "


Shiru ummi tayi kafin tace. "Kaga gaskiya banada daman cewa na yarda harse baffansu ya amince. "


Aadil ne yace. "To ummi inba damuwa se mu jira baffan ya dawo mu tambayeshi tukun. "


Ciki zarah ta koma takara sakin wani kukan, shiko Aadil yayi hakan ne saboda farin cikin aysher dan yasan tanasan amira sosai.




Seda baffa yadawo Aadil ya tambayeshi yaso ya hana amma se Aadil din yaita rokonshi hakan yasa yace. "Shikenan ba matsala amma kaje se goben idan zaku tafi se kazo ka dauketa. " godiya Aadil yayi sosai.


Duban ummi baffa yayi. "Jeki kiramin shatu..."


Tashi tayi bata jimaba suka fito tareda aysher da fuskarta ta kumbura saboda kuka.


Fada baffa yafara mata sosai yana fadin, daga yanzu ko sunzo 'kasan karda Aadil yakara barin Aysher tazo ta kwana a gida, "maza tashi kibi mijinki gobe mijinki zezo ya dauki amira tare zaku tafi can America wallahi bacin Aadil da bazan baku amira ba..."


Cikin farin ciki Aysher ta tashi itada zarah suka fice, bin bayanta yayi da kallo ganin tana murmushi shima murmushin yayi, godiya yasake yiwasu baffa, baffa yasake mishi fada akan bakomai ze dinga biye mataba, kudi yaciro wanda besan adadinsuba yaba baffa amma Sam yaki amsa ijiye musu yayi daganan yafice, bayan yafitane yasa yara suka dinga shiga da kayan abinci kala da kala, koda baffa ya fito yariga yaja motan sun wuce ga sauran kayan nan da aka fito dasu ba'a gama shiga dasuba murmushi baffa yayi yacema yaran su karasa shiga dasu, bayan sun gama ya dauki kudi ya basu sukace ai Aadil yariga yabasu.




Gaba dayansu suna baya zarah da Aysher hakan yasa yazama kaman driver dinsu bece dasu uppanba yaja zuwa gidan granny, dan tanata 'korafi.




Bayan yayi parking dukkansu suka fito, boyhelp din gidan ne yaja musu trolley din zuwa ciki.


Granny dake saukowa daga steps ganin yaron yashigo da kaya bayanshi zarah ne da Aysher se Aadil dake bayansu yasa ta d'aure fuskah tareda fadin."maza ku juya ku koma se yau kukaga daman zuwa se ana gobe zaku tafi nida naso ace a gidana kukayi one week din. " cikin shigan lallashi Aadil yace. "Sorry granny...."
D'aure fuskah tayi. "Zo nan Fatima. "


A hankali zarah ta matsa kusa da ita, kunninta ta riqe. "Kece kikace seyau zakuzo ko dan kece babba. "
Kaman zatai kuka tace. "Bani bace Aysher ce yanzuma da kyar tazo. "


Duban Aysher tayi. "Aisha zonan...."


Shagwabe fuskah Aysher tayi tareda 'boyewa bayan Aadil dan bataso a kama mata kunni, granny tace. "Mikomin ita aadilu maza..."


Dariya yasa. "Kiyi hakuri granny. "
"Bazaka mikomin itan ba to matsa ni inji dalili. "


Kara boyewa Aysher tayi a bayanshi, murmushi granny tayi irin nasu na tsofaffi tace. "Shikenan kai me mata ko, to inkun sake dawowa anan zaka barmin Aysher inga ta tsiya...."


A hankali yace. "Bace kin gan tanba...."


"Mekace aadilu...? "
"Bakomai. "
Murmushi tayi "ku shigo jikokina....."




Dining tasasu suka nufa seda tasasu sukaci abinci sosai sannan ta dubi Aadil. "wai Ina Aabidu yake saboda sha'kiyanci beje ya dauko matarshiba. "


Sosa kai yayi. "Bejin dadine. "
Amma a zahiri cewa yayi baze jeba ta shekara mana.


Be jimaba ya tafi yabarsu zarah, da granny ta hanasu bacci da sha wannan yi tsarki da wannan da kyar tabarsu suka yi bacci, suna jin dadin yanda dangin su Aadil da Aabid suke sansu kuma sunaji dasu.






Washegari.


Koda Aadil yaje dauko amira an gama hada mata kaya se murna takeyi, seda yakara sa aka shigar da wasu kayan sannan yatafi gidan granny ya dauki su Aysher da suka shirya, suka wuce gidan Mami.




Mamima kanta taji dadin jin zasu tafi da amira domin dama abinda ke ranta kenan, Aabid tunda aka fara musu nasiha kanshi na kasa har seda yaji an gama yadago haushi duk ya isheshi, zarah kam kuka tafara sosai, securities ne suka jasu dukkansu zuwa airport bayan Abie ya cikasu da sha tara na Arziqi.




Bayan sun tafi.


Duban Abie Mami tayi. "Am feeling comfortable ji yanda Aadil ke nuna kula ga aysher kaman ba auren had'iba yana bata wani Extra careful hakan ke nuna she's so dear to him, amma Aabid sedai addu'a. "


Wani murmushi Abie yasaki wanda yake nuni da abubuwa da yawa hakan yasa Mami saurin cewa. "Bangane murmushin da kayiba Abie... "


"Kema kanki na boye mikine ban fada mikiba amma aurensu Aadil ba kuskure akayi wajen canzawaba 'ki'kirarren abune..."


Dafe kirji Mami tayi. "Abie kana so kace dagangan aka canza Auren Aadil aka bashi Aysher Aabid kuma zarah.? "


Gyada kai yayi.


Mimi queen ✍️.
2022-06-24, 3:16 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*


*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._

Ba wanda

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads