Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 45461 words

Chapter 3 - NISFUL HAYAT Book Complete by Mimi queen.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

umarnin Mami ne...."


Yana fadin haka yasa kai ya dice, daidai lokacin Zara ke kiranta, da sauri tayi picking "Sis nayi kewanki ace muna gida daya amma yau kwana biyu bamu haduba..." huci zarah ta saki. "Nima nayi kewanki sosai yar uwata...."


Aysher tace. "Ya Aadil yacemin zamu tafi America ran friday harda kee..."
Kai zarah ta girgiza kaman aysha na ganinta. "Aa bansaniba....."


Huci Aysher tasaki. "Zamuje siyayya yanzu dan Allah kifito mu hadu na ganki konaji sauki ba abinda kemin dadi. " Zarah tace. "Okey to shikenan zan leko semuga juna....."


Nan suka katse.


Tashi Aysher tayi ta bude wardrobe doguwar rigar abaya ta saka brown tayi rolling gyalen tafice, tsaye ta sameshi yana ganinta yasakai yafice tabi bayanshi da sauri.






Zarah kam ta window ta hangosu dan haka da sauri ta tashi, sedai tana fitowa falo taga Aabid hakimce ya daura kafa kan center table yana danna system, da sauri ta koma saboda wani irin tsoronshi takeji.




Aysher kam ido taita zubawa ko zataga zarah amma shiru har suka shiga motan Aadil me numfashi suka fice,


Kanta na gefe kan hanya tana kallon yanayin unguwan gaskiya na wa'inda suka amsa sunan sune, shima kam hankalinshi nakan tuki a haka suka karisa babban boutique din na mata, fita yayi hakan yasa ta fice.




Kaf kayan matane hakan yasa yayi magana da wata ma'aikaciyar gun cikin yaren turanci akan ta zagaya da Aysha tazabi abinda takeso.


Riko hannunta matan tayi ta mata murmushi nan suka shige,


Pad kadai ta dauka domin tasan zatafi bukatanshi koda sunje kasar america ba tareda tafada maiba, dan ba abinda batada shi dan akwatu ashirun da hudu ko wacce ita da zarah su Aadil suka kawo musu kuma Kaf kayan kasar waje, dan haka ba abinda take da bukata bayan shi,


Rapping dinshi tasa akai mata sosai yanda baze gane ko meyeba, nan suka fito.
aka fada mishi kudin yazaro ATM suka bashi POS machine ya amsa yasa pin suka cire kudin.




Nan suka koma Mota, sun kusa isa gida se lokacin ta dan dubeshi.."Amma zanje inyi sallama dasu ummi ko....? " girgiza kai yayi "sedai in mun dawo...."




Daga haka bata sake maganaba har suka isa, daki tafada tasaki kuka tareda kiran ummi.


"Ummi sun rabani dake yanzu kuma zasu daukeni su kaini america hakan be musuba wai bazanzo muyi sallama ba, ummi nagaji kizo ki daukeni....." tafashe da kuka.


Lallashinta ummi tafara tareda kalamai masu dadi. "Aysha na kiyi hakuri ki dena bagani muna wayaba meyema se kin wani zo munyi sallama yau kwana biyufa kenan dayin aurenku kuma se aga kunzo me za'a yi tunanin kiyi hakuri kiyiwa kibi mijinki kiyi mishi biyayya kaman yanda yace sekunzo din to ki bari kuma banaso inkara jin kince kin gaji kin gaji da bauta ko me? dominfa ubangiji da kansa yakira aure da bautansa to idan kince kinfara gajiya tun yanzu kina nufin kin fara gajiya da bautan Allah ko me, banaso 'yata karna karaji kinji..... " gyada kai tayi kaman Ummi na ganinta.








*******
Tun zarah na tunanin Aabid ze mata maganan tafiya harta dena yanzu kam ta dauka Aysher da Aadil ne kawai zasu tafi danko ba abinda yafada mata.




_Ranar Friday_


Tana zaune a falo domin yanzu takan fito falo ta zauna kota ganshi ta gaidashi baya amsawa.


Fitowa yayi cikin shigen kayan Nigeria air force yayi kyau sosai, dubanta ya danyi. "Tashi ki shirya kifito zamu wani guri kuma karki dad'e......" wannan shine karo na farko daya taba mata magana dasauri tayi ciki, doguwar rigar atampha tasaka brown me touch na milk tayafa milk gyale ta fito.


Baya dakin hakan yasa tayi waje, cikin mota ta hangeshi kofan motan a bude kafanshi na waje hakan yasa a hankali ta karisa ta bude gaba ta shiga.


Tana shiga ya tada motan zuwa gidan Mami.




A can suka tadda Aysher da Aadil, Aysher na sanye cikin pink material tayi kyau tayafa gyale pitch, Aadil kuma black suit sunyi kyau.


Da sauri suka kariso da sauri zarah ta nufi Aysher sunama juna murmushi, rungume juna sukayi Aysha tasa kuka.


Kallo guda Aabid ya musu ya dauke kai domin ya riga ya haramtawa kanshi Aysher dan matsayin matan Aadil yake daukanta yanzu dukda yana jinta a zuciyarshi har yanzu, shima a bangaren Aadil haka yake daukan zarah yanzu matsayin matar yayanshi.


Daidai lokacin Abie da Mami suke saukowa daga sama, Murmushi mami tayi na farin ciki. "Shikenen suma su Aabid din sun kariso...." sakin juna sukayi suna gaidasu Abie.


Suma gaidasu su Aadil sukayi.


Suka amsa suna Murmushi sunajin dadin ganinsu.




Nasiha sosai Ummi tafara musu akan suji tsoron Allah suyiwa mazajensu biyayya su kuma su rike mata daughters amana.


Ta kare da fadin."sedai kun kawo mana ziyara kafin nan ina fatan nasamu jikoki....Aabid yaushe flight dinku ze tashi....."


Aabid daya wani sha mur jin abinda mami tace yace. "Ba dadewa...." maida dubanta tayi ga zarah dase yanzu ta fahimci abinda ke faruwa. ". 'Yata Allah tsare..." rungume juna Aysha da Zara sukayi suna kuka sosai me ban tausayi, dan karamin tsaki Aabid yaja yanajin kaman yatafi yabar zarah, jinjina kai Mami tayi cikin tausayawa. "Allah sarki en uwa..."


Dubansu Aadil tayi. "Ku bamu guri zamu sirri da yarana...."


Da sauri duk sukai waje, ta dubi Abie. "Harda kai...." Murmushi yayi ya tashi yana fadin."bantaba ganin inda ake Koran miji saboda yaraba...."


Yana hayewa mami ta dagosu tana share musu hawaye. "Kuyi hakuri kunji yarana ai zaku dawo zaku dinga zuwa mana hutu...."


tashi tayi ta haura sama bata jimaba ta sauko tana jan wasu manyan trolley guda biyu
Karisowa tayi ta diresu gabansu. "Ga wannan turarruka ne na musamman tun daga saudia dana jiki dana daki akwai na mitstsikawa a gaba da mama kudinga amfani dasu domin mazajen naku sunasan kamshi sosai.....sannan ko waccenku Abie yabata kyautan miliyan biyar yana hannun mazajenku duk wacce take bukatan kudi kawai kuyi musu magana zasu baku ku kula sosai yarana......"


Godiya sosai suka fara mata, nan ta riko hannunsu suka fito yayinda tasa akaja trolley din zuwa waje.


Kiss ta manna musu. "Am sorry yarana bazan samu daman rakaku zuwa airport ba se munyi waya..."
Kowacce har gaban motan mijinta tasakata yayinda kowacce aka saka mata trolley dinta a boot nan ta musu waving,


Motan Aadil ne tafara fita sena Aabid se bodyguard da sojoji dake binsu a baya.




In banda kuka ba abinda zarah da Aysha suke, yayinda zarah takeyiwa Aabid kallon me san kai be fada mataba ko sallama dasu ummi tayi, yana gefe driving yake amma kukan zarah ya isheshi, dan tsaki yaja tareda wurga mata hanky dago kai tayi takalleshi ko a jikinshi sema maida kanshi da yayi ga titi kukanta taci gaba.




Suna isa airport dukkansu suka fito....


Nanma Aysher suka sake rungume juna, suna isa jirginsu Aabid nayin slow dan haka ya rumgume Aadil tareda fadin. "Take care Dil...." gyada kai Aadil yayi.


Duban zarah yayi. "Let go...."


Nan Aysher ta sake sakin kuka, da kyar suka rabu su zarah suka shiga jirgi.




Special part yake ko a cikin jirgin, dan inda aka ware mishi nashi shi kadai harda bed na bacci, da kujerun cin abinci da bayi,


Guri yasamu ya zauna, dukda akwai wasu kujerun dayawa amma kusa dashi zarah ta zauna.
Tsoro sosai tafara ji jin jirgin ze tashi yasa batasan sanda ta kankame Aabid ba ta cusa kanta cikin kirjinshi tafara kuka ido ya zuba mata.




Har jirgin ya daidaita a sama kanta na kirjinshi ta kankameshi tana kuka, a dake yace. " dan sakeni ko madam...."


Se lokacin ta dago jin jirgin ya daidaita ta sakeshi tareda jingina jikin kujeran ta lumshe ido.




Dan tsaki yaja ganin yanda ta 'bata mishi jiki da jan baki ga hawaye sosai a jikinshi, zare belt yayi tareda tashi ya nufi bayi, koda ya fito ya taddata a yanda ya barta guri ya canza ya zauna domin ya canza shige.






*****
Aadil ko zubama Aysher ido yayi ganin yanda take kuka, dan huci ya saki. "Sannu me er uwa..." Ido ta bishi dashi.
Ya daga kai. "Ai kinsan er uwar Kice kadai ta tafi ni dan uwana be tafiba meyasa ni banyi kukaba se ke kin wani isheni da kuka....mtssww u better keep ur mouth shut ko in kira Mami....." shiru tafara kokarin yi, basu jimaba jirginsu ya tashi zuwa America, dukda Aysher taji tsoron tashin jirgin kujeran data ke kai ta kankame domin suma special place suke a jirgin kuma ba guri daga suka zaunaba dataga ya zauna seta canza guri.






#####
Suna isa 9ja jerin motoci sukazo suka daukesu zuwa dankareren gidan Aabid,


Gidan ya hadu ainun babban mansion ne upstairs me dauke da bangarori da dama, wani daki ya nuna mata a sama. "Nanne dakinki..."


Trolley din da mami ta basu taja zuwa cikin dakin.


Bedroom din ya hadu sosai komai da milk, wardrobe ta bude nan taga cike yake da kaya dsnkare ga wasu dan'kara dan karan akwatuna nan ta bude suma cike suke da kaya na mata kala da Kala dama an zuba sune saboda ita, ga jerin takalma, jagunkuna da kayan kwalliya dasu sarqa, dan kunni da abun hannu tareda turarurruka masu tsada kala daban daban.
. ba abinda babu na bukatan mace a dakin.


Kaya ta cire taja towel data gani sabo agefen gado ta shiga baya, nanma an zuba komai hatta pad da sabbin brush gasunan da yawa.






*******
Manya manyan motoci ne sukazo airport din america daukan su Aysher, Aysher tayi mamakin ganin yanda ake girmamashi manyan turawa sojoji haka suke sara mishi, aka daukesu zuwa gidan Aadil daya hadu dan yamafi gidansu na Nigeria wanda turawa, indiyawa sune ma'aikatan gidan.




Gidan na samane, suna shiga shima ya nuna mata wani daki kusa da nashi yace, nanne nata har zata shige yayi saurin fadin."ga wannan Wayane nasa miki sabon sim kiyi amfani dashi inkikai kira da naki baze jeba...."


Amshewa tayi da sauri ta shige dakin, dakin ya hadu komai pink best color dinta kenan, itama ba abinda babu a dakin komai kusan pink ne hatta bayin, murmushin jin dadi tayi ta fito muryan ummi kadai takesan ji.


Wayan ta dauka IPhone 13 max ne kunna wayan tayi da sauri tasa numban ummi.
"Ummi mun isa...."


. "Yawwa er albarka Ashe itama zarah sun tafi minna dazu mukai waya take fadamin suma sun isa..."


"Eh ummi."
. "to er albarka yame gidan naki...."


Daidai lokacin ya shigo harya canza shige hakan yasa tace." Ummi yana lafiya...."


A sanyaye yace. "Ummi ne... "? Kai ta gyada, ya mik'a hannu. "Bani ita mu gaisa...."


Ba musu ta miqa mishi ya amsa ya kanga a kunni tareda gaida ummi, ta amsa. "Lafiya klau d'ana kun isa lafiya ya hanya..."?
"Lafiya klau ummi ya baffa da amira.? "


. "suna lafiya Amira na gaidakai..."


Yace. "Bata mu gaisa..."


Nan ummi ta ba amira suka fara waya, haushi Aysher tafaraji tana waya da Umminta yazo ya amshe kuma be bataba bayan sun gama waya da Amira katse wayan yayi ya mik'a mata tareda fadin


. "Tashi muje muci abinci..."


Gyale ta dauka suka fito, se taga sunyi waje hakan yasa tabi bayanshi,


Wani babban gurin cin abinci sukaje ido Aysher ta bude tana kallon kasar gaskiya akwai kallo a duniya, seda sukaci abinci sannan ya maidasu gida nan kowa yayi dakinshi.




Zarah kam bayan ta gama wanka ta fito, dukda tanajin yunwa hakanan tayi sallah ta kwanta domin ta gaji sosai.






Comment please 🙏.
Mimi ✍️.
2022-06-21, 7:05 a.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*


*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._

Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*


11& 12.






Washe gari.


Da wuri Aysher ta tashi tayi sallah ta sauko kasa sedai ta taras an gama komai har breakfast an gama yana dinning room,


Seda tayi break sannan ta fito ta koma sama danta shirya.




.......
Zarah tunda asbah ta shiga kitchen ta soya indomie taci saboda wani irin yunwa da takeji , sannan takoma daki tayi sallah ta koma bacci.


Seda gari yayi haske sosai sannan ta farka, ta taras an gyara gidan sosai fitowa falo tayi tana hamma, a hankali ta karisa dinning room takara cin abinci kadan sannan ta sauko falo ta zauna tana kallon Network news.




Aysher na zaune suna waya da Mami, Aadil ne ya shigo da sauri ta sauke wayan tana gaidashi, ba tareda ya amsaba ya mika mata ledan dake hannunshi.


"Kisa wannan anjima zamuje wani guri ogan ninane suka shiryamin party yau na murnan aurena anjima da daddare zamuje banaso su fahimci komai kisaki jikinki....."


Kai ta gyada, yayinda ya fice.


Kayan ta juya bisa gadon, wandone na sojoji se T-shirts irin nasu da hulan sojojin hatta bangles, da sarka da dan kunnin duk kalan kayan sune, tab'e baki tayi.




Se dare Zarah taji shigowan Aabid dan banma tasan sanda yatafi gun aikiba, da sauri ta mike zata haye sama, yayi saurin dakatar da ita.


"Keee...." Chak ta tsaya, karisowa yayi a dake yace. "Gashi Mami nasan magana dake...."


Mika mata waya yayi da sauri ta amsa, barin gurin yayi hakan yasata saurin kanga wayan a kunni.


"Na'am Mami, ina yini..."


a can bangaren Mami murmushi tayi. "Lafiya klau yar albarka tun jiya nake kiran wayanki baya zuwa meya samu wayan....? "
. "wallahi Mami nima bansaniba kawai ya dauke ne namasha ba chajine to nasa amma yaki kawowa..."
Shiru Mami ta danyi. "Okey bari zanyi magana da Aabid din, bashi wayan...."


Sama ta haye nan ta sameshi zaune a falon saman, da sauri ta mika mishi tayi ciki.


"Mami inaji."
"Aabid wayan Zara yasamu matsala...."
Mami ta fada, cikin ko in kula yace. "And so ni Mami ba kudi a hannuna banda kudin siya mata wani wayan...."
Cikin fada Mami tace. "To meye amfanin kudinta dake hannunka, kuma ballema nasan karya kakeyi wallahi kace bakada kudi haba Aabid.."
"Okey Mami zanyi amfani da kudinta in siya mata wayan, okay..? "


Tsaki Mami taja tareda katse wayan tana fatan Allah canzawa Aabid hali akan zarah.




*******
Tsaye yake yana jiran Aysher ta fito, wandon sojojine a jikinshi da T-shirt din sojojin se hula hatta takalmin kafanshi, agogonshi kalan kayan sune kallo guda zaka mishi katabbatar kayan ya dace dashi, yayi bala'in kyau.


Fitowa tayi tana mammatse jiki domin ko hijab babu a jikinta, dago kai yayi yana kallonta, desame shige kala daya suka tasa wandon sojoji da T-shirt se hula irin wandon akanta p-cap, ta jefo tulun gashinta ta baya, batai wani make up ba kwalli da lipstick kadai tasa amma tayi kyau matuka komai nata na sojojine bakaramin kyau tayiba.

Kallo guda tamai ta sadda kanta kasa saboda wani irin kwarjini da cika ido da Aadil yake dashi ba kowacce mace bace zata iya kallon kwayan idanshiba,


Gaba tayi yabi bayanta, dukkansu suna wani irin fitinannan kamshi.


Gaban motanshi kirar Audi ta bude ta shiga, yana karisowa yashiga mazaunin driver yaja suka fice yayinda motocin sojoji tara ke binsu a baya.


Hanya taketa kallo tana kallon kasar na US , gani take kaman a mafarki.


Gab daya she's not comfortable tafiya suke kaman bazasu kaiba can lekki sukaje sukai parking a parking lot na Nire prest boat activities dubanta yayi. "Muje kuma salan kita wannan jin kunyan naki kisaki jikinki bakisan kowa a gurinba duk ba en Nigeria kinji party za'ayi a cikin Boat ki natsu kinji ko? babban boat din US kenan.... "


Kai ta gyada gabanta na faduwa, fita yayi ya zagayo ya bude inda take tareda mik'a mata hannu, kafin ta bashi ya janyota waje tareda rike mata hannu, a sanyaye yace. "Ki zama matar soja mana karki badani duk abinda zanyi......"


Batace dashi komaiba, suka karisa waterfront din yayinda sojoji kusan 20 ke binsu a baya, kallon katoton babban boat din da akai decorating da flowers seablue take, sojojine zagaye da gurin kasancewanshi sojan ruwa wow gurin ya k'ayatu matuka gaba daya decorating din dake gurin da kalan kayan sojojin ruwa akayi komai ,
hatta carfet din da aka shimfida musu tun daga parking lot har zuwa inda su Aadil zasu zauna kalan kayan sojojine,


Jan hannunta yayi suka shiga kirjinta wani irin bugawa yake kaman zai tsage da sauri ta sake dam'ke hannunshi ,


Suna gama shiga jirgin yafara gudu a cikin babban ruwan america, da sauri tasake riko hannunshi bakinta har rawa yake tanaso tayi kuka tace. "Ya Aadil wallahi am scared please banaso wannan 'katon jirgin I don't like water. " hararanta yayi. "Aise kiyi tsalle ki fada ruwan, look back kiga yanda mukai nisa da wurin da muka bari yanzun nan, jirgi tafiya yake idan kuma you can swim back there bismillah. "




Girgiza mai kai tayi hawaye ze zubo mata tace. "To please hide me am shy and am feeling somehow mutane sunyi yawa. "


Tsaki yaja ya jata by fire by force sukai saman jirgin asalin party floor din,
Wow this is paradise busa hall din ya dauka Aadil na shigowa tareda sakin harbin bindigogi yayinda sojijin da suke gurin suka kame tareda yin salute, wasu flowers ne kalan kayan sojoji yazubo akansu balo balo suka fashe, salute Aadil yayi cikin tafiyan cikakkan soja ya isa har zuwa gaban manyansu ya musu salute tareda runsunawa, itadai Aysher nata binshi tsoro ne yakamata jin karan bindiga.


Dan dazon sojojin data gani a gurin sun bata tsoro dakewa kadai tayi tana bin Aadil,


Kaf mutanen dake cikin Boat din kusan irin shigensu sukayi badda ogan ninsu, sedai sukuma normal wandon su sukasa bana sojojiba se rigan sojojin da normal hula ko wanne da matanshi irin shigen da sukai kenan,


Kan high table dake can sama suka karisa sojoji na mara musu baya yana zama da sauri itama ta zauna sukuma sojojin suka kakkare bayansu da gefensu, gabansu cike yake da abubuwan ci da sha.


Tsorata tayi har batasan sanda ta kankameshi ba ganin jerin bindigogin da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads