Showing 3001 words to 6000 words out of 45461 words
Chapter 2 - NISFUL HAYAT Book Complete by Mimi queen.txt
an gama aka soma rabon abubuwan kayatarwa, lalle turare littafan addu’o hisnul Muslim da sauransu haka kowa ya watse yana murna.
Daganan aka soma shirya shiryen kai Amare gidan mahaifiyar angwaye.
Gidan mami akayi da amare, inda ya cika da su yan uwan su Mami dana Abie, matan su Uncle da yan uwa da abokan arziki, da kawayen mami, wa'azi sosai akai ma amare sanan aka fara masu manni ana liki ana rawa kafin abama mami wuri, Mami ta taso tai shiga na alfarma tana murmushi sosai danyau tana cikin tsananin farin ciki tazo ahankali ta yaye hulan alkyabban, fuskar Aysha yafito tana kuka kanta akasa, guda aka dauka ahankali Mami tabude wani dan box dake hanunta taciro wani sarkan gold babba nan aka fara guda dan al'adan sune hakan, ta sanyama Aysha sarkan awuya sanan takamo hanunta tasaka mata warwaro biyu takamo dayan hanun tasamata biyu sanan ahankali tai cupping fuskarta tana murmushi tace "welcome to the family daughter na" ta sumbaci gaban goshinta nan dakin yadau guda anata ihu da ayiriri,
Hulan Alkebban zarah tayi kasa dashi kuka sosai itama Zarah take sarkan da bangles din na gold tasakawa Zarah taredayin murmushi feeling so happy tanajin yaran har can Cikin zuciyarta,
Fuskar zarah ta shafa tareda fadin. "Stop crying daughter na".
Kiss ta mannawa zarah a forehead ta tashi takoma sit dinta nan haka kowace matan dakin ke tasowa one by one suna basu gift sosai Aysha tagaji iya gajiya danhar ji take kaman zata sume,
Mami nata rabon atampopi super super da bargo, glass cup, flakes, dukna kasar waje.
Sai wuraren sha daya sannan aka dugunzuma dasu zuwa gidansu Aabid, da Aadil dake nan cikin GRA, horn sukayi mai gadi yabude babban gidane sosai kato dake dauke da bangare biyu left da right duk duplex ne same design
Kowa bangarenta aka nifa da ita dakeda wani irin mugun kyau ana wake wake,
Alwala akasa Aysha tayi sanan aka bude dakin aka shiga da ita, dakin na wani irin hadadden kamshi turarukan wuta, babban falone da akai komi ash da black aka wuce da ita bedroom dinta dakenan off white da gold akazaunar da ita akan makeken gadonta, family Aadil bayan sun gama yan wake wake da wa'azi suka juya suka mata sallama suka nufi bangaren Zarah da wasu en uwan suka rakata.
Comments more.
Mimi ✍️.
2022-06-11, 4:41 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*
*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._
Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
5&6.
Aysher na ganin an watse an barta tafara kuka kaman wacce ake yankan naman jikinta.
A bangaren Zarah kam, shiru tayi yayinda ta zubama kofa ido tana jiran taga ko akwai wanda ze shigo domin yanzu ita ta sadaqar ta mik'a komai gurin ubangiji,
Sosai Aysher ke kuka.
Wajen 12 na dare su Aadil suka shigo gidan dan harsun kwanta mami taje ta tashesu tamatsa su tafi gidansu.
Aabid ne yafara fitowa daga motan cikin fushi dan Aadil ne yayi driving din, Aadil ya lura da haka shiyasa koda ya fito bece dashi komaiba koda yaga yayi hanyen part dinshi shima se yayi hanyan nashi.
Tun daga falo yakejin kukan Aysher, bedroom dinshi yashige yana shiga ya cire kayan jikinshi ya fada toilet, koda yafito still kukan na damunshi da sauri ya zura jallabiya yayi waje.
Aabid ko yana shiga kai tsaye bedroom dinshi ya shige, wanka ya cillo ya fito tareda sa sleeping dress ya kwanta, zuciyanshi namai kunan yau ba Aysher bace kusa dashi duk burin da yaci.
Zarah kam taji shigowan Aabid tsorone ya kamata na irin rayuwan da zasuyi dan tasan Aabid beda fara'a sosai kaman Aadil.
Tayama Zata iya rayuwa da Lieutenant Aabid a haka wani wahalallan bacci ya dauke Zarah.
Tsaye yayi bakin kofa ya zuba hannayenshi bisa aljihu yana kallon yanda take raira kukan ya kasa tsayar da ita dan besan dame ze faraba,
Duk da taji kamshinshi hakan behanata raira kukan taba, ficewa yayi da sauri hakan yasa ta dago kai tabi bayanshi da kallo tanaci gaba da kukan.
Ko 30mnt beyiba yadawo dauke da ledojin restaurant, zuwa lokacin ta hakura tayi shiru ido ta bishi dashi harya kariso yana mata Murmushi ya dire ledojin bisa bedside table a sanyaya yace
. "Bundle and eat something kukan ba abinda ze miki......" Kwalakwalan idanunta ta bishi dasu.
Yana fadin haka ya fice.
Ido ta lumshe tana tunanin taya zasuyi rayuwa da Captain Aadil, a haka wani bacci itama ya dauketa.
**********
_Asalinsu._
Mahaifinsu Aabid His Excellency Abubakar maina, haifaffan garin bauchine su biyu Granny ta Haifa shida kaninshi Sulaiman (uncle) , Mami wacce asalin sunanta halima ta kasance yarinyar kanwar granny iyayenta sun rasu tun tana karama hakan yasa ta taso a hannun granny.
Tun tana karama Abie ke Santa hakan yasa data girmata kammala karatunta se aka musu aure lokacin Abie yafito takaran gwamnan bauchi cikin ikon Allah yasamu nasara nan sukaci gaba da rayuwa,
A lokacin mahaifinsu ya rasu dan haka suka zama gatan uwarsu, yayinda Sulayman ya auri maryam yanzu haka yaronsu daya tal Farooq sa'an Aadil ne.
Haihuwan fari Allah yaba mami ciki ta haifi da namiji hakan yasa aka samishi suna Aabid, Aabid kyakykyawane tun yana yaro ga farin jini wani irin mugun so Mami da Abie suka daura mawa Aabid.
Aabid nada shekara daya mami ta samu wani cikin ta haifi Aadil tsakaninsu ba wani tazara dan a lokacin granny ita ta amsa Aabid ta yayeshi da kyarsu Mami suka batashi aiko har ciwo yayi.
Sedai duk san da suke tunanin suna yiwa Aabid suna haihuwan Aadil se gaba daya sanshi ya rinjayi na Aabid domin kam watanshi hudu a duniya yafara ciwo, tari sosai harya fara na jini koda sukaje asibiti aka tabbatar musu da ciwan Asma Mami ta haifeshi, hakan yasa hankalinsu yakoma kanshi aka fara bashi magunguna a haka harya taso da cutan.
Sun taso kansu daya a had'e kaman en biyu dan wasuma da dama sun dauka twins ne, cikin soda kaunan junansu Abie da Mami suna sansu fiyeda rayuwarsu haka granny da uncle suke jinsu domin yaran akwai saurin shiga rai barinma Aadil dan yafi Aabid fara'a dashiga mutane.
A kasar England sukayi primary da secondary schools dinsu bangaren islamiyya makam suna zuwa na wani balarabe daya bude a kasar da 'ya'yan musulmai tahfiz in suka tafi ran Saturday da sunday tun safe se dare.
Aadil nada 15ya haddace alqur'ani, Aabid kam seda yakai 20 zuwa lokacin Abie yasauka a matsayin shi na gwamnan bauchi ya zama ex.
A Lokacin suka fara university Aadil fannin sojon ruwa wato navy marine army, yayinda shikuma Aabid fannin Air force.
Aadil yazabi kasar America yayinda Aabid yazabi London.
A London Aabid ya hadu da abokai suka fara canza mishi hali yafara shaye shaye batareda kowa yasaniba, yafara neman en mata.
Tun ba'a ganewa har aka fara gane yana shaye shaye hankalin Abie yatashi sosai hakan yasa yatakura seda ya dawo Nigeria to anan ya karisa university din yayinda suka sa mishi ido dukda haka bawai yadena bane dukda suna iya kokarinsu.
Koda suka gama karatu har PHD sunyi tuni sojojin US sun fara neman Aadil yashiga cikinsu saboda a year din yafi kowa cancanta, seda ya bi shawaran Abie sannan ya amince yafara aiki da coast guard, yanzu haka shi sojan coast guard ne na America.
Aadil ko Abie sam yaki yarda ya koma kasar waje hakan yasa yasamu aiki a Nigeria Air force agent duk dako shima yafisan Nigeria dan Jamima kawarshi da suke holewa ta dawo Nigeria dan er Abuja ce hakan yasa, yasan yanda yayi akai posting dinshi acan sukaci gaba da holewa.
Wani dawowa da sukayine shida Aadil ya hadu da Aysher daganan ya kamu da matsanancin kaunarta, yabi ya matsawa kowa a lokacin har yake fadawa Aadil akan Aysher ze iya komai, hakan yasa Aadil yakosa yaga wacce tayi sa'an nan, hakan yasa yace yaji zejawo hankalin Abie ya aura mishi ita amma se yayi alkawari ze dena duk abinda yakeyi na shaye shaye da neman mata domin ba abinda Aadil be saniba, ba bata lokaci yayi mishi alkawari domin yana santa sosai.
Da kyar Aadil yajanyo hankalin Abie ya amince domin dukkansu sun fisan Aadil saboda rashin lafiyan dayake dauke dashi kuma Abie bashida burinsu Aadil su auri er Nigeria Amma seda Aadil yasan yanda yayi ya amince,
Da sukaje ganin tane Aadil yaga zarah nan shima ya kamu da santa ba bata lokaci yafadi, ba a dau lokaci me tsawoba Abie da uncle sukaje suka samu mahaifinsu aka tsaida magana.
Hakan yasa Aabid yabar duk abinda yakeyi yanemi transfer yakoma 9ja (Minna).
Tun daga karamin matsayi gashi yanzu har Aadil yakai matsayin captain saboda jajir cewa dan yana daga cikin wanda america ke alfahari dasu, yanzu shima Aabid yana matsayin Lieutenant Aadil yanada 29yrs Aabid kuma 30.
Wannan kenan.
_Asalinsu Aysher da Zarah_
Asalinsu cikakkun buzayene
Baffa (Abubakar) shine yaron sarkin Agadas sarkin bararoji na hudu yanada yayyi uku da kannai Uku, auran zumunci aka mishi da ummi me suna Rabi'atu.
Bayan rasuwan sarkin Agadas ne aka nada babban dan shi a matsayin sarki,
Daganan baffa yabar kasar Agadas domin yanada sha'awan zaman Nigeria hakan yasa ya sauka a garin bauchi ya bude gidan kaji yana saida kwayayen da kajin a haka suke rayuwa shida ummi harta haifi Shattima,
Bayan Shattima seta haifi zarah daga zarah se Aysher se Amira daga kan Amira bata sake haihuwaba.
Zarah da Aysher yarane kyawawa amma Aysher tabi Zara hasken fata da kyau da cikowa, sunada kwakwalwa ga saurin daukan abu tun suna 10 suka haddace alqur'ani.
Ga kokari boko da arabi sun taso kusan kansu daya.
Har suka gama secondary school yanzu haka zarah nada 20 a duniya Aysher kuma 18.
Wata rana Aysher ta dawo daga islamiyya tanata sauri a lokacin ta hadu da Aabid, yanemi tatsaya amma sam taki hakan yasa ta kara burgeshi daganan ya binciko inda take.
To kunji asalin kosu su waye yanzu aka fara.
Comments more darling.
Mimi ce✍️.
2022-06-11, 4:41 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*
*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
_____________________________________
_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._
Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
7&8.
Daga Aysher har zarah ba wacce ta makara dan Aisha akan sallaya Asbah ta risketa.
Zaune Aysha tayi gefen gado tayi zuru zuru, idannun nan sun kara ciccikowa dama gasu tubarkallah.
Knocking din kofa taji anayi da sauri ta tashi tareda daukan karamin gyale ta rufe sumarta ta bude kofan, wata maid ta gani runsunawa tayi. "Hajiya breakfast din yazama ready....." Kai ta gyada tareda maida kofa ta rufe.
Ledojin da Aadil ya kawo mata jiya ta dauka tayi waje, kitchen ta shiga ta ijiyesu kan table ta koma dakinta ta kwanta wani baccine ya dauketa.
Bangaren zarah kam bayan tayi Asbah ta fara karatun Al Quran, se wajen 9 sannan wata maid take zuwa fada mata breaks is ready, tashi tayi ta rufe Alqur'anin ta maidashi mazauninshi tayi waje dan wani irin yunwa takeji, bata samu kowa a falonba hakan yasa ta nufi dinning ta zauna.
Arish din tazuba a plate ta hada tea tafara sha.
Muryan Aabid taji yana fitowa yana waya cikin daddad'an muryanshi. "Okey I will be there soon, it's so awful....."
Da sauri taja gyale takara rufe jikinta.
Kallo guda yakaiwa inda take ya dauke kai tareda ficewa, baki ta tab'e bayan ta gama break dinta ta koma daki.
A compound din gidan yaci karo da Aadil yafito yanufi parking lot, murmushi Aadil yasakin mishi tareda fadin. "Bid are yhu ok.....? "
Dan karamin tsaki yaja. "Bansaniba din se yanzu zaka damu ka tambaya.....? "
Hannayenshi ya hada. "Am srry my twin bro....ina zuwa in dis earlier of d morning.....? "
. "Inda zakaje..."
Da sauri Aadil yace. "Ni ai gaida Mami zani. " Aabid yace. "Serious nima can zani......"
Mota Aabid ya bude. "Let go right...."
Aadil yayi murmushi yashige gurin me zaman banza.
******
Aysha kam yunwane ya farkar da ita daga nauyayyan baccin da tafada, wani irin yunwa takeji dan rabonta datasa wani abu me nauyi badda ruwa a cikinta yau kwana uku kenan cikinta har murd'awa yakeyi saboda yunwa.
Hakan yasa tayi waje lokacin two na nemanyi dan an kwashe breakfast an zuba na Lunch a dinning din.
Zama tayi tareda daukan dish ta bude warmers din white rice ne hakan yasa ta dingi bude sauran.
Kuskus kadai ta tsakura da kayan ciki ta tashi ta fara karewa dakin kallo, komai na gidan su Aadil suka zuba dansu sunce basu bukatan komai Amma dukda haka seda baffa yasiya musu kayan daki a wani part aka zuba daban yayinda na nan duksu suka zuba.
Fada Mami tafara musu akan me suka baro matansu da safen nan.
Shiru sukayi, yayinda ta nisa kana taci gaba.
"Sannan nanda sati daya zaku kai su Zara suyi Umra a saudiya kafin suje aikin hajjin dagacen seku wuce India kuyi honeymoon daganan se kowa yakoma bakin aikinshi......"
Dukkansu kansu na qasa se lokacin Aabid yadago ya kalleta tareda fadin. "Mami agun aiki hutun sati daya kadai aka bani Dan Allah Mami ki yarje mana mukoma bakin aikinmu nanda mako daya inyaso daga baya makaisu umuran......."
Shiru mami tayi a hankali tace. "Naji amma sedai dukkanku kowa ze dau matarshi zuwa inda yake aiki inyaso kwadinga zuwan mana ziyara......."
Aadil ne yace. "Mami kinsan......" Katseshi tayi da sauri. "Banasan jin komai umarni nake baku ba shawaraba indai kunaso kukoma gurin aiki nanda one week toba dole sedai ayi yanda nace idan kuma kunce ba hakaba tofa dole kukaisu suyi umura daganan ku dawomin dasu kuma duk karshen week zaku dinga daukansu suje can su kwana biyu su dawo......."
Shiru sukayi dukkansu yayinda suke ganin mami ta takura musu, baki Aabid ya zunb'uro mami tayi Murmushi. "Kayi kagama dole ku zabi daya....."
Da ido Aadil yayiwa Aabid alama gwafa Aabid yayi hakan yasa Aadil cewa. "Mami mun yarda zamu tafi dasu din nanda sati dayan......."
Murmushi tayi. "To Allah muku albarka se kuje kufadawa matan naku sufara sallama".
*****
kanshin designer turare Aysher taji da sauri ta juya inda suka hada ido da Aadil daya shigo yanzu bema lura da itaba.
Runsunawa tayi har qasa. "Ina yini ya Aadil..." Kai ya daga tareda fadin. "Lafiya klau ya gajiyan biki...."
A hankali tace. "Lafiya klau....."
Ciki ya shige yayinda ta tashi itama ta koma.
Tun biyu suka fara ganin baki en ganin amare barinma dangin su Aadil da sukeda yawa sosai, maids ne suke zubo musu snacks da drinks da abinci duk Wanda yazo haka yake tafiya yana santin gidan da Kuma yaba kyau irin na amaren, yayinda duk wanda yazo ze tafi se an bashi jaka me hade da hotunan Amare da angwaye a zuba snacks da sebinnias a ciki da drink,
Wasu en bakin cikin haka suke tafiya cikin hassada.
Karfe hudu en uwansu sukazo, sosai Aysher taji dadi na ganin Amira nan su Iyatu suka kara taho musu da saqon Ummi tururrukane na jiki dana daki tareda wasu magunguna na mata.
Se lokacin ne Aysher ta saki jiki tayi fira sosai.
Seda Iyatu da sauran en uwa suka sake musu nasiha sosai sannan suka koma, sabon kuka Aysher tasa nan suka tafi suka barta tana rerawa......
Mimi queen ✍️.
2022-06-11, 5:54 p.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*
*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
_____________________________________
_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._
Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
9&10.
Ranar Monday.
Aysher na zaune cikin daki domin ba abinda take se zaman daki, waya ta dauka ta latsa numban Ummi, seda ya kusa tsinkewa sannan ummi ta dauka.
"Assalamu alaikum Aysher na......." Aysher najin muryan Ummi tafashe da kuka sosai Ummi tahau lallashinta.
Cikin kuka tace. "Ummi nayi kewanki sosai Amma ke baki nawaba na Zarah kadai kikayi..."
"Injiwa....? " ummi ta tambaya, aysher tace. "Ai ita kike kira ni baki kirana kona kira baki dauka....." ta sake sa kuka.
Ummi tayi murmushi. "Saboda nasan wannan kukan shagwaban naki zakimin shiyasa my daughter Amma nima nayi kewanki....."
"Ummi ina baffa da Amira..." "suna lafiya yame gidan naki...." a sanyaye tace. "yana lafiya...."
Ummi tayi saurin cewa. "Ina aikine yanzu anjima zamu waya ki kula...." tana fadin haka ta k
watse wayan.
Lumban zarah ta lalubo sedai bata kai da dialing ba taji alamun bude kofa alaman za'a shigo, da sauri taja hijabi ta zura.
Aadil ne yashigo sanye da white jallabiya irin na saudi Arabia yayi kyau matsuka se fidda kamshi yake, dan lumshe ido tayi ita kanta tasan Allah yayi halitta.
Runsunawa tayi ta gaidashi, kai ya gyada ba tareda ya amsaba.
Shiru sukayi yayinda tafara wasa da yatsun hannunta.
"Ranar friday zamu wuce America Mami tace nakaiki koda abinda kikeda bukata ki siya...." a sanyaye tace. "Niba abinda nake bukata...." kai ya jinjina. "Okey amma dukda haka ya kamata kishirya muje saboda