Showing 51001 words to 54000 words out of 138623 words
Chapter 18 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt
san asalin su ba haka rana tsaka muka gansu a gidan munafukan Allah asirin ku ya tonu," wata da ga cikinsu ma ta ƙara da cewa"maganarki gaskiya ce maman baffa yara sai shegen kyau ga rashin son shiga mutane ashe su suka son me suke ƙullawa, dama ance tsintacciyar mage bata mage wlh dole mu ɗaukar mata fansa tunda ku bakusan halacci ba, ta janyo ku inuwa kun kaita rana har kunyi silar mutuwarta,'
Nan fa wuri ya ɗau cece kuce hayani ta cika wurin, mamansu mamee na ƙoƙarin ta kare su amma abun yaci tura,
Ga matasan dake waje jira suke kawai a basu dama su halakar da yaran dama haushinsu suke ji saboda rashin basu haɗin kai, basa kula kowa yau ga dama ta samu,
Hankalin husanna ba ƙaramin tashi yayi ba ita dake zaune ido biyu tana jin abunda mutane ke cewa ita kuwa jahad har yanzu bata farfaɗo daga suman da tayi ba,
Mamee ce ta taimaka ta ɗebo ruwa a cup suka yayyafa mata, da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi idonta sunyi jawur, bala'i biyu ga raɗaɗin da take ji a zuciyarta ga kuma abunda tafarka taji mutane na cewa,
ganin cewa dagaske hukunta yaran zasuyi su kashe su suma, yasa mamee gudu izuwa gidansu cikin hanzari ta laluba school bag ɗinta, wayarta ta ɗauko ta dannawa ƴan sanda kira, taci sa'a an ɗaga nan tayi reporting akan abunda ke faru tare da basu address na anguwar,
Abunda yasa tayi hakan kwara hukuncin da ƴan sanda zasu ɗauka akan wanda ƴan unguwa zasu ɗauka, kisan wulaƙanci zasu yi masu ba bincike,
Lokacin da ta koma gidan dakyar ta samu hanyar shiga mutane sun cunkushe ko'ina,
Ta raza na da ganin wasu matasa guda biyu hannunsu ɗauke da galons na fetur ga ashana a hannunsu kira suke abasu hanya su ƙone mayun, saboda rashin imani matan dake cikin gidan suka shiga basu hanya, haka aka janyo su waje daga cikin ɗakin sai kuka suke yi gwanin bantausayi,
Zazzaga musu fetur ɗin suka soma yi ajikinsu nan take numfashin husanna ya soma hau hawa, jahad kuwa ta ƙanƙameta tarungume ta ajikinta sun rungume juna suna jiran ta Allah ta kasance,
A dai-dai wannan lokacin jiniyar motar ƴan sanda ta karaɗe ko'ina, mota guda suka yo sai a kopan gidan dandazon mutanene da suka gani ne ya tabbatar masu da cewa nan ne address ɗin da yarinyar ta basu,
Tabbas a ranar sunga bakar rana, dakyar ƴan sanda suka kwace su, suka sanya su a bayan kanta suka tafi dasu,
Mamee da mamansu sun sha kuka saboda tausayin ya rayuwar yaran zata kasance ?
Case ya koma hannun police sai yadda hali ya bada, a police station suka kwana ana investigation akan mutuwar tsohuwar, ga baƙar yunwa ga tashin hankali, duk yaran su firgita matuka ga kwanan cell sai uban sauro dake cizonsu,_ 😭•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•
*ABBAN SOJOJI*
_mallakin_
*HAFSAT BATURE*
_wannan ƙirƙirarran labari ne wasu abubuwa ma daga cikinsa ƙirƙirarsu akayi domin ilmantarwa faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa_
_gargaɗi ko da gigin wasa ban yarda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba batare da iznina ba, wahala tace ban shiga harkar kowa ba kuma nima bana so a shiga tawa kowa ya tsaya iya matsayinsa_
*page* *43* to *44*
_The Father Of soldiers
Kamar yadda su husanna suka kwana a cell ba bacci itama haka ta kwana ido buɗe, banbancin shine su suna cikin matsanancin hali, ga sauro ga yunwa ga ba wanka komai ya hargitse musu bayin Allah,
Zuciyarta ce ke matsanancin buga mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa, ƴan uwanta na cikin mawuyacin hali, saboda aduk lokacin da wani abu mummuna ya faru dasu sai taji a jikinta,
zuciyarta ce ke matsanancin buga mata, zufa ce ke ta faman sintiri a jikinta, kai kace akwai zafi ne Alhalin yanayin garin sanyi ne,
dukkan ilahirin jikinta sai makekketa yake yi, sam zama saman gadon ya gagare ta, tadawo ƙasa jikinsa ta jingina bayanta, tausayin rayuwarsu ce ta kamasu,
tun suna cikin ciki ƙaddarar su ta soma, sun sha baƙar wahalar rayuwa, ba irin tashin hankalin da basu gani ba, wani lokacin har tambayar kansu suke wai Allah baya sonsu ne? astagfirullah 😥
Amma hakan baisa sehrish tadaina nafilfilin da take yi ba, yau ma rashin tsarkin da bata dashi ne ya hanata yin sallolin, addu'o i kawai take faman maimaitawa duk wacce ta zo mata a bakinta,
Amma fa a daren nan tasha kuka, kamar ba gobe, dole mane sehrish tayi kuka domin kuwa halin rayuwar da suke ciki duk juriyar mutun yaji sai ya matse kwalla,
fargabarta wane hali su husanna ke ciki tana tsoran ta rasa jininta, na biyu wane hali mahaifiyarsu take ciki shin tana raye ko ta mutu? na uku wanda shine take jinsa sosai a ranta wato zuwan SGR, BABBAN YAYA,
tarasa me yasa ya tsaya mata a zuciyarta meyasa take jinsa, meyasa take fargabar ganinsa,
Zuciyarta tana azalzalarta akan son ganinsa, idanunta na kwaɗayin sa shi a idonta, Amma a ƙarshe tayi addu'ar Allah yasa ya zama alkhairi agare ta !!!
sai da asuba bayan ta shiga toilet ta canza pad ɗin cikinta, sanna fa bacci yayi awon gaba da ita,
A can ciki kuwa suna shiryawa zuwan Abban nasu, farin ciki a gun junaid ba'a magana, saboda ya gama tsara shagwa6ar da zaiyi masa in yazo, sannan akwai abunda yake burin ya sanar dashi ,
Har garin Allah ya waye sehrish batasan meke wakana ba, aunty azmi ta shigo ta same ta tana sharar bacci, ganin yadda jikinta ke kerma ya tabbatar mata da cewa sehrish ba lafia ba, har jikinta ta ta6a temperature ɗin jikinta yayi zafi,
Don haka bata attempting tayar da ita ba, kawai sai dai ta gyara mata blanket ɗin jikinta, sannan ta fice,
ganin cewa aiki zai yi mata yawa time zai iya ƙure mata, saboda baƙin da zasu zo yau, da buƙatar su kammala girke girken da zasuyi da wuri,
Kanal yusif ta nema ta sanar dashi halin da ake ciki na rashin lafiyar mai aikinsu tukur, taji daɗi da yasanar da ita cewa, akwai chefs da zasu zo kada ta samu damuwa,
tun 7 suka ƙaraso, kwararru ne a fannin sarrafa abinci kala-kala, su biyu ne, chef ummu da abokiyar aikinta momina, azmi taji daɗin zuwansu, nan fa kowa ya naɗe hannun riga aka soma gudanar da aiki,
Tuni ƙamshi ya soma gauraye ko'ina harta cikin hancina, irin ƙamshin da ke tada mutun daga bacci,
Wurin 9 na safe, jirginsu hajiya azeema yayi landing daga legos, ƙanwar Abbansu ce, hamshakiyar attajirar mai kuɗi ce, tatara har sunyi mata yawa, a tare da ita akwai Captain najeeb da Talal ƙannensu kanal yusif ne da take ruƙo a wurinta, saboda bata ta6a haihuwa ba, lalura ce ta same ta na rashin aihuwa, gashi Allah ya jarabce ta da sonsu kamar hauka,
Hakan yasa Abbansu ya mallaka mata su, a wurinta suka taso har suka girma,
Kanal yusif ne ya ɗauko su daga airport, izuwa gidan murna agunsa har ba'a magana, saboda ganin captain najeeb da Talal, an jima ba'a haɗuba duk da suna ƙoƙarin sada zumunci, aiki ne ya ke hanasu wani time ɗin, saboda aikin soja ba aiki bane na zama wuri ɗaya ba,
Bayansu sai general Ishaq wanda ya kasance shina first born a wurin abbansu wato yayansu gaba ɗaya, wanda ke zaune a kaduna state, tare da matarsa yazo shuwa'arab ce suna kiranta da Aunty Babba, saboda tana auren babban yayansu gaba ɗaya, sun zo ne tare da Hafsat yarsu ɗaya tilo, wadda take karantar military nurse, ynx haka ta kammala karbar training ɗinta aiki take yi, ta gaji abbanta kenan
daga su kuma sai mai bi ma ishaq wato na biyu a wurin abbansu, Abbas mai riƙe da muƙamin Colonel general, tare da matarsa yazo (AMANI) itama balarabiya ce ƙanwar Aunty babba ce yake aure, kuma dama ita ta haɗasu,
A nan cikin abuja suke da zama su ma, babu ƴa'ƴa a tsakaninsu soyayya suke sha,
daga shi kuma sai na ukunsu matashin saurayi bai ta6a aure ba,
Bakowa bane face brigadier general Abuhaisam, shi kaɗai yazo daga jos sai security ɗinsa,
Waɗannan sune suka samu damar halarta zuwa tarbar abban nasu sauran kuma suna kan hanya,
Ina fata dai kun riƙe sunan kowanne daga cikinsu saboda in labari ya tashi basai munsha Wahala ba, 😒
A babban main palour kowannansu ya hallara, domin dama nan yafi dacewa saboda girmansa da faɗinsa gashi set na royal sofas ɗin dake ciki guda biyu ne a jere,
Hajiya azeema ta hakimce a kujera mai mazaunin mutun biyu, jikinta na sanye da french less haɗaɗɗen gaske ash colour an mata riga bubu dashi, ta kashe ɗaurin ɗankwalin nan irin ture gaka tsiya, amma fa ita ba tsiya bace domin tana da gashi sosai shukune a kanta ta ɗaure da ribbom ya zubo har bayanta, hannayenta na sanye da diamond rings uku uku a kowane fingers na left & right hands ɗinta, price ɗin kowane ring ɗaya yayi 1.5million,
Haka ziririyar chain ɗin dake a wuyanta da earrings ɗinta, sun kai kimanin 200m, agogon diamond ɗin dake hannunta ƙirar graff diamonds ce, farashinta ko ba'a magana, billions ne ke magana 😯
Bata jin wuyar kashe wa kanta kuɗi, kai kace ruwan samansu ake tana kwasa, ko kuma daga saman bishiya take tsinkarsu 😂
takalman ƙafafuwanta kuwa kuɗinsu sun ishi wani talakan jari daga ciki hada ni,
aunty Babba kuwa tana cikin wata jigunanniyar riga haɗaɗiyar gaske,
Ta larabawa mai round neck yellow colour abunka ga fara sai ta fito ɗau kamar hurul aini, kafafunta na sanye da high heels tsadaddun gaske, launin rigarta, tayi rolling mayafi a wuyanta, ya sauka har kafaɗarta, amma hakan bai boye dogon gashinta ba,
tana zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku (3 seater) mijinta ishaq shine a gefenta yayi shigarsa cikin manyan kaya namu na hausawa,
Hafsa na a zaune A saman 1 seater, kimono dress ne ajikinta, riga doguwa mara nauyi brown colour, ta ɗaure igiyar rigar a under chest ɗinta, babu head a kanta sai kitson manyan kalaba da akayi mata, ya zubo har gadon bayanta, fuskarta na sanye da light make up, tun da suka shigo kowa na tsoma baki ana fira dashi amma banda ita, cos she's very arrogant, ji dakai ne da ita, bata da mutunci ko kaɗan guyababbiya ce, fitinanniya, ga rashin kunya kamar 6eran gida,
hannunta na riƙe da waya kirar i phone 13pro, sai faman ƴan danne danne take yi,
Amani na zaune tare da mijinta a mazauni ɗaya,
Sai Abuhaisam na zaune jere tare dasu kanal yusif da Captain najeeb a saman 3 seater, sai talal a next chair din dake jikinta su , firar yaushe rabo suke yi, ana ta faman gaishe gaishe gida ya gama katsame wa,
wasu na dannar waya yayin da wasu ke tsoma baki ana fira dasu,
Su khaleed ne suka fito kowannansu na sanye cikin shiga ta alfarma wankan shadda gezna suka ɗauka launi ɗaya blue sky riga da wando, ba ƙaramin kyau tayi musu ba duba da launin fatarsu chocolate,
Nan fa aka shiga yan rungume rungume kowa cikin fara da nuna farin ciki, kowa ya fito amma banda mutun ɗaya wato junaid gashi kowa ya ƙosa ya ganshi,
Duk magana ɗaya biyu sai an ambaci sunan shi, ina junaid? Wai junaid baya nan ne,
azmi ce ta shigo tare da chef ummu hannunsu ɗauke da abunsha, jere acikin tray a cikin wasu fancy cups,
ɗaya bayan ɗaya suka bisu suna miƙa musu, kowa na ɗauka yana sha,
Hajiya azeema tace "ina fata dai an tanadarmana abunda zamu zubawa cikin mu domin ni ko breakfast ban tsaya ci ba na kamo hanya,' tayi maganar ne a lokacin da take ɗaukar cup daga saman tray ɗin da azmi ta miƙa mata,
da fara'a a fuska azmi tace "ae mun tanadarmaku abinci kala kala sai wanda kuka za6a,'
general Abbas ya kalli matarsa dake gefensa yace "me na faɗa miki? ai tun a gida nace ni bazanci komai ba, sai na zonan don na kwashi girkin azmi don ban mantawa da wannan farfesun nata mai zautar da mutun,'
dariya sukayi gaba ɗaya musamman azmi da ake yabon girkinta,
Aunty babba tace "ai ko munyi dabara domin ni kaina zumuɗin girkin azmi nake yi kamar kamar me,"
Cikin sanyin murya Amani tace "aunty azmi zanzo ki koyamin pls wannan dambun shinkafar sbd, baby na yana son shi ssae,'
Yadda tayi maganar cikin kwarkwasa ya basu dariya, aunty azeema tace"amma dai Amani ba ta ido, gashi nan kinsa mijin naki jin kunya, gaban ƙannensa kike ce masa baby da girmansa ,'
dukaddar da kai tayi tana murmushi, shima Abbas ɗin kansa na ƙasa Ya aza idonsa kan screen ɗinwayarsa, su kanal yusif sai murmushi suke yi,
Su azmi da chef ummu sun gama miƙawa koya abunsha don haka suka koma kitchen domin shirya abincin izuwa dining,
_wai dagaske ne su Babban yaya Zasu dawo gobe? Captain najeeb ne yayi tambayar_
_jin an ambaci sunansa yasa hafsat shaƙewa daga Kurbar lemun da take yi, tari ta shiga yi Ba don komai ba sai don jin sunansa domin ta ta6a shan Zazzafan marinsa_😂
Page *45 to 46*
_wlh am so eager so see Babban yaya too😢_
_Subhanah, Walhamdulillah,allahu Akhbar_
"Yeah but we are not sure, ba tabbacin cewa gobe zasu dawo, muna zuba ido dai,' kanal yusif ne ya bashi amsa,
Jinjina kai captain najeeb yayi tare da cewa "aiko bazan kwana ba, yau zan koma lagos, ba dani ba
dariya su kayi hajiya azeema tace "ashe muna da manyan baƙi, lion da tiger zasu dawo kenan, wannan karan bansan da wata rigima zai zo ba, Allah kaɗai yasan jinin da za'a zubar,'
Hankalisu twins ba ƙaramin tashi yayi ba dama suna zaune matse da juna, sunyi zuru zuru, zuciyoyi na bugawa,
Basu kaɗai ba hada fawan da su jabeer da irfan da sauran atakure suke jin kansu, a wurinsu zuwan Babban yayansu ba alheri bane, bawai don basu son shi ba, sai don tsoran abunda zai faru zuwansa,
"ae na jima ina bama ishaq shawara akan ya tunzura Abba, ya aurar dasu, wlh indai su kaji mace atare dasu zasu samu weakness ajikinsu su daina jin kansu tamkar dodonni,' sakin baki su kayi jin abunda aunty babba tace,
Azeema tace "da alama bakisan wanene RAFAYET ba, ai rafayet zuciyarsa tamkar dutse take ! ban ta6a ganin mutumin da mace sam bata gabansa ba irinsa, sam bai da shauqi akan mata, ke shi fa hasalima yadda yake kallon jinsin sa namiji haka yake kallon mace,' 😧
ta ƙarasa maganar tana kurbar lemun hannunta, general ishaq yace "kwara ki faɗa mata da kanki may be she will understand it now, i had been explaining to her about rafayet but taƙi fahimta,' ya ƙare maganar yana kallonta,
Murmshi azeema tayi tare da gyara zama tace "Anzo inda nafi auki, anzo dai dai wurin ba mai sauka, rafayet da kike gani ba mutun bane ........
dariya ce ta kubce mata su kansu dariyar suke ba don komai ba sai don maganarta takarshe da tace rafayet ba mutun bane,
dakyar ta saita dariyar ta ci gaba da cewa, " Ai dashi da mahaifiyarsa halinsu kusan ɗaya ne, kaifi ɗaya ne wasu irin bauɗaɗɗun mutanene, koda yake in mukayi la'akayi da cewa mahaifiyarsa baturiya ce, sannan kuma ba musulma ba, yanayin rayuwarmu da tasu ba ɗaya bace, amma gasky munsha Wahalar fatima fiye da tunanin mai tunani, ta azabtar damu saboda muna kwakwar ƴa'ƴanta, har yau fa ita bata yarda cewa Allah ɗaya bane, taƙi karbar musulunci, kuma bata yarda cewa ƴa'ƴanta sun musulunta ba, in har zasu taka suje wurinta to fa basu ba yin sallah ko karatun qur'ani sai dai in ba dasaninta ba, dakyar fa aka samu rafayet ya musulunta har yakai shekara 20 aduniya ba shi ba musulmi bane,
ta tsagaita da maganar tana sauke ajiyar zuciya, gaba ɗaya sauraronta sukeyi, musamman Aunty babba da Amani su da basu son komai ba game da su rafayrt ba,
Su twins kuwa da fawan jikinsu yayi sanyi domin ana magana ne akan mahaifiyarsu,
Aunty babba tace "nikam inaso nason wacece fatiman nan, ya akai abba ya aure ta ba tare data karbi addinin musulunci ba, Kuma har akayi gangancin barin ya'yanta suyi koyi da addininta ina nufin rafayet da ki kace yakai 20 yrs batare da yakarbi addinin musulunci ba, sannan ina fatiman take a yanzu, don ni ban ta6a ganin ta ba,'
Anzo dai dai wurin, ina fata kowa zai kasa kunnansa ya saurara muda akayi agaban mu, acewar aunty azeema
....... .............Bismillah......... .............
Asalin family ɗinmu Hausa fulani ne, mahaifin.mu bahaushe ne haifaffen garin zariya, mahaifiyarmu kuwa bafullata ce yar jihar damaturu, Haɗuwarsu tafarko a barikin sojoji na kaduna state Allah ya haɗa jininsu har takai su gayin aure ❤
Mu uku ne a wurin iyayenmu banban cikinmu Shine hussain wato (Abban sojoji) tagwaye ne su Allah yayiwa hassan ɗin rasuwa tun kafin su mallaki hankalinsu, Akwai tazarar shekaru a tsakanin mu sosai dashi, shi ne nafarko sai kuma ni azeema daga ni kuma sai ƙanin mu gaba ɗaya, wanda shine autanmu mun girme shi sosai, wato ABUSUFYAN wanda ynx yake zaune a Ƙasar turkey,'
tun yana 20years a duniya, wan mahaifiyarmu ya bashi auren ƴarsa maryam, yarinyace mai ilmin addini sosai ga hankali da natsuwa, maca ce mai saukin kai, bata ɗauki duniya da zafi ba,
Itace matarsa ta farko, sun sha sosai kamar laila da majnun, domin mu kanmu shaida ne akan hakan, duk in yana gari tashiga tarairayarsa kenan, idan aka turasa aiki kuwa nesa ba ƙaramain shiga damuwa take yi ba, duk tabi ta susu ce,
Abban mutunne mai son ƴa'ƴa koda yake bashi kaɗai ba, mu dukkan mu haka muke da son ƴa'ƴa zumuncin family ɗinmu yana da ƙarfi sosai, bama wasa da sada zumunci,
Cikin ikon Allah maryam ta samu ciki, kowa ya hau murna musamman ammin mu grandma ɗinmu, dayake maryam mutuniyarta ce tana sonta sosai kasancewarta yar yayanta modibbo,
Haihuwa tafarko maryam ta haifo kyakkyawan ɗanta, santalelen yaro yaci sunansa Ishaq (wato general ishaq) daga shi kuma sai Abbas wanda ynx yake rike da mukamin colonel general, daga Abbas sai brigadier general Abuhaisam gashi nan zaune kuna ganinsa, daga shi kuma sai major