Header Ads
Showing 132001 words to 135000 words out of 138623 words

Chapter 45 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

942

Ads at the middle of Article

ƙarasa maganar zuciyarta tayi wani irin bugu ta sulale ƙasa a sume.....................................❤
Abun ya ɗaure masa kai, tun kafin yace wani abu mai aikin ya sume tabbas bashi da gaskiya maganar adams ta tabbata kenan,
tsallake ta yayi yasamu wuri ya zauna saman Sofa ɗin, dakan shi yashiga saving ɗin abincinsa, yana ci yana korawa da Cool milk, lokaci zuwa lokaci yana kai idonsa kan mai aikin dake sume ƙasa a baje,
Bayan ya kammala ya wanke hannunsa ya cire tissue ya goge bakinsa,
Sannan ya miƙe bayan ya ɗauki wayarsa dake ringing, picking yayi tare da ƙarawa yana faɗim "Alhamdulillah,Am coming down now,
Gogan naka fa sam ya manta da mai aikin daya sume masa a palor,tun da ya ɗauki wayarnan tasa yasa a kunnansa ya fice daga palor ɗin,
Down stairs ya sauka anan sukan haɗe da Omar suka fice atare,


Abu kamar wasa har ƙarfe biyu na rana yayi ba sehrish ba alamarta, Azmee sai faman nemanta takeyi saboda ta bata new phone ɗin da aka bata, Data shiga bedroom ɗinta taga wayau sai ta ajiye mata wayar cikin kwalinta ƙirar Tecno Camon 18,
Room ɗinta ta koma cike da mamakin ina Reesh taje ne, sam tagaza zama ganin har ƙarfe uku na rana tayi, ta duba ko'ina har bedrooms ɗin sauran amma bata nan, suma duk sun fita bayan sun kammala breakfast ɗinsu hatta junaid bayanan,


Sam ba tayi tunanin ta duba part ɗin Sgr ba, ƙarshe har garden azmee taje da sauran sassa na gidan ta duba amma reeshi bata nan,


da tagaji da neman nata sai ta koma ɗaki cike da zullumin ina Sehrish taje, addu'arta shine Allah yasa kada wani abu ya same ta,


______________________________________


Har wannan lokacin su hosana da jahad na'a store an garƙamesu kamar dabbobi ba sallah ba abinci, yunwa tamkar zata kashe su, hosana duk ta firgice tuni idonta sun juye ta zube ƙasa tana birgima, hakan yasa jahad fashewa da kuka hankali tashe taje bakin ƙopan store ɗin tana faɗin "Dan Allah ku buɗe mana ƙofa !! idan so kuke ku kashe mu kawai ku kashe mu !! laifin me muka aikata ne ? ku fidda mu daga gidan mana wannan wane irin zalunci ne ? Cikin kuka take maganar duk tafita hayyacinta saboda ganin halin da hosana ke ciki,
Amma shiru ba alaman za'a buɗe masu kopa ko motsin mutun babu, domin kuwa aunty babba sun fice da Hafsat izuwa kasuwa don suyi siyayya da kuɗin da Omar ya turo Masu hosana,
Rai a6ace jahad ke dakar ƙopar tana kuka tsoronta kar hosana ta mutu saboda tana kwance ƙasa tana juyi,
tana cikin wannan bugun taji kopar ta buɗe, key ɗin yasaki ,.
ɗagowa jahad tayi da kanta daga jikin ƙopan tana kallonta cikin mamakin ganin ta buɗe,
Cikin hanzarin ta juya ta kalli hosana dake kwance ƙasa tace "hosana kopa ta buɗe ki tashi mu gudu, Wannan matar kashe mu zata yi kwara mu gudu'


da buɗar bakin hosana sai cewa tayi "YaYa Omar Fa"?
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*


_🔥the father of soldiers🔥_


Free pages


*98-99*




*Hafsat Bature Boss Lady*




*naɗauki hutu saboda bani da lafiya ko typing din ma bana iya zaman yin shi, Am srry 4 that😔amma insha Allah da zarar naji sauƙi zan ci gaba*🙏






Jiki a mace jahad ta zauna yaraff !! agefen hosana tana cewa "babu ma hanyar da zamu gudu wlh na tuna sojoji ne ke tsaron gidan Ya Salam ya zamuyi yanzu,
Itama hosanar tashi tayi zaunen ido luhu luhu ga jirwayen hawaye a kumatunta sun galabaita sosai,
"Jahad meyasa har yanzu mutuwa bata zo ta ɗauke mu ba? Jiran me take yi ne?
"Hosana lokacin mu ne baiyi ba, kuma ni bana so in mutu ynx, Ina so naga Sehrish........ta ƙarasa maganar tana shesshekar kuka,
"Nima inaso naganta jahad, amma kina tunanin zamu ƙara ganinta a rayuwarmu ? Yaushe zamu isa gare ta ? tayi maganar tana kallon jahad gaba ɗaya hawaye sun zuzzubo musu
"Nima bansani ba.....bansan yaushe ba, jahad ta bata amsa,
. shiru su kayi zugudun ba mai magana,


A dai dai time ɗin motarsu Aunty babba ta shigo gidan Ash colour ƙirar vibe, hafsat ce ke driving ɗin yayin da aunty babba ke gefenta, sai fira suke suna kwasar dariya,
"Gsky mommy da abun dariya kke, amma kinsa me mom? Yaran nan fa sun ga samu sun ga rashi Allah, kalli fa uban kayan da mu kayi purchasing kai kace na Amarya ne,'
Dariya aunty babba tayi tana cewa"Hmmm ke dae bari, ae baki sani ba da ace Abuja direct Omar yakai yaran nan wlh ba ƙaramin gata zasu samu ba, kinsan Abba da son ƴa'ƴa gashi kuma bai da ya'ya mata toh Allah ina faɗa maki Omar nakai yaran nan can gida, Da mun shiga uku, zasu zo su samu matsayin da mu bamu samu bama,'
"Gsky ne Mommy, muna nan sake da baki sai dae muji sun aure yaya Omar da Babban Yaya,
"Ae wlh dana binne su da ransu" acewar aunty babba,
Fashewa su kayi dariya, yayin da Hafsat tayi parking motar a parking space ɗinsu,
Atare suka fito gowns ɗin ɗazune ajikinsu sai mayafi da suka yayyafa a kawunansu,
Buɗe boot hafsat tayi tana sauko da wasu jigunannun akwatina kamar na lefe, manyan gaske guda biyu launinsu maroon colour, sai ɗan kit,
Cikin sauri wani sergeant ya ƙaraso yana musu sannu da zuwa, sannan ya karbi akwatinan don yashigar musu dashi ciki,
A palor ya ajiye masu akwati nan, sannan ya fuce, su kuma suka shigo hafsat na cewa "Mom ni zan shiga ciki na watsa ruwa, kuma yunwa nake ji,
aunty babba tace "kai daughter harfa restaurant muka biya duk abunda kika ci, bai ishe ki ba? to Allah ba girkin da zan ɗaura, don agajiye nike nima,'' ta faɗi tana wuce Upstairs,
ta6e baki hafsat tayi tare da wuce wa nata room ɗin dake anan down,


Bayan aunty babba ta shiga, rage kayan jikinta tayi sannan ta shiga toilet tayo wanka, tafito ɗaure da towel, closet ɗinta ta buɗe ta ɗauko wata rigar kuma doguwa tasanya mara nauyi, tunkan ta idasa sanya rigar Wayarta dake acikin purse ɗinta take faman ringing,
Cikin sauri ta idasa zura hannun rigar ta ƙarasa inda purse ɗin take saman gado inda tayi throwing ɗinta time ɗin da tashigo,
Zama tayi saman gadon sannan ta sanya hannu ta ɗauki purse ɗin ta buɗe , kuɗaɗe ne aciki sabbi fal Bugun abuja, sauran wanda suka ciro a banki ne na siyayyar da sukayi,
Wayar ta ciro ta duba mai kiran nata sunan *AMANI* ne ya bayanna akan screen ɗin,
Murmushi tasaki domin dama tun jiya take son kiranta,
ɗagawa tayi tare da karawa a kunnanta tana faɗin " Dama tun jira nake son na kira ki abubuwa sun min yawa,'
On the other hand , Amani tace "Aunty laila kenan kin manta ni kin share ni,'
Aunty babba tace "Ke dallah ba dole in manta ki ba, ke bakisan me ya faru ba, akwai labari zazzafa
Cikin zumuɗi amani tace "Bani nasha, am so eager to hear it,
Dariya aunty babba tayi tace "Idan ma a tsaye kike to ki zauna,"
Amani dake a tsaye gaban mirror, taja kujerar dake gabanta ta zauna tana faɗin "Na zauna Auntyna, Ina sauraron ki '
Nan aunty babba ta zayyana mata komai game da su Hosana da jahad da Omar ya kawo mata hada kuɗin da suka kar6a a wurinsa da purchasing ɗin da su kayi masu kaf ta faɗa mata,'
Shiru Amani tayi jikinta yayi mugun sanyi, muguntar aunty babba ta razanata, bakomai ya tsaya mata arai ba, face da tace Yaran suna acikin store tun jiya ba abinci, tuni idonta sun ciko da kwalla saboda ita takasance mai tausayi ce sosai, aranta tana cewa meyasa Omar bai kawosu nan ba tabbas ya aikata babban kuskure domin kuwa tasan tabbas Aunty babba bazata ƙyale yaran nan ba, azabtar dasu zatayi............
Sam ta manta waya suke har sai da muryar aunty babba ta ratsa ta da cewa "Kinyi shiru baki ce komai ba....?
Cikin sauri Amani tace "Ae daɗi ne ya hanani yin magana Auntyna, gsky naji daɗin labarin nan da kika bani kamar kamar me, kin ga yanzu wuƙa da nama suna hannin ki sai yadda kika so zakiyi da yaran, domin kuwa matsala ne a target ɗinmu, babban ma abun burgewar ta kuɗin da kika samu a wurinsa kin ga mun fara samun na ziyartar wurin bokan..........'
murmushi aunty babba tasaki tare da cewa "aikuwa dae kuɗi fa sun fara samuwa, yanzu dae shawararki nake nema akan yaran nifa bazan bari sukai labari ba!
Shiru amani tayi tana sauraranta aranta tace "baƙar muguwa, in sun tashi kai labarin ki hana su mu gani, mtssw haɗamammiyar banza,'
A fili kuma tace "Auntyna kinsan me?
"A'a saikin faɗa" acewar aunty babba,
Amani tace "shawarar da zan baki shine, kada kice zakiyiwa yaran horon yunwa sam wannan bai ma taso ba, saboda kinsan Marshal Omar mutunne mai kaifin basira, wlh muddin yazo kallo guda zaiyi masu ya gane cewa akwai yunwa ajikinsu kuma zai tuhume ki akan hakan, sannan muddin kina so target ɗinmu ya tafi yarda muke so dole fa atlease ki jure ki ɗan basu kulawa ina nufin Kayan da kika ce anyi musu siyayyarsu arinƙa basu suna sanyawa, sannan ki rinƙa barinsu suna yin wanka ko sunyi haske...............
dakatar da ita Aunty babba tayi tare da cewa "Amani me kke Nufi? Ni zan basu kulawa har haka, Allah yakiyaye wlh, ke nifa natsani yaran tun da nagansu, saboda raina nabani cewa nan gaba sune zasuyi sanadiyar tarwatsa mun plan ɗina,"
Cikin lallami Amani tace "Aunty na lura baki fahimce ni ba !! Abun da nake ji maki tsoro shine Omar zai iya yin zuwan bazata nan kaduna, kwatsam ya faɗo What will u do?
Ajiyar zuciya amani tasaki ta wani 6angaren maganar Amani gaskiya ce don haka tace "Shikenan zan duba nagani, amma fa Allah saina sa an zubar da twins ɗin can,'
"Dama wannan ae Wajibun ne Auntyna," acewar Amani acikin zuciyarta kuma tace "Muguwa in Allah ya yarda bazaki ta6a cin nasara akan hakan ba,'
Sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi sallama da juna,"


Bayan amani ta ajiye wayarta ta asaman mirror ɗin gabanta,


tace" dama ni Omar ya kawowa twins ɗin tabbas da sun samu kulawa, iya kaci kuɗine nima zan kwasa, tunda nima Lashe Money ce,
Ta miƙe tana Zagaye acikin ɗakin ta wani 6angaren taji daɗin ɗaukar shawararta da Aunty Laila tayi koba komai Yaran zasu samu salama, dama wayau tayi mata don ta taimaki yaran da taji tace tun jiya suke acikin store garƙame, haƙiƙa ta tausaya musu,
_______________________________________

Ganin har la'asar tayi ba sehrish yasa hankalin azmee tashi baiwar Allah sai faman zirga² take yi tarasa inda sehrish ta shiga, fitowa tayi daga ɗakinta tana faɗin "Anya sehrish lafiya kuwa, karfa ace wani abu ya same ya zanyi nikam, tsayawa tayi riqe da qugu tana tunani can ta tuna cewa sehrish fa tunda ta shiga kaiwa Babban yaya breakfast a ɗakinsa bata dawo ba,
Aikuwa cikin sauri Azmee ta wuce Upstairs ɗin jiki na rawa, aranta tana Allah Allah ta same ta acan kota huta da zullumi,
time ɗin da tashiga part ɗin tunkan ta isa wurins sofas ɗin taga alamun mutun baje ƙasa, da hanzari Azmee ta ƙarasa zuciyarta na ɗar², tana isa hankali tashe take faɗin "Subhanallahi Sehrish kuma kwance a ƙasa? Meya faru ne?
Cikin hanzari ta zukunna tana tatta6a jikin sehrish wani irin Sanyi taji ajikinta, jijjiga ta, ta shiga yi tana faɗin "Sehrish ! Sehrish !!! Ki tashi meya faru ne !?
Shiru babu amsa cikin sauri azmee ta miƙe takai hannu saman table inda Sgr ya kammala breakfast yabar stuffs ɗin asama, Robar ruwa ta ɗauka mai sanyi, jiki na kerma duk ta ruɗe tsoranta karta rasa Ɗan Tukur ɗinta 😂
Da sauri take murɗa murfin roban, tayi wurgi dashi cikin hanzari ta ƙarasa inda sehrish take ta zauna ƙasan, sannan ta ɗebo a hannunta ta yayyafa mata shi a face ɗinta, aikuwa arazane sehrish ta farka firgit ta tashi zaune tana faɗin "La'ila ha'illallah muhammadur rasulillah.......' sai faman zazzare eyes ɗinta take cike da tsoro,
"sehrish ki natsu Aunty azmee ce, meya faru ne," sai lokacin sehrish ta kalli Aunty azmee wadda ke zaune tana fuskantarta, wani sanyi taji aranta murya na rawa tace "Aunty Azmee babban yaya fa? shine....shine...ya firgitar dani bansan me ya faru dani ba...' a rarrabe take magana duk ta tsorata,
Dariya azmee tayi tunkan sehrish ta faɗa mata tasan cewa yau Sehrish taci karo da Sarkin Dawa wato zaki,
"Wani abu yayi maki ne"? ta tambaya bayan ta tsagaita da dariyar,
"A'a aunty azmee, kawai ina leƙen wayarsa ashe ya fito bansani ba, kwatsam ina juyowa haka mukayi Ido biyu dashi, nan take naji zuciyata ta buga daga nan bansan me ya faru ba...amma aunty azmee babban yaya cikakken mutun ne ?
Fashewa da dariya azmee tayi dakyar ta tsagaita tace "Me kika gani"?
Sehrish tace "Aunty azmee idonsa irin na Horrrow ne, kuma ko acikin film ɗin Shu'uma na Aman Junaid khan in zasu koma Aljanu idansu ke komawa Blue......'
wata irin dariya azmee ke 6a66akawa sam tagaza tsayar da kanta, shiriritar sehrish tafi ƙarfinta, ita kuwa sehrish bil'haƙƙi dagaske take bama azmee bayani,
Ganin yarda azmee ke ta dariya yasa sehrish cewa "Aunty azmee meyasa kike mun dariya? nafaɗa miki gsky ne fa,'
Ruko hannunta azmee tayi tare da cewa "wlh sehrish shiriritar ki tafi ƙarfinki, wato tunda suma eyes ɗinsu na komawa blue in zasu koma Aljanu shima kenan Jinsinsu ne koma ki ce shine Aman junaid Khan ɗin ke kuma sai ki zama AYYANARSa ,


tayi maganar ne yayin da suka miƙe atare, jin abunda azmee tace yasa sehrish yin murmushi wato zata zama Ayyanar Babban yaya 😂 acikin zuciyarta tace "Kowaye zai zama Aljani kaliya in hakan tafaru"?


"Sehrish bari na gyara masa part ɗin ki kwashe tray ɗin abincin ki kai kitchen sannan nasan kina jin yunwa sosai tun safe baki ci komai ba, ki tabbatar kinci abinci sannan kiyi sallah hada bath ma," azmee ce tayi mata bayanin tare da sakin hannunta data ruƙe,
Wucewa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin har takai bakin ƙopa Azmee tace "Gift na nan na ajiye maki,'
Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Toh aunty azmeee zan duba,"
Futowa tayi tana tafiya amma sam tagaza rufe bakinta saboda ance zata zama Ayyanar Babban yaya wato mai basa kariya daga Maƙiyansa masu kawo masa Hari,
har ta sauko down stairs tana wannan tunanin aranta tana fatan Allah yasa ta zama Ayyanarsa ta gaske ❤😍


Kitchen ta shiga ta ajiye tray ɗin, sannan ta zuba ma kanta breakfast ta zauna anan taci tayi hani'an (Allah sarki su Hosana) 😥


Bayan ta kammala tashiga bedroom ɗinta, sai da tafara yin alwala tayi sallar azhar da batayi ba sannan tayo wanka ta kimtsa cikin kayanta na gado,
Sai da tazo gaban Mirror Don ta kalli fuskarta sai lokacin ta lura da Kwalin wayar da Azmee ta ajiye mata,
Zaro ido tayi in Amazing ɗin nan hada sa hannu abaki don mamaki,daga bisa ni tasa hannu ta ɗauki wayar, jiki na rawa ta buɗe kwalin ta ciro wayar sabuwa Ƙal da ita, ga charger ɗinta da sauran abubuwa,
Wani irin ihu sehrish tasaki na farin ciki, ita kanta batasan lokacin da tayi tsalle tahaye saman gado tana rawa ba, daga bisani kuma ta koma takwanta saman gadon, jiki na rawa ta kunna wayar sai faman murmushi take saki, haske ta kawo sehrish ta ƙura ido tana kallon screen ɗin wayar,
nan fa tashiga dannarta ba Arziƙi can ta tunano dasu hosana jikinta yayi mugun sanyi aranta tace "Allah sarki su hosana,da ace wayar tsohuwa na shiga dana kira ku mungaisa, bansan meyasa ba'a samun su ba, wane hali suke ciki inaso in sani, itama tsohuwa bansan meyasa ba'a samunta ba,'
Hawaye ne taji sun zubo mata jikinta yayi mugun sanyi, ajiye wayar tayi gefenta, ta yi uban tagumi cikin takaici ada tana farin ciki da wayar amma yanzu farin cikin ya ragu sosai, dama duk ɗokinta akan waya saboda su Hosana da Jahad ne,😥


Shiru tayi tana tunanin ya zatayi, ƙarshe ta yanke shawarar zata amshi numbarsu wurin Junaid baza'a rasa ba may be~~~~~~~~~~~~


Tana cikin wannan zaman azmee ta kwankwasa kopan cikin sauri ta share hawayenta sannan ta tashi ta buɗe mata,
"Sannu da aiki aunty azmee,"


Da murmushi a fuska azmee tace "Yawwa Ayyanar Babban yaya dama inaso nace kin ga wayar ko?
Cikin jin kunya sehrish tace "Eh naganta bansan da wane baki zan gode ba,
Azmee tace "Nasan yau wata daƙer zata iya bacci don ɗoki," tayi maganar cikin Zolaya,.
Kafin daga basani tace "In akwai abun da baki gane ba game da wayar, kiyi ma junaid magana ya koya maki, nagama ya shigo yanzun nan"
"To shikenan aunty azmee i will talk to him,"
Juyawa azmee tayi ta wuce room ɗinta,


Dawo wa tayi ta ciki ta shirya tsaf ta ɗauki wayar sannan ta fuce, a babban falon suka ci karo da Haroon wanda shigowarsa kenan,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads