Showing 66001 words to 69000 words out of 138623 words
Chapter 23 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt
Abba yace "ae ina ji duk cikinsu shine ya biyo halin ummansu komai nata, hatta kyan fuskarsa in ka cire Marshal omar,"
"gsky abba ka tara kyawawan samari masu ilmin addini dana zamani ya kamata ace kowannan su iyanzu ya fidda matar aure tun da aun mallaki komai,"
Aunty babba ce tayi mgnr, wani irin kallo yusif yabi ta dashi sbd baison yaji ana masa maganar aure bama shi kadai ba hada bg Abuhaisam,
"Aunty babba matan ne basu da tabbas, mutun na bukatar tsawon lkc kafin ya fidda wadda ta dace da rayuwarsa, aure baya bukatar gaggawa kuma shi lokaci ne"
Bg abuhaisam ne ya bata amsa, jinjina kai tayi, yayin da yusif yace "you're right yaya haisam, we're waitin for the time, in yayi zamu yi ne,"
dan murmushi aunty babba tayi ita burinta tafara tunzura abba akan Babban yaya da marshal omar saboda abun yazo mata da sauki,
"mgnar ku gasky ne, amma abun da nake so ku sani, shi lokaci baya jira ! lokaci tafiya yake yi, this is the right time daya dace ace kunyi deciding akan sama ma kanku abokiyar rayuwa, its very hard to find a righteous partner in this situation of life, rufe ido kawai mutun zai yi ya canka,"
tayi mgnr tana kallon yusif dake facing dinta, kafin yusif ya bata amsa abba ya katse masa hanzarinsa da cewa "kwara ki fada musu, ynz ni ba abun kwatance bane a wurinku ? ina da 20yrs akayimun aure dayake na mallaki komai na rayuwa, in Allah ya baka dama ka damata alokacin daya dace, gashi ynz Allah ya albarkace ni da ya'ya da karfi na ban tsufa tukuf ba, naji dadin hakan sosai, ada ina jin haushin anyimun aure wuri, amma at the end naga amfanin abun,'
Jinjina kai su kayi kanal yusif yace "pls muna barar addu'arku aunty azeema aunty babba and aunty Amani atayamu da addu'a Allah ya bamu mata salihan mata na gari masu koyi da matan Annabi muhammad (S.A.W) Ba shaidanin zamani ba,"
Gaba dayansu suka amsa da (S.A.W.) kafin suka bi da ameen, suna dariya jin maganarsa ta karshe da yace shaidanin zamani,"
Junaid ya kalli abbansu tare da yin kasa kasa da murya yace "Nima abba atayani da addu'a mace tagari,"
Dariya su kayi gaba dayansu don sun ji shi, fawan yace kama cire batun aure a ranka, domin kai da yin aure sai nan da 20yrs lkcn ka kara hankali,"
Harara junaid ya watsa masa tare da cewa "Yanzun ma da hankali na, abunda dan shekara 30 zaiyi in an masa aure nima zan iya fiye da haka ......."
Bai ida maganar ba bg abuhaisam yayi masa dakuwa da hannu tare da cewa "gidanku ! Ja'iri ina maka kallon ustaz ashe kaima dan duniya ne,"
Abbansu ko murmushi kawai yake yi sbd yasan cewa sarai junaid yayi maganar ne batare da yasan me zasu fahimta ba su,
Aunty azeema tace "yaro ya girma abun sai addu'a'
Dariya su kayi gaba dayansu ,
Ba zato ba tsammani suna cikin wannan nishadin, kwatsam su kaji dirar motoci a tsiyace, ba kakkautawa da gudun gaske suke shigowa cikin gidan, lokaci guda jiniya ta karade ko'ina, hankalinsu ba karamin tashi yyi ba Abun kamar a filin Yaji,
Antayo wa suke ciki ajere suke kurdadowa,
Sehrish sai faman toshe kunnata take da pillow saboda jin tamkar za'a fasa mata kanta, ga nauyin bacci tana ji sam ta kasa kakkauran motsi ta tashi, jiniyar motocin dake shigowa har tsakiyar kwalwarta, sai faman matse ido take ta ciccije lebe,
Kamar daga sama taji sautin harbin bindiga mai karfin gaske kamar fashewar bomb haka taji, a wani irin firgice ta wuntsilo daga saman gadon izuwa kasa gefensa, daga ita har pillow kowa ya ware gefen, bargon ne kawai kankame a hannunta, gaba daya dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi, sai faman zazzare ido take yi, tuni zufa ta soma wanke mata fuska, da karfi take breathing in har mutun sai natsuwa tsaf zaiji bugun zuciyarta,
Wani harbin da aka sake yi nan take ta fashe da kuka, sbd dama a tsorace take da mafarkin da tayi,
Acan ciki kuwa, lokacin da jiniyar motocin nan ta karade ko'ina nan take fawan ya saki cokalin dake hannunsa, idonsa akan junaid sbd yasan cewa sarai junaid yasan da zuwan bazatan da Babban yayan nasu yayi bai sanar dashi ba, su kam sauran musamman aunty azeema da Abban nasu su bg abuhaisam da su kanal yusif farin ciki a wurinsu ba'a magana, juyawa aunty babba tayi ta kalli Amani wadda itama kallonta take wani shu'umin murmushi suka sakarwa junansu jin wadanda suke hari sun karaso,
Su irfan da jabeer kuwa da khaleed kallon kallon suka shiga yiwa juna kowa na sauraran jiniyar motoci yayin da zuciyoyi ke beating
Duk ba wannan ba ina maganar su twins wadanda ke kwance kankame da juna suna cikin shan soyayya suka jiyo sautin nan, zuba wa juna ido su kayi ba tare da kiftawa ba, hankali a tashe Ayaan yace "Maganarka ta tabba jahan wlh shine ya dawo," shiru jahan yayi sam ya gaza cewa komai, gaba daya jikinsu ya gama mutuwa ,
Cikin sauri wasu gabza gabzan sojoji sanye da kaki ga manyan bindigu a hannunsu suka diro daga saman motarsu,
Cikin hanzari suka karasa tare da bude masu mota, fitowa marshal omar yayi yayin da babban yaya ya fito ta other side din, abun gwanin burgewa, haka suka bude wa major general tare da Captain adams motarsu wadda ke bayansu ta Omar, suma suka fito
With respect sojojin nan gaba dayan su suka buga kafa tare da sara musu abun sai wanda ya gani, mu da akayi a gabanmu 😍😂
Sehrish dake a tsorace jiki na rawa ta lallaba ta taso, daga ita sai yar shirt wadda takai mata dai dai guiwa, ba dogon wando jikinta, sai santala santalan kafafuwanta,
Jikin window ta karasa tasa hands dinta dake ta faman kerma ta janye labulen tare da zuge glass din windown, zuba ido tayi tana hangen Zugar sojojin dake a cikin gidan kai kace yaki ne ya taso,
A hankali take lumshe idonta tare da budesu tana kare wa mutanen dake wurin kallo, sam sojojin da sukayi masu kawanya basu bari tagansu ba,
Sai da soldiers din suka dare biyu tare da bude masu hanya sannan sehrish ta samu damar hangensu, Marshal omar ne a gaba sai Mg osman a bayansa sai Captain adams ne, a hankali take kallonsu a ranta tana fadin "wanene babban yaya acikinsu, inaji araina cewa tabbas shine ya dawo,"
Bata idasa tunaninta ba eye balls dinta suka sauka akanshi, kasancewar duk yafi su tsayi nesa ba kusa ba, Allah yayi mishi tsayi, sumar kansa ce tafara hangowa wadda ke kwance luf a bayansa da gefen forehead dinsa, zuciyarta ta dinga ji tana mata wani irin mugun bugu, bata da tabbacin cewa shine, amma ba karamin razana tayi ba da irin kyansa, duk da bata samu damar ganinsa da kyau ba, amma irinsu ko daga nesa ana shaida kyansu, kamar tauraro haka yazama acikin taurari 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
duk yadda sehrish taso ta kare ma wannan da ta hango daga nesa kallo hakan baiyu ba, bakomai take tunawa ba sai wannan hoton na cikin wayar junaid datake yawan gani, tabbas wannan shine na cikin wayar wato BABBAN YAYA,"
zuge glass din tayi tare da janyo curtains din ta rufe, murmushi kawai take sakarwa kanta tare da ajiyar zuciya at same time,
Tarasa ina zata sa kanta don farin ciki, sai faman sakin fara'a take kamar wacce aka ma Albishir da gidan Aljanna 😂
Tarasa tsaye tarasa zaune tarasa ina zata tsoma ranta, tsilli tsilli haka take yawo da yan kafafuwanta cikin room din nata,
A can ciki kuwa lokacin da suka shigo, hankalin Amani ba karamin tashi yayi ba ✨✨✨✨•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·
_Warning ❗❗❗ko da gigin wasa banyarda wani ya ta6amin littafine ba kamar canza wani sashe na labarin nan ba , ko haɗa document ko makamancinsu, in hakan ta faru kuma wlh mutun bazai ji da daɗi ba, duk inda yake a faɗin duniyar za'a samomin shi koda aljani ne ba mutun ba_😡
*page 59 to 60*
A can ciki kuwa lokacin da suka shigo, hankalin Amani ba karamin tashi yayi ba data fara cin karo da marshal omar, duk tabi ta zuzuce, a hankali tace ma aunty babba wadda ke kusa da ita a tsaye tace "Shine "? girgiza kai aunty babba tayi tare da cewa "wannan Shine marshal omar, ki zuba ido kawai bama saina fada maki gashi ba kina ganinsa zaki gane sa da kanki,"
tun kan Amani tace wani abu Babban yaya ya shigo cike da wannan tafiyar tashi ta Qasaita, wani irin bugu taji zuciyarta tayi juyawa tasake yi ta kalli aunty babba wadda idonta ke akansa ko kyaftawa basuyi,
Cikin tsantsar farin ciki kanal yusif yayi sauri zai hugging din omar, dakatar tashi omar yayi da cewa "bari na fara kwasar Albarka wurin Abbana tukunna," murmushi su kayi gaba dayansu especially Abban nasu, karasawa yayi tare da rungume abban nasu, so tightly hannu abban yasa yana bubbuga bayansa yace "I really really missed u my guys" omar yace "i missed u too my daddy,'
Mg osman kam wurin su Bg abuhaisam ya karasa suka shiga rungume juna ana ta faman gaishe gaishe, bayan omar ya gama da abbansu ya koma yana rungume sauran,
gaba daya idon abbansu ya koma kan Rafayet wadda ko kallo bai ishe su ba, kawai bedroom dinsa yake kokarin tunkara,
Cikin sauri bg abuhaisam yace "kai ina zuwa........? dakatar dashi abban yayi daga yi masa magana, kowa binsa da ido yayi,
Cikin sauri junaid ya shiga gabansa don ya riga sa isa sbd key din na hannunsa, can upstairs katafaren bedroom dinsa yake mai hade da palour, Aljannar duniya ce aka shimfida,
tunkan ya karaso Junaid ya bude masa, ya shige ciki, an kawata shi sosai sehrish ce zata fada mana ya haduwarsa yake, 😝
"Amma abba anya Rafayet bai fara shaye-shaye ba? Kalli yadda yabi ta gabanmu ko kallo babu, atlease ko kai ae ya kamata ya tsaya ya gaisar ko,"? abuhaisam ne yayi maganar ransa ya baci sosai,
Aunty azeema tace "kada ku damu indai rafayet ne dakansa zai fito,"
Zama su kayi a saman royal sofas din suna kara gaggaisawa da juna, hankalin Omar bai kwanta ba da yanayin abban nasu, kuma yasan duk akan babban yayan ne, ya kwalfa rai akansa yasaran daya shigo shi zai fara runguma amma sai yaga akasin hakan,
Aunty azmee ce ta shigo musu da abunsha itama da fara'a a fuskarta, tabi su tana musu sannu da zuwa, tare da mika musu abun sha,
Cikin rashi kwarin jiki abban nasu yace "am really glad to see you, ina godiya ga Allah daya dawo mun daku lpy, amma nayi mamakin jin cewa tare da su Omar zaku zo ina ABUSUFYAN din?
Captain adams ne ya bashi amsa da cewa "daga can wurinshi muka wuce us sbd mu tafo atare," jinjina kai abban nasu yayi tare da cewa "hakan yayi kyau,'
"Nima naji dadin ganin ku sosai, dalilin dayasa na tsaya nace dole saina ga ya'yana,' murmushi su kayi jin abun da aunty azeema tace,
"Muna tayaku murnar dawowa cikin koshin lpy ni da yar uwata Amani,' aunty babba ce tayi maganar, mg Osman yace "munji dadin ganin ku gaba daya, Allah yabar zumunci," suka amsa da ameen,
Idon aunty azeema nakan abba wanda jikinsa ke kerma zuciyar ta motsa, jiki ba kwari ya mike tsaye tare da cewa "yakamata ku shiga ciki ku huta, zuwa anjima, nima bari naje ciki,'
Cikin sauri ya wuce room dinsa, da hanzari aunty azeema tabisa,
Yana shiga ciki gaban mirror ya tsaya, idonsa sunyi jawur ransa yayi mugun baci,
Shigowa tayi tana fadin "haba yaya Hussein meyasa ?, duk don sbd da abun da Rafayet yayi yasa ka shiga wannan halin,"
Juyowa yayi muryarsa na rawa tamkar zai yi kuka yace "meyasa zaimun haka ? gaba daya na kwallafa rai akansa, yaushe rabon dana sa shi a ido na? Amma yadawo shine ko kallona baiyi ba? meyasa yake son azabtar dani ne da soyayyarsa kamar yadda mahaifiyarsa tayi mun !? yayi mgnr ne tamkar zaiyi kuka,
(Dama ko acikin gida dan banza yafi shiga rai 😂)
Cikin sanyin murya Aunty azeema tace "Am sorry yaya na, kamar yadda kke son ganinsa shima haka yakeson ganin ka, ni na tabbata akwai dalilin hakan, u shouldn't worry ur seft abt him, "
dagawo su kayi jin tura kopa, marshal omar ne ya shigo, yabiyo abbansu ne sbd shima ya lura da halin daya shiga,
Karasawa yayi inda suke yana cewa "daddy duk akan rafayet ne wannan ? Amma kasancewa sarai ba haka yake maka ba, rafayet bfr mu shiga jirgi yayi ma kansa allura, sbd aikin dayasha kasan yadda yake kamar enjine baya gajiya da aiki, allurar ce bata sake shi ba, just calm dowm ur mind dakansa zai zo ya same ka,in ya samu natsuwa"
ajiyar zuciya abban yasaki jin abunda omar ya sanar dashi, har yaji sanyi aransa,
Murmushi aunty azeema tasaki tare da cewa "ynx hankali ya kwanta ko, zamu iya komawa ciki ko ? Murmushi shima yasaki atare suka fito,
Yinin ranar gidan ya cika fam saboda zuwan SGR Da Marshal omar, mutane kamar kyankyasai sai bullowa suke yi abokanan arziki da kuma yan uwa, da sauransu hada su karare irinsu Hafsat bature yan shisshigi gayya soɗi, 😥
Duk wannan budurin da ake yi Babban yayan na can ciki a hakimce, yana sharar bacci cikin natsuwa, gashi kowa tambayarsa yake yi ina Babban yaya, Ina Sgr, ina rafayet amma shiru, ba wanda yayi attempting zuwa ya tashe shi saboda ba wanda ya isa ya tashe shi yana bacci, mutun yaji naushi alkur'an 😂
Dole fa sehrish ta fito aiki yayiwa azmee yawa, don haka tunkan ma azmeen ta buɗe ta, tayi gaggawar zura dogon wandonta, ta gyaggyara kanta da gashin bakinta,
kamar barauniya haka ta fito, tana tafiya cikin sanɗa ta tsorata da yawan mutanen da tagani, gasu nan bakake da farare kowa dai masha Allah,
Bama wanda ya lura da ita, direct kitchen ta wuce, abun ya bata mamaki ganin junaid tsaye aciki aunty azmee ta jera masa abunsha a tray cikin cups , alamar cewa hada shi ke taimaka mata wurin share ɗinsa wa bakin, saukin kan junaid na bata mamaki he'a so Special 😍
Jikinsa na sanye da t shirt red colour sai trouser black colour, abun ba'a magana,
Sallama tayi ta shiga da murmushi a face dinsa ya dago yana kallonta, itama kawai saita tsinci kanta da sakar masa murmushi,
"Sannunku da aiki aunty azmee, am so sorry ban samu fitowa da wuri ba, because of sleepless night shiyasan ya,' ta faɗi tana wasa da yatsun hannunta,
"Babu komai ae, ga Junaid nan yana tayani, tun da ynx kin fito sai mu fara shirin lunch, tunkan time ya kure mana,"
karasawa tayi gaban junaid tare da kai hannu ta rike tray din dake a hannunsa tace "Bari naje na kai musu,"
"A'a ki barshi kawai, zan kai" ya bata amsa cikin sanyin murya,
"A'a bai dace ace ɗan masu gida yana aikin daya dace ace ƴan aiki ke yi ba,"
ta faɗi tana kokarin janye tray din daga hannunsa,
"Ae ni nace zan iya just leave me to do it ba wani aiki bane mai wahala kawai kaiwa zanyi,"
"A'a ni dai kabarshi pls zan yi tunda nazo"
Zuba musu ido Aunty azmee tayi baƙaramin burgeta su kayi ba,
"Kun ga ya isa haka, junaid ka bashi yakai musu kaje ciki nasan anata neman ka,"
kallon ta yayi suka haɗa ido, ya ɗan murguɗa mata baki kafin yabi ta side dinta ya wuce, ajiyar zuciya ta saki,
Idasa jera mata drinks din azmi tayi sannan ta juya tashiga ciki zuciyarta na bugawa tsoranta kada ta ci karo da Babban yayan nasu, duk da har ynz bata shaida shi ba,
Haka Sehrish ta shiga zarya cikin manyan bakin nan tana miƙa wa kowannansu abunsha, tun tana yi cikin daɗin rai har tafara fidda gumin gajiya, bayan ta kammala suka shiga aikace aikace a kitchen na preparing Lunch,
Lokaci guda kamshi ya gauraye ko'ina, girki na musamman suka shiga yi, abinci iri iri, namu dana kasashen waje, musamman sbd Babban yaya bakowane kalar abinci yake ci ba, sai an tabbatar da tsaftar maiyinsa da kuma amfaninsa a lafiyar jikin mutun,"
Dama azmee ce ke masu girkin sun saba da delicious dinta, sbd sun shaida kwarewarta, da kuma tsaftarta da lafiyar abincin ta,
tana lura da duk wani motsin sehrish wani murmushi data ga tana saki kamar gonar auduga, cikin nishaɗi take aikinta, zumudin son ganinsa take,
mutane sun rage sosai ya raga saura mu na cikin gida kawai, su marshal omar sun samu damar shiga cikin rooms dinsu domin hutawa,
Aunty babba da Amani sun shige cikin daki baki cike da gulma, tsaitsaye su kayi,
"Wai dama haka Babban yayan yake ? Ya ilahi aunty ya hada komai da nake bukata ajikin ɗa namiji meyasa tun farko baki haɗa ni dashi ba sai Abbas"?
Murmushi aunty babba tasaki kafin tace "idan kura na maganin zawo tafara yiwa kanta mana ! Kinsan irin haukan da nayi at the first day dana fara sashi a eyes ɗina, Allah sai da nayi regretting auran Ishaq, Rafayet shine irin namijin da nake kwaɗayin samu ! Amma kaddara ta riga fata,"
Jinjina kai Amani tayi tana kallon auntyn tata, acikin zuciyarta tana tunanin meyasa bata haɗa ta da babban yayan ba ko marshal omar, Amma take yi wa Hayaam tanadinsa, kodan ta kasance ita shakikiyarta ce?
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
***************