Header Ads
Showing 138001 words to 138623 words out of 138623 words

Chapter 47 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

938

Ads at the middle of Article

da yi mata barazana akan zai tona mata asiri in bata biya masa buƙatarsa ba, kullum cikin kuka take tarasa wa zata kai ma kukanta akan haroon, saboda matsa matan dayake sai ta same shi aɗaki kuma ba yadda ta iya dole taje saboda gudun karya tona mata asiri, in taje kuwa haka zai matse ta abango yana shafa jikinta kamar maraye daker take kwace kanta, in jaraba tayi jaraba har bedroom ɗinta yake biyo ta, saboda wani lokacin tana mantawa bata rufe ɗaki ba, saboda tasan ba mai shigo mata in ba Aunty Azmee ba , kamar daga sama yake faɗo mata wani sa'in sai dai taji mutun ya faɗo mata saman gado ya tsoratar da ita, sehrish tasha kuka fiye da tunanin mai tunani duk da haryanzu haroon bai ida tarwatsa mata rayuwa ba, Allah na taimakonta tana kwace wa daga hannunsa ta faɗa toilet ta datse, tasha kuka iya kuka, taso ta sanarwa aunty azmee amma ranta na bata cewa Aunty azmee ba abunda zata iya saboda ƴar aiki ce ita, haka zalika taso ko Junaid ne ta sanar mishi amma sai take ganin tonawa kanta asiri zatayi ƙarshe ma tayiwa kanta sanadiyar barin gidan gaba ɗaya 😥


a 6angaren sgr Sam bai sake tunanin ya tuhumi mai aikin nasu ba, ba don komai ba sai don wasu dalilai, tun ranar da suka haɗa ido ta sume, ya tabbatarwa kansa cewa koma wacece muguwar matsoraciya ce, Muddin yace zai yi mata tsawa to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ta mutu, Saboda irin hakan tasha faruwa dashi, akwai masu laifin da tsawa kawai yake daka musu zuciyarsu ta buga don tsoro, shiyasa ya zubawa lamarin ido zuwa wani lokaci, 👀👀👀👀👀 ~~~~~~~~~~~~~~~~


A 6angaren Junaid kuwa soyayyar sehrish a kullum ƙara ninkuwa take yi, bawan Allah bai da tunani daya wuce na sehrish sometimes ko isasshen bacci bai samu saboda tunanin ta, yaso ace ko chat su nayi don ya ɗebe kewarta sai dai kash a halin da ake ciki ita kanta sehrish batasan inda ta wurga wayarta ba, Saboda tsananin damuwar da take ciki yasa ta manta da wata waya ma, Aunty azmee ta lura da yanayin sehrish domin ko aiki suke wani lokacin tana firgita ita kaɗae, har tambayarta take yi ko akwai wata damuwa, amma sai tace ba komai sai in ta koma ɗaki taita kuka kamar ranta zai fita, duk ta fige ta ram_____


Ataƙaice kenan abubuwan dake faruwa acikin rayuwar waɗan nan bayin Allah, shin me zai faru nan gaba ? kuna ganin Aunty babba zata kyale su hosana ? Mai zai faru in ta sa aka zubar dasu kamar yadda tace? Wane hannu kuma kke tunanin zasu faɗa? Yaya rayuwarsu zata kasance? 😥😥😥


Shin me zai faru da sehrish in haroon ya cimma burinsa? Yaya rayuwar junaid zata kasance aranar da ya gane cewa Sehrish babban yayansu take so bashi ba?😖


ALHAMDULILLAH END OF PART 1
______________________________________
DOMIN SAMUN CIGABAN LITTAFIN ABBAN SOJOJI PART 2, MUTUM ZAI BIYA 300 NE, VIP KUMA 700, WANDA YA SHIRYA BIYA SAI YA TUNTU6I NUMBER TA, 08103884440 KADA KU BARI ABAKU LABARI WLH 👏👏👏






********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels


WhatsApp Number: 08138873799




Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads