Header Ads
Showing 111001 words to 114000 words out of 138623 words

Chapter 38 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

1164

Ads at the middle of Article

izuwa kitchen zuciyarta nayi mata ba daɗi saboda tausayin yaran duk da batasa su wanene su ba amma tasan basu da gata, yaya Omar kuma dama shi mutun ne mai son taimakai wata'kil wani wuri yagansu a wahalce yake son taimakon rayuwarsu, da wannan tunanin Saude ta shige kitchen,
Kallon juna su kayi cikin tsananin tsoran inda za'a kaisu, atare suka tashi haryanzu doguwar rigar material ɗinnan ce ajikinsu, mayafi kawai suka ɗaura akansu sannan suka fito,
Goggo naganinsu ta soma washe baki tana cewa "masha Allah ƴa'ƴan abusufyan ɗina maza ku matso ku kwashi albarka wurin gaggonku, ga kuma abincinku na jiranku,"
Da fara'a suka karasa atare suka zauna suna gaishe ta "barka da safiya goggonmu fatan kun tashi lafiya,"
"Lafiya lou Alhamdulillah, har mafarkin ku saida nayi jira, tsorona kar na farka na taras da bakwanan agidan bansan ya zanyi ba, in banga ƴa'ƴan abusufyan ɗina ba,"
fuskarsu cike da tsantsar farin ciki ga kaunar goggon katsina data shiga ransu daga jiya izuwa yau,"
"Yawwa maza ga shinan kuci ku ƙoshi, in ma bai isa ba aƙaro maku,"
Cike da zumuɗi hosana ta ɗauki plate ta bude warmer ɗin dake ɗauke da soyayyan dankalin turawa ta shake plate ɗin dashi, sannan ta bude ƙaramar kular jar miya ta lafta asama, ta motse ta shiga da turama cikinta,
Jahad kuwa Wainar kwai ta rinƙa haɗawa da slide bread tana cunkusawa abakinta, hannu goggo tasanya ta ɗauki flask ɗin dake ɗauke da ruwan liptop, ta tsaiyaya musu a cup kowa da nasa sannan tace "ga madara nan leda kowa ya zuba yadda zata ishe shi,"
Zame hannu hosana tayi daga irishi ɗin da take ji don haɗama, ta ɗauki milk ɗin ta zazzafa acikin ruwn tea ɗin mai uban yawa, tana jin jahad na cewa "banza kaɗan zaki zuba,"
Harara ta watsa mata tare da cewa "ina ruwanki ! ki ci abunda ke gabanki," sai da taga ruwan tea ɗin yayi kauri yaji uwar madara sannan ta tsagaita ta sanya sugar," ta hada tana sipping ɗinshi,
girgiza kai kawai jahad tayi tare da haɗa nata tea ɗin tashiga kurbarshi tana ci da bread ɗin,"
Kamar kura haka ta lamushe abunda ta zuma sannan ta bude warmer ɗin dake dauke da chicken pper soup, ganin lafiyayyiyar kaza yasa hosana gyara zama, anjima ba'a haɗuwa hannunta har kerma yake yi wurin daukar cinyar kazar tana turawa abakinta, gwanin daɗi kunnanta har rawa sukeyi,
Goggo sai murmushi takeyi tana kallonsu tsananin ƙaunar yaran take ji har cikin ranta,
Jahad kam kunyar abunda hosana keyi take ji kamar ta shaƙo ta take ji, sai faman licking hands ɗinta take kamar mayya,
Ƙasa ƙasa da murya tayi cike da jan faɗa tace "su hosana basaban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas, banza tasamu sai wankarta ake ba baka sai kunne,"
Fashewa da dariya su kayi gaba ɗayansu, ashe goggo na jinsu sai cewa tayi "Inji wa ya faɗi maki cewa gida babu, tab Ke ko kinsan katafaren gidan da abusufyan yake rayuwa acikinsa acan ƙasar Turƙiya? Kinsan irin daukar dayake ciki ? ae wannan bakomai bane, hmmm lokacin da naje turƙiya nakai masa ziyara, in zan ci abinci saiya sa an jera mun kayan maƙwalashe cike da dining tabur ae masu aiki gare shi sun iya girki sosai in sukayi abinci kamar abincin Aljanna don daɗi," ta ƙare maganar tana jaddada musu mgnrta
Tsagaitawa da cin abincin su kayi suna sauraronta baki asake, sukam wai wanene wannan abusufyan ɗin da Goggon katsina ke ta faman labarta musu zancen shi?
Kallon juna su kayi alamar neman karin bayani, goggo tace "ae ku kwantar da hankalinku, ni da kaina zansa abusufyan yazo nigeria ƙafarsa ƙafarku baxan ƙara bari ya tafi yabar yaransa cikin wahala ba,"
Sunnar dakansu su kayi ga dariya na cinsu, jin yadda goggo ke ƙaƙaba musu mutumin da basu san da Existing ɗinsa ba a duniya,
Atare Omar ya fito shi da babban likita sun shirya tsaf,
Goggon na ganinsu tace "Kai dirar yaushe ? ta ina kuka shigo cikin gidan,"
Murmushi Omar yasaki tare da cewa "goggona ke nan, ae jiya muka dawo tare da mutumina, mun same ku kuna bacci,"
Babban likita yace "Barkanka da safiya Mommyna fatan kun tashi lpy' yayi maganar ayayin da yake zama saman 2 seater, shi kuma marshal Omar ya samu wuri gefen gaggo yazauna saboda ya samu damar gaisawa dasu Hosana dakyau,
Atare suka haɗa baki wurin cewa "Barka da safiya yaya Omar dafatan ka tashi lpy," .
"Lafiya Alhamdulillah," ya amsa musu yana mai ƙara azan idonshi akansu," ba ƙaramin daɗi yaji ba ganinsu suna cin abinci,"
Duk kunya ta kama jahad har takasa idasa cin abincin, ita kuwa hosana bakin nan nata dama dama da jar miya, kuma a haka take kallonsa tana sakar mashi murmushi,
Bayan sun gaggaisa da goggo tace "daɗa sai naga ƴa'ƴan abusufyan jiya, ance wai kai ka kawo su naita mamaki nace yanzu har yaran nan sunyi girma haka amma ba'a ta6a nuna musu gidan goggonsu ba sunzo sun gaishe ni,'? Tayi tambayar rai a ɗan 6ace tana kallon Omar,
Jim omar yayi yana kallonta cikin mamaki yace "Suwa kenan"? Goggo ta nuna su hosana tare da cewa "gasu nan mana,"
ɗan murmushi yayi tare da kallon babban likita wanda shima murmushin ne a fuskarshi, sarai sunsan rigimarta, in ba haka ba yaushe Uncle Abusufyan ya ta6a aure balle har aje ga maganar aure,
Babban likita yace "Mommyna ayi mana afwan laifin mu ne, da bamu kawo su ba, kuma hada ƙarin makaranta sukeyi ne boarding school shiyasanya,"
ta6e baki goggo tayi tare da cewa "amma dae nikam ba'a kyautamun ba Allah, yara har sun isa aure amma ban ta6a sasu a idona ba! koda yake ba laifinku bane laifin Sufyanu ɗinne zan hadu dashi sai yayimun bayanin yadda ya hana ni jinina,
babban likita yace "Mommyna kenan, ina fata kina shan maganinki da na baki akai akai? Yayi maganar yana kallonta,
Yamutsa fuska tayi tare da cewa "kai ni na manta da wasu magunguna, suna nan cikin kwandon shara nake zuba su, ai naji sauƙi ynx,"
dariya su kayi gaba ɗayansu hada su hosana, Omar yace "goggo ina fa sauƙi a nan? U need a medicine 4 ur health,"
"Ae narasa meke damun mommyna, magani mai tsada kike zubawa cikin dustbin, gsky bana jin daɗi,"
Tsuke fuska goggo tayi tare da cewa "nifa bansan Iya shege, lafiyata ce ko lafiyarku ? ta tambaya tana harararsu


babban likita yace "lafiyarki ae tamuce mommyna, samun lafiyarki ae shine kwanciyar hankalin mu,"


Omar yace "maganarka gsky ne bro, goggonmu ataimaka adaina zuba magani a dustbin pls yakamata kina sha,"
Murmushi tasaki jin yadda suka damu da ita tace "shikenan, naji zan rinƙa sha daga ynx,"
Bayan sun ɗan tsagaita na wani lokaci Omar yace "goggo ina fata sun sanar dake cewa atare yau zan wuce dasu kaduna gidan yaya ishaq,"
Zumbur goggo tayi ta miƙe hankali atashe tace "bangane me kke nufi ba Omar? dama ba abusufyan bane yace akawo munsu nan ba su zauna wurina ? Bansan shegentaka fa ? Rabani zakuyi dasu ?
shiru Omar yayi just speechless ya ma rasa amsar da zai bata,
Babban likita ne yace "goggo go back to ur seat, lemme explain to u"
tsoki taja tare da cewa "Nifa bana gane ko wane yare a yanzu, in zakayimun magana da hausa kamun," tayi maganar tare komawa ta zauna don sarai taji mai yace, tsohuwar ƴar boko ce ,"
ƴar dariya dr haris yayi kafin yace "mommyna kin gane, yaran nan school suke yi acan, kuma exam suke zana wa, shiyasan ya muke so mu maida su makaranta kar asamu matsala,"
juya masa ƙeya goggo tayi tare da cewa "In ansan exam sukeyi a makaranta maiyasa to aka kawo munsu ? Don aja mun rai ! I hate nonsense wlh,'
Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya ta basu ba gaba ɗayansu, hatta saude dake tsaye a ƙopan kitchen tana sauraran firar tasu sai da ta dara, jikinta duk yayi sanyi Allah Allah take aranta Allah yasa kada goggo ta amince akai yaran nan kaduna gidan Aunty Babba,"
Atare da Omar suka shiga lallashinta don ta amince, sam taƙi yarda har sai da dr Haris babban likita yace "mommyna i promise u da sun samu hutun school zansa akawo mana su nan, su zauna wurinki ko ba haka ba Omar? Yayi maganar yana kallon omar,
Marshal Omar yace "Yeah hakane, dakaina zansa akawo su goggona,"
jiki asanyaye gaggo tace "shikenan na amince amma karku sa6a Alƙwari da zarar ansamu hutu akawominsu in ba haka ba zan sanarwa Abusufyan ɗina,"
Murmushi suka saki atare kafin Omar yace "insha Allah, ' sannan ya kalli su hosana ganin sun kammala cin abincin harsun wanke hannayansu yasa shi cewa "Kuje ku shirya,"
Atare suka miƙe sam basu so zasu rabu da gaggon su da aunty saude, har sun fara tafiya jahad ta dawo zata ɗauki kayan abincin da suka ci Marshal Omar yace "just leave it, bari saude tazo ta kwashe,"
Juyawa tayi suka wuce bedroom ɗin saude suna shesshekar kuka, har cikin ransu basu son rabuwa da gaggonsu da aunty saude jiya izuwa yau sunji tsananin ƙaunar kasancewa dasu,"
Shaf shaf jahad ta fara yin wanka sannan hosana tayi, dukansu suna ɗaure da towel suna shafa mai ajikinsu,"
Hannu tasa da sauri jin hawaye a idonta, goge su tayi da sauri, sannan ta gyara natsuwarta, ta shirya musu breakfast ɗinsu ta shigo da shi palor,
Bin ta kallo dr haris yayi tare da cewa "Omar ga fa future wife ɗina danake baka labari," .
ɗan kallonta Omar yayi tare da cewa "Oh dama ita ce kenan, ni bansan ta ba,"
Dr haris yace "taya xa'ae kasanta, daga rugar fulani nazo da ita, amatsayin wadda zan aura don na nunawa goggonku amma goggo ta maida mun mata ƴar aiki, "
murmushi omar yayi batare da cewa komai ba, goggon kam tuni ta wuce ɗakinta saboda rashin jin daɗi za'a tafi da ƴa'ƴan abusufyan ɗinta
Saude jiki amace ta gaishe su, suka amsa sannan ta ajiye musu tray ɗin, sannan ta juya ta kwashe kayan abincin da su hosana suka kammala dashi ta zuba a tray ɗin ta wuce kitchen, bayan ta ajiye kayan ta koma ɗakinta wurin su hosana, ko ido batasan ta haɗa dasu saboda kukan da take ji, saboda turken wawa,
Wardrobe ta buɗe ta ɗauko musu kayan da zasu sanya, jahad tabata riga da skirt na atampa da mayafi, sannan ita kuma hosana doguwar riga ce ta larabawa, baka sai ƴar guntuwar hijab fara, ba ƙaramin kyau su kayi ba,
Bayan sun shirya tsaf, ta haɗasu duka ta rungume ajikinta, gaba ɗayansu sukaji kuka yazo.musu nan suka shiga yinsa, sun jima kafin su fito,
daker aka samu goggon katsina tafito tayi musu sallama tasanya musu albarka idonta cike tab da hawaye, bayan sun kammala yi musu bankwana suka fito waje,
a jere motocin marshal Omar suke a harabar gidan, dakanshi ya buɗe musu motar da zasu zauna ciki suka shiga atare, sannan shima ya shiga motar dake bayan tasu ya zauna,
a natse ake driving ɗinsu har motocin suka fice daga gidan, suka miƙi hanya har suka fi ce daga welcome To katsina,
(* New destiny has started), 😥*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*




*page 88-89*


wuce azmee tayi dakinta agajiye saboda ta samu ta huta, yayin da tabar sehrish tana faman kwashe dishes ɗin izuwa kitchen, bayan ta kammala wanke komai ta mayar dasu inda suke ta jera,
Sannan ta kama hanyar futowa daga kitchen ɗin, sam bata lura dashi ba sai dae taganshi agabanta kamar Aljani,
Tsorone ya kamata jikinta ya shiga kerma, dariya haroon yayi tare da cewa "Ina son ganinki baby da yaushe zamu haɗu ne,"? Ya tambaya yana kashe mata ido,
Murya na rawa sehrish tace " Zuwa anjima yanzu agajiye nake, inaso na huta,"
Jinjina kai yayi tare da cewa "Okey, ki tabbatar kin kawomin kanki ɗakina, zan jira ki anjiman,"
"Insha Allah," ta faɗi tare da bi ta gefenshi ta wuce hankali atashe, tuni hawaye sun soma zarya a kuncin ta ,


tana shiga bedroom ɗinta ta shiga yarfa hannu tana safa da marwa, damuwa iri iri daga nan sai wancan, babban tashin hankalinta a yanzu batasan da wata manufa haroon ke nemanta ba, runtse ido tayi tare da faɗin "Ya Allah ka tsare ni daga sharrin wannan bawan naka, Ya ilahi ni ynx bansan ya zanyi ba, gashi yace nakai mashi kaina ɗakinsa," ta ƙare maganar tana mai jin bugun zuciya da fargabansa,
Daker ta tsagaita da zagaye zagayen da take yi a ɗakin nata,
gefen bed ɗinta ta hau ta ɗan kwanta eyes ɗinta na facing ceilling thinking abt many things, a haka har bacci 6arawo yayi awon gaba da ita, tasha bacci Ssae, dama ga weather ɗin is so comport,
Ba ita tafarka ba sai around ƙarfe 2 da mintuna har time ɗin sallah ya haura, tashi tayi tana dafe ƙirji domin kuwa har mafarkin haroon sai da tayi wai yace zai tona mata asiri wurin babban yayansu, da ta tabbatar da cewa mafarkine sai ta sauke ajiye zuciya tare da furta "Thank God it was a dream,"


Da hanzari ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala, sannan ta fito ta nufi wardrobe tayi dressing kanta cikin riga da wando, sannan ta ɗauki hijab ta sanya, ta janyo sallaya ɗinta dake a saman murfin wardrobe ɗin dama nan take hanging ɗinta sometimes hada hijabin sallanta,
Shimfiɗawa tayi sannan ta kabbara sallah, a natse take yin ibadarta ta, bayan ta kammala sallar ta zauna saman carpet ɗin ta lankwashe ƙafarta, ta ɗaga hannayenta ta shiga jero addu'a, ta jima hada hawayenta domin tabbas tana ji aranta akwai wasu ƙalubalen da zata fuskanta acikin watan nan, tana roƙon Allah ya bata ikon cinye koma wata irin jarabawace sannan yabata damar tsallake duk wani ƙalubalen da zata fuskanta," 😥


Bayan ta kammala ta miƙe tare da naɗe sallayar ta ninke ta sannan ta cire hijabin ta ninke ta itama ta tura su cikin wardrobe dukansu,


Hayaniya taji daga harabar gidan alamar ana buga ball daga wajen murmushi tasaki tabbas tasan su junaid ne ke wannan, wasan,
Ji tayi tana marmarin itama ta kalli wasan ball ɗin nasu wataƙil ta rage ƙuncin da take ji a zuciyarta,


Da azama ta ƙarasa jikin window ɗinta ta naɗe curtains ɗin sannan ta zuge glass ɗin ta tsaya tana leƙensu,
Su 6 ne acikin ragar filin ball ɗin dake acikin gidan , shi da wasu daga cikin soldiers ɗin dake tsaren gidan,
time ɗin da ta aza idonta akan junaid sai da taji zuciyar ta ta buga, sanye yake cikin kayan kallonsa riga da gajeran wando dai dai guiwarsa kana ganin waɗannan fararen ƙafafun nasa na rainon madara abun ba'ace wa komai,


launin kayan nasa red colour ne, wayyo ruwan kyau white in red dress na pyjamas, abayan rigar tashi an rubuta (ROMEO) No 10,
gaba ɗaya yazama tamkar tauraro acikin su sai faman tsalle tsalle yake ga kwantacciyar sumarnan tashi sai faman yarfo masa take saboda akwai Iska sosai a wurin, hakan ba ƙaramin kyau ta ƙara mashi ba,


Natsuwa sehrish tayi tana kallonshi daga inda take tsananin tausayin shi take ji ganin sai faman cin shi suke, in yasha wahalar cafke ball ɗin su kwace, ji take kamar tayi fiffike taje ta shigar mishi duk da bata ta6a jaraba buga ball ba,
Ransa ne ya basa cewa Sehrish na kallonsa saboda abun a jininsa yake muddin reeesh na a wurin sai yaji a heart ɗinsa sometimes heart beat ɗinsa ke canzawa,
daga inda yake ya shiga waiwayon ta ina zai ganta aikuwa cikin sa'a ya hange ta jikin window ta leƙensu, murmushi ya saki na jin daɗi aransa yana cewa ashe sehrish tana kallonsa kenan may be ma ba yau ta fara ganinsu suna buga ball ba aiko dole ya ƙara himma wurin wasan nasa yasamu yaci don ya burgeta sosai,
Bata lura da cewa junaid ya ganta ba saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu,
Da gudu junaid ya shige cikin su yasamu nasarar kwace ball ɗin cikin sa'a sai gashi yaci, aiko gaba ɗayansu suka sanya sowa suna jinjina mashi, yau yayi abun arziƙi,
Ita kanta sehrish dake leƙensu kamar ta diro ta window ɗin taje inda suke ball ɗin don murnar junaid ɗinta yaci ball,.
Abun ya matuƙar basu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads