Showing 135001 words to 138000 words out of 138623 words
Chapter 46 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt
ji tayi gabanta ya faɗi shi kuwa washe baki yayi yana faɗin "ƴar shila wato guduna kike yi naso ace jiya na Cafkeki da kin gane baki da wayau..
Shiru tayi batace masa komai ba, ci gaba da cewa yayi "kisa me ni a bedroom ɗina yanzun nan ina jiranki, ki taho mun da fresh fruits, in kuma kika ƙi zuwa hmmmmmmm kinsan sauran,
Yana faɗin hakan ya wuce yana sakin murmushi,.
Jikin sehrish yyi mugun sanyi,tsananin tsoron haroon takeji saboda gudun karya tona mata asiri, bakowa tafi ji ma tsoro ba face Babban yaya, batasan wane hukunci zasu mata ba, gashi ta tsorata dashi daga kallon kwayar idonsa ta zube inaga ya damƙe ta 😳
Tana cikin wannan tunanin Muryar junaid ta sauka a kunnanta "Ƴan mata sannu fa,' firgit ta ɗago tana kallonsa, saukowa yake yi daga upstairs yana murmushi jikinsa sane da riga da wando,
A hankali ta furta "junaid"
Ƙarasowa inda take yayi yana cewa "ya kke? Ya nagan ki a tsaye nan"? Yayi maganar yana kallon fuskarta,
"Dama wurin ka zanzo Aunty azmee tace nayi maka magana akan wayar nan" tayi maganar tare da nuna masa wayar dake hannunta,
Murmushi ya saki tare dasa hannu ya karba yana cewa "me kike son sani game da ita?
Tace "Komai ma sannan akwai abunda nake so na tambaye ka ma,"
"Ok, bazan iya jure tsayuwa ba, biyo ni musa mu wuri mu zauna ya faɗi tare da kama hanyar zuwa bedroom ɗinsa bin shi tayi zuciyarta na bugawa saboda tsoran Abun haroon zai yi mata wato yace taje taƙi zuwa,
Ashe haroon na nan yana kallonsu ita da junaid abun ya baƙanta masa rai kuma yaci alwashin sai ya ƙuntata mata,
Shiga ciki su kayi atare wuri yasamu ya zauna gefen gadonsa tare da bata Umarnin ta zauna,
Da ɗan tazara kaɗan a tsakaninsu,bayan sun natsu sehrish tace "junaid dama inaso na tambaye ka game da Numbar nan dana ta6a sawa a wayarka ta ƴan uwana bansan ko za'a samu ba ynx,"
Shiru junaid yayi yana tunani can yace "baza a rasa ba, Last time if i can remember sun turo mun message Lemme check it for u, yayi maganar yana zura hannunsa na dama cikin trouser pocket ɗinsa yayin da right hand ɗinsa ke ruƙe da phone ɗin sehrish,
Sehrish kuwa tunda taji cewa su hosana sun turo sako hankalinta ya tashi burinta taga me suka rubuta,
Zaro phone ɗinsa yayi tare da kunna ta, yashiga cikin messages ɗinsa yana duddubawa, yayin da jikin Sehrish sai kerma Yake sbd fargabar me suka turo,
"Yawwa Allah yaso banyi delete ɗinsa ba gashi ki gani," miƙa mata wayar yayi, hannunta na kerma ta amsa ta soma karantawa kamar haka
*sister maganin hosana fa ya ƙare akwai matsala ta zama wata Xararriya ta hana mu sakat pls ki taimaka mana*
Junaid na lura da halin da Sehrish ta shiga,
lokacin da tazo ƙarshen sakon, zumbur ta miƙe tsaye cikin tashin hankali murya na rawa take faɗin"Innalallahi wa'innna ilaihirraji'un junaid tun yaushe saƙon nan yake ...? ta tambya a rikice,
Miƙewa shima junaid yayi yana cewa "Am sorry sehrish wlh naso na taimaka musu tun lokacin ki duba message ɗin dake a ƙasan nasu ki gani na tura masu sako nace su turomin acct number nasu amma shiru i ave been trying their phone number but always switched off har na haƙura. '
Cikin shesshekar kuka Sehrish tace "Allah sarki hosana, nashiga ukuna bansan ya suka ƙare ba, hosana tana raye kota mutu nasan ba mai taimakon su....." Kuka ne yaci ƙarfinta sosai,
Cikin sanyin Murya junaid yashiga lallashin ta,
Cikin kuka tace "junaid bazaka gane bane...nasan suna cikin mawuyacin hali babu mai taimakonsu ina so naje wurinsu nagansu....' tayi maganar a kasalance,
"Sehrsih in dai anan garin suke ni zan kaiki a mota ta ki gansu,'
Girgixa mishi kai tayi tare da cewa "Ba'anan suke ba junaid" duk tabi ta susuce,..
Ajiyar zuciya junaid yasaki tare da cewa "kada Ki damu sehrish nayi maki alƙawarin cewa da kaina zan kai ki, ki gansu koma ina suke, amma sai Babban yayan mu ya koma U.s saboda in yana nan bazan samu hanyar da zan fita ba,'
tsagaitawa tayi da kukan ta kalle shi tare da cewa "kayi Alƙawarin xaka kaini "
"Eh insha Allah, amma ynx ki goge hawayen naki, ashe kin iya kuka har haka just like a new born baby,' yayi maganar da zolaya yana Imitating ɗinta,
Ita kanta batasan sadda ta fashe da dariya ba, saboda yadda junaid yake kwaikwayon kukanta sai ya koma mata tamkar babyn,
Hannu tasa ta share hawayenta, sannan yace "Kin natsu yanzu"?
"Eh" ta bashi amsa,
Komawa su kayi tare da zama, sannan junaid yashiga nuna mata yadda zatayi amfani da wayar, Sam hankalinta baya akan jawabin Junaid ta tafi can duniyar tunanin halin dasu hosana ke ciki, Apps ya tura mata kala kala a wayr masu amfani daga wayarsa, dayake akwai sim aciki mtn nan take ya buɗe mata whatsapp, Duka ya zuba mata numbers ɗin yan gidansu aciki, sannan yasanya ta a grps ɗinshi na friends,.
Daga bisani ya bata wayar suka yi sallama ta koma bedroom ɗinta, ganin time ɗin Sallah yayi yasanya ta ajiye wayar saman side drawer ta wuce toilet tayo alwala tayi sallar la'asar,
______________________________________
Bayan Aunty Babba ta kammala waya da Amani Fitowa tayi ta sauko down anan tasamu hafsat ta buɗe akwatinan kayan da suka siyo tana duddubawa, Kayane masu kyan gaske, Cord laces, Materials atampha, dogayen riguna kala-kala, Sleeping dress, Inners ba abunda basu siyo ba,hada Shoes & bags na gayu, ga Ribboms , turarurruka , jewellery everthing fa sun sayo,
"Gasky mommy na cha6a fa, kayan nan sunyi kyau saura a ware wanda za'a kai ɗinki,. Hafsat ce tayi maganar tana kallon Aunty babba wadda ke tunkaro ta,.
Gefenta ta zauna saman 3 seater ɗin da take, sannan tace "Zamuyi magana akan wannan zuwa gobe, ynz nagama magana da Amani a waya,'
ta6e baki Hafsat tayi tare da cewa "kin faɗa mata game da twins ɗin can?
"Eh na faɗa mata har ta bani wata shawara,'
"Me tace ita"? Hafsat ta tambaya yayin da take ajiye Veils ɗin dake hannunta cikin akwatin kayan data buɗe
Nan Aunty babba ta kwashe komai da suka tattauna ta sanar mata,
wani irin kallo hafsat tayi ma mommyn nata kafin tace "ke kuma sai kika ɗauki shawararta ko?
Aunty babba tace "eh naɗauka saboda gsky ta faɗa Omar zai iyayin zuwan bazata kuma duk sanda yazo zai fahimci halin da suke ciki zai tuhume ni akan hakan, don haka zan basu kulawa ta wani lokaci kafin nasa a Zubar dasu,'. Rai a6ace hafsat tace "Yanzu mommy har shawarar Aunty Amani zata fi tawa mahimmancin a wurinki !?
murmushi aunty babba tasaki tare da cewa "Ko kusa, kawai akwai abunda na hango ne shiyasanya,"
Jinjina kai hafsat tayi tare da cewa "Shikenan Mommy, amma koda za'a rinƙa basu abinci dole suyi mana bauta acikin gidan nan !!".
"Wannan ae dolene, zasu aikatu kamar jakuna duk wani aiki na gidan nan kansu zai koma," aunty Babba ta bata amsa,
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "daga yanzu na daina wanki da washing maching, Tun da Allah ya kawo mana sauki lallai ne zasu aikatu,
"Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kaisu bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae"
ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,
______________________________
Abban sojoji sashe na biyu wasu haryanzu basu fara payment ba, Free pages ne nake sanyawa yanzu don haka ku hanzarta biya tunkan su Ƙare saura pages kaɗan ma, idan kuka ce zaku naɗe hannu nima zan dakata ne🙅, inyi takaina dama ya lafiyar giwa, abun ya bani mamaki many of u sunyi shiru akan hakan, zamu ba juna mamaki ne insha Allah 😂 Boss Lady ce fa,
Abban Sojoji akwai Nrml grp 300
Special grp 500
Vip (700) iya kuɗinka iya shagalin ka, ni nawa tsarin daban ne nasan yadda zanyi da kowa,🙌 Wanda suka shirya 08103884440, su tuntu6e ni,
*sai naji sauƙi insha Allah zan ci gaba*🙏 Just keep praying for me don bani lfy😥, sannan waɗanda suka ga Pictures ɗina pls don't share it, ban bada Iznin ayimun share ba, sbd bansan bakin wasu ba,bansan me zasu ce ba,🙏😿*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
_🔥the Father Of Soldiers🔥_
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ_ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💞😍
ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ✨
*Mallakin*
*✨HAFSAT BATURE MOH'D✨*
~BossLady~💋
*Final Page In Part 1*
*page 100*⚡
"Kwarai kuwa, yanzu dae ki tattara akwatinan nan ki kai su bedroom ɗinki, Ni bari naje wurinsu naga ya suka kwana, Allah yasa suna raye dae"
ta faɗi tana dariya itama Hafsat ɗin dariyar take yi,
tayi mamakin ganin ƙopan store ɗin abuɗe turowa tayi ta shiga samun su tayi a tsaitsaye sai faman zagaye zagaye suke yi sun jigata sosai,.
Suna ganinta gabansu ya faɗi rass saboda tsoran matar suke ji sam sun gaza magana sai zare ido kawai,
murmushi Aunty Babba tasaki tare da cewa "Ashe kuna raye, gsky kuna da taurin rai,'
Jahad ce tayi ƙoƙarin gaishe ta bata amsa ba sai cewa tayi "ku biyo ni"
Sannan ta juya ta fice suka bi bayanta aransu suna Allah Allah gudun karta yi masu wani abun,
A wani bedroom ta tsaya ta turo door ɗin sannan tashiga, suma suka bi ta ciki, ɗumemiyar katifa ce a ɗakin sai wardrobe ta bango, da ƴar drawer,
"Kada kuyi tunanin a ɗakin nan zan barku, tsohon store ɗin can shine wurin baccinku in dare yayi, na kawo ku nan ne domin kuyi wanka ku samu kuyi sallah, sannan zan baku abinci duk rana plate ɗaya, amma ku sani zaku Aikatu sosai, don Gwamnati bata aikin banza,'
aunty babba ce ke kora masu bayanin nan ba mutunci a fuskarta, a daga tsayen da suke,
Kallon juna su kayi jiki asanyaye koba komai sun samu sauƙi atlease,
Jin sunyi shiru yasa ta daka masu tsawa da cewa "Baku ji ina magana bane, kun wani tsayamin kamar ƙerarrun gumaka,'.
Murya na rawa suka haɗa baki wurin cewa "Zamuyi komai kke so insha Allah,"
ta6e baki tayi tana kallonsu tace "kada kuyi tunanin sauƙi kuka samu a wurina, sam ba haka bane don yanzu uƙubar tafara,"
Jahad tace "Laifin me muka yi maki ?.
dariya aunty Babba tayi tare da kallonta ita da tayi magana tace "bakuyi mun laifin komai ba, kawai kun shiga tsakani na da abun Hari na ne shiyasanya,' tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin,
Shiru su kayi suna kallon juna bakomai ya tayar masu da hankali ba face abunda Aunty babba tace wato kada suyi tunanin sun samu sauƙi yanzu uƙubar tafara, me hakan ke nufi !?!?
ajiyar zuciya Suka saki atare wuce wa Jahad tayi toilet domin ita damuwarta Sallah, Hosana kuwa saman katifar tahau ta zauna idonta cike tab da kwalla luhu luhu Yunwa take ji Over,
Wuce wa kitchen Aunty babba tayi lokacin har hafsat ta koma bedroom ɗinta ta kwashe kaf kayan da aka suyo masu hosana da Jahad ta shige dasu (uwar Son banza)
Sai faman yamutsa fuska take kamar uban wani ya matsa mata ta haɗa musu abinci,..
Duddubawa tayi Cikin kitchen ɗin tana jin bazata Iya girkawa yaran Abinci da hannunta ba, Akwai sauran breakfast ɗinsu na safe da suka rage duk yayi sanyi abincin,
Tsayawa tayi tana tunani aranta kawai ta daure Just for today ta dafa musu ko Indomie ce,
Nan da nan ta kunna gas ta aza pot ta zuba ruwa ciki, shaf shaf ta haɗa kayan haɗi aciki ta zuba musu Indomie ɗin aciki,
Bayan ta kammala dafuwa, ta ɗauko plate mai ɗan faɗi ta baza musu Ita aciki da zafi zafinta sai ƙamshi take yi,
A tray ta ajiye musu ita sannan ta haɗa musu da sauran kayan breakfast ɗinda suka rage na safe, tare da drinks,.
Sai gata tafito ɗauke da tray ɗin ta wuce dashi ɗakin lokacin da ta shiga Jahad har ta fito Tayo wanka tare da Alwala ta maida kayan jikinta, tana a tsaye tana tunanin me zata sa tayi sallah,
Sai gata tashigo ba sallama ajiye musu tayi a ƙasa batare da tace komai ba sannan ta fuce,
Jikin hosana har kerma yakeyi ganin abinci jiki na rawa tasa hannu ta janyo tray ɗin, saboda zumuɗi ta buɗe plate ɗin dake ɗauke da taliyar, a gaggauce ta tsoma hannunta sam bata lura da hayaƙin dake fita ba saboda a makance take da yunwa nan take hannunta yayi jawur, zare hannun tayi tana kuka,
Hankali tashe jahad ta ƙaraso tana faɗin "Hosana meke damunki ne baki ga taliyar tana huci ba ne?
Cikin kuka tace "Yunwa nake ji sosai ne"
"Nasani ae," jahad ta faɗi tare da zama gaban tray ɗin, hannu tasa ta buɗe ƙaramar warmer ɗin dake ajiye cikin tray ɗin,soyayyen dankalin turawa ne da doya da kwai duk ta haɗe masu sunyi mugun sanyi,
Cikin sanyin murya Jahad tace "Ki ci wannan hosana ba zafi duk da yayi sanyi sosai, ruwan kashe gobara ba dole sai da mai kyau ba,"
Hannu suka sa atare suna ci daker suke tura shi cikin baki musamman yam ɗin data sanƙare, sai da suka rinƙa haɗawa da Coke ɗin data kawo masu, bayan sun cinye ne suka koma kan taliyar lokacin ta ɗan gare zafi,sunji daɗinta sosai,
Ba laifi sun ɗan cika cikinsu,
Shiga toilet jahad tayi ta kuskure bakinta sannan tafito ta bude wardrobe ɗin data gani a ɗakin, wasu tsofaffin kayane aciki dama ita Sallaya take nema kuma tasamu,.
ɗaukowa tayi ta shimfiɗa don tayi sallah,
Kamar daga sama ta faɗo musu hannunta ɗauke da kaya, watsa su tayi saman katifar dake ɗakin tana cewa "Gasu nan in kunyi wanka ku sanya,"
sannan ta ɗauki tray ɗin da suka kammala cin abinci dashi ta fuce dashi tana murmushin mugunta ita kaɗai tasan me take ƙissawa aranta,
duba kayan su kayi kala bibbiyu ne dogayen riguna masu kyan gaske, sai jalbaba guda biyu da takalmi silifas shima biyu, shine abunda suka samu,
Jahad tace "ina ji araina yaya Omar ya turo da kuɗi asiya mana kaya shiyasa ta bamu wannan hosana ki tashi kiyi wanka kizo ki canza kayan jikin ki,"
tayi maganar tare da cire rigar jikinta, ta ɗauki wanda Aunty babba ta kawo musu ta zura ajikinta doguwace mai dogon hannu tayi mata kyau sosai launin rigar Pink colour ce, daker hosana tayi wanka itama ta canza kaya daga nan kuma Aunty Babba ta zo tafita dasu domin nuna musu aikinsu
___________Ataƙaitace________________
A kwana a tashi yau wata ɗaya kenan da zamansu Hosana da jahad a gidan general Ishaq haƙiƙa sun fuskanci matsanancin tashin hankai kullum cikin tsoro suke da fargabar me zai je ya dawo, sam Aunty Babba da Hafsat basa raga masu sun mayar dasu Tamkar Jakuna marasa Ƴanci, kullum cikin ƙuntata musu suke, gashi duk wani aiki na gidan duka akansu yake ƙarewa, tun da asussuba Aunty Babba ke tashin su daga bacci tasa su fara aikace aikace, sune wanke wanke, sune shara, sune goge tiles tunda ga ƙasa har saman Bango duk girman gidan nan sai tasa sun goge ko'ina, ga Uban wanki hada na barguna, in sukayi mata kuskure kuwa har bugu take kai musu, ta tsane su kamar mutuwarta, tabbas su hosana da jahad suna cikin masifa kullum cikin kuka suke idan baka samu jiƙaƙƙun hawaye a idonsu ba to zaka samu busassu ne, duk wannan uban wahalar a rana plate ɗaya take basu na abinci su biyu don tsabagen mugunta irin nata, wani lokacin ma sai dae Jahad ta bar ma Hosana saboda tausayi ita kuwa kamar zata mutu da yunwa haka zata jure, dai dai da minti ɗaya basu samu na hutu, in ba ƙarfe sha biyu na dare ba take barinsu su kwanta, kuma acikin wannan tsohon store ɗin nan take garƙamesu sai da asuba ta buɗe su atashi ayi aiki, Wani lokacin idan yunwar dare ta addabesu Dankalin hausar nan dake acikin store ɗin suke ɗauka suna 6arewa suna Ci 😭
Duk dare sai sunci dankalin hausar sannan cikinsu ke ɗan cika, 😔
Duk wannan abun dake faruwa Marshal Omar sam bai sani ba, domin kuwa duk lokacin daya kira waya ya tambaye su sai ta shirga mashi ƙarya, in kuwa yace tabasu yayi magana dasu, sai ta fara Ja musu kunne ta buga musu warning akan karsu kuskura su sanar dashi halin da suke ciki sannan ta basu wayar, kuma agabanta suke yin wayar suna yi suna kallonta tana galla musu harara tana ƙara gargaɗinsu,
lokacin da Omar Ya shirya ziyartarsu ya kira Aunty babba ya sanar da ita zaizo, Jiki na rawa ta gyara su tsaf kamar basu ba hada kwalliya tayi musu, sannan taja musu kunne da barazanar zata kashe in suka kuskura suka tona mata asiri a wurinsa ko kuma suka yi yunƙurin cewa zasu bishi,
tsananin tsoranta yasa har Omar yazo yini guda ya tafi basu ce masa uffan fa, duk da yatafi da mamakin meyasa yaran Basa Dariya? Musamman mai ta6in hankalin saboda yasanta kullum cikin murmushi take, amma zuwan nan nasa harya tafi ko kallonsa basa son yi ba don komai ba sai don gudun kada hawaye su kufce musu yagani ya tuhumi Aunty babba, ƙarshe abun kansu zai ƙare, Wannan shi ake kira da Rana Zafi Inuwa ƙuna 😥😥😥
______________________________________
A 6angaren sehrish kuwa ta shiga halin ha'ula'i, domin kuwa Haroon Ya addabi rayuwarta, ya takura mata over, sam bai mata da sauƙi, ya gama firgitar da ita ya tsoratar da ita