Showing 87001 words to 90000 words out of 138623 words
Chapter 30 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt
muryar Aunty azmee tana cewa "Anaso ana kaiwa kasuwa,"
Ƴar dariya tayi tare da fi ce wa, kai tsaye part ɗinsa ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar,
Kamar kullum a buɗe door ɗin parta ɗinsa take, a hankali tashiga tana sanɗa kamar 6arauniya,
Sai da tayi tsakiyar falonsa nasa tasoma tunanin wai me ma tazo yi? Saboda ko'ina agyare yake tsaf ba datti ko kaɗan, sai walwali wurin yake har yau tana jinjinawa haɗuwarsa,
Murmushi tasaki tana wani tunani aranta, wanda bazai yiyu ba, 😔
Sai da tagama zagaye falon nasa tana tunani iri iri aranta, sannan ta soma gyara sa, babu wani aiki awurin, kawai ta ɗan yi goge goge ne,
tsayawa tari riƙe da waist ɗinta, so take ta sashi a idonta, zuciyarta ce ta bata shawara da cewa "ki ɗan leƙa sa, mana,"
"Anya? idan kuma idonsa biyu fa? In ya kama ni karairaya ni zae yi Allah,' ta bata zuciyarta amsa,
"Ke sai ki bari ya ganki? Ae lalla6awa zakiyi a hankali sai ki dan leƙa,'
Murmushi tasaki tare da tafiya cikin sanɗa, ta tsaya a bakin ƙopan ɗakin nasa, taci sa'a kopan a bude take, curtains ɗin ta ɗan janye tana leƙensa, 👀👁️
Kwance ya ke yana sharar baccinsa, cikin natsuwa a saman Royal bed ɗinsa, kai ka ce da zallar gold aka ƙera gadon, yadda ya ke wani kyalli ajikinsa,
Half body ɗinsa yayi covering ɗinsa da lallausan blanket, hannunsa na dama, ya zagayo dashi har izuwa saitin left ear ɗinsa, yayin da hannunsa na hagu kuma ya ke a saman wide chest ɗinsa,
Bin shi take da kallo kamar kura taga nama, wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, ta rufe masa half face ɗinsa, dogon hancinsa kawai take hange,
Lumshe ido kawai take, ita kaɗae tasan yanayin da ta shiga,
Tana cikin wannan leƙen nasa ko ƙeftawa babu, taji an shaqi wuyanta da ƙarfin gaske, Shaqa ba ta wasa ba,
Wani irin tsoro ne ya ziyarce ta, hankali atashe ta zazzare idanunta,
Muryarsa ce ta ratsa kunnanta da cewa "meyasa ki ke leƙe na !!"?
wata irin zufa ce ta wankowa sehrish, tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idonta, lokacin da ta lura cewa babu shi asaman gadon nasa, yaushe har ya sauko yakuma wuce ta, ya zagayo ta bayanta,harya shaƙi wuyanta,
Wani irin fitsari ne mai zafin gaske ya kufce mata, ji kake zirrrrrrrr yana zubo mata,
Muryarsa ce ta sake karaɗe kunnanta, " baza'a bani amsa ba" 😳😳😳😳😳😳😳
*Hafsat Bature Moh'd Boss Lady* 💋✨👏
*I Need your prayers urgently* 😔💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
_💞Extraodinary Love💞_
*Writer✍️✍️✍️✍️*
*💋HAFSAT BATURE BATURE BOSS LADY💋*
Full episode
~Page 73 -74
End of Chapter 1
*✨✨LAFAZI WRITERS ASSOCIATION* ✨✨
Not edited 😎
Jin shiru ba ta da niyar bashi amsar yasa shi harya fusata, a wani irin zuciye ya buga kanta jikin kopan da ƙarfin gaske, nan take sehrish ta fasa wata irin azababbiyar ƙara mai sauti tare da faɗuwa yaraf a sume,
Wannan sounds ɗin da sehrish ta fidda ne ya farkar dashi daga dogon baccin da ya ke yi, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa yana yamutsa fuska agajiye blue eyes ɗinsa na facing Ceilling,
Hankali tashe sehrish ta farka daga nap ɗin daya dauke ta, sai uwar zufa ke zubowa daga cikin sumar kanta, ashe bayan ta kammala gyara masa parlor insa bacci ne ya ɗauke ta a nan kasan lallusana carpet ɗin dake shimfiɗe, sai faman zazzare kyawawan idanuwanta take, tana shasshafa jikinta don ta tabbatarwa da kanta cewa mafarki ne take ba gaskiya ba,
Ajiyar zuciya ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah Allah na gode maka," cikin hanzari sehrish ta miƙe tare da fice wa daga part ɗin nasa ta koma kitchen ,
Shiru tayi tana ƴan kame kame ashe tun ɗazu azmee na zaune tana jiran.dawowarta,
Tana zaune saman daya daga cikin dining chairs dake a kitchen ɗin, ga tray da ta kammala shiryawa babban yayan breakfast ɗinsa ajiye a saman table ɗin gabanta, ta zabga tagumi tana jiran Sehrish,
Bin ta tayi da kallo ganin yadda ta shigo a hargitse tana wurwurga ido,
"Sannu ko'? Shanyar da ki kayi harta bushe," ta faɗi tana kallon ta,
Sunnar da kai sehrish tayi tana wasa da fingers ɗinta tace "Am sorry aunty azmee wlh bacci ne ya kwashe ni a falonsa without my knowing...'
tunkan ta ƙarasa azmee ta katse ta da cewa "bacci !!! A part ɗinsa!? Kin sha giyar wake ne?anya ko kinsan wanene SGR kuwa? You ave to be very careful sehrish, don't let that happen again if not u will Explain it !!,"
Azmee ta faɗi cikin faɗa faɗa, hakan ba ƙaramin tayarwa Sehrish da hankali yayi ba, ta tsorata sosai tuni eyes ɗinta sun cicciko da kwalla," .
"Aunty azmee tsotsai ne, ba da sani na ba nima, wlh sharrin shaiɗan ne,"
Sototo tayi da baki tana kallonta cikin takaici tace "na gane Ki sehrish whenever u did something wrong sai ki ce sharrin shaiɗan ko? ga iya bada hakuri kamar matar aure tagari,'
duƙar da kai sehrish tayi, jikinta ya gama mutuwa jin aunty azmeenta nayi mata faɗa,
ganin halin da sehrish ta shiga yasa azmee sassautawa da murya cikin lallashi tace "Sehrish ba faɗa nake miki ba, i just wanna u to be very careful in this home, bana so asamu matsalar da zata sanya a kore ki daga aiki, Babban yaya da kike gani mutun ne mai hatsarin gaske !!!, sai kin kula,"
Cikin sauke ajiyar zuciya sehrish tace "Shikenan aunty azmee, insha Allah zan kula, i won't let that happen zanyi komai yadda ki ke so,"
Murmushi azmee tasaki tare da cewa "yawwa my daughter, ko da yake nafiso nace ƙanwata hakan yafi mun daɗi, yanzu dae ɗauki breakfast ɗin nasa ki kai masa,"
"Tom aunty azmee," sehrish ta faɗi tare da sa hannu ta ɗauki tray ɗin, da ƴar fara a a fuskarta ta fice daga kitchen ɗin,
A natse take tafiya, zuciyarta na bugawa especially in ta tuna abunda Aunty azmee ta sanar da ita nacewa he's a dangerous man, hakan na kara tsoratar da ita,
tana cikin tafiya taji dirar Ball a ƙasan kafarta, ƙiris ya rage ta saki tray ɗin saboda ta tsorata, bin ball ɗin tayi da kallo kafin ta ɗago taga wanene ya jefo mata ita,
Sai faman murmushi yake ta saki, kamar gonar auduga, bawan Allah yasha wahala, kwallo kamar ibada duk zufa ajikinsa sai wanko masa face ɗinsa take,
"Junaid" ta faɗi acikin zuciyarta, a fili kuma sai cewa tayi "Sannu da dawowa"
Sam yaki mata magana, tun da yasa ta a idonsa, notikan kansa suka kwance, zallar ƙaunarta ce ke gudana a cikin zuciyarsa, karasawa yayi tare da duƙawa Yayi yakai hannu ya dauki ball ɗinsa, sannan ya ɗago tare da aza eyes ɗinsa cikin nata yace "Yunwa nake ji, ashirya mun snacks akawo mun a bedroom ɗina tare da coffeee i wll be waiting,, ya ƙare maganar yana kashe mata jiki da wannan smilling ɗin nasa,
Ita ma kanta batasan time ɗin da, ta shiga mayar masa da martani ba, na murmushinsa, tarasa dalilin dayasa take jin wani sanyi a ranta aduk lokacin da idonta suka shiga cikin na junaid (Why?)
daker ta amsa Iya amsa masa da cewa "insha Allah ynx zan kawo,"
"Ok" ya faɗi tare da bi ta gefenta ya wuce upstair duk tana, a tsaye tana kallonsa, ƙiriniyarsa na burgeta sosai,ko tafiya yake yi yana dan tsalle haka, .
Sai da junaid ya 6ace mata, sannan itama ta wuce sashen sgr ,
Time ɗin da ta karasa a bakin kopan sai da ta tsaya ta karanta addu'o'in neman tsari da sharrinsa sannan, ta shiga ciki da sallama,
Ba zato ba tsammani taji wannan sanyayyiyar muryar tasa so sexy ta amsa mata da cewa "Wa'alaikam salama,"
Wurgo ido tayi ta hangosa kishingiɗe saman royal sofa ɗin doguwa, kansa na saman hannun seater ɗinta, yayin da idonsa ke kan Laptop ɗinsa wadda ya aza ta saman stomach ɗinsa, kasancewar yana daga kwance, jikinsa na sanye da jallabiya fara, masha Allah kyau iya kyau, ba'a magana, masu sa kyau tayi kyau ba 😂
Jikinsa sai kamshin turaren imperial majesty ke tashi, wani irin daddaɗan kamshin kasancewar duk wani lotion da soap da yake using dasu bama perfumes ba kaɗae masu kamshi ne na fitar shari'a, kasancewar shi, ma'aboci son ƙamshi ga tsafta,
Lumshe ido sehrish tayi, tana jin wani irin heart beating, kamshin sa na rikitar da ita,
A hankali take tunkararsa, sai da taje dab dashi sannan murya na rawa tace "Gm sir," shiru bai bata amsa ba, hakan yasa ta jin fargaba,
Zuru ta ɗanyi tana tunanin kawai ta ajiye masa ta fice, har time ɗin eyes ɗinsa nakan Laptop ɗinsa yana daddanawa,
har ta ja da baya zata ajiye masa tray ɗin a samar tables ɗinsa muryarsa ta ratsa ta da cewa "Is this the right time daya dace a kawo min breakfast ɗina "?
Shiru sehrish tayi gabanta na faɗuwa, a cikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne, tabbas akwai matsala, saboda ita azmee ta sanar da ita cewa ba'a tashin shi daga bacci in yana yi, and now kuma yana complain ba'a kawo masa breakfast ɗinsa da wuri ba? to tayaya mutumin da ba'a tashin sa daga bacci zaisan ankawo masa breakfast ɗinsa da wuri !!!?
wannan jinkirtawar da tayi bata bashi amsa ba, ya sashi fusata, aiko tana a tsayan nan ba ta lura ba, ya ƴunƙura yasanya ƙafarsa da karfin gaske dama ga tsayi ya harba tray ɗin dake hannunta, nan take komai ya kife ƙasa, ya tarwatse food warmers ɗin da sauran tarkacen, zaro ido tayi tare da dafe ƙirji gabanta na faɗuwa, tsananin tsoro ne ya bayyana a fuskarta,
Cije lips ɗinsa kawai ya keyi, ganin koma wanene yaƙi moving, wani irin motsi taji bana wasa ba, aiko da gudun gaske ta fi ce daga falonsa, wato da ace sehrish tabari wannan motsin da taji yayi da ba ƙaramin naushi zai kai mata ba,
Kamar daga sama su ka ci karo da azmee wadda ke ƙoƙarin Fitowa daga kitchen ɗin, tana ganin sehrish gabanta ya faɗi, aranta tace "yayi tsiyar,"
Fashewa tayi da matsanancin kuka a lokacin da taganta, agaban azmee jikinta har wani jijjiga yake yi, sai kerma la66anta ke yi,
Hankali tashe azmee tace "menene sehrish me ya faru,? ta faɗi tana jiran bayani daga wurinta,
daker kukan da sehrish take yi ya tsagaita, cikin matsanancin kuka take korawa azmee bayani,
" ...aunty ..azmee...baaa...ke ki ka ce ba'a tashin sa daga bacci ba....ynx fushi ya keyi ba'a kai masa breakfast ɗinsa da wuri ba..ba ki ga yadda yasa ƙafarsa ba ya harba tray ɗin abincin komai ya watse, bansan ya zanyi ba," tana magana tana yarfa hannu, sai faman jan majina take yi, duk ta firgice,
Shiru azmee tayi saboda dama ba wannan ne karo na farko da yake faɗin cewa ba'a kaimasa breakfast ɗinsa da wuri ba, gashi mafi yawancin lokutta bacci yake yi, kuma ba uban da ya isa ya tashe shi yana bacci, saboda kamar ɗan wrestling haka yake, Naushi yake kaiwa, gaba ɗaya kannensa su fawan dasu Irfan ba wanda baije tashe shi daga bacci batare da ya naushe shi ba, shiyasa kowa yayi nesa dashi, ake barinsa sai ya kammala baccinsa ya tashi dakansa, sannan kuma ya hau jarabar ankai masa karin kumallonsa a makare,"
"Aunty azmee ba ki ce komai ba, ya zanyi? gashi can ya 6arar da abincin shima wata matsalar ne, ya za'ae abashi hakuri na samu naje na kwashe wanda ya zubar na zuba masa wani"?
ta ƙare maganar tana kallon azmee wadda tayi zuru cikin rashin sanin mafita,
yarfa hannu azmee tayi tare da cewa "wlh nima bansan menene solution ba, mutun ɗaya ne zai iya shawo kansa, kuma ba kowa bane face Junaid...."
"Naji kamar ana maganata a wurin nan," junaid ne yayi maganar wanda ke saukowa daga saman stair ɗin, jikinsa sanye da jeans da farar t shirt,
Bin su yayi da kallo musamman sehrish wadda ke tsaye, ido luhu luhu tasha kuka, yau taga tashin hankali,
Ajiyar zuciya Azmee tasaki ganinsa cikin sauƙi,
"Junaid matsala aka samu," azmee ta faɗi tana kallonsa,.
"Meya faru"? Ya tamvaya yana kallonsu,"
Nan azmee ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar mishi, kamar yadda sehrish ta faɗa mata,"
Murmushi yasaki tare da kallon sehrish wadda ta sunnar da kanta kasa, yace "Calm down ur mind, in dai Babban yaya ne, ni ne controller ɗinsa, just wipe ur tears," ya faɗi yana nuna tears ɗin dake zubowa daga eyes ɗinta,.
Hannu tasa tana goge su kamar yadda junaid ya bata umarnin ta share su,"
Sannan yace da aunty azmee "a shirya masa wani breakfast ɗin, ynz zan zo na karba," yana gama faɗan hakan ya juya tare da wuce wa izuwa upstairs part ɗin Sgr,"
"Yanzu sai kiyi murmushi, junaid da ki ke gani shine masarrafin babban yayansu, shi ke juya shi kuma ya juyu," azmee ce tayi maganar tana kallon sehrish,
Ita dae har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba, ta jima tana mamakin abunda sgr yayi, yadda ya hauro da ƙafarsa ya harba tray ɗinta ya kife kasa ba ƙaramin mamakin hakan tayi ba, maimakon taji haushinsa, sai ma taƙara jin ƙaunarsa na ninkuwa azuciyarta 💋
Da sallama junaid ya shiga falonsa yana faɗin " babban yayan mu, gani na iso, nazo na takura maka na hana ka sukuni,"
Jin Voice ɗin junaid yasa, Rafayet tashi zaune daga kishingiɗen dayake, ya mayar da laptop ɗinsa, saman desk ɗinta, a hankali ya ware idonsa akan junaid tare da cewa "sai ynx zaka so wurina? Ina ta fama da yunwa arasa wanda zai tashe ni ko"? yayi maganar yana lumshe sexy blue eyes ɗinsa,.
da murmushi junaid ya karasa yana faɗin "am so sorry babban yayanmu, kaima kasani, na damu da cikin ka sosai, shiyasa ko breakfast banyi ba tun safe, kai kawai nake jira ka farka muci atare" ya karasa maganar tare da russinawa ya rungumosa sannan ya manna masa kiss a gefen face ɗinsa,
Lumshe idonsa yayi, har cikin zuciyarsa, tsananin kaunar yaron ya keyi ba don komai ba, sai don kasancewarsaa mai tsananin biyayya ga iya magana, minti 5 yayi yawa ga junaid ya sace zuciyar mutun especially da wannan murmushin nasa, shiya sanya Hafsat bature ta kamu da tsantsar ƙaunarsa 😥
Juya wa junaid yayi ya kalli, tray ɗin da babban yayan nasu yayi watsi dashi a ƙasa, cike da daɗin baki yace "subhanallahi ya akai kayan abincin nan suka zube ƙasa, ni nasan aikin tukur ne bari na kwashe na canza wani,"
Ya karasa ya zuƙunna yana tattare kayan, duk rafayet nabinsa da ido, sai da ya kammala kwashe komai ya mayar acikin tray ɗin sannan ya ɗauka yana cewa "am coming now yayanmu,"
Sannan ya fice, ajiyar zuciya yasaki lokacin da ya fito daga part ɗin nasa, kitchen ya wuce, azmee kaɗai yasamu aciki ta kammala hada masa wani bf ɗin acikin tray,
Miƙa mata na hannunsa yayi ta karba sannan ya ɗauki wanda ta haɗa masa asaman table, ya dago yana kallonta yace "Ina Sehrish take,"? Murmushi azmee tayi kafin tace "ta tsorata ne sosai, ta koma ɗaki ynz," .
Yace "ok amma aunty azmee yaushe zaki faɗa mata cewa nasan cewa ita maca ce ? Inaso tasani pls !" yayi maganar da shagwa6a,
Ƴar dariya azmee tayi kafin tace "insha Allah yau zuwa anjima, zan faɗa mata,"
Murmushi yasaki ya fice yana faɗin "Can't wait to see," dariya azmee tayi tare da cewa "Romeo kenan,"
Itama fice wa tayi daga kitchen ɗin don tajima yau tana aiki acikinsa since morning kamar enjine,
Yana zaune yana jiran junaid, sai gashi ya shigo, hannu rike da tray, a saman table ɗin dake gabansa daga gefe ya ajiye masa shi, sannan shima yazauna gefensa tare da cewa "Babban yaya zan iya baka a baki," ɗagowa sgr yayi yana kallonsa face ɗinsa tamkar zaiyi murmushi yana kallonsa, wannan fadancin na junaid ba karamin tafiya yake dashi ba,
Plate junaid ya ɗauka, ya shaƙe masa shi da chips har yayi sauro don yasan Babban yayan nasu baya wasa da cikinsa, akwai bama ciki haƙƙinsa 😉
Tura masa plate ɗin yayi agabansa, naɗe hannun jallabiyar jikinsa yayi, junaid ya zuba masa ruwa ya wanke hannunsa acikin bowl, sannan ya soma ya zura hannusa yana ɗibar chips ɗin yana turawa a bakinsa, in kaga yadda yake wawuro wa yana turawa a small mouth ɗinsa sai kayi mamakin tayadda akai abincin ke shiga, saboda ƙankantar bakin nasa,
Robar cool milk ya dauka ya zuba masa acikin glass cup ya tura masa a side plate nasa, ga fresh fruits ya acikin hadadden plate ya ajiye masa ga sauran delicious,"
Junaid ne yazauna yana saving nashi, bayan ya tsagaita ya zuba msihi ido yana murmushi, ɗagowa sgr yyi suka haɗa ido yace "what"
"Kyau nake kallo fuskar babban yayana," junaid ya basa amsa,
"Duk kyau na, nakai ka junaid,"? Ya tambaya yana kallonsa, ɗan sunnar da kai junaid yayi tare da cewa "kai na musamman ne yayana, komai naka na musamman ne, haka kyan ka ma,"
dan ta6e baki sgr yayi yana kallonsa ayayin da yake mika hannu ya dauki cool milk ɗin dake acikin cup ya kurba sosai tare da mayar wa ya jiye,
Sannan cikin natsuwa yace "Ni kam tunda nake aduniyar nan, tun da Allah ya halicce ni a duniyar nan , ban ta6a ganin yaro mai shiga rai mai sace zuciya ba irin ka! junaid u are so special to me i don't know how to explain it but I really really love u so much, just tell me whatever u want am ready to do it for u,"
daɗi kamar zai kashe junaid jin yadda babban yayan nasu ke yabonsa, sam ya gaza rufe bakinsa har sai da sgr ya maimaita cewa "ka faɗamin komai kake so nayi maka insha Allah,"
Cikin sanyin murya junaid yace "babban yaya murmushinka kawai nake so, dan Allah kayimun koda