Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 138623 words

Chapter 34 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

945

Ads at the middle of Article

ta ke sanar da ita, shine tasa ta kira mata yaran tagansu,"


"Jahad me yasa take kallon mu? bata son mu ko? Korar mu zatayi ko"? Hosana ce tayi ƙasa ƙasa da murya tana raɗawa Jahad a kunne,


Jahad tace "nima bansani ba, amma ina tsoran kartace bata son mu, in ta kore mu, ina zamu sa rayuwarmu? Cikin raɗa suke maganar tasu, duk sai da suka gama raɗe-raɗen sannan su kaji goggon katsina ta fashe da dariya tare da cewa


"kun ta6a jin inda uwa ta guji ƴa'ƴanta !? Ku fa jinina ne, ƴa'ƴan abusufyan ae ƴa'ƴana ne halak malak,"


Kallon juna su kayi jin abunda tsohuwartace, atare suka hada baki tare da cewa "ABUSUFYAN kuma wanene shi ? mu bamu son shi ba,'
ɗaure fuska goggon katsina tayi tare da cewa "Bansan shashanci in ma zolayata ku keyi to ku daina, ni ba amun irin wannan wasan yanzu na burkice, ku faɗamin gaskiya ku ba ƴa'ƴan abusufyan bane,?


Babu wasa a fuskarta tayi tambayar,


hankali atashe suka ce "wlh bamu son shi ba, bamu son wa kike magana akai ba, mu yau muka zo gidan nan,"
Sassauta murya goggon katsina tayi tare da cewa"kuna nufin ku ba ƴa'ƴan abusufyan bane ? Ni zaku raina wa hankali ko? Kubar ganin nafara tsufa da hankali na wlh Wannan furfurar da kuke gani akaina, bata tsufa bace ta arziƙi ce," 😡
ta yi maganar tana hararansu, cikin tsananin tashin hankali jahad tace "wlh goggo gaskiya muke faɗa miki, bamu son shi ba, mu ba ƴa'ƴansa bane,"
Jin yadda jahad ta karyatata yasa ta fashe wa da matsanancin kuka, zaro ido su kayi ganin tsohuwar na sharar kwalla, kuka fa sosai hada jan majina tana faɗin "saboda na fara tsufa kke gudu na ko? ban ta6a tunanin ƴa'ƴan abusufyan zasu guje ni ba, wlh sai na kirasa a waya nasanar masa tashin kunyar da kukayi wa goggonsa wlh baxai ƙyale ku ba...'
tayi maganar tana shesshekar kuka abun kamar a mafarki su hosana da jahad suke kallon lamarin,
Jin kukan goggo yasa saude fitowa daga kitchen hankali a tashe karaso wa tayi tana faɗin "Subhanallahi goggonmu me nake gani haka kamar kuka a idonki,'
Ƙara fashe wa da kuka gaggon katsina tayi tare da cewa " saudatu dan Allah waɗannan ba ƴa'ƴan abusufyan bane? tayi maganar tana nuna su Hosana da hannunta,
Sakin baki Saude tayi galala cikin mamakin rigimar goggon katsina, girgixa kai tayi tare da cewa " wlh narasa meke damunki goggo ! Sarai fa kinsan cewa Uncle abusufyan bai ta6a aure ba ko? wai yaushe ma yayi budurwar ballantana ma aure har akai ga ƴa'ƴa, anya goggo kina shan maganinki akai akai'?
Miƙewa tsaye goggon tayi idonta cike taf da kwalla fuskarta a damuje tasa idonta cikin na saude tace" saudatu hada ke za'a ƙaryatani ko? ke ma kallon zararriya kike mun ko? saudatu da hankali na wlh, waɗannan yaran ƴa'ƴan abunsufyan ne, Jini na ne ina ji ajiki na, dan Allah kudaina mun yawo da hankali wlh zuciyata zata iya bugawa in mutu a wurinnan,"
Goggo tayi maganar cikin ƙunar rai da jin ɗaci aranta saboda ita harga Allah ta tabbatarwa kanta cewa tagwayen nan ƴa'ƴan abusufyan ne, mutun da bai ta6a aure ba, hasalima ma ba a nigeria yake zaune ba gaba ɗaya,
Shiru saude tayi tana kallon goggo dake ta faman kuka kamar ƙaramar yarinya aranta tace "tabbas goggo fa hauka ya tashi gadan gadan, don haka a kunnan babban likita dole nasanar mishi a bincika kwakwalwarta in ba haka ba kawai daga ganin yara sai kice wai ƴa'ƴan Uncle sufyan ne, yau yau ɗinnan fa yaran nan suka fara zuwa gidan nan tab lallai akwai matsala awurin nan........", muryar goggonce ta katse ta da cewa
"Saudatu kinyi shuru baki ce komai ba? ƴa'ƴan abusufyan ne ko?


Yarfa hannu saude tayi saboda tama rasa amsar da zata bata,


Jinjina kai goggon katsina tayi tare da mayar da idonta kansu hosana da jahad waɗanda jikinsu keta faman kerma saboda tsoran tsohuwar don sun lura tana da ta6in hankali,
Rai a6ace tace "Wlh ku ƴa'ƴan abusufyan ne !! Ni zakuyiwa karya don kutmar ubanku !! Kunci buhun ubanku ƴan kan uba
!!! ,
Hankali atashe su hosana ke kallonta, saude kuwa aza hannu tayi akai tana faɗin"goggo dan Allah kidaina !! Kidaina zaginsu mana akan abunda basu sani baaa......


tunkan ta ida goggon tasa hannu ta buge mata baki, dafe baki sauden tayi don taji zafin bugun,


Ci gaba da magana goggon tayi a birkice tana kuka, " Ae dama nasani ba wanda zai goyi bayana akan magana ta, amma ni nasani wlh ku ƴa'ƴan ZAINABU ne, dama haka uwarku take kamar ku ɗinnan, shegen taurin kai da kafiyar tsiya, kunnan ta kamar na zomo, fitinanniyar yarinya ƙiri-ƙiri ta guji jini na, dama sai da nace mata cikin jikinta na Abusufyan ne amma taƙi yarda ae dama nace mata jiki magayi amma taƙii ji, kunnan ƙashi ko ae ynx nasan taji jiki bawan Allah bai mata komai ba amma taƙisa, wlh cikinsa ne ku ƴa'ƴansa ne amma kunƙaryata ni, ga falo falon kunnuwanku nan irin na abusufyan shima dayake baijin maganata kangararre ne yaƙi jin magana ae gashi nan......


Zuba kawae goggon katsina takeyi ba ƙaƙƙautawa kai kace radiyon da bata da saiti, notikan kanta sun kwance sai faman zazzaga musu bala'e take yi, tana yi musu magana akan mutanen da basu san da zamansu ba,
tashi su kayi atare su ka tsaya suna kallonta haƙika sun tsorata da tsohuwar tuni idonsu ya cicciko da kwalla,
Goggon katsina bata dakata da surutun ba har sai da Saude tace "goggon kiyi hakuri dan Allah, nima na yarda cewa su ƴa'ƴan Uncle sufyan ne, sai yanzu na ƙara lura da kamannin nasu dagaske ne abunda kika faɗa,
saude na gama faɗan maganar ta kalli su hosana tayi musu alamar su amince suma da maganarta don asamu ta lafa,
Cikin sauri suka zube saman guiwowinsu agabanta tare da cewa "Dan Allah kiyi haƙuri goggonmu, munyi miki laifi, tabbas mu jininki ne mu ƴa'ƴan abusufyan ɗinki ne, ki yafe mana munsa kin zubda hawayenki,"
Sanyi goggo taji aranta dama ita burinta kawai su amince cewa su ya'yansa ne, hannu tasa tana share hawayenta, bayan ta kammala ta miƙa hannayenta tare da ruko nasu ta tsayar dasu tsaye fuskarta da murmushi sai kace ba wadda tagama sharbar kuka tace " Alhamdulillah har hankali na ya kwanta ynx, amma fa kun wahalar da gaggonku sosae kun sani ina ta faman zubda hawaye na, da ace abusufyan na nan kuma yasan abunda ku kayi ma goggonsa tabbas sai ya muku dukan tsiya" ,
Sunnar da kai su kayi tare da cewa "ayi mana afuwa goggonmu, bazamu ƙara ba insha Allah,"
Murmushi tasaki tare da cewa " ku koma kuzauna ƴa'ƴana, yanzun nan zan kira mahaifinku a waya ku gaisa," 🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️


BossLady❤️ Inaso naji ta bakin ku game da annoucement ɗina nasan kowa ya karanta, sannan comment akan page ɗin yau 👏👏👏
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*


ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ🌹❤️
*Mallakin*


*🌹Hafsat Bature Moh'd*🌹


~BossLady~💋


Page 81-82 part 2


*Meaning of name sehrish is an arabic name, ma'anar sa kuma Glamorous Personality* 🌹


Har haɗa baki suke yi wurin cewa "mahifinmu kuma ! A waya !?.
Da ƴar dariya a fuskarta tace"Eh mana, ae kullum sai ya kira ni mungaisa,' tayi maganar ayayin da ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinta don ta ɗauko wayarta,
Hannu suka aza akai alamar sun shiga uku, ita kanta saude tama rasa me zatayi abun ya ɗaure mata kai, lamarin goggo sai addu'a tsufanta da rigima yazo mata,
"Kada ku damu kunji kawai, ku kwantar da hankalin ku, in ta kawo muku wayar ku amsa ku gaisa dashi amatsayin mahaifinku, Uncle sufyan ya riga da yasan rigimar Goggonmu wayayye ne shi zai fahimce ku,"
Saude ce tayi musu wannan bayanin, jiki amace suka amsa mata da cewa "Toh,"
Sannan ta juya ta koma kitchen saboda tabar girki saman gas,
Zuru su kayi suna jiran zuwan gaggon katsina da waya, babban tashin hankalinsu yarda zasuyi waya da mutumin da goggo ta ƙaƙaba musu a matsayin mahaifinsu wanda basu ta6a gani ba kuma basu san kowanene shi ba,"
suna nan zaune zuciyarsu nata bugawa sai ga goggo ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da waya sai faman zabga murmushi take yi,
Koda su ka ganta gabansu ne ya faɗi rass don su a tsorace suke,
Miƙa musu wayar tayi tare da cewa "Maza ga mahaifinku nan akan layi kuyi masa magana,"
Kamar bazasu kar6a ba haka su kayi daker Jahad tasa hannu ta karbi wayar goggon tare da karawa a kunnanta tace ,"Assalamu alaikum,"
daga can 6angaren taji wata natsattsiyar murya ta amsa mata da cewa "Wa'alaikum salam,"
sai da jahad tayi jimmmm kafin ta daure ta cije tace "Abba Jahad ce ɗiyarka, ina fata kana cikin koshin lpy,"
Abusufyan ya amsa mata da cewa "lpy lou Alhamdulillah My daughter, kin yi missing ɗin abbanki kuwa,"? Yanda yayi maganar ba ƙaramin kashe ma jahad jiki yayi ba, sai kawai taji hawaye na ƙokarin zubo mata,
Murya na rawa tace "Nayi missing ɗinka sosae abbana, ina kewarka," tayi maganar ayayin da take dab da fashe wa da kuka, cikin sauri tace "Abbana ga hosana ku gaisa, itama tayi kewarka sosae,"
"Okey bata wayar," ya umarce ta,


Miƙawa hosana wayar tayi jikinta na kerma, hannu hosana tasanya ta karbi wayar tare da karawa a kunnata, duk goggo na tsaye tana kallonsu sai faman murmushi take yi, (ta haɗa Bomb)


Tashi jahad tayi cikin sauri ta wuce bedroom ɗin saude tana shesshekar kuka tana idasa shiga ɗakin ta faɗa saman gado tare da fashe wa da matsanancin kuka, bakomai bane ya karya mata zuciya ba face tunda suke arayuwa basu ta6a sanin daɗin soyayyar mahaifi ba ga Uban amma bai da amfani,"


A can kuwa tun da hosana tasanya wayar a kunnanta tace "Abbana dagaske kaine mahaifin mu kamar yadda goggo ta faɗa,"
On the other hand abusufyan yace "My daughter are u doubting abt ur father? nasan kinyi kewata ne shiyasanya kike kokwanto akaina,"
aikuwa jin ya tabbatar mata da cewa shi mahaifinsu ne yasanya ta fashe masa da kuka tare da cewa "dama nasani kaine mahaifinmu, ba wancen mugun ba, sai da nace ma Oumma mu bamu kama dashi mummunane shi mai baƙar zuciya amma taƙi yarda, ni nasani ba abban mu bane, babu uban da zaiyi wa ƴa'ƴansa haka, kaine mahaifinmu,......"
Katseta yayi tare da cewa "Silent pls, sorry my daughter bana fahimtar zancen ki i was busy now, zan kira anjima,'
yana gama faɗan hakan ya kashe wayar saboda baisan inda zancen nata ya dosa ba, shi dai kawae ya amsa kira ne kamar yadda goggonsu ta sanar dashi cewa ƴa,ƴanshi sun zo, sarai yasan rigimarta shiyasa yabisu a hakan,
Ganin ya katse kiran yasa hosana fashewa da kuka, wurgi tayi da wayar goggon saman kujerar sannan itama ta miƙe tana ci gaba kuka ta wuce ɗakin saude,
Jikin goggo yayi sanyi, ita a tunaninta abusufyan bai kula da yaransa shiyasa suke kuka, don haka taci alwashin zata sashi dole saiya zo nigeria ya ɗauki ƴa'ƴansa ya koma dasu can qasar da yake zaune, a ranta tana cewa "in banda shiririta irin ta abusufyan ka kama hanya ka tafi ƙasar Turƙiya kabar yara cikin damuwa, gashi nan sai faman kuka suke yi, Allah ni da kai ne, saina sanar wa AMMI halin da ake ciki,
Ta idasa maganar tata tare da sa hannu ta ɗauki wayarta ta wuce dakinta tana ci gaba da surfa bala'e akan rashin adalcin abusufyan,


............................................SEHRISH.........................
tun da suka koma ciki take jin zuciyarta wasai, hankalinta kuma ya ƙara kwanciya yanzu,
Gaba ɗaya matasan gidan sun kammala dinner ɗinsu kowa ya koma bedroom ɗinsa,
Babu kowa ita kaɗae ya rage ta kai wa Babban yayansu dinner ɗinsa, shine kaiwa bai sauko yaci ba, dama azmee tace sometimes kai masa ake a part ɗinsa,
Tsoranta kar yayi mata abunda yayi mata da safe, wato da yayi watsi da tray ɗin hannunta,
A natse take tafiya zuciyarta na ɗar ɗar hai ta haye upstairs ta wuce part ɗinsa da sallama ta shiga babu kowa aciki, agyare yake tsaf haske ta ko'ina ga ni'ima acikin palor insa,


A hankali tasanya kafa tashiga ta ƙarasa gaban table ɗinsa ta ajiye tray ɗin ta tsaya riqe da ƙugu tana jiran fitowarsa bin ko'ina take da kallo tana ƙara jinjinawa haɗuwarsaa, .
bakomai ke fisgarta ba fa ce sanyayyan ƙamshin dake tashi tana burin wata rana ta samu damar da za ta ɗan miƙe ƙafa a saman 3 seater ɗinsa ta kwanta, 😌😒


Sauko ƙafarsa yayi fara tass babu takalmi a kafar jikinsa na sanye da sleeping dress red color masu laushin gaske, jikinsu akwai zanene flowers masu kyau, riga da wando ne abunka ga handsome stylish man ga kira sun bi shape ɗin jikinsa kai kace don shi akayi kayan, kyau kam ba'a magana ku kun sani ae,
tana cikin wannan kalle kallen idonta ya hango mata shi to fa nan take ta rasa duk wani karsashi na jikinta, bin shi kawai take da kallo, cike da wannan tafiyar tasa ta nigogin basawa ya karaso hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa, halittar kyawunsa ta kara fitowa sosai daga saman rigar ƙirjinsa a buɗe yake farar fatar sa ta bayyana muraran,
Sai kamshi jikinsa yake kamar wanda aka tsamo daga kogin turare,
Ga sumar nan tasha gyara sai salƙi take tana ɗaukar ido,
Zama yayi yana naɗe hannun rigarsa,
Sai da rishi ta dai dai natsuwarta sannan tace "Barka da fitowa Babban yaya,"
"Yawwa," ya bata amsa a takaice,
Har cikin ranta jin daɗin muryarsa take saboda yanayin yadda hausarshi ke fita irin ta wanda bai ƙware ba,
Cikin girmamawa sehrish ta sake cewa "Me kake buƙata na zuba maka,'?
ta tamabaya saboda kartayi ba dai-dai ba,
"Abun da ya dace," ya bata amsa,
Murmushi tasaki tana kallon face ɗinsi musamman gashin girarshi da eye lashes ɗinsa,
Hannu tasa ta buɗe plate ɗinda ke ɗauke da friend meat (tsiran nama) yasha kayan ƙamsi yaji mai yaji komai,
tura mishi tayi agabansa sannan ta ɗauki bottle milk ta zuba mishi a glass cup ta ajiye masa,
bayan ta gama ta ɗan ja da baya tana ƙare masa kallo, yanayin yadda yake ɗaukar tsiren yana turawa a bakinsa ba ƙaramin kyau yayi mata, ji take ina ma da hali ta bashi abaki saboda ta sauƙaƙe mishi wahalar ,😒
Wayar sa ce dake ajiye cikin bedroom ɗinsa ta soma ringing da sautin gaske taken wakar nan ta Imran khan (Satisfya) wadda yake cewa "am rider,provider, bring the heat girl i will bring the fire,"
gyaran murya yayi tare da cewa "My phone," cikin sauri sehrish ta wuce bedroom ɗinsa asaman pillow ta samu wayar ɗauka tayi jiki na rawa kamar ta riƙe bomb haka take ji, ta riƙe wayar manya ba,
Fitowa tayi da sauri taje ta miƙa masa, sai da ya fara cirar tissue ya goge hannunsa sannan ya sake tearing ɗin wani acikin hannunsa sannan ya miƙa hannu ya karbi wayar tare da picking call ɗin ya kara a kunnansa,
Zuru sehrish tayi tana jira taji mai zai tattauna acikin wayar, sai dai kash cikin harshen spanish yake magana kalma ɗaya ce sehrish ta tsinta, da taji yace "Mom,"
Jinjina kai tayi aranta tace "Ina ji da mamansa yake waya, ashe mahaifiyarsu na nan, ko tana ina ne ita?
ta, tambayi kanta ba amsa,
babban burinta yanzu shine su haɗa ido dashi atlease yasan da zamanta sam bata tunanin hakan zai iya janyo mata matsala acikin gidan,
A tunanin sehrish SGR bai ta6a kallota ba, tabbas hakane amma rana ta farko da tayi masa 6arin fruits a bedroom ɗinsa, ya hangeta ta cikin mirror ya ganta a matsayin namiji tsaye cikin fargaba a time ɗin, duk da bai shaida kamannin fuskarba amma yasan cewa namiji ne mai kula dashi wato ɗan aikinsu,'
Kammala wayar yayi tare da mayar da wayar ya ajiye gefensa, yaci gaba da cin dinner ɗinsa sehrish na saving ɗinshi in ya kammala da wannan ta zuba mishi wancan haka suke abun nasu,
Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana kallon sumar kanshi ba ƙaramin jan hankalinta Sgr yake yi ba, hakan yasa bata gajiya da tsayuwarda take yi na saving ɗinshi tamkar mirror haka ya koma mata, tana cikin masa wannan kallon muryarsa ta ratsa ta da cewa "Kallon ya isa haka, ko saina shaƙe ne,"
Cikin sauri da jin kunya sehrish ta mayar da idonta ƙasa tana mai mamakin yarda akai Sgr yasan cewa tana kallonsaa murmushi tasaki saboda jin daɗin mgnarsa tabbas tana ji aranta cewa yana da sauƙin kai he's not arrogant kamar yaddda ta ɗauka,
...................... ..,,.....................................


A tsiyace ya shigo da motar layin gidan a dai dai gate ɗin gidan ya dakatar da ita, ya shiga buga uban horn kamar zai tada motar gaba ɗaya saboda karar da take yi,
"Kai!! uban waye ke mana horn haka,"? ɗaya daga cikin sojojin dake gadin gidan ne ya tambaya da ɗaga murya, akwai yasamu amsa dai dai dashi sai ji yayi ance "Ubanka ne kazo ka duba,"
Abun ya basu mamaki aiko afusace sojojin nan suka tunkaro motar kamar wasu zakuna har haɗa hannu suke wurin buga glass ɗin motar tare da cewa "Come out !! ,"
"Ae basai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads