Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 138623 words

Chapter 20 - Abban Sojoji Book 1 Complete .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

948

Ads at the middle of Article

kuka fawan yace"idan ta mutu fa ba tare da ta karbi addinin musulunci ba, azabar Allah zata tabbata akanta ne, kuma wuta zata shiga, aduk lokacin dana tuna wannan ina jin ƙunci araina...'
Ayaan ma yace "abba bai kyauta mana ba, kullum cikin zullumin makomar mahaifiyarmu muke,'
Jahan yace "kuma bata son mu, ta kama hanya tayi tafiyarta, ko waiwayan mu bata yi, ita wata irin uwace? cikin rashin tausayi ta tafi ta6ar ƙaninmu shi da bai mallaki hankalinsa ba, da tun farko Abba ya za6a mana uwa tagari munyi rayuwarmu cikin salama, da ynx labarin ba haka zai kasance ba,
"Kada na sake jin wani daga cikinku yayi magana, ku koma ku zauna, koba komai ae kuna da mu, wani irin gatane bamu nuna muku ba, mu fa jini ɗaya ne, babu wani banbanci a tsakanin mu ! ku kun kasance jinin dake yawo ajikinmu, kasancewarku farar fata ba hakan yana nufin kun fita daban acikin mu ba, kuma don mahaifiyarku ta tafi ta barku ba hakan yana nufin kun rasa wani sashe na jin daɗin rayuwarku ba,
Da ran mu da lafiyarmu bazamu ta6a bari hawayen ɗaya daga cikin ku ya zuba ba, Allah ya riga ya haɗa kuma ba wanda ya isa ya raba, nasan cewa abunda Ammy take yi muku bakwa jin daɗinsa, shine abunda yasa ku ke jin kan ku daban, to inaso kusancewa zumunci a tsakaninmu yanzu ya SOMA,


Wannan maganar ta yayansu Ishaq yasa su jin wani sanyi a ransu, har suka samu ƙwarin guiwar koma wa suka samu wuri suka zauna,


Suna cikin wannan zaman motoci suka soma antayowa cikin gidan da gudun gaske da wata irin jiniya, wannan alamu ne dake nuna cewa Salahuddeen hussein ya dawo wato chief of army staffs,
Farin ciki a wurinsu ba'a magana, Abbansu jigon rayuwarsu, backbone ɗinsu ya dawo cikin ƙoshin lafia,
Lokaci guda hayaniya ta kacame agidan manyan mutanen da suka zo tar6arsa ba adadi, sai faman marhaban lale ake yi, gidan ya cika fam da manyan mutane ko'ina ya ɗauka, su azmee da chef ummu da momina sai faman kai komo suke wurin rarraba musu abunsha,
Abban nasu ba ƙaramin daɗi yaji ba lokacin da yaga warriors soldiers ɗinsa cikin ƙoshin lafiya, murna a gunsa ba'a magana, sai dai har yanzu baiga Sanyin idaniyarsa ba, gashi ya matsu daya gansa, duk da ɗumbin mutanen dake kansa hakan bai hanasa ambaton sunan JUNAID ba, ❤


dakyar fa mutune suka lafa har abban yasamu damar shiga haɗaɗɗen bedroom ɗinsa, wanka ya shiga bayan ya fito ya kimtsa cikin jallabiya fara, kallon kansa yayi a cikin dressing mirror murmushi ya sakarwa kansa tare da cewa "ABBAN SOJOJI" a fili ya yi maganar,


Abba mutunne mai matuƙar daraja da cikar kamala, mutunne da kowa yake kwaɗayin haɗa iri dashi ba don komai ba sai don sanin kyawawan ɗabi'unsu, mutun ne dayasan darajar ɗan adam, yana da sauƙin kai sosai, hakan yasa naƙasa dashi ke prouding dashi a matsayinsu na shugabansu ❤


Mutunne mai matukar tausayi, hannunsa a buɗe suke indai wurin taimako ne baya gajiya, irin waɗanɗan mutanen na musamman ne su, domin suna da kishin ƙasarsu, shiyasa suke sadaukarwa kansu ga ƙasarsu, kowa zaiyi burin ya mallaki uba irinsa 💕


Kwanciya yayi a saman katafaren king size bed ɗinsa, domin ya samu relief kafin ya wartsake ya gana da ƴa'ƴansa,


A can ciki kuwa kowa ya hallara a saman dining table domin gudanar da ɗa'amin, su azmee sun kammala jera komai, saving ɗinsu kawai suke kowa na faɗin abunda yake son ci, su kuma suna zuba masa,:


Cikin natsuwa kowa ke zubawa cikinsa, suna cikin cin abincin aunty azeema tace "wai ina baby junaid nifa na ƙosa na gansa, i really missed him so much,' ta idasa maganar tana tura dambun naman da ta dumbuzo a hannunta, sam bata wasa da abinci,
Fawan yace "hmmm indai junaid ne ynx zaku gansa, yunwa ta koro sa, nasan yana cen rungume da pillow kamar jinjiri yana sharar bacci,'
gyaran murya Abbas yayi "idan ana cin abinci ba'a magana,' ya faɗi cikin zolaya,
Amani tace "amma agida fa muna yi," dariya su kayi gaba ɗayansu jin abunda tace,


....,..........SEHRISH.........................
A 6angaren sehrish kuwa, baiwar Allah jiki fa yayi rau, ido a kumbure ta farka daga bacci, duk ta tsorata da mafarkin da tayi akansu Husanna, tayi wani mummunan mafarki akansu, cikin mawuyacin hali, jikinta ya gama mutuwa, hawaye ne kawai ke rolling down on her cheeks, tana jin zuciyarta babu dɗi, tana kewar siblings ɗin nata, tana jin cewa bata kyauta ba, da tayi nesa da su amma ya zata yi? the hard way is the only way 👌


Cikin sauri ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta fito, jikinta na ta faman rawa, kayan nan da tafara zuwa aiki dasu gidan at her first day, su ta ɗauko, wato burgujejan wandon nan Falazu,
Wanda ƙafar mutun 5 sai ta shiga ciki ba tare da ya matse su ba, pink colour sai riga ta maza launin ruwan madara (milk) mai ma6allai dayawa ajikinsu da aljihuna, ta gyara gashin bakinta ya zauna raɗau, sannan ta nannaɗe sumar kanta kamar yadda ta saba,
ta aza hukar nan, yar tashi da kwakwa sannan ta aza kuma mayafinta launin wandon daga saman hular ta naɗe shi,
sai da tatabbatar da komai ya zauna raɗau,
Sannan ta fito gabanta na faɗuwa saboda taji alamun bakin nan fa sun iso, suna cikin gidan batasan ya zasu kalleta ba, ko'ina na jikint rawa yake yi saboda zazza6in da take ji,
tun daga inda take ta hango su a zungureran table din, binsu da kallo tayi, musamman aunty babba da Amani da tagansu ƴan larabawa, ga kuma su ishaq da abbas da abuhaisam da sauran duk batasan su ba, amma kamanninsu ya tabbatar mata da cewa yayyansu Kanal yusif ne,
"To fa wanene wannan kuma, baƙon saurayi ku ka yi ne:? .
Sai da sehrish ta firgita jin maganar aunty azeema, lokaci guda kowa ya ɗago yana kallonta 👀
Cikin sauri azmi dake tsaye akansu suna saving ɗinsu dasu chef ummu tace "he's our new house boy, tukur yana taimaka mun wurin aiki sosai,"
Jinjina kai azeema tayi tare da cewa "that's gud"
ƙarasawa azmi tayi ta ruƙo hannun sehrish tare da janta izuwa kitchen suka tsaya, sannan ta kalle ta tace "meke damunki ƙanwata na shiga na Same ki jikinki zafi baki lafia ne,"
Hawaye ne suka soma zubo ma Sehrish cikin nuna tsananin damuwa tace "aunty azmi dan Allah ki taimake ni, ke kaɗai ce zaki iya taimako na a halin yanzu, ina cikin tashin hankali...'
"tell me whats happening wit u? Azmi ta tambaya,
"Aunty azmee ina ji araina cewa ƴan uwana suna cikin mawuyacin hali, inaso naje nagansu, dan Allah ki taimakamin naje katsina na duba su koda kwana ɗayane ina tsoran na rasa su bani da kowa sai su..... .....'
kuka ne yaci ƙarfinta ta gaza ƙarasa maganar, azmi ta janyota jikinta tare da hugginta ɗinta tightly a jikinta tace....
"I feel your pain sehrish,ina mai takaicin sanar dake cewa bazai yiyu ba hakan!
ɗagowa sehrish tayi daga jikinta tana kallonta ido jawur, cikin muryar kuka tace "meyasa aunty azmi"?
"Banso na sanar dake ba amma ynx dole ne kiji, sehrish kuɗin da na baki na aikin ƴan uwanki, bana salary ɗinki bane kawai, hada kuɗaɗen dana jima ina tarawa domin na yi amfani dasu, na haɗa miki duka sbd na tausayawa halin da ki ke ciki sosai, salary ɗinki bazasu isa ba dole saina cika miki, a yanzu haka da nake miki magana nikaina banda kosisi domin duka na tattara miki su...."
Shiru ta ɗanyi tana wani tunani idonta akan sehrish, ita kuwa jikinta yayi sanyi ba don komai ba sai don jin cewa Azmee hada kuɗinta ta haɗa mata don ta biya kuɗin aikinsu husna, sai taji ta ƙara ƙaunar azmi sosai, tana da matuƙar tausayi, ga kyan hali
"ki daina kuka sehrish, duk kan tsanani yana tare da sauƙi, ki daina sa damuwa aranki, insha Allah ba abunda zai sami ƴan uwanki, Allah yana tare dasu, maganar zuwanki wurinsu zanyi ƙoƙari akan hakan amma ba yanzu ba,'
cike da rashin kuzari sehrish tace "shikenan aunty azmee, nagode sosai bansan da wasu irin kalmomi zan gode miki ba, narasa mahaifiyata amma gashi Allah ya bani ke alokacin da nake cike da jimamin rashin wani nawa akusa dani mai sharemun hawaye na,
Murmushi azmee tayi kafin tace "samu wuri kizauna, me kike so na kawo miki ki ci? tun da safe baki ci komai ba,' tayi mgnr cikin nuna damuwarta,
"Aunty azmee i cant eat anything now, zuciya ta tashi take yi bani da kwanciyar hankali,'
dafa shoulder ɗinta tayi tace "Calm down your mind reeshi na, just ave a seat, bari na haɗa miki abu mai daɗi mana ki ci, zaki ji daɗi,'
Ajiyar zuciya sehrish ta saki, wuri ta samu a saman dinner table ɗin dake a kitchen ɗin ta zauna, tana jiran azmi,
a tray ta shirya mata abun tattaunawa, ta ƙaraso da murmushi ta ajiye mata tana faɗin"Ina mai tabbatar maki cewa indai ki kasa wannan Cheese burger ɗin abakin ki sai kin manta da duk wata damuwa da ki ke ciki, musamman in ki ka haɗa da Cornflakes ɗin Zan haɗa miki ynx da madara haɗi na musamman ,'
Wani irin sanyi ne ya ratsa reeshi haƙi ka azmi ta musamman ce acikin na musamman, cikin sanyi murya ta furta "thank u aunty azmee kina ji dani sosai, only God can rewards you,'
"Don't worry your self reeshi i just wanna see you always in happy mood, bana so naganki cikin yanayi na damuwa,' ta faɗi hakan a yayin da take ƙoƙarin juyawa,
Murmushi sehrish tayi ta zuba wa tray ɗin ido, Cheese burger ce aciki tare da hot dog ga sandwhich, lumshe idanunta tayi aranta tana tunanin me ƴan uwanta suka ci su 😥
ruwa azmi ta ɗebo a Dispenser mai zafi cikin tea cup, ta haɗa wa sehrish cornflakes yaji madara da sugar, tasan cewa sehrish akwai son zaƙi shiyasa ta zuƙa mata shi,
Ƙaraso wa tayi ta jiye mata shi a gefen tray ɗin, sannan tace "ko kina buƙatar wani abu ne?akwai sauran abubuwa da muka haɗa masu daɗin gaske,
yar dariya sehrish tayi ganin yadda azmi ke treating ɗinta sai kace ƴar masu gida,
"oh dariya na baki?dama dariyarki nakeson gani kuma gashi naki har dimple ɗin nan naki ya lotsa,'
azmi tayi maganar tana kallonta, cikin jin daɗi sehrish tace "daga ynx zan rinƙa yin dariya aunty azmee tunda kina so insha Allah,'
hannu azmee tasa tare da jan kumatunta tace "yawwa haka nake so my daughter, bari na shiga ciki, keep enjoying ur meal banda loma,' .
ta faɗi hakan cikin zolaya kafin ta fice daga kitchen ɗin,
tana fita sehrish ta fashe da wani irin matsanancin kuka ba don komai ba sai don, tunawa da ƴan uwanta, kuka take bil haƙƙi da gaske hawaye na sintiri a face ɗinta, Allah sarki baiwar Allah, aduk lokacin da taga abu mai daɗi agabanta zata ci sai ta tuna da ƴan uwanta, wane hali suke ciki? shin sun samu abunda zasu ci kuwa, in ta tuna hakan sai taji ɗaci aranta, maganar oummansu ta tuna a inda take cewa


_sehrish ke ce mai wayau acikin ku, dan Allah duk runtsi duk wuya kada ku rabu ko bayan raina, ku haɗa kanku ina son ku sosai ƴa'ƴana rabin raina_ 😭




Hafsat Bature


*page 51 to 52*




Abban Sojoji


*💋romantic love story btwn Sehrish & Surgeon General Rafayet💋*


_Heart touching story abt a Triplet_😢


mamaki ya ke ganin taƙi ɗauke eyes ɗinta akansa, kuma bata da niyar daina kallonsa, hannunta har rawa yake yi wurin ajiye spoon ɗin da ta ɗauko,


Lumshe idanunsa yayi a hankali yana ƙare mata kallo acikin zuciyarsa yana cewa "Ya Allah ka mallakamin wannan baiwar ta ka,'


A yayin da sehrish ke cewa"
_tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan kyakkyawar surar Junaid duniya ne_💋


_shigowar azmee ne ya dawo dasu daga wannan tunanin na ƙurawa juna ido kowa ya waske_


cikin fara'a azmee tace" junaid me ka ke bukata ne na kawo maka? naga baka ci komai ba,


A cikin zuciyarsa yace"kallon ta danake koshi nake Aunty azmee"


A fili kuma yace" nima cornflakes ɗin zan sha, a haɗo mun da fresh fruits'


"Junaid ba ka son cin abinci ko? Kafi son ƴan lashe lashe kamar Tukur"?


Wani irin murmushi ya saki jin abunda azmee tace har time ɗin idonsa nakan sehrish wadda ta mayar da idonta kan cheese burger ɗin dake gabanta so take ta ɗauka taci amma zuwan junaid yasa duk ta dabarbarce sai ƴan kame-kame take




"Aunty azmee ae we are the same ni da shi,'


Azmee tace "gsky saina haɗa maka da farfesu mai zafi zaka ji daɗinsa,'


Junaid yace "its ok am waiting,


zuciyarta sai faman ɗar ɗar take yi mata, kamar mara gsky koda yake ba gaskiyar ae,


Shi kam ya zuba mata ido yana kallonta, yarinyar ta kwanta masa a heart ɗinsa, just he is affected 💘


Azmee ce ta ƙaraso hannunta ɗauke da plate wanda ta zuba masa farfesun ganda aciki, ajiye wa tayi a gabansa, sannan ta koma ta Kawo masa fresh fruits ɗin daya bukata acikin wani haɗaɗɗen round tray,


sannan ta koma ta kammala haɗa masa corn flakes ta kawo masa,
A hankali ya furta "shukran aunty azmee'


azmee ta juya ta fice tana ɗan murmushi bata ta6a sanin cewa junaid Romeo bane na gaske sai da ya gane cewa reeshi maca ce ba namiji ba, ❣️




Ƙamshin farfesun gaban junaid ne ke ta faman kai mata hari, ɗagowa tayi tana satar kallonsa,


A hankali yake sa hannu yana ɗaukar gandar ta dahu tayi tubus taji kayan haɗi na kamshi, irin wadda daga kasa a baki zata dagargaje😋


A hankali yake turawa abakinsa yana tauna, ganin bai kara ɗagowa ba yasa tayi saurin wawurar burger ɗin tana turawa a baki,


Muryarsa ce ta katse ta "Ki ci a hankali," ya furta yana ɗan smiling ashe ya ɗago bata sani ba


kaɗan ta gutsara ta maida ta ta ajiye, hot dog ɗin ta dauka tana ci,


a yayin da shi kuma ya ɗauki spoon yana shan cornflakes ɗin da azmee ta kawo masa,


Wani tunani ne ya faɗo masa aransa a lokacin da yake kallon sehrish wadda take ta faman ƴan kame kame,




Bin ta da kallo yayi aransa yace " Wani abu na ban mamaki nikam, ko ya aikai take matse boobs ɗinta, suyi flat tamkar babu, dama Allah yasa su 6ace muga yarda zata yi........




Shi kansa baisan dariya ta kubuce masa ba, har ya fetsar da cornflakes ɗin dake bakinsa, zuba mishi ido sehrish tayi gaban ta na faɗuwa tsoranta kada ace wani abu junaid ya ganu wanda zaisa ya gane cewa ita maca ce,😳


Sai faman tiƙar dariya ya ke yi ba kakkautawa, sam ya gaza stopping kansa,


Tamkar tv haka ta ƙura wa junaid ido yana dariya, fararen hakoransa jere rass take kallo ga ƴar wushiryarsa siriri ya,




ganin ya kasa controlling kansa ya sa ya miƙe ya kama hanyar fita yana ci gaba da dariyar,




Abun ya bata mamaki, ganin ya tashi yana ta dariya gashi baici abun kirki ba, anya junaid yana da lafia kuwa? Ko dai yana da psycriatric disorder ne?




daga bisa ni ta ta6e bakinta alamar i dont care taci gaba da shan abunta,


Bedroom ɗin abbansu ya wuce directly, a hankali ya tura kopan ya shiga, samun shi yayi a tsakiyar gadon ya baje abunsa, ya warware,


Murmushi ya saki ganin abban nasa, har cikin ransa yaji daɗi ganinsa ya dawo cikin ƙoshin lafia,...




"Lallai abba abu yayi kyau, shine an dawo ko a neme ni, aiko yanzu baccin nan naka zai ƙare,'


Ja da baya yayi sannan ya watsa a guje ya faɗa saman gadon sai ajikin abban nasu a firgice cikin magagin bacci abban ya rinƙa faɗin "a miko bindiga 6aro ya shigo '


fashe wa da dariya junaid ya yi, yana kallon abban nasu wanda idonsa ke a rufe yana ta faman sambatu,'


tabbas yaji nauyin mutun akansa, amma sam ya gaza buɗe eyes ɗinsa sbd a gajiye ya ke,


Cikin rashin imani junaid yasa hannunsa yana gwale masa idanu, sunyi ɗan ja, biji-biji yake ganin junaid sai faman zabga murmushi yake,


Cikin nishaɗi ya ce "Abba its me your heart beat, i came here to disturb u, 🤣


a hankali abban ya idasa buɗe idanunsa, a firgice ya yunkura ya janye junaid gefe ɗaya, ba ƙaramin tsorata yayi ba, saboda idonsa wani farin aljani nuna masa sai da ga baya gane cewa she junaid ne,




"Yanzu ka kyauta ? dama ina ji an hau saman jikina nasan cewa kaine, duk duniya babu maiyi mun haja sai kai,'


"Cikin shagwa6a junaid yace "ka dawo baka neme ni ba abba,' ya ƙare maganar yana zumbura masa baki,




yatsina fuska abban yayi yana kallonsa aransa yana cewa " ynx fa sai yace zaiyi mun kuka shi ala dole gabu auta, bari na jaraba shi nagani ya canza ko hanyarzu yana nan yadda na barsa,




ɗaure fuska yayi tare da nuna ma junaid hanyar fit yace "kai tashi ka fice mun bana son takura jarababbe,'


cikin yanayin mamaki junaid ya ce" abba Ni kake ce ma jarababbe? Kadawo baka neme ni ba kuma shine kake korata ?




Abba yace "ka ga tashi ga fice mun tunkan nawaje suji mu,' ya faɗi yana kara tamke fuska,
.ganin cewa dagske abban nasu yake yasa ahi tashi jiki a sanyaye ya sauka daga saman bed ɗin ya isa bakin kopa, bai bude kofan ba tsayawa yayi yana jiran abban ya bashi hakuri,




ɗan juyawa yayi da kansa ya saci kallin abban nasu wanda ke zaune tsakiyar gadon, haɗa ido sukayi lokaci guda 👀
narai narai da ido junaid yayi alamar zai yi kuka, shi kam Abban abun ɗaure masa kai ya ke yi, har wani sa in tunani ya ke anya Junaid namiji ne ba mace ba? Ace har yau mutun jin kansa ya ke

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads