Showing 1 words to 3000 words out of 28315 words
Chapter 1 - HALIN MAZA Hausa Novels Complete by Maman khairat .txt
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji
(maman Khairat)📚📚
*Alhamdulillah ina godiya wa Allah subuhanahu wata,alah daya bani ikon kammala littafina mai suna y'ancin mata yanzu nazo muku da sabon labari mai ratsa zuciyan mai karatu"kudai kunsani bana rubuta littafin da bai faru da gaske ba duk labarina yafaru"ina mai sanar muku zan sake littafin k'arshen wannan watan karki sake ayi babu ku, mata kushirya dan nasan ,zakuji abunda wasu mazan sukeyi wasu sunyi dace ,wasu akasin haka kukasance dani maman Khairat a k'arshen watan nan ina mana fatan alkairi.*
*Littafina na kud'ine akan farashi mai Sauk'i d'ari biyu zaki biya kud'in ki ta wannan asusun Amina maaji 4271914014 FCMB ko katin Mtn ta wannan number 08068748984 .*
True life story
Paid book 200
Free page 1/10
🅿️1️⃣⏩2️⃣
D'AND'ANO
FIKA LOCAL GOVERNMENT
"Wallahi Zainab nagaji da wannan halin naki,tunda kikasamu wannan matsalan makantan shikenan kika bijuro,da rashin mutunci " nifa nagaji aure zan sake in kuwa bansake auren ba toh sai dai kitafi gidan Ku dan nagaji bazan iya ba ." yanzu Nafi,u tunda nasamu wannan matsalan shikenan duk ka ,cenzamun mena rageka da shine kace in daina yin,abinci na amince kace kaine in kadawo daga bige bigen ka zakayi "Yau kuma waye yazuga Kane ?" har sai anzigani kafun kinnuna ban ,isa da gida naba kenan ko,toh bari kiji zanyi miki rashin mutunci sannan a makantan naki,zaki dingayin girki duk ranan dana tarar da wata wai tazo tayaki aiki toh abakin auren ki,ai aure kikazoyi kid'auka ibada kikeyi.
Ficemun yayi daga gidan "maza kenan ina tina lokacin da Nafi,u yake rawan k'afa a kaina yau nice dan matsala tasame ni shikenan, nazama ,abun banza a gareshi,bayan tasana diyan shi nasamu matsalan maza basuda mutunci ,babu amana basu yadda da k'addara ba,in banda k'addara mezanyi da Nafi,u nasan nafishi kyau nesa ba kusa ba,toh mezai gayamun ,shifa yasiyo Salford yafesamun a idona ,a lokacin sauro yayi yawa yana fesawa nikuma zan fitoh naji abu mai zafi,a ido na kafun inyi wani yunk'uri tsabagen gigicewa a she a ruwan datti dayayi wanki naje nawanke ,ido na ga rad'adi ga zafi na gigice babu kalan, magiyan da banyi mishi ba yakaini a Asibiti amma yace babu mai a mashin d'inshi haka muka kwana ido sai hawaye har ,gari yawaye ,a lokacin nafara kallon dishi dishi sai kusan k'arfe goma mukaje Asibiti ,gun masu yankan kati mukaje dake cikin Asibitin Fika munyi sa,a sunyi kusan k'arewa sai kusan k'arfe sha biyu muka kalli likita ,bayan munzauna likitan yace meyafaru ?nayi mishi magana ,d'auko wani abu yayi ya haska idon ina ganin shi amma ba Sosai ba ,sai jinshi nayi yayi magana"gaskiya in kunyi sa,a zata yi kallo da idon ta amma sai kun kashe kud'i d'ayawa wannan maganin yanada k'arfi Sosai bugu da k'ari taje tawanke idon da ruwan datti ga omo a ciki "zan turaku Gombe zakuje kuduba likitan ido babban mune Doctor Najib ,zai taimaka muku yanzu haka idon yafara duhu Ku hanzarta kuje karfa kuce zakuyi kwana biyu bakuje ba ,dan babu a bunda bazai faru ba" likita babu yadda za,ayi gaskiya bamu samu kud'i ba sannan kasan yadda garin yake in akwai magani abamu muje mujarraba.
"ba lalle ne ya muku aiki ba nabaku shawara kuyi amfani da shi kawai zaifi muku,ga wannan zan rubuta muku kuyi amfani da shi ,kafun gobe zai wanke idon in kuwa kunda ce za,a siya mata gilas " mungode ,tunda muka fitoh ba kallo nake yi Sosai ba haka yata sauri yabarni har na,isa kusa ,da mashin d'in natsaya,jinayi yadaka mun tsawa "ki hau mutafi badai gulmanki neyasa ba kikazo kika tsaya a bakin k'ofa ,takaici yayimun yawa ga zogin da idona yakeyi mun ga rashin mutuncin Nafi,u ,hàka nahau muka wuce unguwar mu dake bogaru a cikin garin Fika,mun isa gida kenan nashiga shikuma yafice bai dawo ba sai dare in natina tun safe banci komai ba ga itace nake amfani da shi,haka yadawo yarufe ni da fad'a ,wai banyi girki ba tsabagen rashin imani,banga yataho da maganin da likita ya rubuta munba haka nabud'i baki nayi mishi magana ya rufeni da fad'a tun ina magana har nadaina ,ido na yafara rufewa nadena gani gaba d'aya ,a lokacin da nayi mishi magana yace mun k'arya ne nasan tunda likita yacemun muje babban Asibiti toh nasan akwai matsala Sosai inaji nadaina gani ,da tsakar dare natashi zanyi fitsari naga nadaina gani natashi Nafi,u yamun jagora amma yak'iyimun haka na laluma na d'ebi ruwa naje gaba da d'akin mu na tsuguna rayuwa, kenan duniya abun tsoro,a kwanakiñ Nafi,u ne mai aikin komai dan wanka shiyake yimun aikin yau da kullum da ba aikin namiji ba ,yaki sanarwa iyayen shi har saida nayi sati biyu kafun naga y'an gidan su sunzo, a bakin k'ofa ya tare su suka juya,daman ba sona sukeyi ba sunso ya auri yar uwarshi ba ngizim ba dan ni bangizimi yace da bolawa da ngizimawa basa shiri, sukeyi ba ,a nan ne nasamu tsangoma daga garesu duk kansu dan ni a potiskum nake nashigo cikin bolawa amma basu nunamun soba kirarin su babole mai da d'anwani naka,amma nikam akasin haka,Nafi,u yasoni nasoshi,yanzu nasamu matsala ya juyamun baya banfad'a a gida ba kashe din da Nafi,u yayimun ga k'aramin ciki danake da shi Wanda bazai wuce wata hudu ba ,nata tina irin gatan danake da shi a gidan mu banida wani sukuni yayar kawar mamana da aka had'ani da ita yaranta suna zuwa mun duk ranan kasuwa amma sati uku basu zoba shiru.
Ina cikin tinanin nan har a zahar yayi haka na laluma na wanke tukunya na d'aura abinci,nàgama,tinowa nayi da Nafi,u yabar wankin k'ananan kayanshi take natashi,na yadda ,makafi Allah yayi musu wani baiwa mai tarin yawa a makantan nawa duk wani aiki ninake yi Allah yayi Nafi,u da son abun duniya ga kwad'ayi shiyasa gidan shi baka rabashi da abun dad'i ko yau she gashi d'an siyasa ne'kusan mangari ba yadawo "Zainab yunwa nakeji " gacen abincin ka tashi yayi ya d'auko yazauna yanaci sai da yacinye kafun ya d'ago "waya miki girkin nan?" nice "aa keda bagani kikeyi ba " Allah yanayi mun jagora"kinga yau nasamu kud'i har nera dubu sittin, "da yanzu kikaji wannan ciwon da sai muyi amfani da shi wajen yimiki magani" yanzuma bai bacci ba,bakiji yadda,likitan yace ba"haba Nafi,u wannan wani irin rashin adaci ne meke damun ka baka juyamun baya ba sai dana rasa ido na"menene dalilin ka narufe ni a gida kenan ?"banaso mutane sugane kin makance zasuyi mun dariya.
"Tunda bazaka taimake niba kabarni inje garin mu zasu nemamun nagani tunda nagama maka amfani " haba Zainab mai kyau nine yau kike kirana Nafi,u ina bebyn da kikecemun ?"nadai nafad'a daga yau "koma gana bai yiba yawuce d'aki " kinyi wanka ?aa yanzu zanyi"ki shirya nayi miki"banaso girkima da wanki nayi sai wanka ne zai gagare ni banaso,a wajen wankan yata damuna bude hamatanki ware k'afanki ,a wanke ko,ina tunda ba kallo kikeyi ba karyayi wari ga, yata habaici shine nace zanyi da kaina.
Watana biyu kullum babu abunda yacenza zani wataran ya ajiye key nasace d'aya a ciki na b'oye a ranan yayar kawar mamana tazo tata bugawa ina wanka ina fitoh wa nañufi k'ofar naji muryan ta"Anty ina zuwa bari na jefo miki key d'in kibude ki shigo "lafiya kuwa?" Jefa mata key nayi tabud'e tashigo"Zainab lafiya kuwa "Anty bari muzauna bayan mungaisa ne nabata ruwa" meya sameku?"makancewa nayi garin yaya,labari nabata"shege Nafi,u wato yasan yayi tsiya shine yaje yacemun kintafi potiskum a she abunda yayi kenan "gaskiya wasu mazan bazasuga manzo. Allah ba wannan cutar tayi yawa asana din shi ki makance ga ciki maza sundad'e suna cutar mu amma akwai Allah sai yayi mana sakayya,gidan sirikan ,ki haka yace kinyi tafiya dan munhad'u da kanwar mijin naki take gayamun bakenan ranan su khadija sunzo sunce k'ofar a rufe take ,sai jin tsayuwar mashin d'inshi mukaji duk nariki ce " waye yabud'e k'ofar nan ?"ganin Anty shema,u yasa yayi shiru"kacemun batanan kame kame yafarayi....
Maman Khairat ce
[11/8, 20:47] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji maman Khairat📚📚
*Wannan labari yafaru da gaske sai ma rage wasu abubuwa danayi dan karatun yazo cikin Sauk'i maza mutanan mu in babu Ku gari babu dad'i kundade kuna cutar da wasu matan sanadiyar Ku komai yake tarwatse wa kukasan ce dani,a cikin wannan watan dan kawo,muku littafin Halin maza ni maman Khairat nake yi muku fatan alkairi*
Littafin nan nakud'i ne zakibiya d'ari biyu ta wannan account number Amina maaji 4271914014 FCMB ko katin Mtn ta wannan number 08068748984
True life story
Paid book 200
Free page 1/10
🅿️3️⃣⏩4️⃣
Da yare Anty shema,u takeyi mishi fad'a ,akan ya taimaka ya sanar da iyaye na gudun gar wataran ruwan zafi ya zube mun ,a ka'afa sai jinayi "nifa kifita ta har kata da matana irin kune kuke zuga matan, mutane ,ina ruwanki dangin dangarere,ko kinbada gudumawa a cikin aure na toh kisani banason katsalan da sannan bance kigayawa kowa ba kasancewar garin mu k'aramin gari ne,wani sai yayimun mummunan zato" Nafi,u kaji kunya bahali bane na mutanen kirki kinji ko in banda kema waya cemiki ki shigomun gida?"Nafi,u nafi k'arfin kacimun mutunci har raina ya b'aci wallahi Allah sai yasaka mata sannan katina kai d'an siyasa ne in ba,ace asiri kayi da matar kaba tunda jama,a sunsan shahara da kayi,a siyasa .
"Ina ruwanki " Zainab kiyi hak'uri zanje ingayawa iyayen ki ,suzo sutafi da ke karki mutu ,wataran inajin muryan Anty shema,u tafice ranta a b'ace "ke Zainab nadawo gareki uban wa yabud'e mata k'ofa ?" Allah ne yatoh ni asirin ka yau kamanta baka danna kwad'on ba mutane dayawa sun shigo sunga halin danake ciki dan haka nabasu labari ,in yaso sai kasake ni "shiru yayi yana tina magan ganun Anty Shema,u ko zama bai yiba yafita k'ofar a bud'e yabar shi ,inata zama duk tinani ya dameni ba natabbata in aka gwada jinina zaihau duk da banida hawan jini.
Anty Shema,u bata wuce gidan taba gidan su Nafi,u tayi dake Korori,tayi sa,a mahaifin shi yana gindin masallaci ,aiken yaro tayi yakirashi " sannu da yare takeyi mishi ya amsa dan bolawa akwai son yaren su "lafiya kuwa ?" abunda Zainab tagaya mata shita tagaya mishi yayi mamaki"amma yaron nan shifa yace tayi tafiya ko" bari muje kiran wani Aminin shi yayi suka wuce sunyi sallama na amsa ,jin muryan su "sannun Ku da zuwa lalume naketayi in da taburma yake " sannu Baba yauwa "abun da yafaru da ke kenan?" eh Baba nida kaina nasake gaya musu har abunda bangayawa Anty Shema,u ba wato wanki"yanzu abunda yaron nan zaimun kenan nasan uwar shi ce kezuga shi in ba hakaba meye na d'aukan zafin har haka ka auro yarinya a baka amanar ta kak'i kulawa da Amanar rayuwa ta b'aci gaskiya mudin yara zasu dinga halayya irin wannan bai kamata a basu aure ba. gaskiya" fad'a yatayi abokin shi sai hak'uri yake bashi tayare ."in yadawo kice ina neman shi kodan ma tunda mangari ba yakusa zanjira shi,minti goma sai gashinan kallon Baban shi yayi"Nafi,u kacika azzalumi mungu kaduba yarinyan nan rawan kafar d'akayi a kanta kabiye wa Gaji ko ?"zata kaika tabaro ka"umarni nake baka ka kai ta Asibiti in kai bazaka biya kud'in ba nizan biya mungu kawai ,a haka tayi maka wanki har da girki kwana bakwai nabaka dan bazai ,iyu ba ka d'auko yarinya da idon ta gata har da juna biyu "abu na biyu kagayawa iyayen ,sannan bazaka turata gida ba sannan bazakayi aure ba shine tashi yayi zai tafi " Baba "banason maganan banza .
Harkai ka,isa kasani nibanida mungu hali sai dai na uwarka kagado dan jini yafi ruwa gangaruwa" wato wannan Antyn naki zanyi maganin ta nizatayi wa munafurci masifa yatayi har yawanka mun mari biyu nasha kuka nayi dana sanin auren Nafi,u da dare maman shi tazo duk k'ina da sukeyi ta tausayamun Sosai sunbar mun k'anwar shi d'aya dan takula dani yana dawowa ya koreta .
Washe gari
Misalin k'arfe goma sai ga Antyna da mamana da Babana dan ni maisunan maman Babana ne Babana gandiroba ne a fursuna yake aiki wajen horar da masu laifi ,inajin muryansu,sunyi sallama nafashe da kuka.
FAWARI
Wata unguwa ce a cikin garin damaturu unguwa ce da tahad'a manyan masu kud'i da talakoki da y'an kasuwa babu nisa tsakanin su da gidan sarki akusa da wata makaranta International Sadiq da Zuwaira masoya ne, na ,asali Wanda kowa yasan da soyayyar su in kaga Sadiq to dole zaka kalli Zuwaira ko yarone yaga Sadiq sai yace bari yakira Zuwaira Umma tasan da soyayya mai k'arfi sukeyiwa junan su"Zuwaira kibi samarin yanzu a sannu wallahi zasu kaiki subaro ki kewato bakejin maganan kowa sai na Sadiq ko mahaifin ki baki ishe shi kallo ba in da Sadiq a gefen kiko toh zakiyi nadama nidai fatan danake yimiki ,Allah yasa kuzama ma aurata Amin ya rabbi nagode Umma .
Da dare Sadiq yazo tagaya mishi duk abunda Umma tagaya mata da nasihan da Umma tayi mata"na fuskanci iyayen ki sunayi mun kallon mayau dari amma kuma zanbasu mamaki,sun hanamu hira a mota nazo, k'ofar gidan kun ma bai I shesu ba amma kuma "kayi hak'uri karka bari su Ummi da Ba,a su b'ata maka rai gaskiya " shikenan beby yawuce ai kena keso ,sai da yabata kiss a kumatu ya shiga mota yawuce
Abunda basu saniba babu Wanda yasan inane gidan su Sadiq har ita kanta Zuwairan yace a old BraBra suke haka kullum yake gaya mata ranan yace ta shirya suje yanuna mata gidan amma wataran in ta shirya zai kawota yanzu da rana ya nuna mata wani gida a matsayin nan ne gidain su,maza mutanan mu ashe kam banan neba Asalin Sadiq d'an gashua ne wani unguwa, unguwar manyan attajire ne a unguwan suke mahaifin shi babban mai kud'i ne kowa yasan Sadiq bayajin magana dan wataran sai yi kwana biyar a hotel Sadiq gumtsa shine asalin sunan da kowa ya sanshi da shi ...
Waye Sadiq shin auren nan zai iyu kuwa?
Ba halin mazan zai yimata ba kuwa duk kubiyo ni amsar tana cikin littafin Halin maza
Maman Khairat ce
[11/8, 20:47] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji (maman Khairat)
Zaku, iya tuntub'ana ta wannan number 08068748984
True life story
Paid book 200
Free page
🅿️5️⃣⏭️6️⃣
Naji dad'in ganin iyaye na Sosai mahaifiya tane ta rungumeni naji d'umin jikin ta sabon hawaye ne yasake Zubo mun"mamana kiyi hak'uri meyafaru dake,nasan in ba k'addara ba babu yadda za,ayi mahaifina yazo gida na,inason in kawo musu abinci amma banason in tasarwa iyaye na hankali"Baba Nafi,u mungune mara tausayi ga rashin imani"duk naji meyake damun ki?"ido shine cikon rayuwa har gara kurma jine bayayi,in yaga abunda zaicutar da mutum zaiyi nuni da abun "basu labarin komai nayi, iyayena ne banida kamar su," amma wannan yaron Shari,a zamuyi da shi ,in bashi yarinya da idon ta ya makantar mun da ita "mubi komai a hankali " ke mama kiduba Zainab ko kallo batayi "zanje gun mahaifin shi,yabani takaddan yarinya ta" mahaifiya ta tausayi ne da ita mahaifina shikuma yanada zafi bai san gidan su Nafi,u ba amma zaiyi tambaya,munsha hira da su Mama Antyna ne tayimun girki mukaci ,inayi ina jansu da hira Nafi,u ne yayi sallama Anty Hafcy ta amsa,nikuwa nace mishi sannu da dawowa ya amsa cikin fara,a na fuskanci tunda laluran nan ta sameni tsanata Nafi,u yayi"Wato kacika D'an adam butulu na maman Khairat "munzo ne kabamu takaddan ta,kiyi mun rai Anty zannema mata lafiya zanje in da akace inje,a lokacin ko,kud'i banida shi sunyi babu dad'i kamar yadoke ta cen mukaga Baba ya shigo yana ganin sa ya wanka masa mari" har kai ka,isa dakuwa na d'aure ka ,inadai jinsu lalumo mama nayi ,a kan tabada hak'uri a Baba bayan la,asar dukan su ,suka tafi gida kusan mangari ba yarufeni da duka ko tausayi na baiji ba sai ceman yayi gobe in shirya muje Asibitin garin ,nan cemishi nayi to Allah yakai mu ,munje gun likitan yana ganina," nasan daman bazaka kaita ba ,wannan abun ne zai faru"mekuma zanyi maka?...
Maman Khairat ce
Maman Khairat
[11/8, 20:47] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
Story and writing by Amina maaji maman Khairat
Littafin na kud'ine kai tsaye ki tuntub'i wannan number 08068748984
Paid book 200
Free page
🅿️7️⃣⏩8️⃣
."Likita a taimaka " bawani taimako in Allah ya so ku zata,iya warke wa ,in Allah yasoku "daman daga ganin ka nasan zakayi taurin kai " saboda mekace haka "gashi kuwa magana akeyi a kan lafiyan ido amma kai baka duba yanayin matar kaba.
Shiyasa kuke jawo mana zagi agun mata " babu ruwan ka likita iyali nane fa,taya zakadin ga shi gemun "Allah yabaka hak'uri " tashi Nafi,u tayi yabar office d'in ranshi,likitan ne yarako ni har gun mashin d'in Nafi,u yayi mana fatan alkairi ,tunda mukaje gida babu abunda Nafi,u yacemun sai kusan mangari ba ",Zainab yanzu kam nakaiki Asibiti sai iyayen ki sudaina zagina da habaicin da sukeyi mun ,in tambaye ki'wai da mutanan gidan Ku sukazo mekika ce musu"" Kaine silan makancewa na"wato kedai kina yawan d'aura mun laifi"kabani mamaki Nafi,u a she daman haka Halin mazan yake kuna cutar da mata dayawa "katina lokacin da karikice a kaina kullum kana hanyar garin mu yau kuma nazama abun k'i agareka ina cewa da kakeyi" duk rintsi muna tare ko da ciwo .
Nagode wa Allah da bawani matsalan ne ko wani ciwon yakamani ba "da abunda zakayi mun sai yafi wannan " duk irin wanke Nafi,u danayi bai sashi yaji wani kala ko, tausa duk maganan da nakeyi mishi wanki nakeyi k'ananan kayan shi ido nane yafara k'aik'ayi"dan Allah kazo ka k'arisa wannan wankin ido na yadame ni"kibari in ya lafa sai ki cigaba ni, yanzu fitama zanyi "shikenan a dawo lafiya .
Tun lokacin da Nafi,u yafita tinani natayi Sosai ,meyasa banbi iyaye na muntafi ba, meyasa ban koma gidan Su da zama ba ,kashi dana sani da nabisu,babu kalan tinanin da banyi ba a lokacin da Nafi,u yake rubibina ,a ranan da abun zaifaru shi yayi mana wanke wanke da girki,inaji da laulayi Allah sarki duniya ,
Haka natashi nahad'a wuta zanyi mana girki,abun takaicin ba wani gida nake kaiwa ba amma kullum sai nayi girki sau biyu