Showing 24001 words to 27000 words out of 28315 words
Chapter 9 - HALIN MAZA Hausa Novels Complete by Maman khairat .txt
maka iyawar shi ta dalilin ka nayi karatu in da ba kaddaran nan yashigo cikin lamarina ba yazan zama haka .
Jin muryan Doctor mukayi" Nafi,u nasan baka gani sosai wannan shine likitan daya fara dubani shina aura sannan kaddaran ciwona yajawo mishi rabuwa da iyalen shi karka damu haka Allah ya tsara lamarin shi dan haka ina maka fatan samun nasara sannan shawarata karkace zaka dauki mataki a kan lami badawo maka da idon ka zatayi ba inayi maka fatan alkairi tare da gamawa da duniya lafiya Allah yayi jagora yarufa asiri zamuci gaba da kulawa dakai in sha Allahu .
"Malam nafi,u karka damu zamu baka kulawa ta musamman in sha Allahu yanzu zaku wuce gida fika a dinga amfani da magungunan Allah yajikan iyaye .
" Doctor bana fishi a kan komai jarabawa ce tazo da haka amma in sha Allah nasamu ilimi dayawa a kan makanta na in kana da lafiya za,a dama dakai in kuwa babu lafiya babu mai kulawa da kai sai masoyin ka nagode .
Sai naji tausayin Nafi,u yakamani na tausaya mishi in natino da makantan da nayi abun sai yadameni sosai Allah yabashi lafiya rayuwa kenan ina gadaran da Nafi,u keyi duk yatashi a banza kenan .
Zara,u
Wasa gaske sai gashi na haihu nasamu namiji anyi suna dan gina sunzo babu abunda ba,ayi ba da Sadiq yaga mai lafiya na Haifa sonshi daban ne shida sabeer"Sadiq yanzu kam yakamata muyi hakuri murungumi kaddara kaduba yadda Allah ya cenza lamarin shi dan Allah"nagode Zara,u kiyafe mun abunda nayi miki a kwai abunda nayi yake damuna"yara uku yan mata Wanda nashafa musu wannan cutar bayan bayyanu war ciwona basuji ba basu ganiba"shawarata a nan shine ka aure su dukan su muzauna dan in kabari wani ya aure su zasusha zagi da tsan gwama ne "kina ganin babu matsala ?" babu komai yanzu na amince muyi hakan Allah yayi mana jagora ya rufa a siri haka nayi hakuri a kakai komai na yan matan da sadiq ya yaudara abun da zai baku mamaki duk yaran masu kud'i ne nayi takaici amma dana tina yanzu dani sadiq yakeji komai tare mukeyi gafaran uban giji yata nema Allah ya yafe mishi "har yanzu yagagara manta zuwaira dan duk lokacin da takawo mun ziyara sai yata kallon ta ga mijin ta kishine dashi na masifa .
Damuwar mu hadata mukeyi muyi maganan komai lalle duk macen da bata had'u da sharrin maza ba tagode wa Allah shine zai zame mata gata dan yafitar da ita daga fada wa uku ba " Allah nagode maka a haka na haihu uku Amina Binta Sadiq nasha wahala banaso Allah ya jarrabi wata kamar yadda nayi dana sanin biyewa maza gashi har mahaifina yakoma ga Allah ban nemi yafiyar shi ba ina rokon Allah ya yafemun yayi mun jagora .
Zuwaira yaranta hudu tazama babbar mace mijin ta yanaji da ita sosai munzama kamar yan uwa mijin ta suna mutunci da sadiq sosai sadiq yazama babban magidan ci in kagan mu bazakace muna dauke da wani ciwo ba Allah kenan Allah kayi mana zabi mafi alkairi .
Tammat Tammat
A nan nakawo karshen littafina mai sunan Halin maza kuskuren da kecikin littafin nan Allah ya yafe mana darasin cikin littafin Allah ya hadamu a kan ladan masha Allah .
[11/8, 20:48] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️6️⃣5️⃣⏭️6️⃣6️⃣
Kwana nana uku banga Sadiq ba haka nayi kwana bakwai babu ko dirin Sadiq in ba mijin gantali ba dabai San mutuncin iyayena ba tayama za,ace akan sarkin ka ya rasu ka gagara zuwa kuyi gaisuwa wannan wani kalan rayuwa ne mai cike da rud'ana kullum burina aurena yarabu haka yaro na yakama rashin lafiya babu gaira yazo yarasu gidana nakoma acen akayi mishi sutura yashiga raina sosai Sadiq ko zama bai yiba irin Wanda ake zama dinnan ko ya hakuri babu tsakanin mu"Zara,u naga sai fishi kikeyi miye matsalan kenan "babu Sadiq naga duk bamuma a junan mu jajeba " Sadiq mahaifina ya rasu amma kokacemun ya hakuri taya dan yaron ka yarasu zanwani cemaka ya hak'uri kokince in sakeki babu saki tunda amanan auren ki mommy tabani .
Tsabagen bak'in ciki rushewa nayi da kukan bakin ciki tayama za,ace inci gaba da zama da Sadiq ko tahalin yaya zanrabu dashi tundaga ranan nadaina yadda wani mu,amala ya k'ara shiga tsakanin mu da Sadiq.
Bayan shekara biyu
Abubuwa dayawa sunfaru har da danfaran da wasu sukayiwa Sadiq ya tsiyace sosai gida jen gadon shine yarage a hannun shi sai aikin dayake dashi ranan zuwaira takawo mun ziyara tayi mungun tausaya mun "Zuwaira kigode Allah Abdallah bashida irin tarin matsalolin rayuwa irin na Sadiq" Zara,u maza fa sunan su maza Abdallah shima yanada nashi matsalan takura da masifa abu kadan yata surutu Sabeer babu dama yazo gidan mu sai kiga yadaure fuska narasa dalilin yin hakan shidai sai Aliyu babu ruwanshi da bayaron da ya Haifa ba.
Nagaya miki maza sunada matsaloli dayawa amma bake ganewa saboda halin Sadiq gaskiya bantaba jin mai mungun hali ba nifa garama da ya talauce yanzu abun da sauki sosai akan da.munwuni munata hira soai munzama kawaye sosai a rayuwan duniya akwai kalu bali masu tarin yawa sosai a rayuwa.
"Kiga yanzufa ciki gareni gashi mai tsananin laulayi banason cikin ma rabo nekawai " karki damu Zara,u nasan kina gudun haihuwa irin su nusaiba "kaman kinsani kuwa Allah dai yarufa asiri kawai zamuce Amin .
Zainab
Bayan nahaihu yarona yayi wayo nakoma kano k'aro karatu na shekara biyu lokacin Doctor yatafi karatu kasan waje amma kullum muna asibiti abun yadan ganci asibiti akullum mutane biyar biyar zamu duba wasu suzo in tausaya musu dan idon ya lalace sai dai in rubuta musu magungunan da zai rage radadin ciwon mutum na k'arshe da zan duba nabada umarnin a shigo da shi suna shigowa nace sannu malam zauna " katashi Nafi,u bazan duba kaba lalume yafara "muryan wanakeji kaman Zainab " nice nan sannan nine zan duba ka bazan taba duba kaba kasani nayi kaurin da koda kakai k'arana zan,iya bude asibiti nawa wanda koda ankore ni zan dogara da kai na"zainab meyasa abu baya wucewa a gareki kiyi hakuri kiyafe mun ninefa mijin ki Wanda mukayi auren soyayya "dakata jahili ni karka kuskura ni matan wanine kafice mun koda zaka mutu bazan duba kaba " nasan kinfi karfi na amma kisani rayuwata fansa ce a gareki kiyi mun rai dan Allah ko yanzu nasan kinfi k'arfi na nesa ba kusa ba afuwan ki nake nema kiyafe mun .
Yabani tausayi in ka kalleshi zai baka tausayi take shedan yata bijuro mun da abubuwan da yayimun amma haka nadaure na duba shi"kayi hakuri ido daya ya mutu daya ne zai yi kallo amma ba sosai ba kayi hakuri daya ya mutu daya zai tashi sai kadage da shan magani "bakomai nagode haka yafi ta nawuce gida nagagara bacci dan tinanin Nafi,u yaban tausayi nasan makanta akwai wahala ,lokacin da yafita yagayawa maman shi nice likitan tayi mamaki" muncutar da ita gashi Allah ya daga darajan ta "haka Allah ke ikon shi Allah yabaka lafiya muwuce mukarbo maganin
Watan su shida suna zuwa karban magungunan kafun yafara samun sauk'i kadan kadan gilas aka bashi ina tausaya mishi yau fa duniya tazama abun tsoro.[11/8, 20:48] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️6️⃣1️⃣
Wallahi Nafi,u muddin kace dan uwanka bazaiyi bacci ba kai ko rintsawa bazakayi ba badai mugunta kasaka a gaba ba kayiwa Amira dayake auren sadaka ,aka baka amma ni da sadaki ka auro ni kaji dakyaui "lami kenan nasan duk wani hanya da zanbi dake tunda kince haka muzuba mugani .
Ficewa yayi daga gidan ko sauraron su lami bai yiba sai sayayi kwana hudu yadawo ,ga kayan abinci amma babu abunda za,ayi cefene saboda rashin mutunci irin na Nafi,u yadauki aure ba,abu bane mai daraja
Bayan dawowar shi daga yawon siyasar shi Yakama Amira yayi mata duka take zazzabi ya rufe ta" muddin nika zalunta Allah zai yimun maganin ka a gidan muzan kwana mai dawo dani gidan nan sai Allah yana fita tafice tayi gidan su ran maman Amira ya baci tatafi gidan su Nafi,u tayi sa,a kuwa mahaifin shi yanan"lafiya kuwa? "ba wajen kinazo ba nazo ne gun mijin ki yau zan touna miki asiri Wanda duk duniya sai ta sani malam sa,idu " Nafi,u ba danka bane da cikin shi aka shigo gidan ka,dan lokacin tana dauke da juna biyu na sati hudu bugu da kari da asiri ta aure ka babu kalan biye biyen da batayi ba sai data mallake ka,in kaduba zakaga basuyi kamaa da kannen shi ba ,su farare shikuma baki babu ta,in da kuka had'a jini .
Maman Nafi,u kamar tanitse shekara talatin tana boye sirrin ta sai gashi a dalilin Nafi,u an touna mata a siri wannan tijaran dame yayi kama "babu kuma abunda zai faru sannan niki gayamun abunda nayi naga mutuncin dayake tsakanin mu ,nace bari muyi auren nan a she shegen yaron ki bashida mutunci . mahaifin Nafi,u ne ya zauce " yanzu da gaske ne abunda nakeji"kayi hakuri "zanbarki kizauna a gidan nan amma aure tsakanin mu yakare shidin ma zakiyi zaman yaranki..
[11/8, 20:48] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️6️⃣2️⃣⏭️6️⃣3️⃣
Zara,u nifa natsani wannan yaron na kema kiduba kodai kece baki iya haihuwar yara masu lafiya ba meyasa "bani ke bada haihuwa ba Allah shikeyin komai babu wani abun da zan,iya yi ajikin dan Adam ko shima zaka kasheshi ne kamar yadda kakashe Nusaiba kacika mungu karshen ka bazai tabayin kyau ba shegen mugunta gareka ,kudin gadon su yafito gidaje uku ne sukafita a rabon shi da kudade dayawa ya cenza mana gida yasiyi mota duk da kafar jenta yakeyi yana kuma karban magani sosai rashin mutuncin sadiq gabama yakeyi yadan rage wasu abubuwan amma har yau tsanata sadiq yakeyi sosai narasa inada zuciya amma tunda muka kasance gudaya da sadiq sai yazama ko musu bana iyayi mishi.
Wannan wace irin rayuwa ce duk iyaye nane suka
" kawo mun wannan abun taya zasu watsar dani" kiduba irin soyayyar da ke tsakani uwa amma nikam iyayena basu yadda da kaddara ba har yau basamun kallon mutunci tunda ko nemana basayi. Yau nasa a raina zanje gida koda jefeni za,ayi dan natashi da begen mahaifina danazamo yar gata a gareshi shuryawa nayi nanufi kofar gida natari abun hawa nawuce ,nanufi unguwarmu Nayi nawa ina doson kofar gidan mu naga mutane dayawa banyi wani yunkuri ba sai jin wasu nayi suna cewa ga Zara,u da mahaifin ta ya mutu da sunan ta Allah sarki Allah yamishi rahama haka na k'arisa cikin gida a she ko kaishi ba,ayi ba duk kallo yadawo kai na ,fadawa dakin da aka kwantar da shi nayi nafashe da kuka ,kayafemun Abba na bangujeka ba ina sonka kaddara ce tarabamu Allah yamaka rahama kayafemun yanzu ni matar aure ce kayafemun bantaba dai na tinanin kaba kayi mun afuwa rikeni akayi aka shiga dakin umma na dani itama kuka mutuwar tazama guda biyu dan ajiyan zuciya ba,abata tayi shikenan rai yayi halin shi.
Zainab
Doctor nagaya maka moh'd zai zo amma banji kace komai ba mekenan kake nufi"zainab yakamata kigane nifa duk abunda nakeyi inada hankali kisani babu mugunta a cikin shirin da nakeyi "natabbata maza duk halinku d'aya shiyasa bakuda tabbas a cikin lamarin Ku ,kuna bani mamaki tabbas " koma meye kifad'a amma kisani daraja nake nema miki sannan kikula da cikin jikin ki"ciki kuma?e kinada juna biyu .
Ficewa yayi yabarni amma taya Doctors yazama haka yanzu na tabbatar maryam hakuri takeyi da Doctor dan yanzu nadai na yadda maza masu imani ne dan haka zanzage in duba duk wani matsala zan magance matsalan amma yanzu abubuwan sun cekube Allah dai yarufa yarufa asiri shiryawa nayi nafice gun aiki nabar gidan lokacin da naje office masu jirana suna dayawa haka nata duba marasa lafiya wasu daman nagansu dawowa sukayi.
Bayan nagama aiki nazagaya dan duba marasa lafiyan dasuke kwance alhamdulillah ina tsaye a kazo aka kawuce da wani Mara lafiya natausaya mishi dan idon yanata ihu haka na tattara nawuce gida dan lokaci yayi .
Na dauka Doctor yadawo gida ne amma ko ,idon shi bangani ba dan asibiti d'aya muke aiki amman mu ba d'aya bane har mangariba kafun yadawo "sannu da zuwa " yauwa a na Neman ki a gun aiki ankawo wani Mara lafiya idon shi sai tsiyayan ruwa yakeyi abun tausayi wai matarshi ce ta soke mishi ido da kifiya kuma duka biyu andai bashi taimakon gaggawa "subuhanallahi na tausaya mishi makanta babu kyau kokadan " amma gaskiya sai gobe tunda yanzu dare yayi "kishirya muje kawai kefa kikace zaki bada gudumawa a duk Wanda irin laluran toh meyasa zakice haka " Doctor banjima da dawowa ba na daura girki ne fa"kibari zan k'arisa kishirya in rakaki "toh nidaga ina aka kawoshi daga k'auye .
Cikin sauri nashirya mukaje da sauri muka k'arisa kafun mushiga kukane muketaji nace a shigo da shi kod'aga ido na banyi ba baranta in gakowaye cikin dakin gaggawa na taimako muka shiga allura nayi mishi kafun nafara duba idon ido d'aya ya ziyaye daya da saura dubawa nayi narubuta magani akan sudubo sukawo mun na tausaya mishi sosai koganin fuskar shi banyi ba nafito mukaci karo da maman Nafi,u bata ganeni ba amma nikam nagane ta " sannu mama yauwa ya gida wakuka kawo "zainab kece daman " e nice mama "munkawo Nafi,u ne bashida lafiya " ayya Allah yabashi lafiya zanwuce "dakata zainab yaushe kikawarke daga makanta ?" Allah ne yawarkar dani "ki tsaya zainab kitaimaka mana kigayawa likitoti suduba idon nafi,u dan yana cikin uku ba" babu komai zasu duba shi aikin sune ina moh'd "yana gida "Allah sarki sai da safe bayan mundawo gida da Doctor munzauna munacin abinci ne"Doctor nifa yau nahad'u da maman Nafi,u wai Nafi,un ne bashida lafiya har take tambayana yaushe na warke.
" baki bata amsa ba ?"nabata amsa dai dai da tambayan da tayi mun "amma abun yabani mamaki tou meyasa naganta a gun masu matsalan ido ,kodai tazo duba wanine" ya isa haka zainab kodai sokike kiduba shine ina ruwan ki"Allah yahuci zuciyar ka abun duk bai kai haka ba kayi hak'uri
Washe fari k'arfe bakwai nafita aiki dan duba lafiyan idon mutumin ina shiga naga mama abun yabani mamaki"mama karfa kucemun jiyan Nafi,u naduba "e shine " wallahi danasan nafi,u ne bazan tab'a dubashi ba gara ya mutu babu ido gara in dauwama bana aikin ido Nafi,u mungu azzalumi macuci nagodewa ,Allah d'aya amsa addu,a ta kacutar dani nasha azaba ka musguna mun yakaga Allah yadawo da kai hannu na Allah kenan "toh bari kaji bazan taba dubaka ba garama kakoma duk garin da kakeso tafiya nafarayi,mama takirani" Zainab kitaimaka"mama kenan amma kuncika masu son kanku wato lokacin da laluran ido yasameni keko tausayi na bakeji sai kita gayamun maganganu masu zafi danki yayi mun walakanci dan haka koda zai mutu babu ido bazan taba dubashi ba"zainab kiceceni kiyi hakuri karkibarni da jinyar nan nasan bazan taba warkewa ba amma zansamu lafiya"Nafi,u kakeda suna banida lokacin ka kunemi wani yamuku aikin nikam bazanyi ba .
Mama kibawa zainab hakuri taya tazama likita taya tasamu sauki wayyo ido na zan mutu amma lami tacuce ni Allah ya,is a bazan yafe ba munguwa kuka yafarayi ga idon anrufe ba,ason kuka kokadan .
Bayan nazauna a office nafara aiki nu nagodewa Allah da yanunawa Nafi,u iyawarshi yasa nazama makahuwa yanzu mace tasashi makanta nayi farin ciki na gudaya da Allah yasa ka mun na gu biyu kuma na tausaya mishi saboda ni ma,aikaciya na kiwon lafiya naci gaba da aiki na amma naki duba shi babu kalan zuwan da ba,ayi ba amma nayi shiru ko kulawa banyi ba...
[11/8, 20:48] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: 🌸🌸🌸🌸🌸
HALIN MAZA
🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️6️⃣4️⃣
Umman zarah ce tayi magana"zarah kitashi kitafi gidan ki kinga bakida lafiya sannan kince yanzu ke matar aure ce kar mijinki yayi fishi" umma nagaji da auren gaba daya yanzu a shirye nake da in zama mutumiyar kirki dad'in ma k'addara tace tazo da wannan yanayin yanzu nagane duniya nakoyi darasi .
Kibarni inzauna mutane suzo suyimun kallon arziki karkisa wasu suyimun mummunan addu,a akan bananan mahaifina yarasu "kiyi hak'uri kitafi gobe kigaya mishi mahaifin ki yarasu ko kuma kikirashi a waya zaifi " zanyi wannan amma koda nakira ba lalle bane yadauki watar tawa"kardai kice bazaman dadi kukeyi da mijin nakin ba?"e ummana aure ne danayi cikin azaba da rud'ani "kiyi shiru kikirashi kawai.
Kiranayi yata ringin amma ko dauka bai yiba cen ya dauka" yane zarah"mahaifina ne Allah yamishi rasuwa danazo za,a. Kaishi "kice baki nemi gafara ba na tausaya miki gaskiya kinyi irin nawa kenan ,ko tanka mishi banyi ba cen nayi shiru" kidawo ki d'auki kayanki kawai sai kikoma Allah yamishi rahama "Amín .
Nabada labarin komai a umma nakafun mutane sukata shigowa wasu kallo nasukeyi kawai sunrasa bakin yin Magaña narasa wani kalan kallo sukeyi mun kai d'an adam wasu gulman sunrasa abunda zasuyi gidan mu yazama gidan yan gai suwa da kuma gulman jama,a kawai d'an adam kenan .
Zainab duk wani magiya anyi mun nakasa hak'ura da duk abunda Nafi,u yayimun inaji ina gani ,aka fita dashi aka cenza mishi asibiti zuwa kano basu samu fuskan yimun Magaña ba takaici ya gagara barina in dinga zuwa gun aiki " Doctor zubamun ido yayi bai k'ara cemun komai ba dan yaga irin yadda raina yabaci sosai kuwa duniya kenan .
[11/8, 20:48] MAMAN KHAIRAT CE📖✍🏿: HALIN MAZA
Tammat Tammat Tammat
*I nan nakawo k'arshen littafina mai suna halin maza littafi ne dayayi duba a kan halayyan wasu mazan da irin kalubalin da matan su suke fuskan ta dagajin sunan littafin kinsan anyi mafa kowa ce budurwa ina yimata fatan alkairi tare da fatan hadata da miji nagari ba ,mai irin halin sadiq ba Allah kad'amu a kan ladan nida makaranta littafin halin maza sai kunji ni da sabon labari mai * zuciya tare da kalu balin da wasu yan matan suke fuskanta a kan har kan social media.*
*Nida na rubuta labarin Amina maaji maman Khairat zaku,iya tun tubana ta wannan number wajan kawo naki labarin zamu rubuta sannan mu sadaukar