Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 40195 words

Chapter 10 - ZAMAN AURE Book Complete Document .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

535

Ads at the middle of Article

ya dora da,




"Bawanan maganar my dear,yanzu de meye labari,me kamal zai samu?




shiru tayi tare da dada lafewa a kirjinsa tana wasa da gashin fuskar sa ahankali ta dago ta kalleshi ,hada ido sukayi,yadaga mata gira, yatashi yasawa kofar key yadawo kan gadon tare da rage kayan jikinsa nan yashiga sarrafa ta cikin kwaraiwa,gabadaya kamal ya susuce,yazama kamar zakin da yaga abinci ,kasa jurewa sakna tayi saboda yadda yake gurzarta ahankali tafara fitar da numfashi da sauri da sauri,kamal kuwa bema san tanayi ba,har sai da yasami nutsuwa sannan ya daga ta ,yana sauke numfashi ,sai lokacin ya kula da yanayin da matar tasa ke ciki,cikin kasala ya mirgina kusa da ita tare da janta zuwa jikinsa yazubamata ido,take hankalinsa yadan tashi yashiga kiran sunanta




"sakeena! sakeena!




shiru yaji tayi ,kan ya kuma yin wata magana yajiyo muryar Hajiya tana kiran sakeena,ido ya zaro waje ya shiga tunanin ya zeyi,hannu Hajiya tasa ta murda kofar mezata gani,






*Jameel*




~~Ajiyar zuciyar Hajiya ta sauke tare da sauke tagumin da tayi ta dubi dan nata a karo na biyu tace,






"Dan marayan zaki,maganar gaskiya nadade ina jiran wannan rana domin kullum cikin rokon Allah nake akan Allah yai maka zabin alkhairi game da *zaman auranka* da labiba,hakikanin gaskiya jameelu bakai saar mata ba ,to yanzu tana ina ?"




"nabarta a gida ,nace mata mutukar ta fita to abakin auranta"




"Allah ya kyauta ,yashiryeta"




kan yaamsa da kalmar ameen wayarsa ta shiga ruri hannu yasa yadauki wayar da yaajiye kan center table,yana dubawa yaga sunan momy kamar baze dagaba sai kuma ya daure yadaga tare da kara wayar a kunansa ,cikin masifa momy tafara magana




"Jameelu me labiba taimaka da zaka marar min ita ,dama acikin *zaman aure* akwai mari ,to bari kaji wlh baka mari banza ba dan sai.....




katseta yayi da fadin,


"momy bata fadamiki abinda taiminba ,kuma nafadamata wlh intasake ta fita abakin auranta "




"sannu mara mutunci ,to bari kaji labiba ta na gida,kenan hakan na nufin kasaketa ,ko me kake nufi"?




"kwarai kuwa momy, nasaki labiba,saki uku,tunda taketare sharadin dana gindaya mata"




yanagama fadar haka ya katse wayar
tare da mai da dubansa ga Hajiya,ya kwashe komai yafada mata,shiru tayi can tanisa tace,




"Saki ba dadi Danmarayan zaki,to amma wani lokacin masalaha ne ga maaurata, Allah yasa haka shine mafi alkhairi"


"Ameen Hajiyata"




yafada yana share kwallar da ta gangaro masa,


labiba kam ana fadamata ,ta kurma uban ihu,take tayanke ,












*Abdulmalik*








~~cikin kankanin lokaci inna ta isa gidan su Ruhaima tana shiga ta tarar da umman Ruhaima tana aiki ,sallama tayi da sauri ta juyo ta zuba mata ido can kuma tace,




"maraba sannu da zuwa,shigo mana"


"aa,basai na shigo ba,gashi nan abawa yarinyar nan ,dan Allah ku gaggauta zuwa kwashe kayanku dan Abdulmalik aure zaiyi"




"ikon Allah ,to shikenan mungode Allah yasa haka shi yafi Alkhairi"




"Ameen"


cewar inna tanagamafada tai tafiyarta ,Ruhaima kam tana tsaye tana kallon ikon Allah take ta rushe da kuka ,hankalin ummanta ne yadawo kanta take ta karasa kusa da yar tata,






inna tana fita kai tsaye gidan su mariya ta nufa akofar gida taci karo da ita ,da sakin fuska ta dubeta tace,




"Aa mariya ina zuwa haka, babar taki na ciki"?




"tana ciki"


"to,yar albarka ,bari inshiga,sai kindawo"




ciki inna tashiga tasami babar mariya zaune a rumfa tana gyaran zogali da faraa ta tareta nan tasami guri tazauna,kusa da aminiyar tata,


Abdulmalik kuwa tunda yashiga daki zazzabi mai zafi ya rufe shi ,da kyar yaiya daukar wayar sa ya kiran layin abokinsa mai suna mansur,yana dagawa yace




"mansur pls kazo gida kasameni yanzu"




"To"


kawai yace,ya katse kiran,nan yadada dukunkunewa baajima ba,mansur ya karaso,waya yaiwa Abdulmalik yakarasa,cikin tsananin jin sanyi yatashi ya fita a mota yasami abokin nasa cikin tsananin tashin hankali mansur ya dubi abokin nasa,










*Hafeez*




~~cikin rashin kunya da tsiwa Areefa ta dubi Hafeez tace,




"Hafeez,Alhj Namadi ne ya kawo ni kayi duk abinda zakayi,kai wayasan irin abinda kakeyi,ba sai Allah ba,to kaimin duk abinda zakai haba"




cikin tsananin mamaki Hafeez yake duban bakin Areefa,har ta gama,can yanisa yace,




"mekike nufi,Areefa,kina zargina nane"




"oho,nide banceba,amma de koma mene ne kafini sani"




ransa ne yabaci yatashi yabar mata parlorn daki ya koma yakwanta,






da daddare yana kwance a daki ,yakirata tanajinsa taimasa banza tai kwanciyar ta a parlor,


washegari da wuri Areefa,ta shirya tabar gidan ,Hafeez yana fitowa ya tarar da Areefa bata nan zama yayi yarasa ma mezaiyi,wayar sa,yadauka ya shiga neman layin Ashanty,sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga,








*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:33AM,2017]






*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦



*💦N I G*💦












*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦








*NA*


NASEEBA I UBA💐












*Hasbunallahu wani imal wakil la haula wala kuwata illa billahi aliyul azeem*👏🏻










*HIP HIP HIP HURRY,HAPPY BIRTHEY IN ADVANCE MY DEAR UMMI AISHA,I WAS LATE IN WHISHES BUT LET ME DO IT NOW,I WHISH U A DAY SOFT AS SILK WHITE AS MILK SWEET AS HONEY AND FULL OF BLESSING AND HAPPINES I LOVE U MORE THAN DESERV SIS*🎂🎂🎂🎂🎂
















*29*










~~cikin tsananin mamaki Hajiya taga kofar dakin ansa mata key ,a hankali tafara kiran sunan sakeena ,ji tayi shiru ,kamal kuwa yana rungume da ita tana ta sauke numfashi sannu a hankali, ana haka lubna ta fito daga nata dakin duban Hajiyar tasu tayi tace,




"Hajiya lafiya naganki a nan ,meyafaru da aunty sakeena"




"lafiya kalau Auta,inason dada duba jikin nata ne ,kuma ga shi ankammala karin kumallo da tafito ta karya,dazu kofar a bude take ,amma kinji yanzu ansa key"




"Hajiya kenan ,tunda kika jita shiru karshanta bacci take inta tashi zata fito,bari inje ingaida abba indawo"




"to shikenan Auta nima gani nan zuwa"


duk abinda ake a kunnan kamal yana jinsu ,yana ta kokarin ganin numfashin sakna ya dai daita ,ga cikinta da ya dunkule waje daya,hakan ba karamin daga masa hankali yayi ba, ahankali tafara sauke ajiyar zuciya tare da daga ido ta zuba masa ,murmushin karfin hali tasakar masa tare da lumshe idonta,cikin sauri kamal ya fara jera mata sannu ,kai kawai ta iya daga masa,tashi yayi ya nufi toilet ya hada musu ruwan zafi yadawo ya taimaka mata ta mike ,da kyar yar kara tasaki sakamakon dunkulewa da cikin jikinta yada yi,da ssuri yasa hannunsa ya toshe mata baki tare da girgiza mata kai,ahankali ya tallafeta suka nufi toilet din,shi ya taimaka mata wajen wankan shima yayi ,gaba daya yadada susucewa da kyar ya iya hakura suka fito,gafen gado sakna tasamu ta zauna,kai tsaye akwatin kayan ta ya nufa ya daukko mata wata doguwar riga mara nauyi,tare da dakko mai yashafa mata,yasa mata rigar ,kiss ya sakarwar cikinta,shima ya shirya tsaf,dubansa tayi tace,




"kayi kyau mijin sakeena,amma kwalliyar tayi yawa gaskiya"




dariya yayi,tare da shafa kyakkyawar fuskar ta yace,




"Nagode matar kamal,to amma fa neman aure zani ,tunda ke kinzama raguwa bazaki iya jure bukatar mijinki ba"


yafada yana kashe mata ido,da sauri ta dago ta zuba masa dara daran idanunta mikewa tayi ta nufi bakin kofa da niyar bar masa dakin cikin sauri yasha gabanta tare da janta jikinsa ya shiga rarrashinta fisge jikinta tayi ,ta kuma sa hannu ta murda key din ,tana budewa taci karo da lubna abakin kofar,










*Jameel*








~~cikin tsananin tashin hankali labiba tafara birgima akasa tana ihu tare da fadin,




"Nashiga uku,momy wlh inason sa ,bazan iya rayuwa ba tare da shi ba,na cutar da shi, ya hakura,betaba cemin komai ba,na mallake shi na mallaki dukiyar sa wayyo Allah na,asirin dana dade inai masa ne ya karye ko momy"?




hankalin momy ne yai masifar tashi dataga yar tata kamar ta zauce,dagata tayi suka nufi daki ,nan tashiga yimata saka da bakin zare,tare da nuna mata hanyar da bazata bulle da ita ba,ta dora da,


"Haba labiba,jameel din banza akan sa kike wannan kuka,to bari kiji infada miki,inbanda kaddararan cikin jikin ki,da da zarar kingama idda zaki sami wanda ya fishi"




cikin kuka ta dubi momyn tace,




"wallahi momy bazan sami kamar jameel ba, nariga narasa shi kawai kuma wallahi ke kika jamin faruwar hakan "


shiru kawai momy taiwa yar tata karshe ta tashi tabar mata dakin,




jakarta tajayo ta dakko wayar ta ,nan ta shiga neman layin kawar ta ,sai da ta kusa tsinkewa sannan ta dauka,




jameel kuwa yadade tare da Hajiyar sa ,sannan yai mata sallama ya nufi gidansa,yana shiga dakinsa ya nufa,ya shiga bincike durowowin gadonsa takardunsa ya ke nema yadade yana dubawa sannan ya gansu ,parlor ya koma ya zubawa takardun nasa ido,wayar sa ce tafara ringing yana dubawa yaga sunan abokinsa usman,murmushi yayi sannan ya danna tare da kara wayar a kunnan sa ,




"Hello muryar nakeji kamar ta abokina usman"


dariya usman yasa da yaji muryar jameel ,yadora da ,




"jameel kenan ni ne mana lafiya kuwa najika so silent akwai matsala ko "?


ajiyar zuciya jameel ya sauke sanan yadora da ,


"usman kana gari kenan "


"nadawo jameel ,yanzu haka ma ina hanyar zuwa gidanka inafatan kana gida"?




shuru jameel yayi kamar mai nazarin wani abu,a hankali ya bashi amsa tare da godewa Allah da dawowar usman ,zama yayi yacigaba da jirans karasowar sa,










*Abdulmalik*






~~cikin son jin damuwar abokin nasa mansir yake tambayar Abdulmalik shiru kawai yaimasa tare da cigaba da dafe kansa,ahankali yace,




"mansir asibiti zaka kaini,koma de meye mayi maganar daga baya"




"To amma abokina zanso.......




hannu yadaga masa alamar yai shiru ,yadora da,




"Dan Allah dan annabi mansir kabarni ka na neman dada bani ciwon kai ,nace zanfada maka koma mene ne ko"




sanin halin abokin nasa ne yasa mansir yin shiru ,yaja motar suka nufi asibiti basu jimaba suka karasa sundan dade kafin susami ganin likitan suna shiga Abdulmalik ya yanke jiki yafadi,da sauri likitan yataso ya nufo kansa hankalin mansir ba karamin tashi yaiba,




inna,kuwa bayan sungaisa da babar mariya ta dada gyara zama tace,




"wato Hajiya asabe, dama zuwa nayi nemawa Abdulmalk auran mariya,dan dada karfafa zumuncinmmu"


shiru Hajiya asabe tayi can tanisa ta dubi aminiyar tata tace,




"To,naji dadin batukinki Binta,to amma ina matar sa take,kinsan fa mariya bazata zauna da kishiya ba "


dariya momy tayi sannan ta dora da,




Ruhaima,kuwa innalillahi kawai take furtawa cikin tausayawa ummanta tafara yimata nasiha tare da kwantar mata da hankali murmushin karfin hali Ruhaima tayi ana haka sai ga mahaifinta ya shigo ganin yanayin da yar tasa take ciki ne yasa shi saurin zama tare da mai da dubansa ga umman ta,








*Hafeez*




~~Ashanty tana daga wayar Hafeez tai shiru ajiyar zuciya yasaki sannan ya dora da ,




"Hello my dear Ashanty,kina lpy"




"lpy ,yau ka tuna dani kenan,ai wlh Hafeezu,baka da mutunci"




"yi hakuri tawan ,kiyimin uzuri wlh abubuwa ne suka sha kaina amma de yanzu kina ina?




"Hmm,ina inda kasanni mana,har yanzu bancanja sheka ba tukunna"




"yauwa tawan kinajina yanzu ina gidana ko zaki zo kosameni"




dariya tayi sai datayi mai isarta sannan tace,




"Hafeez kenan bama kai kazo ba ni zanzo lallai kam"




"eh akwai dalilin dayasa nake son kizo ne pls"




shiru tayi can ta nisa tare da tauna cigam yace kas ,tace,


"ok badamuwa kajirani nana minti 30"




"yauwa tawan "


sukai sallama suka kashe wayar tashi yayi yanufi kitchen dan nemawa cikinsa abinci,




Areefa kuwa tana fita kai tsaye gidan su Hafeez ta nufa tana shiga tasaki kuka ,cikin tashin hankali mahaifiyar sa tashiga tambayar ta




"Areefa lafiya meyafaru,ina Hafeezun"






shiru tayi can tashare hawayenta ta dubi mahaifiyar tasa tace,










*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:31] ‪+234 814 620 5819‬: [6:00AM,2017]




*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦


*💦N I G*💦












*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦








*NA*


NASEEBA I UBA💐








*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillahi azim*👏🏻👏🏻














*Dedicated this page 2 my brother Nazeer yusif muazu ango 2 be may Allah bless ur marrige live in peace ,Happines love , and Honest ya Allah! i whish them 2 live 2gether Ameen*👏🏻💔









*30*










~~cikin sauri kamal ya labe abayan kofa sakna kuwa murmushi tasakarwa lubna tare da jan hannunta suka nufi parlor ,dubanta sakeena tayi tace




"kanwata, har kintashi , Hajiya fa ?"


" tun dazu, Hajiya,suna parlorn Abba ita da mama,tun dazu take ta murda kofar ki arufe"




shiru sakna tayi can ta dago ta kalleta tace,




"Ayya nakoma bacci ne,yanzu de yunwa nakeji wlh me Hajiya taimana,?




"tea da dankali da kwai ,amma ke,me kike son ci ?"




" wlh,lubna dama zansami kunu da nasha ,shi nakeson sha banason shan tea"




"Ai kuwa naga Suhaif yana shan kunu,bari inje inkarbo miki"




"yauwa kanwata nagode sosai"




dariya lubna tayi ,ta tashi tafita ,cikin sauri sakna ta tashi ta leka dakinta ,dariya tasaki saboda yadda kamal ya labe abayan kofa,cikin tsokana tace,




"kazo Hajiya tana kiranka "




dariya kawai yaimata tare da janta zuwa jikinsa yashiga kissing dinta da sauri tazame jikinta ta fito daga dakin kan doguwar kujera ta samu ta kwanta tare da sauke, numfashi,da sauri kamal yabar dakin ,batare da kowa yaganshi ba,kai tsaye dakin abban su ya nufa ,sallama yayi ,aka amsa ,sannan yasa kai ya shiga,kusa da abban yakarasa yazauna,tare da gaisheshi,sannan ya juya gurin su Hajiya da mama suma ya gaida su,ana haka sai ga yayansa shareef shima ya shigo,nan suka hadu sukaita hira can kamal yadago da kansa tare da narkar da fuska yadubi mahaifin nasa,yace,




"Abba, dan girman Allah yau zantafi da sakeena ,tunda tadan sami sauki"




Hajiya ce tai caraf tace,






"kamalu wani ne yafadamaka tasami sauki ko kuma shiga kayi kaganta"?




shiru yayi bece mata kala ba ,sai sosa kai da yakeyi,dubansa ta kuma yi akaro na biyu tace,




"To,bainda zaka tafi daita,ai baka san darajar ta ba,shiyasa kake cutar da ita a *zaman auranku* "




Abba ne ya dubi Hajiyar yace,




"Haba ,Hajiyar lubna,meyasa kike haka ne ,meye amfanin hanashi matarsa,akan wane dalili kikai haka,dama ido kawai na zuba miki,to tun da girma da arziki ki bashi matarsa su tafi"




shareef ne ya gyara zama tare da dubi abban nasu yace,




"wlh Abba kamal yana da matsala gaba daya besan hakkin
*zaman aure* ba,gwanda abar yarinyar nan ta huta ,inbaya ganinta kila yasan amfanin ta"




"Haba sharifi,yazaka fadi haka ,ai ita fitina kwantar daita ake ba dada tayar da ita ba,abashi matar sa kawai,kai kuma kamalu kaji tsoran Allah a *zaman auran* ku kaji"


cewar mama tafada tana kallon kamal abba ne ya katse zancan da duban kamal yace,




"kamalu tashi kaje ka dau matar ka kutafi gida,Allah yakara sauki ka kula da ita kaji ko"




"to ,Abba nagode Allah ya kara girma yaja kwana,mama atayani godiya,
Hajiya muntafi,yaya shareef sai ka fito"


banza Hajiya taimasa ta dauke kanta,
yana gama fadar haka ya fito kai tsaye dakin Hajiyar ya nufa ,sakna na zaune ita da lubna suna kallo,ya shigo hade rai yayi ya dubi sakna ya ce ,




"oya,sakeena hado kayanki zamu wuce"


da sauri ta dago da kanta tadubeshi,lubna ce tai caraf tace,




"yaya kamal Hajiya fa tace kar ka tafi daita kabari tadada samun sauki"


cikin fushi hade da murtike fuska ya nufi kan lubna,














*Jameel*






~~Jameel yadade zaune yana jiran karasowar usman can wayar sa ta hau ruri da sauri yasa hannu ya dauka yana dubawa yaga usman dinne dannawa yayi tare da kara wayar a kunnan sa ,


"usman ka karaso kenan"




"eh gani a kofar gida"




"ok"




kawai yace,yafita acikin mota ya tarar da shi ,jikin motar ya karasa tare da kwankwasa glass din ,cikin sauri usman yafito,murmushi suka sakarwa junansu,tare da rungume juna kai tsaye gidan suka nufa,a parlor suka yada zango jameel ya dubi usman yace,




"Abokina ka ganka kuwa,gaskiya ka kama kasa,meye labari ne"?




"jameel kenan wace kasa ,kawai de ina samin kulawa ne daga gurin madam,yanaji gidanka shiru ko madam bata nan ne"?




shiru jameel yayi can ya nisa yace,




"kai amma mutumina kayi saa gaskiya ,ai ni lamarin baacewa komai sai de addua kawai"




"banfahimci zancanka ba abokina meke faruwa"




shiru jameel yayi can yadubi usman ya kwashe komai game da yanayin *zaman auransu* yafada masa har aikin da yarasa a dalilin matar tasa ,usman ya tausaya masa sosai can yadago ya dubi abokin nasa yace,




"Amma banjin dadin zancan nan ba jameel to ,yanzu wane aikin kakeyi"?




"Haba usman ina maganar aiki ,bana komai fa yanzu ai kai de lamarin baa cewa komai kawai"




dubansa usman yayi yace,




"tohm shikenan abokina yanzu abinda nake ganin zaayi shine,




"kakawo takardunka inkaiwa yayana dan ya bude sabon kamfani dama ana ta daukar maaikata "




cikin farin ciki jameel ya mikawa usman takardunsa
yace,




"kasan kuwa neman aiki zantafi,kai amma naji dadi gaskiya abokina"




"bakomai jameel ai ana tare,yanzu abinda zaayi shine gaskiya ka nemi mata ka aura,dan zaman ka haka ba zeyuba"




arazane jameel ya dubi usman yace,




"dan Allah usman mubar wannan maganar ni wallahi tsoran mata nakeji"






"haba jameel ai ba duka suka raro suka zama daya ba dan haka mubar maganar na dan Allah"


bayadda usman ya iya,kyale shi yayi karshe yai masa sallama ya tafi ,






labiba kam kawarta mero tana daga wayar tace,


"Kawata,kina ina akwai matsala,jameel ya sakeni dan Allah kizo"




"subahanallah ,kai amma abu be dadiba yanzu kina ina kawata"?




"Aa,ina gida mana kizo kifadamin yadda zanyi kinde san irin son danakewa jameel ko"?




"gaskiya ne ,sai dai bana gari labiba,amma na kusa dawowa,innadawo zanzo"




dan haushi labiba ko amsa bata bawa mero ba ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta cikinta ta shafa ta lumshe ido,








*Abdulmalik*






~~Da sauri likitan ya nufi inda Abdulmalik suke ,daukar sa sukayi suka daura shi kan gado nan likitan ya shiga duba shi tare da yimasa gwajin jini take ya gano yadda jininsa yai masifar hawa mai da dubansa yayi ga mansur yace,






"Gaskiya jininsa ya hau sosai,kuma hakan zai iya haddasa masa mutuwar barin jiki domin yana da damuwa ,sosai "




cikin tashin hankali mansir yadubi likitan yace,




"Tabbas yana da damuwa sai dai bansan damuwar sa ba,dan befadaminba ,yanzu likita meye abunyi?






"eh to dole zamu bashi gado dan sai ankwantar dashi anabashi agajin gaggawa yanzu naimasa allurar bacci ,zaamaida shi dakin dayakamata ya kwanta"






"Tohm shikenan Dr nagode sosai"






haka kuwa akai aka bawa Abdulmalik gado ,yanata bacci mansir yana zaune yazuba masa ido can tafara motsi ahankali yana kiran Ruhaima ,




inna kuwa tana can bata san halin da danta yake cikiba,duban babar mariya tayi tace,






"Haba kawata ai yanzu haka ma daga gidan su matar tasa nake nakai mata takardar saki ,ai sunrabu ,bata da hali fa yarinyar nan wlh cutar yaron nan takeyi gashi ba haihuwa take ba,saboda haka nan kusa nakeson ayi komai agama"






"Aa to ai shikenan bakomai nabashi auran mariya bari yayan ta yazo zanfada masa"






"yauwa to madalla nagode ,bari intafi sai kinjini agaidamin da yar tawa"




tana gama dada tai gaba kai tsaye gida ta nufa tana zuwa tasa mukulli tashiga dakin Abdulmalik a rufe ,hankalinta be tashi ba sai da taga dare yayi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads