Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 40195 words

Chapter 12 - ZAMAN AURE Book Complete Document .txt

Ads the beginning of article before Image

03 Jun 2024

540

Ads at the middle of Article

ciki,ahankali yashiga sarrafata gabadaya yafita a hayyacinsa ,sai da komai yalafa,sannan yadagata tare da mirginawa can gefe yana sauke numfashi,ahankali sakeena tadube shi tace,




"Honey bee,nagaji ,wallahi kana bamu wahala"




dada mirginowa yayi kusa daita yajata jikinsa acikin kunnanta yarada mata magana,dariya tayi tare da cusa kanta akirjinsa,tashi yayi yahada musu ruwa ,yafito,taimaka mata yayi ta mike da kyar suka nufi toilet,dakansa yaimata wanka shima yayi ,sannan suka fito tare da sa kayan bacci masu kyau ,suka koma,suka kwanta,fuskar sa sakeena tashafa tare da kiran sunan sa,




"Honey bee"


"Naam matata,yaakayi ko akara ne"


da sauri ta girgiza kanta tare da fadin,




"Aa,da wuya fa,kawai de inason mugodewa Allah bisa sauyin da mukasamu na *zaman aurenmmu* "




"gaskiya ne,matar kamal Allah mungode maka,ai shi *zaman aure* hakuri da juriya yake bukata ko ba haka bane,shiyasa nakewa Allah godiya dayabani mata mai addini da hakuri"




jintayi shiru ne yasashi dada duba fuskar ta ganin tayi bacci ne yasashi yin murmushi tare da dada gyaramata kwanciyar ta a faffadan kirjinsa yaja bargo yarufe su,




Ahaka rayuwa tai ta tafiya cikin farinciki da kwanciyar hankali,yau tunsafe kamal yafita aiki,bejima da fitaba sakeena na kwance tana bacci ,sai jitayi kamar antsira mata allura a gigice tafarka,nan tashiga sintiri tun tana iya tafiya har ta durkushe gashi ta gigice tarasa inda wayar ta take,












*Jameel*




~~sunkuyar da kai yarinyar tayi ,tare da komawa daki tana tashi yadubi usman yace,




"Abokina wacece wannan gaskiya ta hargitsamin lissafi"


dariya usman yayi tare da duban jameel yace,




"kanwar Huda ce,munira ,kana ciki kenan"




"sosai ma kuwa ,gaskiya abokina kayimin iso gareta,dan gaskiya naga matar aure"




"angama abokina ,ina zuwa"


tashi usman yayi yanufi dakin Huda aciki yasami munira dubanta yayi yace,




"kanwata inbadamuwa abokina yanason ganinki"


Huda ce ta dago tadubi mijin nata tace,




"yallabai kafasan halin munira bason kula maza take ba"


"aa Huda,kibarta mana tazo su gaisa,


shiru tayi tare da kallon munira tace,




"jeki kiji"



tashi tayi tafita jameel na zaune yana kallon Tv tashigo murmushi yadada sakar mata tasami guri tazauna suka gaisa yagabatar mata kansa take suka kulla soyayya karshe yaimusu sallama yatafi,


kaitsaye gurin Hajiyar sa yanufa ,yanazuwa yai shaidamata yasami matar aure murna tayi sosai wayarsa ce tashiga ringing dubawa yayi yaga sunan momyn labiba,kamar baze dagaba can kuma yadaure yadaga,




"jameelu labiba ce ba lafiya tahaihu muna asibiti"




"ok gani nan"


mai da dubansa yayi ga Hajiya yace,




"Hajiya wai labiba ce ba lafiya tana asibiti"


"subahanallah to ai sai mutashi muje"




tashi sukayi suka nufi asibitin suna zuwa suka ci karo da momy tanata faman kuka,karasawa sukayi suka shiga tambayar ta ,




"ya mai jikin,ta haihu ne "?




"Tahaihu sai dai danbarai"


kai tsaye jameel office din likitan ya nufa dan jin abinda yasami labiba yana shiga yabashi hannu suka gaisa tare da yimasa bayanin abinda yasameta ,fitowa yayi yasami Hajiya yafadamata gawar babyn akabasu ,jameel dayaga babyn sai da yai kuka ,kai tsaye gida suka wuce akaimasa suttura aka kaishi gidansa na gaskiya,labiba kam bata san abinda kefaruwa ba kwanan ta biyar a asibitin sannan tafara dawowa hayyacinta,zaune take tana kurbar ruwan tea jameel da abokinsa usman sukai sallama suka shigo,ido tazuba masa,










*Abdulmalik*






~~cikin sauri likitan yashigo dan duba jikin Abdulmalik allurar bacci akaimasa cikin kankanin lokaci bacci yadaukeshi,


Rabia naganin yasami bacci taiwa mansir sallama tanufi gida dan sanarwa da inna ,kai tsaye gidanta tanufa abakin kofa suka cikaro da inna cikin tashin hankali ta dubeta




"Rabi,ina Abdulmalik din "


"inna yana asibiti akwance bashi da lafiya,amma yaji sauki"




"subahanallah,rakani gurinsa Rabi,nashige su"


bayadda Rabiia taiya haka suka kuma juyawa asibitin taraka inna tana zuwa taganshi kwance yanata bacci da sauri takarasa gaban gadon nasa ta kamo hannusa tafara sharbar kuka,








*Hafeez*








~~cikin sauri yadubui Ashanty yace,




"Ashanty ga mama ta nan,da yayata ,yanzu ya zamuyi kenan"




"oho kai kasani ,nikam bani da damuwa da hakan sai kasan yadda zakayi"




shiru yayi can wayar sa takuma daukar kara jiki asabule yadaga cikin bacin rai maman tasa tace,




"Hafeez wai mekake har yanzu baka karaso bane,meyasa kake haka ne "


"mama yanzu zanzo inbude muku"






"uban me zaka bude mana"?




"kofar"




"kai banason hauka bacewa nayi kazo gida kasa meni ba,ko de kafara shaye shaye ne,Hafeezu"




ajiyar zuciya yasauke tare da fadin ,"aa mama afuwan gani nan inshaallah"


duban Ashanty yayi yace,




"tawan ,tashi muje kishirya in saukeki a gida da yamma kijirani"




banza taimasa tanufi daki tasaka kayanta shima ya shirya suka fito atare kai tsaye gida yakaita sannan yanufi gidansu tunda yakarasa yake zabgawa Areefa harara itama hararar sa takeyi zama yayi yashiga gaida mahaifiyar tasa wani banzan kallo tawatsa masa take jikinsa yai sanyi,yashiga rarraba idanu,












*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [6:35MA,2017]






*®💦💦NASEEBA GAWO*💦💦💦




*💦N I G*💦








*ZAMAN AURE*
💦🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦




*NA*


NASEEBA I UBA💐










*Hasbunallahu waniimal wakil*👏🏻














*34*










~~Tunda kamal yafita hankalinsa yakasa kwanciya gabadaya tunanin sakeena ne yahana zuciyar sa sukuni,duk motsin da yayi sai ta fado masa arai,wayar sa ya dauka yashiga neman layinta ,tana ta ringing bata dauka ba,dada shiga damuwa yayi,mai da dubansa yayi ga abokinsa Adam ,yace




"Adams,bari inje gida wallahi gabadaya hankalina yana kan sakna,Allah yasa de lafiyar ta kalau,abinka da mai tsohon ciki"


dariya Adams yayi tare da duban abokin nasa yace,




"yasalam,gaskiya kam abokina gwanda kaje kadubata kagani,irin wannan gigicewa da kayi haka,ashe yanzu kana son cikin nata,yaakayi haka kuma mutumina"?




dariya kawai kamal yayi ya mike tare da daukar mukullin motar sa ,yafita,cikin sauri ya figi motar tasa ,bewani jimaba ya karasa gida,mukulli yasa ya bude kofar gabansa inbanda faduwa baabinda yake,kai tsaye parlorn ya nufa ya shiga kwala mata kira ,shiru bata amsa ba,daga cikin daki yafara jiyo nishin ta,da sauri yakarasa dakin halin da yaganta aciki ne yai masifar daga masa hankali,da sauri yakarasa gabanta,yana kiran sunan ta,




"Sakeena,lafiya ,ko haihuwar ce"




shiru tayi tare da runtse idonta,takama hannusa ta kankame ,kasa zare hannunsa yayi saboda rikon datayi masa,cikin sauri ya dauketa yasata a mota,tare da dawowa ya daukar mata mayafi da kayan babyn da suka hada,cikin matsanan cin gudu yafigi mota,kai tsaye asibitin Annury ya wuce da ita,cikin kankanin lokaci aka shigar da ita,dakin haihuwa,kamal dada gigicewa yayi dayaga anrufo kofar andakatar da shi abakin kofa,wayar sa yazaro yakira Hajiyar sa yafada mata,cikin kidima Hajiyar take masa magana,




"Kamalu,yanzu kuna ina"?




"Hajiya muna asibitin Annury,dan Allah Hajiya kitaho ,sakeena zata mutu"




"Haba kamalu kana haukane ,wace irin mutuwa, daga haihuwa sai mutuwa kanutsu kaji ko,kafadawa ummanta ne?"




"Aa Hajiya banfada musu ba"




"yauwa kar ka fada musu,kar adaga musu hankali, badadi fadar nakuda,gani nan zuwa"




kashe wayar yayi tare da lekawa dakin da sakeena take inbanda salati baabinda takeyi ,baajimaba Hajiya ta karaso kamal yana ganinta yakarasa gabanta tare da share kwallar da ta zubo masa,dubansa tayi tace,




"Haba kamal meye abin kuka addua zakai mata ,tana ina?


" tana wancan dakin ,wallahi Hajiya tana shan wahala "


kan tayi magana sunjiyo ,
wata razananniyar kara da sakeena tasaki wacce tajanyo hankalin kamal da Hajiya ,da sauri yakarasa bakin kofar dakin yana kokarin shiga wata nurse ce ta dakatar da shi ,sai da Hajiya taimasa magana sannan yadawo tare da samun guri yazauna,can sai ga nurse din data hanashi shiga dakin takuma fitowa da sauri suka nofota ,dubansu tayi da sakin fuska tace,


"congratulation,
tasauka lafiya,ansami baby boy"




farinciki ne yakama kamal tare da daga hannu yagodewa Allah ,dada dubansu nurse din tayi tace,




sai dai wani hanzari ba guduba,


zuba mata ido kamal yayi dan jin me nurse din zata fada,












*Jameel*






~~Dkewa jameel yayi yakarasa gaban gadon da labiba,take yana daga tsaye suka gaisa da momyn ta, fita tayi tabasu guri,mai da dubansa yayi ga Labiba




"sannu yajikin naki"?


kasa amsawa labiba tayi,tazuba masa ido kawai tana kallonsa,usman ne yakatse mata tunanin datakeyi




"Labiba yajikin naki sannu Allah yakara lafiya"




ahankali taamsa da


"Ameen nagode"




wayar jameel ce tashiga ringing da sauri yasa hannu yazaro yana dubawa sunan *munira* ne yabayyana a screen din wayar dagawa yayi tare da sakin murmushi




"Hello sweethert ,ya kike,yajin dadi"




labiba dake zaune tana kallonsa suman zaune tayi tare da dada zuba masa ido,sai da yagama wayarsa tsaf ,sannan yadubeta yace,




"labiba mu zamuwuce,ga wannan kirike ko zaanemi wanin abu Allah yakara sauki"


usman ma yabata kudi tare dayimata fatan samun lafiya ,yafita kantaankare jameel har yakai bakin kofa da sauri takira sunansa,




"Jameel!


ahankali yaja yatsaya batare da ya juyo ya kalleta ba,sai da takuma kiran sunan sa,sannan ya juyo suka hada ido,cikin sanyin murya tafara magana,




"jameel dan Allah kayafemin abinda naimaka abaya ,wallahi nayi nadama,bazan kuma ba,kataimaka min kamaidani dakina,jameel kaine rayuwata kaine farinciki na pls"


malalacin murmushi jameel yasaki tare da dubanta yace,






"karki damu labiba,nayafe miki,amma batun komawar ki gidana,kinmakara dan ni ahalin yanzu ma nakusa aure,kema inai miki fatan samun mujin da yafini,batun kuma nine rayuwarki ai bata taso ba dan haka ki manta dani sai anjima,Allah yakareki da lafiya inadada mika godiyata gareki bisa rainon cikina dakikai min dafatan Allah yajikan babyn mmu ameen"




yanagama fadar haka yafita,wani kuka ne ya kwacemata,momy datafita dan bawa su jameel guri ne tashigo akidime dan ganin halin da diyar tata take ciki,cikin kidima tashiga tambayar ta,






"labiba,meyai miki ,maramutuncin yaron nan "




"momy jameel mai mutunci ne ,kidena kiransa mara mutunci ,wallahi momy kincutar da rayuwata,kinrabani da mijina"


momy rasa ma mezatacewa labiba tayi kawai sai tashiga hada kayanta zata tafi,kuka labiba tasa mata,




jameel ne zaune gaban mahaifiyar sa yana bata labarin matar da yasamu zai aura murna tayi sosai tare da fadin




"yanzu abinda zaayi shine,zanje da kaina insami kawun ka ,infada masa dan bazaai wasa ba"




"Hajiya da wuri haka,mezai hana abi abin sannu ahankali"




"Danmarayan zaki kenan,to kode baauren zakayiba"


dariya yayi tare da shafa sumar kansa ,










*Abdulmalik*






~~kwannan Abdulmalik uku,a asibiti aka sallameshi yadawo gida ,sai da yayi sati guda sannan ya warware yakoma aiki,inna kam ta tura kanin baban Abdulmalik neman auren mariya cikin kankanin lokaci akasa rana duk wannan bidirin daakeyi Abdulmalik betaba zuwa zance gurin mariya ba,amma bata damuba,dan itama bawani sonsa takeba,yanzu haka zaune suke shi da inna suna dan taba hira ,can tanisa tace






"Abdulmalik yakamata kaje kugaisa da mariya kaga biki yanata karatowa ko"




shiru yayi can yanisa yace,






"zanje inna inshaallahu"




yanagama fadar haka yatashi,dan bayason jin zancan wata inba na Ruhaima ba"




da yamma yashirya yaje gidansu Mariya tajima kan tafito,can sai gata ,ido kawai yazuba mata yana karewa halittar ta kallo ja tayi ta tsaya tare da gaidashi a yangace,hade rai yayi sannan yaamsa ,basu wani jimaba yaimata sallama yatafi bin bayan motar sa tayi da kallo,tace,




"zaku shigo hannuna ne,daga kai har innar taka"




haka lokaci yai ta tafiya ranaku suna juyawa suzama sati haka sati yana juyewa yazama wata yayin da wata yake zama shekara,bikin Abdulmalik da mariya yarage saura sati daya inna tanata ta hidima, anfara biki cikin farinciki da jin dadi abangaran ango Abdulmalik kuwa abun bahaka yakeba domin jiyake kamar yakashe kansa ya huta saboda bakin ciki,yau takama daurin aure da kyar yaje daurin auran nasa da tarin abokansa ,anyi komai angama da daddare aka kawo amarya dakinta,












*Hafeez*




~~maman Hafeez ce tadubeshi ranta a mutukar bace tafara magana,






"Hafeezu,meyahada ka da matarka"?




sumar kansa yashafa tare da lumshe ido,dan shi besan mezai cewa maman tasa ba,maganar yayar sa ce takatse masa shirun da yayi




"Hafeez kaifa muke sauraro"






"yaya nibansan abinda naimata ba amma ita tafada da bakinta mana"




maida dubansu sukayi ga Areefa mama tace,




"Areefa fadi duk abinda kikasan yanayimiki"






nan ta karkace tashiga fadar karya da gaskiya ,sai datagama sannan yadago ya dubeta yace,






"Areefa kiji tsoron Allah karfa kimanta zaki mutu"






"Rufemin baki Hafeezu baka da gaskiya dan haka kaima kaji tsoran Allah karike yar mutane da amana meyasa baka son zaman lafiya ne wai ,haba,Areefa kiyi hakuri kinji kuzauna lafiya kuyi hakuri da juna"




"inshaallahu mama nagode sosai Allah yakara girma nagode"




"bakomai tashi ka dau matarka kutafi"




tashi yayi suka fita,tunda suka shiga mota yake aunamata zagi tare da harara dubanta ya kuma yi akaro na biyu yace,






"wallahi Areefa kinji narantse bakici bulus ba kubude banzayan kunnuwanki masu kama da kashi kijini


nan da kankanin lokaci zankara aure,dan nikam bazan zauna da fasika ba,mazinaciya kawai"




Arazane Areefa ta juyo takalli Hafeez,cikin zafin nama tasa hannu ta,














*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3/19, 10:32] ‪+234 814 620 5819‬: [9:18PM,2018]






*_®💦💦NASEEBA GAWO_*💦💦💦






*_💦N I G_*💦








*_ZAMAN AURE_*
💦 🤦🏻‍♀🤦🏻‍♂💦












*_NA_*


*_NASEEBA I UBA_*💐












*_Rabbi yasir wala taasir Allahumma yasir alaina_*👏🏻






*_Inabawa masoyan wanga littafi hakuri bisa tsaikon daaka samu na rashin ganin posting dina kwana biyu hakan yafaru ne bisa wasu dalile da suka haddsa faruwar hakan bisa wanga daliline yasa nafara rubuta sabon novel dina mai suna SANADIN ABOKI, sakamakon yawan tambayar da ake min ci gaban labari ,zankokarta wajen ganin nakarasa muku labarin inshaallah, duk zaku dinga ganin posting din wanga novels din guda biyu kullum,bawanda zanajiye da yardar mai kowa mai komai,nasan masoyana zasuce,Naseeba tazama surbajo ne,🤔mai rubuta novel biyu at one time,to zande jarraba ingani ko zaniya, faruwar hakan shi yatabbatar min da ana mugun tare,karfa ku manta farin cikinku shine naseeba ismail Gawo_*👌🏻😘












_*35*_










~~cikin zakuwa kamal ya shiga sauraran abinda Nurse din zatace,dada gyara dan karamin hijjabin ta tayi tace,




"yauwa,agaskiya matarka tana bukatar jini dan tazubar da jini da yawa"




cikin rawar baki kamal yadubi Nurse din yace,


"Haba,Hajiya wani irin jini ,meye amfanin nawa muje adibi nawa asamata,banason narasa matata"




Hajiya ce tadafa kafadarsa tace,




"Dan girman Allah ksmalu kanutsu,wai meyasa haka ne,yata injininsa zaiyi adiba asamata "




"tohm Hajiya badamuwa,kuje agwada agani inyayi dai dai sai adiba ,amma gaskiya kuyi da hanzari"




"tohm shikenan bari muje"




cikin kankanin lokaci akai komai aka gama,cikin saa jinin su yayai daidai dakin hutu aka maida sakeena aka jona mata karin jinin ,tunda kamal yai tozali da Babyn nasu yaji wani farinciki yarufe rungume shi yayi ajikinsa,sai da Hajiya tadubeshi tace,




"Oh ni yasu,yanzu kamalu bakajin kunya kakama da ka kankame da kanason dan kadinga watangaliya da da mahaifiyarsa lokacin datake da cikinsa,banishi nan"


kunya ce takama shi ,yamika mata dan,dada zubawa sakeena ido yayi tana ta bacci tarame sai uban haske datayi,tausayinta ne yakamashi,kankace kwabo,yanuwa da abokan arziki suncika asibitin kowa na yaba kyawun jaririn ,lubna batasami zuwaba,sai yamma ,saboda rigestiration din datakeyi har lokacin Sakeena bacci take,bata tashiba sai wajen 6:30,ahankali tafara bude idonta jitayi cikinta fayau,hannu tasa tashafa,tozali tayi da ummanta zaune da Baby ahannu,ahankali tafara kiran sunanta


"wash,umma cikina ciwo yakemin"


da sauri ta mike ta yo kanta,tare da jera mata sannu,likita aka kira yazo yadada dubata,tare da cire mata robar jinin daakasa mata,nan aka kimtsa mata jikinta aka hada mata tea tadansha,sai yanzu aka mika mata Babyn kunya ce takamata,dakyar takarbeshi ta zuba masa ido kamar su daya da Kamal,ana cikinhaka,sai ga Kamal din yadawo,farinciki ne yakamashi dayaga Sakna ta tashi har ta zauna ,cikin farin ciki yashiga gaisar da ummanta , kasancewarHajiya ta tafi gida tadawo,fita tayi tabasu guri,cikin farinciki Kamal yakarasa gaban gadon yazubawa Sakeena ido,tare da rungumesu ita da babyn yashiga jera mata sannu,ahankali tadago tadubeshi tace,




"Honey bee,bazan kuma ba,wlh"


dariya ce tasubuce masa,yashiga tambayar ta,


"Sakna bazaki kuma me ba,baki san ribar *zaman aure* shine samun zuria ba,ko kinmanta to bari kiji inbaki labari wasa farin girki ,just the beging inji bature"




shuru tayi tana murmushi,kukan da jaririn yakeyi ne yaadawo dasu nutsuwarsu dubanta Kamal yayi yace,




"Maman Baby akulawa Kamal dansa mana,kidanbashi yasha "


shagwabe fuska tayi tace,




"Nide gaskiya baniya ba,kuma fa dazafi wallahi dazu baka ji zafin danaji ba"


hade rai yayi tare da dubanta yace,




"ni naiya ai ,bari kigani"




Babyn yakarba yakara mata shi ajikinta , cikin sauri kuwa jaririn yakama yaitasha ,sai da yakoshi sannan ya kwantar dashi,




dariya abin yaso bawa Sakeena ,Kamal sai rawar jiki yake dasu,lallai ta yarda *zaman aure* dan hakuri ne,


kwanan ta biyu aka sallamosu,kai tsaye gidansu aka wuce,daita.








*_Jameel_*






~~Kuka sosai Labiba take yi ,Momy kuwa bata fasa hada kayantaba,zuwan mahaifinta ne yasa ta dakata ta hakura da tafiyar da zatayi nan yashiga yimata fada,




"Haba, Hajiya Zainab akan me zaki biye mata,baki tausaya mata halin datake ciki,meyasa kike haka ne ,ku wallahi mata wani lokacin baku da nisan tsinkaye wallahi,to yanzu inkika tafi kika barta wa zai kula da ita , tambayar ki nake"?




shiru tayi tana sauraran fadan da mai gidan nata yake yi can tanisa tace,


"Haba Alhj,sai kace kamanta halin labiba,wallahi yarinyar nan daka ke gani tana da damuwa fa ,halinta sai ita,bakaji magan ganun datadinga fada min ba dazu"




"Naji ai hakuri ake shi dama mara lafiya ai sai kabishi asannu, kide zauna ki kula daita da me zataji ne wai haba"


Labiba de inbanda sharar kwalla baabinda take,dan sai yanzu tada tabbatarwa da kanta irin son datakewa Jameel,kwananta 14 aka sallamota,suka dawo gida,




kullum cikin kunci zuciyar ta take,aranta take dadin,


_lallai duk matar data zalinci mijinta a_
*zamantakewar aure* kanta ta cutar yau gashi tarasa farincikin rayuwa,




kamar yadda Hajiyar Jameel tafada ,anaika gidan su Mnira nemawa Jameel auranta ,iyayanta sun amince,ankai kudi hade da sa rana ,murna gurin Jameel baamagana ,bayan yadawo daga aiki ne,kai tsaye gurin Hajiyar sa ya wuce,tana zaune, tana lazimi yashigo tare da samin guri yazauna,sai da tagama sannan tadubeshi da faraa kwance kan fuskar ta tace,




"Dan marayan Zaki andawo,yaaiki"




" yauwa Hajiyata Nadawo aiki angode Allah sannu da gida"




"yauwa ga abinci inzaka ci"


kan yabata amsa
wayarsa tashiga ruri ,hannu yasa a aljihu yazaro ta,kan yadaga ta katse,dubawa yayi yaga mai kiran nasa Murmushi yasaki mai dan sauti wanda yajanyo hankalin Hajiya ,dubansa tayi tace,




"kai dawaye kake murmushi saikace wani sabon ango"




"Haba Hajiya ai sabon angon ne,Munira ce"




"Hmmm,Allah sarki ,yauwa yakamata kafara gyaran gidanka,kuma afara hado lefe,kaga bawani lokaci aka sa mai yawa ba"




"To,shikenan Hajiya inshaallahu zaayi"


Nan suka cigaba da hirarsu irin ta d'a da uwa,Jameel jinsa yake kamar wani sabon mutum tunda yarabu da Labiba,komai nasa yadawo daidai.










*_Abdulmalik_*






~~Kai tsaye dakin Inna aka fara kai Mariya,inna kamar tahadiye ta dan murna,nan tai mata nasiha ,suka fito da ita,aka kaita nata dakin wanda yasha kayan daki dai dai gwargwado,yan kai amarya suka watse,aka bar amarya ita kadai,sai faman raba ido take,ango yana can kwance,a gurin abokinsa,yanata fama dashi yataso yarakashi,yaki ,dubansa abokin yayi yace,




"Abdul tunda kaki ,tashi inrakaka ko, ,to dan bani guri inason inkwanta dan bacci nakeji wallahi"




"oh! korata ma kake yi nagode, Allah yasa nima inada makwanci "


"kwarai kuwa,wanda ma yafi nawa,mutumin dayake da sabuwar amarya ina zaahada shi da gauro"


cewar abokin nasa yafada ,yana dariya kasa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads