Showing 6001 words to 9000 words out of 40195 words
Chapter 3 - ZAMAN AURE Book Complete Document .txt
ta rikice* dazu da safe "
Shiru yayi yana juya kalamanta, me take nufi da *kasa ta rikice* bashi da wannan amsar dole sai ita zata war ware masa wannan kullin.
Abangaran Abdulmalik da inna kuwa yarasa da wacce kalma zai rarrasheta can ya tashi ya nufi kitchen ya dakko plate da cup yazo ya zuba mata doya da kwai sai kunun gyada ya tura mata gabanta yace
"innar Malik dan Allah kiyi hakuri kici inshaallah bazaa kuma makara ba "
Fakar idonsa tayi taga abinda aka kawo mata hadiyar yawu tayi can tanisa tace
" Naji amma wlh aka yimin irin haka bani ba abincin gidan ka, haba yaro ya hadu da karfan kafa ni wlh raina bayason matarka ko kadan saboda wayo take maka "
" ki de yi hakuri Inna ki dena fadar haka, yanzu me zaa dafa miki da rana "?
" duk abinda kuka dafa ina ci kai da zaabawa meye na ka nazaba "
Shiru yayi karshe yaimata sallama yatafi gishirin ta ta dakko taci gaba da kullawa tanayi tana mita
Sanda Abdulmalik ya karasa gida Ruhaima ta kammala komai tayi wanka jiran sa kawai tana jin shigowar sa ta fita zuwa parking space ta tareshi da faraa rungume ta yayi tare da sakar mata kiss ciki suka nufa duban sa tayi tace
"Sweet Malik sannu da zuwa, ka dade zo muje kaci abinci "
" kai my dear ba lokaci na makara a wajen aiki sai dai ki zuba min intafi dashi, bari nayi wanka "
Shiru tayi saboda yadda take ta jiransa yazo suyi break fast, tashi tayi taje ta zuba masa a kula ta koma daki ta taimaka masa ya shirya cikin sauri ya fita ta koma parlor tayi nata break fast din kwanciya tayi tana hutawa take bacci ya dauke ta cikin bacci taji sallama kamar ta inna gabanta ne yafadi.
Bangaran Areefa kuwa tun safe take ta shirye shiryen tarbar Hydar karfe uku dai dai ya iso cikin farin ciki ta tare shi nan suka zauna a lafiyayyun kujerun parlorn sai karairaya take masa ta caba ado duban ta yayi yace
". My love kinyi kyau Allah yasa nazama mijin mai kyau "
Dariya tayi ta dau juice ta shiga zuba masa sai da ya hada hannun sa da nata sannan ya karba ajiyar zuciya ta saki kallon ta yayi cikin wani irin kallo yace
" My love, wannan ajiyar zuciyar fa ta mecece "
" cikin sanyi da kashe ido, tace
"Hydar ne sila"
Dariya yayi sosai Kan ya bata amsa suka ji ana buga gate din gidan da karfi cikin mamaki Areefa ta kalli Hydar shi dinmma ita yake kallo.
Hafeez kuwa cikin kwarewa ya shiga sarrafa khady janta yayi zuwa daki nan suka zube a gado suka shiga aikata barnar su ahaka
Suka raba dare suna abu daya, rungume ta yayi tsam a jikin sa ahaka bacci ya daukesu be farka ba sai 7 nasafe yana tashi wayar sa tafara ringing da sauri ya duba ganin mai kiran ne yasa gabansa faduwa da sauri ya kara wayar a kunansa bayan ya mai da duban sa ga khady wacce take ta baccin ta
*NASEEBA GAWO*
โ๐ป
[3/19, 10:28] โช+234 814 620 5819โฌ: [6:32Am,2017]
*ยฎ๐ฆ๐ฆ๐ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐ฆ๐ฆ๐ฆ
*๐ฆT
*ZAMAN AURE*
๐ฆ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐ฆ
*NA*
NASEEBA I UBA ๐
*Wallahu galabun ala amrihi wala kinna akasarin nasi la yaalamun*๐๐ป
๐ฆ
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*๐ฆ
*Assalamu alaikum masoyan littafin Naseeba Gawo hakika naji dadin yadda littafin kannan mijina ya nishadantar daku har kuke tabbatar min da yafi zaman aure dadi to dan Allah kuyi hakuri yadanyi nisa mugani hakika littafin zaman aure yazo da wani salo wanda yatara akalla taurari 6 domin in muka duba da irin rayuwar da muka tsinci kanmmu a wannan zamani abu akwai ban tsoro da tausayi a ciki, amma fa Naseeba bata ce baazaman lpy a gidan aure ba, aa kawai dai ina yawan jin damuwar da ke cikin wasu gida janne, kar ku manta ban san gidan ki ba labarina kirkirara nayi Allah yabamu zaman lpy a gidan auran mmu AMEEN Godiya ta musamman gareki Garkuwar Fulani bisa kwarin gwiwar da nasamu daga gareki bisa wannan littafin na zaman aure gaskiya na yarda ana mugun tare*๐ค๐ค
*7*
~~~Sanda sakna ta shiga toilet din kamal yana cikin barb yana ta danna jikinsa duban sakna yayi da lumsassun idonsa yace
"oya sakeena tai maka min ki tayani wanka bazan iya ba "
" Hone beey, dan Allah ka dena abinda kake wlh ba kyau Allah ya hana "
Shiru yayi mata hannu tasa tafara cuda shi janta ya zuwa jikin sa a hankali ya fara kissing dinta tun tana tureshi har ta hakura ahaka Suka gama wankan suka fito akan gado suka zube ya zuba mata ido can yanisa yace
" my dear dan Allah kiyi hakuri da ni da halina inshaallah zan dena duk wani hali mara kyau ki cigaba da yimin addua kinji "
Hannun sa takama ta hada da nata tare da Lumshe ido tace
" Honey be, naji dadin abinda kace ina nan kuma ina tayaka da addua "
Rungume ta yayi tsam a jikin sa tare da kissing din karamin bakinta zame jikinta tayi taje ta kawo masa abinci ta zuba masa tare da tura masa gabansa dubanta yayi yace
" Nakoshi gsky tunda da kaina zanci "
Yana gama fada ya kwanta dariya sakna tayi can ta nisa tace
" I am so sorry Honey bee, taso inbaka kaji "
Tasowa yayi nan tashiga bashi yana ci ahaka har ya koshi dubanta yayi yace
" my dear yau munyi baki ne?
"Eh mama tazo yanzu haka ma lubna tana daki anan zata kwana "
Ido yazaro waje cikin yar kidima yadubi sakna yace.
abangaran jameel kuwa tashi yayi yabi bayan labiba tana kwance a gado tana ganin sa ta dada tsuke fuska bayan ta yaje ya kwanta ya rungume ta can ya nisa yace
" Everlasting kinsa jameel a duhu meye maanar kasa ta rikice "?
Shiru tayi kamar bazata amsa ba can kuma ta dubeshi tace
" eh, ina nufin alada nake ko zaka karbi hakkin ka ahaka ne "
" Aa haba dai amma dai gaskiya yaimin shigar wuri wlh Everlasting ina cikin damuwa komai kiga inayi karfin hali ne kawai "
" Allah sarki sai kai hakuri ai yanzu de yunwa nake ji wlh "
" ok bari inkawo miki abinci "
Tashi yayi yaje ya dakko kayan abincin yazo ya zuba mata taci sai da ta koshi sannan Shima yaci
Wayar sa tafara ringing yana dubawa yaga sunan Hajiya ta a jikin screen din wayar da sauri ya dauka tare da kara wayar a kunansa yace
" Assalamu alaikum, Hajiya barka da dare "
" waalaikasalam, barka ka de *Dan marayan zaki* kwana 2 dafatan de lpy, ina labiba "
" lpy kalau Hajiya tana nan kalau tana gaisheki"
Wata harara labiba ta zabga wa jameel dauke kansa yayi kamar be ganta ba,
"To alhmdulillah, yanzu kazo ina son ganin ka duk abinda kake kabari kazo "
" To shikenan Hajiya gani nan zuwa "
Sukai sallama ya kashe wayar mai da duban sa yayi ga labiba wata uwar harara ta zabga masa tace
" ina kuma zaka je Jameel "?
" zanje gurin Hajiya ta ne ko da wani abun "
" Kwarai kuwa Dan wlh ba inda zaka "
Shiru yayi yarasa ma me zaice mata can ya nisa yace.
Abangaran Ruhaima kuwa a gigice ta tashi ta fito a tsakar gida ta tarar da inna da mamaki tashiga yaimata sannu da zuwa cikin isa ta dubeta tace
" sannun ka de, ai ta kwada sallama kina jin mutane ko saboda raini yayi kyau "
" wlh inna bacci nake yi shiyasa kika ji Shiru kiyi hakuri "
" Dole ki bacci ai Ruhaima kinci kin ta da kai, abun haushin ma ke ba haihuwa kike ba, kazo gida me makon kaji ana gida ana hayaniya irin ta yara amma ina "
" Hajiya dan Allah kiyi hakuri shigo ciki "
" Aa barni anan bazan shiga ciki ba "
Shiru Ruhaima tayi ta nufi kitchen ta kawo mata nama da lemo duban ta inna tayi tace
" ki dauke kayan ki banaci "
Tana gama fada ta dan kashin gida take bacci ya dauke ta ahaka Abdulmalik yazo yaga inna da sauri ya karaso inda take ya shiga tashin ta tana ganin sa ta fara kuka cikin daga murya ya shiga kiran Ruhaima.
Abangaran Areefa kuwa cikin sauri ta nufi bakin gate dan jin waye tana isa bakin gate ta tambaya
"Waye ne?
"Ashiru ne Abdulmalik ne ya aiko ni gurin ki "
" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bude ta karbi skon ta maida kofa ta rufe ciki ta koma suka ci gaba da hirar su da Hydar kamar ba matar aure ba
Shi kuwa Abdulmalik yana ganin kiran manajan su ya kidime da sauri ya daga wayar
"kazo kasameni yanzu ina jiran ka "
Mai da duban sa yayi ga khady tashi yayi ya shirya ya ajiye mata kudi ya dau kayansa ya fita
*NASEEBA GAWO*
โ๐ป
[3/19, 10:28] โช+234 814 620 5819โฌ: [5:55Am,2017]
๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐
๐
*ZAMAN AURE*
๐๐๐๐คฆ๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐
๐
*NA*
NASEEBA I UBA ๐
*Alhmdulillahil Ala kulli Halin Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*๐๐ป
*8*
~~~Mamaki sakna tayi ganin cikin kankanin lokaci kamal ya kidime duban sa tayi tace
"Honey bee me yafaru naga kamar ka razana da jin kalamai na lpy de ko
Sumar kansa ya shafa tare da kwantar da kansa akan cinyar ta yace
"my dear Allah ya sa lubna bata jiyo ni ba dan nasan wlh sai ta fadawa mama halin da ake ciki "
Ido ta tsura masa cikin gano dalilin sa na fadar haka can ta nisa tace
" Haba honey bee ta yaya zan bari lubna taji sirrina da kai ai kamar na dabawa kaina wuka ne kar fa ka manta *mijina sirrina* ne, nide abinda nake so da kai kawai ka gyara wlh ba kyau fa Allah ya haramta shan giya kai ka halatta "
Rufa idonsa yayi kamar mai bacci yana jinta sai can ya bude ya zuba wa kyakyawar fuskar ta ido a hankali yace
" Najj bani guri inkwanta malama
Matsa masa tayi ya kwanta ta koma gefansa itama tayi kwanciyar ta ahaka
bacci ya daukesu
Da safe da wuri lubna ta tashi kitchen ta shiga ta hada musu break fast ta kammala ta jere Kan dining daki ta koma tayi wanka sakna bata tashi ba sai wajen 8 :30 saboda zazzabin da yarufeta da kyar ta yunkura ta tashi kamal yana kwance yana ta bacci a hankali ta ke tashin sa
"Honey bee pls wake up "
Sumar kansa ta shafa a hankali ya bude idonsa murmushi ya sakar mata ya shafi fuskar ta ji yayi jikin ta zafi rau, da sauri ya dubeta yace
" my dear me yasameki haka naji jikin ki zafi Allah ya sa ba ciki ne da ke ba "
Shiru tayi kamar bata ji shi ba ta mike da kyar zata shiga toilet luuu tayi kamar zata fadi da sauri ya karasa ya tare ta ta fada jikin sa toilet din ya nufa da ita nan yahada musu ruwan dumi yayi mata wanka shima yayi suka fito wardrobe ya bude ya dakko mata wata doguwar rigar material pink yasa mata shima ya dakko hadaddiyar shadda fara kal yasa turare ya fesa yazo zai fesa mata ta ture hannun sa hade da toshe hancinta murmushi yayi yace
"me hakan yake nufi kenan my dear "
" Honey bee, wlh bana son kamshin turaran ka gaskiya "
" sakna wlh mutukar ciki ne dake to ina mai tabbatar miki a kwai matsala "
Banza tayi masa ta fita zuwa parlor biyo ta yayi yana ta masifa ganin lubna zaune tana kallon sa ne yasa shi yin.
Jameel kuwa kallon labiba yayi yace
" Haba everlasting Hajiya ce fa ke son gani na pls kiyi hakuri inje in dawo kinji "
Murmushi tayi ta dube shi tace
" ok badamuwa jameel sai ka dawo "
Kiss yasakar mata ya tashi ya shiga toilet dan watsa ruwa labiba kuwa da sauri ta tashi ta rufe kofar parlorn ta zare mukulin ta boye ta sami guri ta zauna
Jameel kuwa cikin sauri ya shiriya ya fito parlor dan fita duban ta yayi yace
" Everlasting sai na dawo, me zan siyo miki "?
" Bana son komai, ka gaida Hajiya da kyau "
Tana gama fada tayi daki ta mai da kofa ta rufe tana dariya, shikuwa jameel kai tsaye hanyar fita ya nufa da karfin sa yaja kofa abin mamaki a rufe take da mukulli dabawa yayi yaga ba key din ajiki kansa ya dafe ya nufi hanyar dakin labiba shima a rufe a hankali ya shiga buga kofar yana kiran sunanta banza tai masa ya kusa minti talatin a tsaye karshe ya gaji ya dawo Kan kujera ya kwanta sai juyi yake ta faman yi ahaka bacci ya dauke shi
Da safe da wuri ya tashi yayi aiyukan da yasaba ya kammala ya nufi daki dan yin wanka sai lokacin labiba ta fito cikin kwalliya ido kawai ya zuba mata ya shigewar sa toilet ita kam parlor ta dawo ta zauna ta ja kular gabanta ta zuba dankali da kwai tafara ci tana cikin ci ne taji ana buga kofa tashi tayi dan budewa tana budewa taga Hajiyar jameel ce
Abangaran gidan Abdulmalik kuwa Ruhaima tana kitchen tanai wa inna abinci taji Abdulmalik yana ta kwalla mata kira da sauri ta ajiye ludayin hannun ta tafito wata uwar harara inna ta watsa mata duban sa tayi tace
"Sannu da zuwa malik "
" yauwa, ya kika bar inna a nan baki kaita daki ba kuma ina abincin ta "
" wlh malik sai da nayi nayi da inna ta shigo ciki taki ko abincin taki ci "
Salati inna tasaka ta hau matse ido sannan ta dora da
" yan nan kiji tsoran Allah yaushe kika ce in shigo dakin ku kai amma yarinyar nan kin iya sharri "
Abdulmalik kam rasa ma me ze cewa inna yayi can ya dubeta yace
" kiyi hakuri inna inshaallah zaa gyara yanzu taso ki dawo ciki "
"Allah ya sawake ba inda zanje wlh ai yanzu abinda zakai min ka burge ni shine kasaki wannan matar kawai shine ka cika dan halak"
Cikin sauri da kidima Ruhaima da Abdulmalik suka dago suka kalli inna
Areefa bata bar Hydar ya tafi ba sai bayan magariba tunda ga wannan ranar kullum sai ta fita sun hadu da Hydar ahaka ta hadu da wani Alhajin birni nan suka shiga soyayya kamar ba matar aure ba
Hafeez yana fita wajen aikin sa ya wuce nan ya shiga office din ogan nasu takarda ya dakko yabashi yana dubawa yaga taransfer akai masa zuwa kano be bata lokaci ba ya shirya ya nufi kano sanda ya isa gida Areefa bata nan mamaki ya shiga yi nan ya shiga neman layin ta akashe
*NASEEBA GAWO*
โ๐ป
[3/19, 10:28] โช+234 814 620 5819โฌ: [9:28 Pm, 2017]
*ยฎ๐ฆ๐ฆ๐ฆNASEEBA GAWO ๐ฆ๐ฆ๐ฆ*
*๐ฆN I G*๐ฆ
*ZAMAN AURE* ๐คฆ
๐ฆ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐ฆ
*NA*
NASEEBA I UBA ๐
*Alhmdulillahil Ala kulli Halin Allahumma ya mukallabul kulubi sabbit kalbi ala dinika*๐๐ป๐๐ป
*9*
~~~cikin dakewa da basarwa kamal ya dubi lubna yace
"ke, yaushe kika zo kin wani zubawa mutane ido "
Sunkuyar da kanta tayi can kuma ta dago ta dube shi tace
" jiya muka zo da mama, ina kwana yaya "
" lpy kin tashi lpy "
" lpy kalau, Aunty sakna antashi lpy "
" lpy kalau lubna sannu da aiki na barki da aiki ko, kiyi hakuri wlh yau natashi da zazzabi ne ".
" Ayya sannu aunty".
Tabe baki kamal yayi yaja kujera ya zauna, sakna ma zama tayi ta dau cup ta fara zuba masa ruwan tea plate din soyayyan kawai ya bude take sakna tafara yunkurin amai tashi tayi ta nufi toilet da sauri yana zaune ko motsawa beyi ba kallon lubna yayi yace
"oya lubna jeki taimaka mata "
Tashi tayi ta bi bayan ta shi kuwa mai da hankali yayi wajen cin abincin nan sa, a haka suka fito sai sannan ya mike ya rungume sakna a jikin sa ya shiga yi mata sannu dauke kanta tayi can ya dubi lubna yace
" lubna kawo mata tea tasha "
A hankali sakna ta dago ta dube shi tace
" Honey bee, bazan iya sha ba pls ka barni "
" Aa my dear kisha kadan sai muje asibiti ko "?
hannu yasa ya karbi cup din da lubna ta zubo ruwan tea da kansa ya shiga bata tana sha, kadan tasha ta dauke kanta, duban lubna ya kuma yi yace
" jeki dakko mata mayafinta "
" To yaya "
Kai tsaye daki ta nufa ta dakko mata mayafinta ta kawo da kansa ya karba ya yafa mata suka bar lubna a gida suka nufi asibiti suna isa suka shiga ganin likita cikin kankanin lokaci ya dubata take ya gano shigar ciki na sati shida da fararsa ya dubi kamal yace
"congratulation abokina matarka na da ciki na tsawan sati shida "
A razane kamal ya dago ya dubi likitan hade da watsawa sakna wani irin kallo jikin ta ne yai sanyi ta tsura masa ido
Labiba kuwa duban Hajiyar jameel tayi tai mata sannu da zuwa da sakin fuska taamsa ta sami guri ta zauna cikin kwantar da murya ta gaishe ta
"Hajiya ina kwana ya hanya "
" lpy kalau yar albarka kuna nan lpy de ko "
" lpy kalau Hajiya, bari akawo miki abinci "
" Aa yi zaman ki ina Dan marayan